ranshi.....amma babu yanda ya iya.
Wata rana yana d'aki bayan Usman ya kawo mishi shi ya tafi, Datti na wasa da yaron har yayi barci a gefen kafad'an shi.........Nana da taji shiru ta fito tana neman shi ta duba ko ina bata gan shi ba.......gashi babu wanda ya damu da ya san inda yaron ya tafi.......sai taji kuka ya zo mata mai tsananin k'arfin gaske" da ace d'an sunnah ne a yanda aka ji wurin shi shiru da hankalin kowa sai yafi tashi amma da yake ba ta hanyar aure aka same shi ba babu wanda ya damu duk da dai suma sun san ya b'atan.
Dabara ne ya fad'o mata ta duba d'akin Fu'ad ko zata gan shi...., haka ta haye sama tana sharar hawaye.......ga mamakin ta tana shiga ta ganshi yana sharar barcin shi hankalin shi kwance shima baban nashi barci yake yi......da masifa ta zo zata kwace d'an ta Datti ya bud'e ido ya sauk'e su fessss akan ta.
" Ina zaki kai min d'a?
"Maganar sai ya bata haushi taja tsaki" au dama kana da d'a ne ban sani ba.......,
"Hannu ta kai zata d'auke Sadeeq yayi saurin rik'o hannun ta yana murzawa a hankali," babyna i'm sorry na putting d'in ki through much pains kiyi hak'uri rabon yaron ne ya sa".
Sai ga hawaye ya fara bin saman fuskar shi" Uncle kenan baka ji kunyar fad'a min maganar ba ina ce tun yana ciki ka sheganta min shi kuma kayi niyar kashe shi at the end kuma kana beginning d'ina bayan har yanzu kana claiming baka san komai ba.......kuka ne ya kwace mata ta hau sheshshek'awa.....Uncle me jikina yayi maka kake so? Me yasa ba zaka amsa laifin cewa Jikina kake so ba.........., Uncle ka saka rayuwa ta cikin bakin ciki....... Yaure tsakanina da kai bashi yihuwa ko da ace ba jinin mu d'aya bane da aunty Aina........, kamar yanda ka d'auki lalurar ka a matsayin k'addara ina so ka d'auki rabuwa da ni a matsayin k'addara, bana son ka Uncle i hate you!!!!!!
Yanda yaji maganar ta a ranshi kamar saukan mashi ya runtse ido da sauri zuciyan shi na mishi azabar rad'ad'i......k'almar rabuwa da baby shi ya fi komai d'aga mishi hankali a duniya.......gashi k'arfi da yaji so ake a raba shi da ita.
"Baby da nayi miki laifi amma na tuba ki yafe min.......Sadeeq jinina ne ina k'aunar shi fiye da yanda kike tunani......wallahi baby da kin san irin k'aunar da nake mishi baki isa ki furta hakan ba".
Murmushin yake tayi wanda yafi kuka ciwo tace" da kana k'aunar shi tun kafin yazo duniya baka yi yunkurin hana shi zuwa ba........, kana ganin irin tsanar da ake mishi a cikin gidan nan amma baka yi yunkurin komai ba........,
"Shiru yayi yana tunani shi kan shi ya san abunda ta fad'a gaskiya ne shine wanda ya kamata ya share mishi hawaye tunda shi ya yi silar kawo shi duniya ta gurb'atacciyar hanya.......yana cikin tunanin ne har ta d'auki Sadeeq ta tafi da shi bai sani ba.
Ba ita ta zame ko ina da shi ba sai d'akin ta da yake b'angaren tsohuwa kusa da na Aina ta dire Sadeeq akan gado time d'in har ya tashi a barci yana kuka........., nono ta bashi ya k'i k'arb'a sai kuka yake yi da ta rasa abunyi sai itama ta rushe da kuka tana mishi wasa tana wak'a ko zai yi shiru.......taho taho d'an yaro nayi maka gata.........,kowa baya sonka yace kai shege......,duka hantara da kyamar ka suke yi.........tunda uban.....ka ya k'i ka......ba wani mai....maka gata.
Ta jima sosai tana wakar ta bata sani ba ashe Fu'ad ya shigo ya tsaya yana sauraren ta......haye mai uban d'umi yaji ya sauko mishi sai ya rungumo ta ta baya yana kuka kamar k'aramin yaro......." Ni zan bashi kulawan da ya rasa a wajen mahaifin shi......ba zan bari ya wulakanta ba dai-dai da rana ba zan bari ya san cewa bani na haife shi ba..........d'an Datti nawa nima.
"Ya Fu'ad Uncle Datti mugune.....duk da dai na san cewa ba ta hanyar aure muka same shi ba amma na tabbata babu uban da zai kyamace d'an shi......., Sadeeq bai da wani gata a gidan na, kiyayyar shi tayi yawa a gurin kowa na gidan nan.........
"Banda ni da ke Nana idan kowa ya k'i shi mu muna son shiiiiii.
Kuka suke yi sosai daga su har yaron kamar dama can yana ya san abunda suke fad'a .
Shirye-shiryen bukin Nana ya kankama a lokacin ne Datti ya d'aga hankalin shi ya fito musu b'aro-baro yace shi zai aure Nana.....mamaki sosai suka yi har suke zargin anya kanshi d'aya? Ya aure ya, ya aure k'anwa.
Ana gobe d'aurin auren hakalin shi idan yayi dubu ya tashi.....da dai ya ga tabbas da gaske ake za'a d'aura auren nan ya shiga rokon Nana akan karta amince a d'aura mata aure da Fu'ad shi zai aure ta......tace aure babu fashi da yana son ta ya zalunce ta.
Da abu ya dame shi ya same su Alhaji yana kuka yace" zan fad'a wallahi baby d'in nan nawa.......don Allah ku karku raba ni da ita........, daga nan ya kwashe komai ya fad'a musu har da hotel d'in da yake kaita suna hutawa duk ya fad'a musu"
"Sosai suka firgita da jin abunda ya fad'a" da gaske ne kai ka yi wa Nana ciki".
"Eehhh ehhh wallahi nine don Allah ku yafe min".
Inalillahi wa ina ilaihiraji'un sai yanzu suke jin k'amshin gaskiya akan abubuwan da Nana take fad'a a baya......garin yaya suka yi sakaci har hakan ya faru? tambayan da kenan suke fad'a a zuciyoyin su.
Alhaji da ya cika da tarin al'ajabi da b'akin ciki yace" kai da muke tsammanin ba lafiyayye bane yaushe ka samu lafiya ka aikata wannan b'arnar.
"Lalura ce nima ba da son raina bane na d'aura ma kaina sha'awar ta.......
Aina taji wani irin mahaukacin kuka ya zo mata ashe dama Datti cin amanar ta yake bata sani ba? Ina alkhawarin da ya d'aukar mata a baya na cewa ba zai cutar da ita ba? Me yasa ita da take mace ta rik'e mishi kanta shi kuma bai rik'e mata kan shi ba yayi taraiya da k'anwar ta".
Kallon Nana ta yi wacce tun d'azu take rusar kuka tace" Kaico na da na yarda da yaudarar d'a namiji fiye da rayuwar k'anwata........duk irin abubuwan da Nanar take fad'a ta toshe kunnuwan ta k'arshe ma tace k'azafi take mishi ashe yaudarar ta yake da kalama ta.
Ita dai bata ga amfanin zaman aure da shi ba bai amfane ta da komai ba......tana nan tana rik'e mishi kanta amma shi jikin wata yake so ba nata ba..........
Tsohuwa dai baki ya mutu sai suma take yi tana farfad'owa, duk irin tsanar da take nunawa Sadeeq ashe da uban shegen a gidan, kaiiiii Datti baiyi halin bugun girma ba..... ba a banza abar shi ya dame shi da ciwo ba, a d'au yarinya a bashi k'arshen sakamakon da zai nuna musu kenan.
Mari baba Babba ya wank'a mishi ya had'a mishi naushi da k'afa kan kace me sai ga jini ya b'alle mishi a baki.........
Ka ban kunya wallahi ban tab'a tsammanin haka daga gare ka ba........sirrin da kake boyewa kenan da baka nuna ba ka sa muna zaluntar yar uwar ka".
"Umma dai kunya had'e da bak'in ciki duk ya ishe ta ace d'an da ta haifa da cikin yayi tarayya da k'anwar matar shi uwa d'aya uba d'aya? Tausayin Nana da Sadeeq ya mugun kama ta musamman Sadeeq da bai san komai ba suka d'auki k'aran tsana suka d'aura mishi.
Hawaye taji ya soma zubo mata ta matso cike da tarin takaici tace" ba mu da muka baka amanar yarinya ka cutar ba kanka ka cutar........, tana gama fad'a ta d'auki Sadeeq ta mik'a mishi d'auki d'an ka tafi da shi daga yau mun cire ka acikin family d'innan bama son sake ganin ka.
"Sai a sannan ne hakan shi ya mugun tashi , don Allah Umma kiyi hakuri ta rainar min shi idan yafi haka wayo sai a dawo min da shi".
" Uban ka nace, ba za ka d'auke shi ba ko har sai ka hasalini nayi maka baki.......da muka baka amanar ta mun had'a da shi ne ina ce kai ka samo shi daga baya........don haka ka tafi ka bamu wuri.
"Yaron kamar ya san za'a raba shi da uwar shi ya saki kuka yana mik'a mata hannu ta d'auki shi sai tausayin shi ya kama Nana taje da gudu tana kuka zata k'arb'e shi baba babba ya rik'e ta da sauri......barshi ya tafi da tsiyan shi raino kam kin gama yi mishi sai ya d'aura daga inda kika tsaya.
Tana ji tana gani haka Datti ya tafi da Sadeeq uba kuka d'a kuka uwa kuka.......da dai sauran masu saurin kuka suma suna taya su.
Datti na fita Fu'ad yayi saurin bin bayan shi ya sha gaban shi" yaya ka ga takun",
Nayi amfani da kwakwalwata na cusa maka k'iyayyar Nana a zuciyan ka........., a halin yanzu tafi kowa tsanar ka......., ka san me? Na raba ka da ita ne dan na cimma burina kuma" kana ji kana gani sai na aure Nana na cusa maka bakin ciki wanda zaka dawwama a cikin ta.
" Wawan shak'a ya kai mishi da hannun shi d'aya yana huci kamar mayunwacin zaki....... Idan har ban aure ta ba kaima baka isa ka aure ta ba......., bangaje hannun shi Fu'ad yayi ya shige ciki ya barshi.
Haka ya ja yaron shi ya bar gidan daga bakin k'ofa ya tsaya yana k'are ma gidan kallo zuciyan shi nayi mishi zafi.......
*eedatou*
*💫SHINNING STARS WRITERS ASSOCIATION*
'''The more we shine bright the more we educate and enlighten our readers.'''
~Attention pls akwai mistake a page na baya, idan akace gobe ne auren Fu'ad da Nana har aka kore Datti a gidan, ga abunda zan saka a wajen" lokaci na tafiya gashi yanzu bukin Nana na dad'e matsowa", ban sani ba na saka wancan laifinane da ban editing ba ku min uzuri ku gyara, ngd.~
4️⃣1️⃣—4️⃣2️⃣
Mota ya shiga da Sadeeq a hannun shi ya had'e kan shi da steering motar yana rusar kuka har da majina........su Umma basu mishi adalci ba da suka raba shi da Nana sannan suka raba Sadeeq da mahaifiyar shi..........., kallon Sadeeq yayi a lokacin har ya gaji da kuka yana sake ajiyar zuciya..........rafa suman kan shi yayi sai yaji sabon hawaye ya sauko mishi" kayi hak'uri son nayi sanadiyar kawo ka duniya ciki kazamin rayuwa..........., da ace ta hanyar aure aka same ka da baza raba ka da uwar ka ba.......hawaye msi d'umi yaji ya sauko mishi sai ya k'asa tsare su..........da kyar ya iya d'aga ya jan mota ya bar gidan..........
Ba shi ya tsaya a ko ina ba sai a gaban wani makeken shago na ga ya parking ya fito da Sadeeq a saman kafad'an shi ya shige ciki........,
Shopping yayi ma yaron sosai na kayan abincin yara da rigunan sawa da wando, kayan wasa da dai sauran su daga nan ya nufi gidan shi.
Tun a hanya Sadeeq ya fara barci har suka iso bai tashi ba ya samu ya kwantar da shi ya koma gefen shi ya kwanta tare da jawo shi jikin shi sai ga hawaye ya fara kwaranya a fuskan shi.
Cikin dare yaron ya farka yana ta sandara kuka sosai kamar ranshi zai fita......., Datti ya tashi a firgice ya d'au ledar da ya shigo da shi ya had'a mishi costant yana bashi a baki maimakon ya karb'a sai ya hau kawar da kaiiiiii shi dai mamar shi yake bukatan gani a lokacin.
Hawaye na bin fuskan Datti yana d'aga k'afa da kyar dick d'in shi na mishi zafi amma ba sosai ba yaje ya d'auko zani a d'akin Aina ya goya shi yana yawo da shi a parlour duk Sadeeq sai dad'a k'ara kuka yake kamar zuga shi ake.....hankalin Datti idan yayi dubu ya mugun tashi......" Shi kam ji yake ya ma fi yaron bukatar bukarta hakuri kawai ya fishi. Rasa inda zai yi da shi ya kunce zanin da sauri cikin daren ya zare car key d'in shi ya nufi gidan su Alhaji ya hau buga musu k'ofa su bud'e, duk suka firfiito cuz daga d'akunan su suna jin kukan yaron karancewar dare ne".
Zubewa yayi a gaban Nana ya mik'o mata yaron hawaye nata kwaranya a idanuwan shi" don Allah ki k'arbi d'an ki kar ki bari a raba ki da shi........ba don hali na ba ki rik'e Sadeeq kina jin irin kukan da yake yi ki tausaya mishi........help me, help me please i beg you".
Fu'ad na ganin sai tausayin shi ya kama yaron da yana da halin baiwa Nana d'anta da yayi.
Wani mahaukacin kuka taji ya zo mata tana so ta k'arb'i yaron har ranta tafi bukantan shi a kusa da shi.......me yasa su Ummi basa tausayin ta basa tausayin Sadeeq dan ya kasance ba d'an sunna ba?
"Umma taci ka fammmmm da shi sosai " Ya san ba zai iya rik'e d'an ba ya haifa ?wa ya ajiye da zata yi rainon shi? Tsabar b'acin rai ji take kamar ta wank'a ma Datti mari.....bai ji kunyar abunda ya aikata ba shine yake cewa a rik'e mishi d'an shi".
" Kaiiiii Abubakar ka fita a idona na rufeeeee, wai ba anyi maka iyaka da gidan nan ba?
"Ummi don Allah!!! don Allah ki taimaka kar kiyi min hakan.......ki sassauta min hukuncin nan ya min sauri da yawa ba zan iya d'auka ba".
" Baba na san kaiii zaka fi Umma fahimtar halin da nake ciki......kaima namiji ne kamar ni.......baba ka san jarabawar da nake ciki na lalura ta......, ka fahimtar da ita cewa ba laifina bane, laifin k'addara na ne........tasssss ya ji an d'auke shi da wani mahaukacin mari wanda ya gigitar da shi saura kad'an ya saki Sadeeq ya fad'i k'asa Nana na ganin haka tayi tsalle ta rik'e Sadeeq tana kuka wi-wi, shi kam da ya tsorata ya dad'a k'ara sautin kuka ya gama sadakarwa cewa zai fad'i ne.
"Rungumo shi ta yi tsammm jikin ta tana mai jin tausayin shi a ranta har take nadamar kin biye ma Datti da tayi lokacin da, shi kam Sadeeq sai ya manne a jikin ta ya hau ajiyar zuciya.
Scene d'in ya matuk'ar ba ma Aina tausayi sosai sai ta hau ba ma Umma hakuri.......please Umma ku tausaya wa yaron ba dan halin uban shi ba......" Saurin katse ta tayi cikin fushi" kee rufe min baki kin fini sanin abunda nake yi ne? Idan kika kara saka baki a maganar nan sai na hada da ke naci mutuncin ku........marar kishin kanta kawaiiii.
"Ke Nana wuce ki shiga cikin gida".
Zata tafi kenan baba babba yace" mik'a mishi d'an shi........,kwalla ne ya zubo mata ta hau sharar su......."babu yanda ta iya haka ta mik'a ma Datti Sadeeq, cikin wani irin hali Datti yace" kema kin goya bayan na tafi da shi kenan? Kin goya bayan a raba ki da d'an ki......., kin manta da ranar da cike da cikin shi kike cewa a bar miki d'an ki da hannun ki zaki raine shi.......zaki yi mishi gata ashe irin gatan da zaki yi miki kenan? Nana idan na k'i Sadeeq yana ciki ke kika so shi har ya zo duniya wani riba zaki ci in kika rabu da shi idan kika rabu da shi? Dama kin haifo shi ne dan ki mishi tab'on da zai nuna mishi baida gata? A yanda yake maganar muryar shi har tsarkewa yake yi, a take jikin shi ya d'auki rawa............,
Yanda take jin maganar shi a ranta kamar diran kifiya........, ba k'aramin ratsa mata kwakwalwa yake.........bata da wani zabin da ya wuce ta bi umurnin iyayen su, haka tana ji tana gani ta mik'a mishi d'an cakkkkk ya rik'e hannun ta ya had'a da nashi suka matse Sadeeq gam a jikin shi" Son ka taya ni rokar mana mommy karta guje mu we really need her by our side............, karta bar mu muyi maraicin ta.........", sai hawaye ya gabgaro ma yaron kamar ya fahimci abunda uban yake fad'a ya hau mik'a mata hannu yana so ta d'auke shi..........,matsanancin kuka ne ya kwace mata ta shafa tare da bashi peck tace" i'm sorry for letting you go, forgive your me son", tana gama tayi d'aki gudu.
Wannan k'aron sai da zuciyoyin su ya k'arye saboda da tsananin tausayin yaran, Ummi ce