x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 6 - UNCLE DATTI JIKINA YAKE SO

  • 15001 words
  • 18000 words
  • Out of 86070 words

Category: Romance Story +18

Views 338

01 Sep 2025
Start ads
After Image Ads
irin malalacin kuka mai tsuma rai.
        Binta yayi tana ja da baya har yayi nasarar had'a ta da jikin bango! Bugun zuciyoyin su ne ke tashi da k'arfi ta yanda su biyun suna iya jiyo bugun zuciyan junan su, dafa hannun shi yayi a jikin bango d'ayan kuma ya dafe goshin da shi".
          Murya k'asa k'asa yace Nana kin san abunda kike fad'a kuwa? Kin san wani irin hali nake ji game da ke? ya kwantar da murya kafin yaci gaba da cewa" please ki ji tausayina ki bani had'in kai, u are all i need". Shima ya shiga taya ta kukan.
          Yaya zaiyi da zuciyan shi da ke hura wutar kusantar Nana? Shi kam idan bata bashi had'in kai ba bai san a wani hali zai kasance ba, me yasa ba zata amince ta shayar da shi zuman ta ba?
         Duk tambayoyin nan ma kan shi yake jerowa yayin da waye suka shiga bin kuncin shi babu kakkautawa.
        Kokarin rungumar ta yayi tayi saurin ture shi tace" wa'iyazubillah! Shin baka jin kunyar mummunar kiddurin ka akaina ba? Dan Allah i beg you idan gwadani kake son yi ka daina bana so, kar kayi kokarin dasa tsanar ka a zuciya na".
        Kuttttttt ya dunk'ule miyau mai d'aci yana kallon yanda bakin ta ke motsawa a hankali in a hot and romantic way, kasa jurewa yayi ya kai bakin shi cikin nata ya had'a ta da k'arfi ta yanda ba zata iya kwatan kanta ba.
            Na kwadaitu da yawa a kanki ta yanda ko a halin yaya sai na cimma  buri na a kanki, d'aukar ta yayi cakkkkk ya dire da a kan three seters a haukace ya shiga rabata da kayan jikin shi, cuz of macewa a muguwar sha'awa idanuwan shi sai da suka kad'a sosai fiye da d'azu like mai maye, mitsil- mitsil ya hau yi tana ihu da iyakacin k'arfin ta tana tsine mishi amma atafirrrr yaki sak'in ta, da dai taga yana neman rabata da kayan jikin ta ta daddage ta kwad'a mishi cizo a hannu shi ba shiri ya sake ta yana yarfewa".
            A d'ari ta runtuma a guje tayi d'akin ta ta danna lock ta nemo riga ta saka ta shiga aikin kuka kamar ana zare ranta.
           Shigowan Aina kenan bata tarar da kowa a parlourn ba gashi duk a hargitse yake ba kamar yanda ta bari d'azu ba, tsintar kanta tayi da nufar d'akin Nana ta kai hannu ta murd'a handle d'in k'ofar da zumar ta shige ciki taji ta gammmmmmm.
          Mamaki taji sosai cuz ta san a ko da yaushe a bud'e yake idan an danna lock to dare ne, to ina Nanar taje ne? "Bari da nayi nocking". Rufe bakin ta me da wuya taji sheshek'ar kuka na tashi a hankali daga d'akin ta manna kunnen ta a jikin door d'in domin ta tabbatar da zargin da take a zuciyan ta.
         Jin muryar Nana ne cikin dishashiyar muryar ta take kuka hakan ya mugun d'aga mata hankali ta hau bugun k'ofar bammm....... bammmmmm da k'arfi kamar zata b'alla tana cewa" Nana ki bud'e!!!! bud'e min kofar nace!!!!! Oh! my Nana wai bakya jina ne..........., baza ki bud'e ba ko................
           Haka dai ta karashe maganganun ta amma firrrrr Nana bata bud'e ba, she was shocked and confused wai ace yayan ta kuma mijin y'ar uwar ta yana neman biyan bukata a kanta?
       Upon all the love he showed her his intentions is to destroy her life and all her happiness, have he forgotten she was his beloved Nana? Have he forgotten her age she don't have the strength to carry him, ba zata iya d'aukan lalurar shi ba.........., Namiji mugu ne!!!
           Haka dai take ta jin maganganun Auntyn tata ta k'asa ko da kwakwaran tashi ne balle ta bud'e mata, ji take moment d'in kamar almara, da wani ne ya fad'a mata cewa Datti zai iya aikata hakan babu tantama daga ranar ta kulla gaba mai tsanani a tsakanin su cuz of yards da tayi da shi.
        Da dai ta gaji da bugun k'ofar ta koma d'aki da sauri ta hau bincika drawer d'inta tana duba extra key, da kyerrrr ta samu a saman wardrobe ta d'auka tayi d'akin Nana da gudu har tana tuntub'i taje ta bud'e ta shige ko maida k'ofan bata yi ba.
            Idanuwan ta ne suka yi arba da Nana a mak'ure a guri d'aya jikin sai rawa yake yi, fuskar ta kuwa cike yake da tsantsar tsoro, firgici, da kuma kad'uwa, tana ganin Aina taji wani k'arfi ya zo mata tun kafin ta k'araso tayi gudu ta fad'a jikin ta ta fashe da matsananciyar mai k'arya zuciyan mai sauraro, hakan ya mugun d'aga ma Aina hankali ta hau jero mata wasu tambayoyi? Me yake faruwa ne Nana? Fu'ad ya shigo gidan ne bayan bana nan? Ki nutsu ki amsa min tambaya ta Nana........., ta rik'e ta da hannu biyu tana girgizata alamar ta dawo cikin hayyacin ta let her explain every thing".
          Allah sarki y'ar uwa da dad'i ji yanda ta rikice ta damu da son sanin abunda ke damun ta, sai taji tausayin Aunty Aina da kuma kanta ya mugun kamata cuz bata yi sa'an miji ba,  fuska biyu gare shi he betrayed them.
          Da kyar ta iya bud'e baki cikin kukan ta tace" Aunty Aina gida zan koma JIKINA YAKE SO! UNCLE DATTI JIKINA YAKE SO!!!!!
             Saurin ture ta tayi daga jikin ta cikin fusata tace"da hankali ne Nana? Kin san ko me kike fad'a kuwa? sharrin da zaki ma Datti kenan? Duk irin son da yake nuna miki ya fifita kowa a kanki yanzu irin sakayyar da zaki nuna mishi kenan?
         Rusar kuka take yi kamar ranta zai fita, me yasa Aunty Aina baza ta fahimci cewa Datti MACUCI ne azzalumi, me yasa baza ta yarda da ita ba take kok'arin karya tata".
           "Wallahi Datti ba sona yake ba JIKINA YAKE SO!!!!! da ace shi mai sona ne ba zai nemi ya lalata min rayuwa ba..................
          "Shut up karna sake jin wannan magar daga bakin ki!!!!!, me kike da wanda bani da shi da har zaki ce Datti zai samu a wajen ki dududu nawa kike? Wayon ki da shekarunki sun k'asa ki fahimci abubuwan da kike ma Datti kazafi a kai, anya ba wani ke shirin sauya miki tunani ba? Rai a matuk'ar b'ace tayi maganar domin kuwa iya wuya Nana ta kawo ta.
          Shiru ne ya wakana a tsakanin banda sheshek'ar kukan Nana da ya gama karad'e ko ina babu abunda ke tashi a d'akin.
           " Ki yarda dani Aunty Aina wallahi da gaske nake........, fuskar da kike kallon Uncle datti da shi ba hakan yake ba yaudarar ce kawai, Na tsane shi........, bana so na bud'e ido na kalle shi.........., duk duniya babu wanda na tsana kamar ..........., Allah yayi gaskiya da yace masoyi ya kan rikid'a ya koma makiyi".
           Tasssssss taji ta d'auke ta da gifitaccen mari ba shiri ta dafe kuncin ta, tun da take wasu sabbin tsiraren hawaye suka soma zarya a kuncin ta".
         Aunty Aina kam ji take kamar ta nad'a mata d'ankaren duka wanda zai saka ta dawo daga hayyacin ta.
           Da kike ikirarin cewa Datti JIKIN KI YAKE SO ko a littafin Hausa kin tab'a jin cewa Namiji mai lalura wanda bai d'auke jinsin mace a bakin komai ba yana bibiyar mata, to idan baki sani ba yau ki sani Datti baya d'aya daga cikin jinsin maza masu sha'awa, idan ma mafarki kike yi to ki farka, ni da nake matar shi cikakkiyar mace wanda Allah ya had'awa diri kyaun sura da komai ban d'auke mishi hankali ba sai ke kwaila wacce da wuya ma ko kin fara k'irgen dangi a k'irgin ki?
              Inalillahi wa'inna ilaihiraji'un! Me yake shirin faruwa dani ne? Dole ne Aunty Aina ta karyatata cuz ta san irin mijin da ta aura, idan kuwa haka ne tana da aiki jaaaa da zata saka ta yarda da maganar ta, to wai ma wace irin hanya zata bi ta fahimtar da ita?
         "Aunty kin san dai haka kawai ba zan yi kasafi ma Uncle Datti ba dan na cimma buri na, ina ma zaki gaskata maganar ta............., ina ma zaki yarda cewa abunda na fad'a gaskiya ne, wallahi billahil Azeem ba kasafi nayi mishi ba, kin san irin shak'uwar da nayi da Datti wallahi ko makiyina ne shi ba zan yarda ayi mishi kazafi ba balle shi".
             " Kin koyo k'arya da bakar zuciya, bayan neman had'a fad'a tsakanin wa da k'ani yanzu kin fake da neman b'ata mishi suna, to ki sani under one condition zan yarda da ke..........., ina so ki nemo duk wata hanya da kika san zaki proving min har na yarda da gaskiyar ki,
         Kuka ta kuma rushewa da shi cikin tsananin tashin hankali tace" ta yaya zan samo kwararren shaida da zan gaskata kaina bayan k'ofofi a rufe take!
           Oho! Ke kika sani", tana fad'ar haka tayi shigewan ta tafi ta bar nana cikin wani irin hali kuka wi-wi-wi tayi da idanuwan ta wannan shi ake k'ira rana zafi inuwa k'una, daren ranar ko runtsawa bata yi ba".     

eedatou

*💫SHINNING STARS WRITER'S ASSOCIATION*

'''The more we shine bright the more we educate and enlighten our readers.'''

https://m.facebook.com/110896360504039/photos/a.110896457170696/110898470503828/?type=3&source=45

🍇🍇🍇 *UNCLE DATTI*🍇🍇🍇.
                 '''JIKINA YAKE SO!'''
                             ©
                      *eedatou✍🏻*
'''Follow and ✅ote me on Wattpad''': *eedatou*   

*ina masoyan littafin BAMU DACE BA da UNCLE DATTI JIKINA YAKE SO! mu garxayo nesa taxo kusa xaku iya samun cigaban wannan shahararrun littattafan a naira dari uku kacal 300 idan kuma d'aya kake so xa'a biya naida d'ari biyu wanda shahararriyar marubutan sun baje basirar su littafin UNCLE DATTI JIKINA YAKESO da BAMU DACE BA ya kunshe abubuwa da dama*
'''tsantsar soyayya
tausayi
yaudara
butulci da tsantsar cin amana'''

       Zaku iya biya ta wannan asusun bankin 6029126848 *FIRDAUSI MUHAMMAD MAINASARA* *KEYSTONE BANK* ko kuma 2081506334  *SAIDA DAUDA MUSA*UBA* Ko kuma katin waya  da takardun shaidan biya kud'i a asusun banki ta wannan numban 07037194106 ko  kuma 08141739141
idan kun tura zakuyi screen short na shaidar kun biya ku tura ta wa'innan numbobin

*karku bari a baku labari*

                     1️⃣1️⃣—1️⃣2️⃣

B'angaren Aina tunda ta bar d'akin Nana, d'akin Datti ta nufa tana kunkuni ciki-ciki tana cewa" wai ni nana zata raina wa hankali? Ko ina yarinyar ta kwaso makircin banza da bakin hali, wallahi Nana halin ta ya sha bam-bam da na zuri'ar mu", har ta shigo cikin d'akin bata k'arasa fad'ace fad'acen ta ba".
         Datti na daga uwar d'aka yaji muryar ta ya fito da sauri, lafiya wife kike ta masifa ke kad'ai wa ya tab'a min ke".
       Kwafa taja mai k'arfi cike da tarin takaicin me yasa bata kama Nanar ta nad'a mata d'ankaren dukan da zata dawo cikin hayyacin ta ba".
         Tsintar kanta tayi da tsantsar jin kunyar k'azafin da Nana tayi mishi, anya zata iya fad'a mishi kuwa? Kai ko me zai faru gara ya faru, yaga ya san irin zaman da zaiyi da Nana idan da hali ma ya d'an ja baya da ita tunda ta kasa fahimtar halayen Datti.
         Jin shirun yayi yawa  ya jawo ta jikin shi ya tausaya murya yace" kin yi shiru wife baki amsa min tambaya ta ba". Sai yanzu ta samu damar amsa mishi wallahi ba wai shiru nayi maka ba kawai dai rasa abunda zan fad'a nayi, maganar ce da nauyi da kunya bayan haka idan kaji dole sai ranka ya b'aci  hakan hmmmm hmmmm, sai ta hau kame-kame".
             D'aurin d'ankwalin da ke kanta ya zame a hankali suman ta suka baje a samar kafad'an ta, hannu ya kai yana wasa da su yace" ina sauraranki, just tell me".
      "Ka san me?
A'a, tare da girgiza mata kai.
          Diffffffff tayi shiru hakika ta so ta b'oye mishi amma zuciyar ta ya gaza hakura, wai ace duk irin son da kake nuna wa Nana ta rasa irin kasafin da zata yi maka sai na sharri? Cewa tayi wai jikin ta kake so!
         What!!!!!! Yayi saurin ture ta daga jikin shi tare da nanata k'almar jikin ta nake so! Ta yaya zan nemi yarinyar da ta taso a gabana, wacce d'igan hawayen ta na bugan zuciya ta........... Wallahi Nana bata yi min hallaci ba, so take ta shafa min bakar fentin da ba zan iya gogewa ba."
          Ganin yanda hankalin shi ya tashi sosai tace" kwantar da hankalin ka my one ai fenti kam sai dai ta shafa ma kanta amma ba kai ba, ni shaida ce kuma iyayen mu shaida ne baza ka tab'a aikata mummunar aiki ba, mun fi kowa sanin irin lalurar da take damunka shekara da shekaru wanda har abada babu maganin ta, muryar ta ne ya soma rawa da kyar ta iya saitawa tace" tunda nake da kai baka tab'a ko da romancing d'ina bane ballantana aje ga maganar sex.
         Wani irin sassanyar ajiyar zuciya ya sake a heart d'in shi cewa yake" I'm sorry wife bani da wani zab'in da ya wuce na cin amanar ki, i tried harder naga na cire sha'awar Nana but every day and night tamk'ar dad'a hura min sha'awar ta ake".
            Daren ranar Aina sai jujjuya maganar Nana take yi a ranta da kyar ta samu ta runtsa, Datti kuwa ko a jikin shi domin ya san babu wani k'ofa da ya bari wanda zai tona asirin shi.
         Washe gari da safe har d'aki Nana tabi Aina ta tarar da ita tana gyaran bed ta gaishe ta ciki-ciki ta amsa. A cikin dare d'aya duk idanuwan ta sun jeme sun kod'e.
           Matsawa tayi gefe kad'an ta tallafe fuskanta da tafin hannun ta tana kollon yanda Aina ke gyaran tana so tayi mata magana amma sannin kanta ne ba sauraran ta zata yi ba sai ta wuce kawai ta fita za ta  d'aki ta tarar da Datti a parlour yana waya, har ta  wuce  yace" Ke Nana zo nan". Kamar bata ji shi ba tayi banza da shi". Ba k'iran ki nayi ba ko bakya jina ne", ta taho tana gimtse fuska".
          " Zauna anan", yayi mata nuni da kujerar da ke gefen shi.
        Ido yabi ta shi yana kallon ta for  some minutes yana karantar ta ya hango zallar kiyayyar shi ne a bayyane a fuskar ta". Huci mai zafi ya fetsar. Me yasa kike da taurin kai ne Nana? Me yasa baza ki bani abinda nake nema ba kika wahalar da ni? Kina tunanin kina da wata mafita ne?
         Zuciyanta ne ya soma bugawa da k'arfi dakewa tace" Allah shine kad'ai mafita kuma shine shaida na". Shi zai kare ni daga sharrin ka".
         Eye glass d'in fuskar shi ya cire ya sake binta da kalo yana mamakin yanda take zaro zance, kar dai yarinyar nan ta daina ganin mutunci na? To ya na iya dole ne daure tunda ita ce jigon yaruwa na".
           Tunda kince haka mu zuba ni da ke, ba zan fasa bibiyar ki ba kuma baki da wani makwanci da ya wuce d'aki na, Tashi yayi ya fita Office ya barta tana ruwan hawaye.
           Taci kuka sosai kamar ranta zai fita da kyar ta lallashi kanta ko sallama da Aina bata yi ba tayi Family house d'in su tana isowa ta tarar da su a parlour suna hira, cikin kuka ta shigo ta fad'a jikin tsohuwa tace" I'm dead", na daina zama da Datti kenan umma, Ummi........., JIKINA YAKE SO!.
               Da mugun mamaki suka d'ago suna kallon ta, cikin had'in baki su biyun suka ce" bamu fahimce ki ba", yi mana maganar gwari-gwari ko zamu fahimta".
           Da kyar ta iya tsagaita kukan tana jan ajiyar zuciya irin ta wacce taci kuka sosai d'innan sannan ta kwashe komai ta fad'a musu, salati suka saka gabaki d'aya suna mamakin abunda ya fito daga bakin ta".
         Ummi ce dai ta fara magana tace" Kin ban kunya Nana, ban tab'a zata irin sakayyar da zaki nuna ma Datti kenen ba, ke kuwa ba zaki duba irin halaccin da yayi miki ba? To ki sani ko mutuwa tana shakkar idon mahaifiya".
           Tsohuwa da ta cika tayi fammmm tace" kyale ja'ira sakarya, ince ba shine ke sangarta ki da ranki ya b'ace yayi fushi da mu amma kya zo da wani zance marar dad'in ji?
          Umma dai na jin su bata tanka musu ba har saida tsohuwa ta gama maganar ta kafin tace" abu d'aya ne ya b'ata maganar ki ya kuma hana mu gaskata zancen ki, yanda kika san dutse haka Datti ya d'auki jintsin mata shi yasa baza mu yarda da abunda kika fad'a ba".
           Guntun hawaye ne ya zubo mata", me yasa rayuwa
End Ads