suka ji kwana biyu wurin shi shiru, amma sai tunanin su ya basu wata k'ila gajiya yayi yayi zuciya ya koma gidan shi.
Aina ma bata wani damu ba tun da rashin ganin shi da bata yi ba.........sai dai acikin kwanakin tana jin fad'uwar gaba mai tsanani.......time to time gaban ta sai ya fad'i.
Wata rana da daddare tana barci tayi wani mugun mafarkin da ya d'aga mata hankali wai Datti na ta amman jini yana nuno mata wata yarinya a can nesa da su bata iya ganin fuskar ta, kokarin rarrafawa yake ya kamo yarinyar a duk sanda ya kusa zuwa dafffff da ita sai ta b'ace, duk sanda ya so ya kamo ta baya iyawa gashi jini ta hanci jini ta baki duk ya b'ata mata jiki da shi.........., bakin shi ta lura yana motsi kamar yana so yace mata wani abu.........sai ta kai kunnen ta kusa da bakin shi tana kuka.........kice rokar mini ita......, Na.......,sai ga gudan jini k'ato ya futo mishi ya fetsar idanuwan shi na rufewa a hankali........ganin haka ta tashi ta runtuma a gude duk yanda ta so ta d'aga k'afa ta kamo ta amma sai ta k'asa, har ta gaji ta hau nishi da kyar tana d'aga k'afa sai ji tayi an Saki salati ta bayan ta da k'arfiiiiii a take awon muryar ya hau yawo a kwakwalar ta.........a take tsoro da firgici suka kamata ta juyo da sauri dan ta gane muryar Datti ne.......... firgigittttttttt fa farka a barcin ta hau salati tana dube-dube ita kad'ai.....wannan dare bata kuma komawa barcin ba gani take idan ta koma zata tarar ya mutu.
Washe gari wuni tayi jugumm duk an rasa gane kanta banda sunan Datti babu abunda take fad'a............., ita gida zata koma ta nemo mijinta tana son shi bata so ya mutu ya barta, shine fa hankalin su duk ya tashi Alhaji da kanshi ya d'au key na mota ya nufi gidan Datti ya tarar k'ofa a garkame mai gadi ya sanar mishi cewa rabon shi da ya ga maigidan da matar gidan har ya manta, ba dan zaman mutunci da suka mishi ba da ya dad'e da barin gidan ya gaji da bauta babu salary.
Da Alhaji ya dawo ya fad'a musu abunda ya faru sai hankalin su ya fi na farko tashi, sunyi sakaci da wauta da har suka yi tunanin yana gida bayan sunfi kowa sannin halin da yake ciki.......kar shima guduwan yayi.
Ummi kam rushewa tayi da kuka dama k'irisss take jira" duk laifin mu ne da muka yi watsi da halin da yaron yake ciki gashi nan shima ya gudu kamar yanda y'ar uwar shi ta gudu".
Mardiya kam banda kuka babu abunda take yi ita tafi ganin laifin Umman su fiye da na kowa.....tana sane da hurar da Umma ke yi mishi........gashi nan ta jawo brother d'inta was no where to be found.
Baba Babba cikin dakiyar zuciya yace" ba kuka ya kamata kiyi ba Ummin Nana........., idan da laifin mu a sakacin b'atan shi shima ai da nashi laifin........, munfi kowa dacewa ya fad'a mana damuwan shi mu da muke a matsayin iyayen shi amma baiyi hakan ba.......me yasa ba za mu fusata ba".
"Baba karami zaiyi magana Alhaji yayi saurin dakatar dashi" ya isa hakan yanzu mafita muke nema ta yanda zamu b'ollo wa lamarin, yanzu yaya kuke ganin za'a yi?
Gugum suka yi bai tare da samun mafita ba kowa na bin kowa da kallo.
Suna nan carko-carko a parlourn har wajen k'arfe bakwai na dare ko wannen su sai uban zufa yake had'awa, Usman ne ya shigo gidan a dai-dai wannan lokacin yana ganin su ya sha jinin jikin "shi.......bab....a sannun ku", ya fad'a cikin inda-inda.
Around takwas da rabi sai ga Usman ya shigo gidan dan ya duba shi sai ganin su yayi ko wannen su hankali a tashe, ba shiri ya ja jinin jikin shi cike da fargaba.
Kallon kurilla suka yi mishi suna mamakin zuwan shi a wannan daren ko dai shima ya samu labarin cewa Datti ya gudu ne........?
Tsohuwa dai k'irjin ta sai bugu yake fattttt fatttt tana so ta tambaye shi amma tsoron ta kar ace shima Usman d'in bai san inda Dattin yake ba.
" Don Allah ya Usman kar kace kaima baka san inda yake ba.........., bana son ka furta min cewa d'an uwana ya b'ace ba'a san inda yake ba........, duk a cikin kuka tayi maganar.
"Shiru yayi kamar yana tunani......, ya so ya b'oye musu amma condition d'in da Datti yake ciki ya sa ba zai iya b'oye musu ba cuz he is in a critical condition, Datti bai gudu ba yana nan cikin gidan nan fama yake da rashin lafiya shi yasa baku ganshi ba, ku biyo ni na inda yake, yana fad'a ya haura saman D'akin Fu'ad da sauri suna bin shi a baya.
A kwance suka tarar da shi a kan bed fuskar shi ya kod'e fatar jikin shi ya koma kamar na mai ciwon Aids, yana had'a ido da su sai ga hawaye babu bakin magana.
Aina ta rushe da gunjin kuka ta rungume shi cikin rashin sa'a garin fad'awa jikin shi ta bata sani ba ace hannun ta ya kai wajen peppered bananar shi ya kwalla k'ara da k'arfi tare da nuno wajen yana yarfe hannu, yaji azaba sosai kamar ranshi zai fita.
Saurin ture ta daga jikin shi Usman yayi..........kunya ce ta sa shi tayi k'asa da kai sai yanzu yaji rashin dacewan abunda yayi.........,
Muryar Alhaji yaji yana cewa" me ya same shi a wajen ne yake ihuuuuu haka?
Da murya irin na marar gaskiya yace" Allah baba ku gafarce, na b'oye ban fad'a muku ba cewa Datti na fama da ciwon al'aura kuma ciwon ne ya kwantar da shi ya hana shi fitowa".
"Whattttt ka san me kake fad'a kuwa?
" Ba tare da ya furta komai ba yayi yunkurin zame bed shit d'in tsohuwa da su Umma suka yi saurin kawar da Ido su baba Karami suna gani sai da suka kad'u, salati suka saki gabaki d'aya dai-dai lokacin Usman ya rufe su Mardiya suka juyo da kan su, sai gani suka yi iyayen maza suna had'a gudu sun rasa ta cewa.
Shigowan Fu'ad kenan ya tarar da abunda ke faruwa, da ya d'au ka ba wani abune mai girma ba sai da ya shigo ya gani da idanuwan shi hankin shi sai ya tashi........., sai yayi nadamar kin fad'a ma iyayen su da yayi, ko da yake ba laifin shi bane hasalima bai tab'a gani ba sai yau, da d'inma maganar su yaji shine ya san cewa Datti baida lafiya amma bai san cewa ciwon yayi tsanani har haka ba.
Fad'a baba Karami yake yi cikin fushi ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ta ciki" yanzu a naku wautan kuna sane da halin da yake ciki shine baku fad'a mana ba? musamman kai Fu'ad ku kwana tare ku tashi tare da mutum yana jin jiki kamar haka baka fad'a a d'auki mataki ba?
" Mugun kallo ya watsa ma Usman a ranshi cewa yake zaka yi baya ni ne, a fili kuwa yace" wallahi baba ban san rashin lafiyar nashi ya kai har hakan ba, ga babban maci amana nan da ya b'oye muku, kuma ya san komai yake binnewa, duk suka bi bayan Usman da kallo.
"Kallon Datti yayi da gefen ido ya ga yana girgiza mishi kai yana ruwan hawaye ma'ana yana warning d'in shi no matter what happen karya sake ya fad'a kawai sai yace" Kaiiiiii Fu'ad kaji tsoron Allah me na sani da har zan b'oye musu?
"Da safen nan ina wajen aiki ya bugo min waya ya sanar dani halin da yake ciki shine nayi mishi treatment lokacin sauri nake yi cuz ina da aiki shi yasa ban fad'a muku ba......., ko shigowa na da niyar fad'a muku nashigo da naji kuna tambayana shine na kawo ku inda yake".
Mamakin irin k'arfin hali na Usman yayi sai ran Fu'ad ya b'aci zuciya ne ya kawo Fu'ad iya wuya yace" Wallahi k'arya kake munafuki, ya san komai boye muku yake son yi!!!!!!!!!!!!
"Baba sirrine rufaffiya wanda ku baku sani ba..........
" Usman Adalcin da zaka yi ma Datti kenan ka fad'a musu.........na san shi ya gargad'e ka da hakan shi yasa baka son fad'a........,idan har Datti ya mutu ka sani kana da laifi mai tsokaa kaima Allah ba zai barka ba.........,
Sai jikin Usman yayi sanyi sosai ya juyo yana kallon Datti kayi hak'uri abokina dole na fad'a musu su san komai, daga nan ya kwashe komai ya fad'a musu, da irin shawarar da ya ba ma Datti na aikata barnar da yayi duk ya fad'a musu.
"Sunyi mamaki sosai har ransu basu gamsu da abunda Usman d'in ya fad'a ba, k'ila sun shirya hakan ne dan wani nufi na su amma bari suji daga bakin Datti.
" Datti da gaske ne abunda Usman ya fad'a a kanka?
" Hantar cikin shi ya kad'a, Usman baiyi mishi adalci ba da ya fad'a musu........, amma ko da zai mutu ba zai tab'a amsa laifin da bakin shi ba, tunda basu da wani hujja da zasu bayar wanda zai tabbatar da hakan.
"Abba ban san komai ba sharri suke min.......,
To kunji yace bai aikata komai ba kuma muma mun yarda da hakan
Shiru Usman yayi dama ya san dole za'a rina ba kowa ne zai yarda da abunda ya fad'a ba haka kuma dole sai ansha daga da Datti wajen fad'ar gaskiya.
Suna cikin hakan ne wani irin wawan ciwon ciki ya turnik'e Datti.......numfashin shi ya hau d'aukewa sama-sama, sai nishin azaba yake yi...........,suka d'ago shi zasu da niyar su kaishi asubiti yace musu a'a ba zai tafi ba........su barshi a gida kawai rayuwar shi ne ya zo k'arshe, ciwon ajali baya jin magani.
Mata suka rushe da kuka wi-wi da hawaye.
" Fu'ad dai hawaye kawai yake yi........ko mutuwa ce zata d'auki d'an uwan shi yafi son ya bayyana musu komai zai fi mishi kwanciyan hankali ko da ya mutu ne..............., sai dai Dattin yana da taurin kai yak'i bada had'in kai, gefe ya matsa shi kad'a yana feeling pains kamar an tsoka mashi a kasan zuciyan shi, dole ne ya tursasa d'an uwan shi ya fad'a laifin da ya aikata,
Dole ya bi duk hanyar za zai bi ya cimma burin shi na tursasa mishi fad'an gaskiya ba zai barshi ya mutu a matsayin mai laifi ba........ta wace hanya zai bi yayi hakan...............
B'angaren Nana yau tun safe bata fito ba tana d'aki sai wajen k'arfe tara na dara taji uban yunwa ya kamata ta fito tana neman abinci.
Har ta d'eba zata koma taji k'afarta ya zungure wani abu.........bata sani ba ashe da mutum a parlourn dama yau through babu wuta shi yasa bata gan shi ba.
Tsoro taji zata koma da baya yayi saurin riko hannun ta tun d'azu ya zo yana jiran zuwan ta, Amintacce ne ya bugo mishi waya yace duk halin yaya ya san yanda zaiyi ya kawo mishi amanar shi, gashi damar da yake da shi kenan idan har ya bari ta tafi ba lallai ne ya samu wannan daman ba.
Ihuuuu zata kwala yace" shttttttt nine fa, sai tayi shiru cuz ta gane ashe mutumin nan ne dai.
A masifan ce ta cuno baki kamar yana ganin ta" malam sake ni na koma ko?
"Naji zan barki amma da kin bani lokaci kad'an........
" Baza ka tab'a samun lokacina ba....har abada ka daina yaudara ta da fake fuskar ka", ta fizge hannun ta zata shiga.
"Naji na yarda daga yau amma yau d'aya ki bani lokacin ki idan yaso har abada karki sake bani, rashin bani had'in kai a wannan lokacin zai iya haifar da matsala babba.
Ganin yanda ya marairaice mata ya sa tace shikenan na yarda.
" Alfarma nake nema ki bini mu tafi wani waje ni kuma nayi miki alkawarin a cikin daren nan zan sada ki da mahaifan ki..........., karki yi zargin cutar da ke nake son nayi nayi miki alkawarin cewa babu abunda zai same ki.
Ba dan ta yarda ba ta bishi sai dai dan yayi mata alkawarin cewa ba zai cutar da ita ba.
Mota suka shiga ya ja suka bar gidan........., garin babu haske shi yasa bata gane unguwar da suka shiga ba sai ganin ta tayi a wani gida suna isowa yace ta fito.
Cikin gidan ya nufa da ita.......kasancewar akwai solar a gidan shi ya bata daman ganin ko ina sai take jin kamar ta san gidan amma decorations d'in ya banbanta da wanda take tunanin gidan ne.
Har matakalan bene suka taka suna isowa dai-dai bakin wani k'ofa yayi dailing number ya saka wayar a kunnen shi" hello mun iso muna bakin k'ofa..........ka fito please.
Muryar da taji a wayan ne ya tsinkar mata da gaba ta juyo ta aika mishi da kallon shine ko?
Kai ya gyad'a mata ba alamar eehhh ba tare da yace komai ba.
K'arar bud'e k'ofa suka ji Nana ta zuba ido ta ga wanda zai fito, she shocked sosai da fuskar da ta gani a gaban ta,.........tunanin fuskar ne ya fad'o mata a rai, sai yanzu take kanin fuskar tayi matching da wanda take gani a gaban ta...............Mene dalilin wani buri ne yake da shi akan ta da rufe ta a guri d'aya?
Lallai akwai lauje cikin nad'i bata tsammaci ganin wannan fuskar a matsayin ammintacce ba.............
*eedatou*
*💫SHINNING STARS WRITERS ASSOCIATION*
'''The more we shine bright the more we educate and enlighten our readers.'''
Masu neman littafin daga farko don Allah ku yi hakuri yawan ku ya sa banzan gama biya muku bukatu ba duk yawan typing da aikin gidaba zai bari na samu daman tura muku ba.
3️⃣9️⃣—4️⃣0️⃣
Shima sai kallon ta yake yi cikin wani irin yanayi marar misaltuwa.....har yanzu yana jin tsananin sonta na ratsa shi.....Ya Fu'ad dama kaine Amintacce ka b'oye min baka fad'a min ba? Me yasa ka raba ni da gida ka jefa ni cikin kunci........me nayi maka da na deserving haka daga gare ka.........., ashe dama kiyayyar da kake nuna min har ta kaiiiii ka raba ni da gida ka kawo ni ka ajiye ni inda babu dangina.........? Shin baka tausayina ne.......baka tausayin baby d'in da ke cikina ne.........? Hawaye taji ya sauko mata tayi saurin bada baya tana gogewa.
" Kalaman ta sun hurting d'in shi sosai bai so ace ta fad'a hakan ba, even though da baya shiri da ita amma doesn't mean cewa har abada zai tabbata da kiyayyan ta.
Ba tare da ya furta komai ba ya kamo hannun ta tana turjewa har suka shige d'akin..........cakkkkk ta ja ta tsaya tana kallon mutanen da ke wurin bata tab'a tsammanin cewa zata sake had'u da su a wannan lokacin ba hasali ma ta cire tsammani da ganin su.........,dai-dai nan suka juyo a tare, lokaci guda mamaki rikicewa da tsantsar farin ciki ya dabaibaiye su"Na.....nah, Aina ta fad'a da mugun k'arfi.........dam dam dammmm zuciyar Datti ya buga......, yana had'a ido da ita a take jikin shi ya d'auki rawa.......hak'oran shi suka fara kad'awa kattt katttt kattttt.
"Ina kika shiga Nana muka neme ki muka rasa, me yasa zaki tafi ki bar mu, sai ga hawaye na bin fuskar Aina, ita kanta ta san cewa hawayen nan na farin ciki ne domin tayi missing k'anwar ta.
Tsohuwa tsabar farin cikin ganin y'ar jikallen ta taje da gudu zata rungume ta taji abu ya tok'are mata ciki da ja da baya dan ta ga menene wannan abun......., ido biyu tayi da zungureren cikin Nana sai ta taji gaban ta ya mugun fad'uwa ta d'ago hijabin ta doka salati da k'arfi...........ciki Nana?Wa ya d'irka miki ciki,?
Sai murnar su ta koma ciki" duk suka rud'e suma hankalin su ya tashi sosai. Wuta ne ya d'auke ma Ummi sai take jin har ranta da ma bata dawo ba akan ta dawo musu da muguwar tsaraba wanda basa fata samun shi.......Nana ta jawo musu abun kunya ta b'ata ma family d'in su suna.......duk irin tarbiyar da ta basu amma sai da ta ware k'afa ma wani k'ato ya d'ura mata ciki? Nana dai sai hawaye take yi ta kasa tsaida su.......baba