x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 3 - UNCLE DATTI JIKINA YAKE SO

  • 6001 words
  • 9000 words
  • Out of 86070 words

Category: Romance Story +18

Views 312

01 Sep 2025
Start ads
After Image Ads
ne ya b'arke a tsakanin su har har Fu'ad wanda tun shigowan su yake d'akin shi bai sun zo ba ya fito yana latsa waya ya tarar da su, sosai yayi murnar ganin su dan shi mutum ne mai faram- faram da mutane saidai ko kad'an baya son raini ba kamar Murja ba wacce take miskila, idan ba wanda ta sani sosai ba bata fiye sakewa da mutum ba.
Laaa auty ashe kun taho? Ehhh wallahi Fu'ad yanzun nan ma kuwa".
Nemo wuri yayi ya zauna ba tare da ya d'auke idanuwan shi a kan wayan ba".
Wai ina mutuniyar ne ban ji duriyar ta ba? yana nufin Nana kenan, Datti yayi mishi harar k'asan ido yace" me zaka mata?
" Yaya kenan da ka tambayar wajen Nana sai kace me zan mata? Me ma nake dashi da zan bata". umma ki ji min yaya fa? Ya juyo ya shagwab'e fuska yana kallon mahaifiyar shi wacce tun d'azu sai murmushi take yi.
"Hmmmmm ka ma dai da taka kalar fitinar, kai ma ka dai san halin yayan naka sarai, ni dai na ga ranar da Nana zata bar gidan nan ayi mata aure ko binta zaka yi gidan miji ohoo"?
Dariya suka saka su duka banda shi da
Rad'e rai yayi sosai, bai san me yasa ba yaji zuciyar shi ta tsaya cakkkk, ba komai ne ya ya sa hakan ba illa maganar umma, sannin kanshi ne duk son shi da Nana dole watarana sai tayi aure ta koma karkashin wani, to wai ma me ye na suka wannan tunani? Idan tayi aure me matsalar ka aciki? jefo ma kanshi tambaya yayi yana mai tuhumar kanshi.
Nana kam tana can b'angaren mahaifiyar ta tunda ta shigo gidan ta lik'e mata sai surutai take mata, Sallama aka yi aka shigo" Fu'ad ne ya shigo Nana ta wani had'e rai kamar wanda bata tab'a sanin shi ba, yana sane da hakan amma ya fuske cuz shi dai haka kawai yarinyar bata wani burge shi, ya rasa dalilin da yasa brother d'in shi ke nan da nan da ita tamk'ar duk familyn itace kad'ai gare su".
Kallo d'aya yayi mata ya d'auke kai ya koma gefen ummi dama a parlour suke ya bi lafiyar three seaters ya kwanta tare da fad'in" Ummi yunwa nake ji ko zan samu ragowar abinci a wajen ki?
Murmushi tayi mishi tace" Fu'ad kenan me zai hana? Idan ma babu ai sai na saka Nana ta dafa maka".
Saurin mik'ewa yayi ya zauna da mugun mamaki yace" what? Wata Nanar ba dai wanan ba?
" Ita d'in dai da ka gani a gaban ka?"
"Me wannan zata iya dafawa banda jagwalgwale?"
Dariyar sosai ta saka dama da wasa tayi maganar banda abunshi du-du-du nawa Nanar take da har zata saka ta dafa mishi abinci ita da ko tafasa ruwa ba'a koya mata ba?, mai da wukar wasa fa nake maka." Ga mamakin su, ji suka yi Nana ta saki tsaki mai k'arfi duk suka bita da kallon mamaki, magana ce ta hau yi a zuciya bata sani ba ashe ya fito fili tana cewa", Allah ya sawwake ma na dafa ma abinci, wallahi ko yunwar kashe ka zata yi ba zan dafa ma ba gara ka mutu............ummi saurin buge bakin ta tayi da k'arfi tana cewa" ja'ira sai dai ke ki mutu amma ba shi, banda bakar zuciya ma d'an uwan ki kike ma fatan mutuwa?,
Sosai yayi mamakin rashin kunyar Nana yarinya k'arama kamar ita ace ta gasa mishi magana dan rashin kunya har da ja mishi tsaki? nan da nan yaji ranshi ya mugun b'aci idanuwan shi ne suka sauya launi saboda b'acin raiya, kyale ta kawai ummi zanyi maganin rashin kunyar ta, yaja kwafa ya koma ya kwanta".
Ba tare da ta bi ta kanshi ba ta hau wa Nana fad'a ta inda take shiga ba ta nan take fita, Nana kam ta sa kuka da gudu tayi b'angaren umma, hira suke yi amma tun daga nesa yake jiyo sautin kukan ta yaji gaban shi ya mugun fad'uwa, iso wajen su tayi na ganin Datti ta dad'a k'ara saurin kukan ta ta fad'i k'asa tana birgima tana cewa" an tsane ta, dama ba son ganin ta make a gidan ba", a rikiceyayi wajen ta da Sauri" ya Salam !!!!!! da wata irin dashashiyar murya yayi maganar me ya same ki kike kuka? Wa ya tab'o min ke? Yi shiru Nana ta ki fad'a min".
Jawo ta yayi a jikin shi yana lallashin ta ita kam tamkar ingizata yake haka take ji, ta dad'a lafewa a jikin shi cike da shagwab'a ta cigaba da rera kukan ta". Shiru yayi na y'an wasu dakika yana sauraran ta, yayin kukan nata ke dad'a rasa shi, k'irjin shi yayi mishi nauyi da yawa kamar an aza mishi dotse a ka. Ba komai ne yafi d'aga mishi hankali ba illa kukan Nana da ko kad'an baya k'aunar ji. Ganin ba zai iya jure hawaye a fuskar Nana ba yayi saurin raba ta da jikin shi ya dunk'ule hannun shi ya kaiwa iska naushi yana huci kamar mayunwacin , su ummi kam banda ido babu abunda suke binshi da shi, ita kam ba ma kukan Nana bane, yanda duk ya rikice akan ta ne ya mugun bata mamaki har ta fara zargin cewa gaba akwai kallo tsakananin su, ba dan Aina shakikiyar Nana bace wallahi babu abunda zai hanatayi zargin cewa Datti na tsananin son Nana, ba so irin na wa da k'anwa ba, so na auratayya".
Hannun shi d'aya ya aza a saman kafadar ta, dayan kuma ya d'ora a saman lab'an shi yayi da tsigar lalashi yace" sheeeee......., kana ya tausasa murya a hankali yace" kukan ki nasa nima naji kamar nayi kuka angel, kina so nayi kuka ne Nana?
Ta girgiza kai tana sheshshek'ar kuka, to idan bakya so nima nayi dan Allah ki fad'a min, wa ya saka ki kuka?"
Sai yanzu ta samu damar tsagaita kukan nata, ta hau kora mishi bayani har ta gama, ji yayi ranshi ya kuma baci sosai fiye da na farko a zuciye yayi hanyar b'angaren Ummi duk suka bi bayan shi cuz a tsorace Duke da lamarin shi".
Tarar da su yayi hankalin su kwance suna hirar su har ga Allah sun ma manta da mai ya faru dan Fu'ad had ya tashi ya sako abincin yana ci yana zuba santi wai ya rasa tsakanin ta da Umma wa tafi iya girki, banda tsiya da dariya babu abunda take mishi, ga zaton su sai ji suka yi Datti ya damko Fu'ad da k'arfi ya sharara mishi mari ji kake tasssssss, ya nuno shi da hannu yana wuci idanuwan shi had rufewa suke cuz of tsabar b'acin.
How dear you!!! Wa ya baka dama ka saka baby angel kuka?
Ba su umma kad'ai ba hatta ummi duk sun rikice sun rasa abun yi yayin Fu'ad ya dafa da kuncin shi yana murzawa ba kad'an marin ya shige shi ba, a take yaji ranshi nayi mishi suya, ji yayi ya tsana yarinyar tsana mai matukar gaske, a yanda zuciya ta d'ebe shi kamar ya kama ta ya nad'a mata duka dan ya wuce haushin tunda akan ta ne d'an uwan shi ya mare shi.
Ya had'iye miyau mai d'aci zuciyar shi cike da dafi yace" yaya akan Nana zaka mare ni? Me kuma tace nayi mata?
Yi min shiru munafiki ni zaka tambaya?
Shiru yayi tare da jefa wa Nana harar tsana ya ja kwafa ya fice daga parlourn abincin da bai gama ci kenan ba ya nufi main parlour ya zauna. A take yaji wani irin tukukin bak'in cikin ya ya kama shi, ba shiri ya ciro waya a aljihun wandon shi ya shiga failing numban friend d'in shi Kamal.
Bayan ya d'aga wayan ne ya shiga kora mishi labarin abunda ya faruwa yana gamawa yace" wallahi tallahi na sha alwashin sai na illata rayuwar rayuwar ta..........! sai na  maida  Datti abun tsana da kyama a waken al'umma..............., domin kuwa sai na d'auki fansar abunda yayi min............bashi ne kuma sai ta biya, aka ce ramakon gayya sai tafi ta gayya zafi!!!!!!! kit ya kashe wayaan ba tare da ya jira komai ba".
Abunda bai sani ba ashe a kunnen baba babba yayi maganar da ma ya part d'in tsohuwa ya so ya zauna a nan.
Kunnuwan shi na jiye mishi mugayen zantuka daga bakin fu'ad ya daka uwar tsawa yace" Baka isa ka cutar da Nana ko ka tozartata ba...........kuma ina mai tabbatar maka da cewa duk abunda ya same ta kaine sila!!!!
Shan jinin jikin shi yayi ,sumi-sumi ya mik'e ya bar parlourn.

B'angaren Datti kuwa bayan barin Fu'ad wajen ya ja hannun Nana keeee suka fita daga gidan Aina na ganin haka tabi bayan su da sauri gyale a hannu sanin kanta ne muddin ta bari suka tafi to sai dai ta taho a motar kasuwa, ko acab'a gashi a al'adar ta bata kaunar sa.
A mota kuwa masifa yake tayi har suka iso gida, yayin da take jero dankaren dana sani a zuciyan shi," ji fa daga zuwan su ko minti talatin ya tabbata basu kai ba amma dan rainin yaron nan sai da ya sanya mishi angel kuka, Aina kam shiru tayi abunta gudun karya sauke haushin a kanta cuz kad'an daga aikin shi kenan, Nana kam ko a jikin ta sai ma dad'in da take ji a ranta musamman da ta ga ya mare Fu'ad dama haka take so cuz Fu'ad nayi mata shishshigi da yawa,

A raina nace; Nana at this aged kike cewa gardeden kato namiji kamar Fu'ad yayi miki shishigi?
Sati guda suka d'auka ba tare da sun waiwaye gidan ba cuz fushi sosai Datti yake da su ummi, a cikin satin ne ma ya neman ma Nana wani tsadadden makaranta cuz a wajen yake so ta zana jarabawar ta ta JSCE. ABUBAKAR TAFAWA BALEWA INTERNATONAL SECONDARY SCHOOL shine makarantar da ya samar wa Nana shi ke kaita ya d'auko ta, kuma ya nemar mata mai yi mata extra moral lesson zuwa wani watan za'a yifara mata lesson.
A ranar da ya kawo mata form d'in makarantar ba karamin murna tayi ba, kasancewar ba wani tazara sosai tsakanin gidan su da kuma makarantar. Ranar farko da Nana ta fara halartar makarantar ta ga sauyi sosai, tsarin makarantar kuya ya kayatar da ita matuk'a.
Principal office ya fara kaita yayi mata registrations both PTA da school fees d'inta, daga nan ya damkata a hannun principal na makarantar ya nuna mata ajin ta tare da introducing d'inta gaban sauran y'an uwanta students.
Bayan fitan shi ne wata fara tsiririyar yarinya mai tsawo kad'an, wanda shekarunta ba za su wuce na Nana ba ta taho ta zauna a kujerar ta, time d'in Nana na bud'e litattafan ta tana rubuta sunanta a jiki da kuma ajinta, JS2B shine ajin da naga Nana ta rubuta a kan littafin ta, tana jin zuwan yarinyar amma bata d'ago ta kalle ta ba balle ta sa ran zata kulata, ganin haka ya saka yarinyar ta bugi bencin a hankali lokaci guda tace" hi", a sannan ne ta d'ago ta kalle ta d'auke kai tare da amsa mata ciki-ciki.
Ta so ta ja Nana da hira amma bata samu fuska ba, ba shiri ta koma seat d'inta da zauna dan ko kala Nana bata kuma furta mata ba, tana nan zaune ita kad'an ta har teacher ya shigo ya gabatar da darasin shi, a ranar sun sha darasi sosai almost duka periods d'in sai da aka shigo musu, Nana har gajiya tayi Allah cikin ikon shi closing hours na cika Lamar had'in baki sai ga datti ya parking mota a d'an nesa da ajin su kad'an yana jiran ya ga fitowan Nana.
Daga bakin ajin su ta tsaya tana kallon yanda mata da maza ke ta giftawa, duk ta kosa taje gida cuz yunwa ta kama ta sosai, kamar ance ta d'ago ta hangi motar Datti da sauri ta nufe shi, daga nesa ya hango ta ya tsare ta da ido, fuskar ta ya fara kalla ya ga tayi wani irin fresh zai oya rantsewa da Allah a kaffff makarantar babu wacce rayi na biyu balantana ta kama kafar Nana a kyau
Duk da karancin shekarunta bai hana ta fahimci cewa Uncle Datti ya gama nisawa a kogin tunani ba, ya kafe ta da ido gashi ya kasa d'auke su daga gare ta ya sa ta yin gyaran murya kamar wata babbar mace" eehheennn", yayi firgigitttt ya dawo daga hayyacin shi tare da zira hannu a aljihun wandon shi ya fiddo da hanky yana share zufan da ya karyo mishi".
Muryar ta ya ji ya daki dodon kunnenshi har ya saka shi saurin numshe ido kana ya bud'e su a hankali ya maida hanky. Ba komai be ta fad'a ba illa nuje ko?", ta nufi kofar motar ta bud'e ta shige abinta, yana ganin haka ya shige mota shima a kasalance ya tada motar sai gida.
A parlour suka tarar da Aina tana cin pepper soup na kayan ciki ga fresh milk a gefen ta ta baje tana ci tana sipping at the same time kuma tana watching Hausa series film na Labarina wacce yake zuwa daga tashar Arewa24. Muryar Aina taji da sauri ta maida kofin fresh milk din ta ajiye dama ta kai baki kenan zata sha.
Murmushi tayi fuskar ta na bayyana tsantsar jin dad'in ganin y'ar uwar ta tace" maraba da zuwan student, har kun taso ne?"
Kai ta d'aga mata tare da zare site bag d'inta tayi jefi da shi kan kujera tayi kitchen da sauri ta d'au spoon ta zauna a gefen Auntyn tata itama ta hau ci, uncle Datti kam tsayawa kallon ta kawai yake yi, sai yanzu ya fahimci cewa dama can yunwa ce ta dame ta shi yasa d'an surutun da take mishi ma bata yi ba".
Aina ce ta mishi barka da dawowa, ko zama bai yi ba ya sa kai ya fita yace ma Aina zai je ya dawo nan ba da dad'ewa ba.
Bayan sun gama ci Nana ta tattara plate d'in ta kai kitchen ta d'auraye sai ga aunty Aina ta shigo itama dama ta d'ora girki tuwon sakwara zatayi da miyar egwisi, har ta daka sakwarar ta ta nad'e a leda ta saka a flask saura miyar kenan ta gama had'awa shine ta koma kitchen ta zauna tana cin kayan ciki.
Nana na gama wankewa ta juyo tana kallon Aunty Aina da fararen idanuwan ta, tana kallon yanda take jujjuya spoon d'in kamar baza ta CE komai ba sai kuma naji tana cewa", auty Aina girki nake so ki koya min".
Dariya ta kusa ba ma Aina har sai da ta kusa sakin murfin pot din dan dariya ma har kwalla take fiddawa, da kyar ta iya tsagaita dariyar tata tace"Nana girki fa kika ce? Ina me ina iya girki yanzu dududu nawa-nawa like? Ki bari zuwa gama idan kika k'ara shekaru akan na yanzu sai na koya miki".
Had'e rai tayi cikin rigimar ta ta cuno baki tace" Allah aunty da gaske nake, d'an rainin sense d'in nan ne fa ya yarfa ni gaban ummina yana cewa ban iya komai ba", shi yasa nake so ki koya min cuz bana son raini".
Da mugun mamaki ta tsaya tana kallon ta, ta fahimci cewa da Fu'ad take yi shi yasa manyancen ta ya mugun bata mamaki, tsawa ta daka mata tace" Fu'ad d'in ne kike gayawa haka? to shikenan bari na k'ira shi a waya na fad'a mishi ya min maganin ki ta yi hanyar d'aki ta sauri sai ga Nana ta bita a baya tana mata magiya, cuz cikin ta ya d'uri ruwa sosai, sanin kanta ne muddin Fu'ad ya ji wannan labarin to wallahi babu abunda zai saka ya zo har gidan ya b'abb'alata gashi wanda yake tsare mata fad'an baya ya fita.
Dan Allah Auntyna kar ki calling d'inshi........, wallahi ban sake raina shi......., dan Allah mana auntyna........, idan ya ji b'allani zai yi".
"Ai gara yayi maganin ki tunda bakya jin magana,"Ta ciro waya ta wani dake tana latsawa ala ita da gaske take, Nana da tsoro ya gama kammata ta yi fici-fici da ido kamar wata munafuka, ta kwantar da muryar tace" haba Aunty Aina wallahi da gaske nake, Allah na ratse ban k'arawa, ta dakata da latsa wayar ta jan kwafa, Allah ya taimake ki da yau sai kin yabawa aya zakin ta, tana fad'a ta sa kai tayi kitchen Nana na ganin haka ya saki sassanyar ajiyar zuciya irin ta relief kana ta bi bayan ta, cikin rashin sa'a ta tarar har Aunty Aina ta gama miyar tana shirin barin kitchen d'in kafffff suka yi da Nana wacce take nokewa a bakin k'ofa.
Kamo hannun ta tayi suka nufi parlour ta suka zauna suka tarar ashe an gama shirin "Labarina", Kamar dama da su aka canja program d'in aka saka "akushi da rufi", program na yau dai akan miyar agusi za'a yi shi, murmushi Aunty tayi ta d'an gyara zama tare da kallon Nana wacce d'ungurugum hankalin ta na ajan Tvn bangon kana ta maida kai itama tare da tattara nutsuwar ta, a take aka hau gabatar da shiri tiryan-tiryan ake bayani da kuma gwada yanda ake sarrafa miyar duk inda Nana bata gane ba ta na tambayar Aunty Aina ita kuma ta mata bayani yanda zata fi d'auka.
A ranar kusan abinci kala uku Nana ta koya a wajen Aunty Aina sai bitar shi take yi a kwakwalwar ta tana imagination ga ta nan a kitchen tana dafawa."
B'angaren Datti kuwa majalisar su ya nufa ya zauna a gefe shi kad'ai ya na sauraran maganganun abokan nashi", shauki!!! shaushi shi yaushe zai ji shauk'in nan? Yaushe ne zai d'auke mace a matsayin abokiyar more rayuwa? Yaushe ne zai ji dad'in mace, ya nuta ta da ita, mace ta jiyar da shi dad'in da maza suke ji a jikin su? Yaushe ne zai ji son sexxx a ranshi?, tunowa yayi da Ainar shi mace mai kyau da kyaun diri amma ko kad'an baya jin sha'awar ta kamar yanda yake ji akan sauran mata, sosai ya nisa a tunanin ya gama mantawa a inda yake sai ji yayi an buge kafad'an shi, da sauri ya dawo cikin hayyacin shi yana bin shi
End Ads