yana sallama kofar d'akin.
Tsabar rud'ewa kasa amsa sallamar tayi, sai tashi da tayi ta zauna tana kallonshi da mad'aukakin mamaki.
Fati ce da tayi rigingine kan gadon salma ,ita halin da 'yar uwarta tashiga yake damunta.
Ita ta amsa sallamar tare da bada izinin shigowa.
Tare suka shigo da nusaiba, ta je ta ajiye ledojin da ta karb'a daga hanun ahmad snn ta d'auki sallaya ta shimfid'a mishi.
A hankali ta sake komawa ta kwanta ta tana gyara zanin dake lullub'e a jikinta.
Lokaci guda kuma taji hawaye na jika mata fiska.
Ita kad'ai tasan irin azabtuwar da takeyi, yanzu kuma da ta ganshi sai taji ,abin ya qaru mata.
Gaisheshi fati tayi ya amsa idonshi na kan salma.
"Ya jikin?"
Ya cewa salma.
Shiru tayi tamkar bata san da ita yakeyiba.
"Daure ki tashi mu tafi asibiti a duba ki."
Da sauri kuma muryarta na rawa tace "Ni lafiyata lau."
"A hakan, yanda kika kudundune ,kika kwanta?"
"Bacci zanyi ."
Ta bashi amsa.
"To me ya hana ki cin abinci kuma."
"Na koshi."
"ban yarda ba."
Shiru tayi mishi.
"Ta so ki d'an tab'a wnn ko kad'anne salma."
Ya fad'a cikin sassauta murya.
Jin bata amsa kuma bata motsa ba ya kaurara murya "Sauko mana."
Shiru ta kuma yi.
"Kin san Allah, idan baki taso ba d'ura zan miki, kuma ki sa wasa ki gani , zaku rik'e min ita aiko kanwarmu."
Ya fad'a yana maida dubanshi gun su nusaiba
"Sosae ma ."
Nusaiba tace.
D'an bud'e idanunta kad'an tayi tana kallonsu.
"Kunga, Fatinmu, kuzo ku rik'e min ita naga idan ba d'uran aka mata ba ba ci zatayi ba."
Ya fad'a yana nad'e hanun farar shirt d'inshi.
Wuff ta tashi tana raba ido dan duk a tunaninta da gaske yakeyi d'uran zai mata.
"yauwa qanwarmu miqo min plate."
Da sauri nusaiba ta fita ta kawo plate.
Ita kuwa salma binshi take da kallon mamaki ya wani zo ya zauna musu tsakiyar d'aki har da tankwashe qafafu kamar mai neman gafara, har da wani cewa zai mata d'ura.
Ajiye mishi plate d'in nusaiba tayi ta koma ta zauna kusa da fati.
A cikin ledojin da ya shigo dasu ya bud'e d'aya, ya juye cikin plate d'in .
Take qamshi ya cika d'akin har yawun su nusaiba ya tsinke ,banda uwar gayyar dan babu abinda zai burge ta a yanzu.
Gasasshen nama ne ruwaΒ² wanda yaji kayan had'i sai tiriri yakeyi.
Ya sake fiddo kwalin exotic babba mai sanyi dan har rab'aΒ²
yakeyi.
Had'e fiska yayi yace "Sauko mana."
Su nusaiba ko sun zuba ido suna kallon drama.
"Ko dai d'uran za'ayi ne?"
Ya fad'a yana yunk'urawa kamar zai tashi.
Ai da sauri ta sauko ta zauna kusa da plate d'in tana ta fama gyara zanin da ta lullub'a dashi, kasancewar top yellow da skirt baqi a jikinta ,kuma top d'in 'yar qarama ce.sai bakar hula da ta sa akanta.
Ganin duk tabi ta takura kanta yasa shi cewa fati "Miko mata hijabi."
Miqa mata fati tayi ta amsa tasa snn ta ture zanin yayi kasa.
Kawar da kanshi yayi ya maida hankalinshi kansu nusaiba hakan ya bata damar ci kad'an ta cire hanu.
Dan dama tana tunanin yanda zata bud'e baki taci yana kallonta.
Tana cire hanu ta matsa a hankali ta kwantar da kanta kan katifar .
Da ido nusaiba ta mishi alama.
ya juya ya kalleta.
"Har kinme?"
Da sauri tace .
"Na qoshi wlh ,ahmad dan Allah kada kace na qara.
Tausayi ta bashi yanda take magana muryarta na rawa .
Exotic d'in ya tsiyaya a qaramar glass cup d'in da nusaiba takawo.
"Amashi wnn kisha to."
Ya fad'a a tausashe.
Bata son yawar magana shi yasa ba musu ta karb'a tasha rabi, zata ajiye yayi saurin tareta da cewa .
"Yi haquri ki qarasa shi mana."
Har wani langab'e kai yakeyi.
Kafa kai tayi ta shanye snn ta maida kai zata kwanta.
"Taimakeni ki zauna ya d'an shiga jikinki tukuna salma."
Ya dakatar da ita daga kwanciyar da takeson yi.
Hakan yasa ta zama ta lumshe idonta tare da d'ora hanunta kan goshinta.
Ita matsalarta a yanzu ganinshi da takeyi shi yake dad'a tayar mata hankali idan ta tuna da yanzu mijin wata ce sai taji kamar ta kurma ihu .
Duk da taji dad'in kulawar da ya bata, tunda tasan amaryar ya baro yazo yana fama da ita taci abinci, hakan ya nuna mata da gaske ba son auren yakeyi ba.
Matsowa yayi kusa da ita cikin tausasa murya yace...
[17/12 06:25] Hajara: *ππIN SO CUTANEππ*
*Fasaha Online Writers.*
*F.O.W*
*By Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*
16.
ππππππ
*Ban manta da ku ba .*
Reedah malaysia.
Zaa princess.
Fatima (Bazamfariya)
Mmn Sa'ad.
Mmn sadiq.
Fadhilatu Ali.
Habiba Muhammad.
Ummi Aisha.
Mmn Humaira.
Amina jaji.
Ahmatallah.
Kai kuna da yawa fa masoya.
*Allah ya bar k'auna*
*Ana tare.*ππ
"Salma dan Allah kirufa min asiri ki cire damuwa a ranki, idan kinayin haka hankali na tashi yakeyi ya kikeso inyi, dame zanji .
Abinda kin riga kin sani Salma ce a zuciyar Ahmad, to meye naki na d'aga hankali.
Kin ga saboda kin d'aga wayata da kikayi yau haka na wuni da zazzab'i ko uabinci ban iya ci ba."
Da sauri ta bud'e ido ta kalleshi, idanun duk sun rine sun kankance.
"Yanzu haka ka wuni baka ci abinci ba?"
"To ya zanyi kin min rowar muryarki ,kuma nasan idan ba kina cikin damuwa ba baza kiqi d'aga wayata ba, qarshe ma kika kasheta gaba d'aya."
"Yi hakuri."
Ta fad'a kamar zatayi kuka.
"bazan hakura ba kuma haka zan kwana da yunwa indai baki bar damun kanki da d'aga hankalinki ba."
"zan bari wlh, dan Allah kaci abinci, bari nusaiba ta kawo maka."
"a'a ni bazanci abinci gidan surakanina so kike ace bani da kunya?"
"Ba wani rashin kunya."
Basar da zancen yayi da cewa "to yaushe zaki bar damuwan naji kince zaki bari."
"Na bari ma, kaci dan Allah."
"Ban yarda ba har sai naga murmushin kan kyakkyawar fiskarnan."
Bata san sanda murmushin ya sub'uce mata ba, su ma su nusaiba dake kallonsu saida suka murmusa.
"Yauwa to,ko kefa, kinga yanzu idan na koma gida zanci abinci hankali kwance, Nusaiba ,fati, ga amanata, ko na tafi kar a barta cikin damuwa, kar abari ta kuma zama da yunwa ,snn kada kubar ciwonnan ya sake damunta."
Dariya dukansu sukayi, cikin dariyar nusaiba tace "lucky abun baiyi yawa ba?
ta ina zamu ga ciwo kuma mu hana shi kamata?"
"Ku qoqarta dai qannena."
Ya fad'a yana mik'ewa.
"Yauwa ina wayar auntynku?"
Fati ce ta bud'e bedside drawer ta miqa mishi.
Kunnata yayi yana mita ,"Waya cajinta a cike aka kasheta kawai dan a quntata rayuwar bawan Allah."
Miqa mata wayar yayi a taimakeni kada a kuma kasheta ,ko zan samu barci."
"Kai lucky", nusaiba ta fad'a tana dariya.
"Allah da gaske nake , idan banji muryarta ba baxan iya bacci ba."
Ah, lallai abin azeemunne.
Sunkuyowa yayi kusa da ita "Zan tafi salma , Allah ,qara qarfin jiki, ya yaye miki wnn zafin kishin."
Harara ta sakar mishi, ya kama kunne yana dariya.
Sallamarsu yayi ya tafi ,Salma sai binshi da ido takeyi .
Saida ya fita ta lumshe idonta ,ta yi rigingine kan katifa.
Nusaiba da fati da suka tafi rakiya suka shigo.
Suna shigowa nusaiba taje ta zauna a inda ya tashi ta wani tanqwashe qafafu kamar dai yadda yayi d'azu.
"Sauko kici ."
Ta kwaikwaiyi muryar ahmad har da wani had'e ranta.
D'an bud'e ido salma tayi ta kalleta taja 'yar siririyar tsaki.
"Kinsan Allah idan baki taso ba d'ura zan miki, fatinmu zaki tayani aiko?"
Ta sake kwaikwayon shi.
Dariya ce ta ciyosu daga fatin har salma suka shiga darawa, salma kuwa tana dariyar ta d'au pillow ta jefeta dashi tana cewa "Mara kunyar banza."
Kama baki tayi "Oh aini naga rashin kunya soyayya gaban yara ba ko kunya, ke d'in ma harda biye mishi kina wani marairaicewa da kashe murya."
"Allah ya duba miki adda nusai."
Fati tace.
"Bari ma na duba menene a babban ledan can, mutane
duk sun gama tsinka mana yawu ,da nice ke aunty ai sai na bar muku sud'i wnn uban qamshi, amma har wani yanga kike, Fati ,kin san me?
Inaga a gurin da yayanmu yake sayo mana lucky ya sayo naman nan, baki ji k'amshin iri d'aya ba, har ma da d'and'anon."
Ta k'arishe tare da jefa tsoka na biyu cikin bakinta.snn taci gaba da
bud'e sauran ledojin tana surutai.
Fruits ne cikin babban ledan, kama daga lemu ,ayaba, kankana, apple, abarba dss.
Fati ce tazo ta kwashe tana cewa "Bari a je a nunawa ummi tukuna buku kwad'aima."
****** ****** *****
Yana komawa gida ko hanyar d'akin amarya bai kalla ba.
Wankanshi ya shiga yayi snn ya kira salma suka sha hirarsu.
Washegari haka salma ta tashi jiki ba k'wari, da ka kalleta kasan akwai damuwa a tattare da ita.
D'akin al-amin ta leqa bayan ta gama shiryawa zata tafi makaranta , ta sameshi yana karyawa.
Gaisheshi tayi tace "yayanmu rabo na da kai tun jiya da safe."
"Na shigo da daddare ummi tace min lucky yana d'akinku,yazo dubiya.
Shiru tayi tayi qasa da kai, kiran sunan lucky da yayi yanzu har yasa gabanta fad'uwa.
"Salma."
Yace bayan ya ture kwanon d'umamen da ya gama ci.
"Na'am ."
Tace gabanta na tsananta fad'uwa dan tasan shi d'in ma dai bai wuci maganar auren ahmad zai mata ba.
*Gaisuwar takice swt sister , Halima Auwal, Allah ya qara miki lfy da kwanciyar hankali.*
[17/12 06:25] Hajara: *ππIN SO CUTANEππ*
*Fasaha Online Writers.*
*F.O.W*
*By Anty Rukie (Mmn Abduljalal)*
17.
ππππππ
"Ina so ki nitsu ki bani hankalinki ki saurareni dan fahimci abinda zan fad'a miki."
Gyad'a mishi kai tayi ba magana kam.
"Kinga aurennan da kike gani, nufi ne na ubangiji , shi aure muqaddarine snn kamar yadda kike ga mutuwa ta ke d'auka idan tazo ba jinkirtawa, haka shima aure, idan lokacin shi yazo ba makawa sai anyi shi.
Babu wanda yake auren matar wani ,kamar yanda babu wanda zai haifi d'an wani, sbd haka, ki dad'a tabbatarwa kanki cewa lokacin auren ahmad ne yazo kuma anyishi akan lokacin da ubangiji ya qaddare shi.
Dan yayi aure ba shi yake nufin baza kuyi aure ba, a'a lokacine da rabo, idan da rabo kamar yaune, sai kiga anyi ya wuce.
Idan kuma kika ga bakuyi auren ba dama can Allah bai hukunta zakuyi bane, sai ku sawa zuciyoyinku haquri da tawakkali.
Wani lokaci mutum yakanso abu matsanancin so, amma sai kiga ya zamo ba shine alkhairi a gareshi ba, mafi alkhairi yana can ta inda ba'a yi tsammaniba.
Wani lokacin kuma mutum yakanqi abu ba tare da yasan abinda yaqin shine alkhairi a gareshi ba.
Ni dai shawarar da zan baki ki sawa zuciyarki haquri da dangana, ki nemi zab'in alkhairi wajen Allah.
Bayan haka akwai abinda na lura dashi.
Soyayyar ahmad ya rufe miki ido yasa kin manta ko ince kinyi watsi da abubuwa masu muhimmanci.
Kin yi karatu kina da ilimin addinin ,bakya buqatar na fad'a miki cewa duk waraka tana cikin qur'ani.
Na fahimci ayanxu ahmad shine weak point d'inki, inda bakiyi watsi da karatun qur'ani ba yaushe damuwa zatayi miki yawa har ta sa miki ciwo.
Ki riqe Qur'ani ki samu waraka daga rabbil izzati, salma, ki daure ki cire duk wata damuwa, duk abinda kika ga ya faru da bawa dama can *Rubutaccen al'amarine*.(Aysha Ali Garkuwa)
Allah ya sa kin fahimci abinda nake nufi."
Ajiyar zuciya ta sauqe ,lallai al-amin ya haifu cikin malam, yawancin abubuwan da ya fad'a yanzu kusan irinsu malam ya fad'a mata.
Lallai tasan tayi sakaci da karatun qur'ani dan idan bata manta ba takai aqalla sati biyi bata karanta ba.
Sosae taji dad'in shawarwarin da ya bata har tanajin kamar damuwarta ya yaye.
Sbd haka ta mishi godiya .
Shi ya rakata yana bata shawarwari har ta samu abin hawa ya biya mata ta shiga ta tafi.
Daga wannan rana Salma ta koma karanta Al-qur'ani mai girma fiye ma da yadda take yi da, snn bata wasa da tashin dare tana nemawa kanta sauqi gurin mamallakin sammai da qassai.
Cikin ikon Allah kuma kashi tamanin cikin d'ari na damuwarta ya yaye, bata da wata matsala illa ta kishin Ahmad dake mintsilinta sa'i da lokaci.
Auren da yayi baisa ya daina zuwa gun Salma ba, zuwa yakeyi kamar yanda ya saba.
Ganin haka yasa wata rana ,bayan bikin ahmad da sati biyu Ummi ta k'ira salma tayi mata magana.
"Salma yanzu abinda kike yi kina ganin kina kyautawa?"
"Me nayi ummi?"
"Yaronnan ahmad ba aure yayi ba."
Dummm, taji kirjinta ya buga ,dakyar ta bud'i baki tace "eh..aure yayi."
"To me yake kawo shi wajenki kullum?"
To fa me ummi ke nufi kenan dan ahmad yayi aure saisu rabu kenan? ai shi ba son auren yakeyi ba.
Tunanin da takeyi kenan.
Ummi ta katse ta da cewa
"Da kefa nake , nace me yake kawoshi wajen ki kullum."
Nanma shiru salma tayi heart d'inta na dukan tara tara.
"Salma , ya kamata kuyi wa kanku fad'a.
Ita yarinyar ba rai ke gareta ba. , yanzu ke zaki ji dad'i ace kiyi aure ,amma kullum mijinki ya bar ki a gida yaje wajen zance?"
Wani rarass zuciyar salma yayi, mijinta yayi mata haka kam ai ya kasheta da ranta , inaa baza ma ta iya ba.
"Salma ki sani duk abinda aikata wa wani kai ma sai an maka, watakil ma fiye da abinda ka aikata. Kin so kanki da yawa salma ,kin manta fad'in manzonmu annabi Muhammad (S.A.W)
"Laa yu'uminu ahdukum hatta yuhibbu li'akhiihi maa yuhibbu linafsihii."
"Imanin d'ayanku bazai cika ba har sai ya so wa d'an uwansa abinda ya sowa kansa."
"Salma ko kin manta da wannan hadithin.
Shin idan kukayi auren ma haka zaku je kuyi ta wulaqantata kuna nuna mata ita d'in ba komai bace?
Shin ke baza ki nuna mishi yayi adalci ba ,kanku kawai kuka sani.
Ko kin manta irin azabar da Allah ya tanadarwa namiji mara adalci tsakanin matansa?
A tunaninki soyayya kike nuna mishi kenan?, sam wnn ba soyayya bace, soyayya ta gaskiya itace ka taimakawa masoyinka ya tsira daga fad'awa halaka.
Bari kiji na fad'a miki , yau koda ba ahmad bane ya aure ki, alhakin baiwar Allahn nan bazai barki ba, sai Allah ya bi mata haqqinta, saikinga sakayya ganin idonki.
Ba baki ko fata nake miki ba, ina guje miki abunda zai hana ki kwanciyar hankali ne a gidan aurenki tunda kin bada gudummawar tashin hankalin wata a gidan aurenta.
Kiyi wa kanki fad'a ,ku gyara tun abu baiyi nisa ba, ki guji d'aukan haqqi, ki kuma taimaka wa ahmad ya tsira daga halakar dayakeso ya jefa kanshi, ni dai na gaya miki."
Jiki a sanyaye salma tace" na gode ummi, in shaa Allahu zamu gyara, hakan bazata kuma faruwa ba ."
"Da dai yafi muku."
A sanyaye ta mik'e ta fita daga d'akin ummi ta shige nasu.
Sulalewa qasa tayi ta zauna dab'as, ta fara tunani.
Lallai ta yarda da maganar ya al-amin da yace ahmad shine weak point d'inta,soyayyar ahmad ya sa ta manta da abubuwa masu muhimmanci.
Lallai tayi contributing wajen cutar da matar ahmad, in itace abin ya faru da ita ya zatayi ,ina zata sa ranta ?
Ajiyar zuciya ta sauqe a fili tace "dole ayi wa tufkar hanci."
To ko ya ahmad zai d'auki zancen?
*Mom Hanan ceπ₯*
[17/12 06:25] Hajara: *ππIN SO CUTANEππ*
*Fasaha Online Writers*
*F.O.W*
*By Anty Rukie (Mmn Abduljalal)*
18.
ππππππ
*This page goes directly to u my other half ,Nafeesat Abdussalam (Mrs Bashir Bello.)*
*LYSM.*β€β€β€
Saida ta gama tunaninta snn ta tashi ta d'au wayarta ta qirashi.
Bayan sun gaisa tayi shiru ta rasa ta inda zata fara.
Shi mamaki ne ya cikashi kasancewar Salma bata kiranshi saidai shi ya kirata ,snn kuma basu jima sosae da gama waya da ita ba, to me ya faru?
"Lafiya salma?"
"Magana zamuyi ahmad."
"magana wace iri ?"
"Mai muhimmanci."
"Lallai kuwa mai muhimmancine tunda aka qirani ,kuma ansan anjima zanzo, me ya faru ?"
"Ahmad pls kar kazo yau , in fact ma inaso ka rage yawar zuwa wajena da kakeyi dan Allah."
"Kashe zan kiraki." yace .
Tun bata kashen ba ya rigata kashewa ya kuma k'iranta.
"Salma?"
Ya qira sunanta cikin tashin hankali.
"Kece kuwa?"
"Nice Ahmad."
"Nayi miki laifine?"
"Baka yi min komaiba ahmad."
"To wa yakeso ya shiga tsakaninmu?"
"Babu kowa, so nake matarka ma tasamu lokaci da kulawarka dan tana buqatar hakan."
Bashi ba hatta ita mai maganar zuciyarta bugawa takeyi da qarfi.
"Salma kice min kin samu wanda ya fini shi yasa kikeso ki rabu dani ta wannan hanyar."
"ko kad'an ba haka bane, ahmad muna shiga haqqin baiwar Allahn nan, kasani Allah babu ruwanshi da kana sonta ko baka sonta ,iyaka dai akwai igiyoyinka qwarara akanta,.
Kamar yadda kake da haqqoqqi akanta haka itama akwai haqqoqinta da suka rataya a wuyanka, abu mafi A'ala gareka shine kayi qoqarin sauqesu ,tun kafin hakkinta ya kamaka.
Ahmad bamu kyautawa yarinyar nan, itama Allah ne ya halicce ta kamar yadda muma ya halicce mu, tana da zuciya da rai kamar yadda muke dasu.
Me yasa zamu cutar da baiwar Allah bataji ba bata gani ba.
Kayi tunani bafa ita ta kawo kanta gareka ba, kawo ta akayi, auren nan babu mamaki ita ma ba sonshi takeyi ba tayi haquri tayi biyayya ta zauna a gidanka.
Aurennan fa ya riga ya d'auru ba kwance shi za'a yi ba.
Allah kad'ai yasan abinda ke b'oye.
Kayi haquri ka yarda da qaddara , ka riqe matar ka hanu bibbiyu ku zauna lafiya zaka ga ribar hakan in sha Allah.
Cikin sauri yace "Salma kina nufin kin barni kenan?"
"Ban barka ba ahmad, ina tare dakai in shaa Allah, ni dai burina kada mu shiga hakkin baiwar Allah, Allah ya kama mu."
Sai a snn ya sauqe ajiyar heart.
"To me ya had'a hakan da zuwa gunki kuma?"
"Ahmad so kake su malam su hanaka ni suce baza kayi adalci ba?"
"To naji amma dai zanzo yauko?"
"A'a banda yau banda gobe."
Zaro ido yayi tamkar tana ganinshi, yace "Banda yau banda gobe ma, anya salma?"
"Mu daure dai Ahmad."
"Na shiga uku ni Salman salma zata kashe ni."
Dariya ta fashe dashi "Haba ahmad be strong mana, mutuwa guda?"
Shima dariyar yayi. jin yayi dariya tasan komai normal yanxu sbd haka ta kashe wayar.
Har yanzu zuciyarta bata bar bugawa ba, ita kanta ta jinjinawa qoqarinta da kanta.
Bin wayar yayi da kallo snn ya ajiyeta gefe.
Nazarin maganganun salma ya shiga yi, duk da ba a yau kuma ba a kanta ya fara jin ire iren maganar ba ,amma ta salma tafi shigarshi .
Tariyosu yakeyi d'aya bayan d'aya yana auna su kan mizanin hankali .
Tabbas ta fad'i gaskiya , zaiyi qoqari yaga ya gyara.
Kamar kullum yau ma da kusan magriba ya shiga gidan, sallama yayi cikiΒ² kamar dai yadda ya saba, amsa mishi tayi, tayi mishi sannu da zuwa, duk da tasan ba lallai bane ya amsa, tunda sai ya ga dama yake amsa mata magana.
Ga mamakinta sai taji ya amsa ba tare da ya d'au lokaci kamar yadda ya saba ba.
Kitchen ta koma taci gaba da ayyukanta.
Can ta fito zata shige d'akinta sai ganinshi tayi zaune cikin falonta.
Bin falon yakeyi da kallo yana tunanin ,gidan da ya gina da sunan salma, falon salma , yau wata ce a ciki ba salma ba.
Ikon Allah kenan Ahmad.
Itakuwa mamaki ne ya cika ta dan tunda ta zo gidan bai tab'a shigowa falonta ba ,sai dai taji motsinshi a falonshi, iyakaci dai tana iya qoqarinta taga sun had'u da safe ko ta yaya dai ta gaisheshi,