bisa sallaya bayan ta idar da sallar isha'i.
Babu abinda takeyi illa tunanin Ahmad dan tayi kewarshi ba kad'an ba.
Ji tayi nusaiba ta kamo hanunta tana cewa "Aunty salma zo muje kiga wani abu.,"
Ganin yadda nusaiba take kamar bata cikin nitsuwarta yasa ta tashi ta bita.
Har suka isa kofar gida snn ta saki hanunta.
"Me kika ce zan.."
Bata ida maganarta ba taga Ahmad tsaye a gabanta ya langab'e wuya yana kallonta ,irin kalan tausayinnan.
Da sauri ta juya zata koma yayi saurin shan gabanta.
Itako sarauniyar sa eyes sai ta hard'e hannayenta tana kallonsu.
D'aure fiska tayi tabi gefenshi zata wuce ya sake tareta.
Ganin abinnata da gaskene yasa shi yin kneeling a gabanta yana kallon cikin idonta.
Kawar da idonta tayi daga kallonshi snn tace "Meye haka kuma Ahmad."
"Ki min duk hukuncin da kikaga zaki iya amma banda haramta min ganinki da magana dake.
Na yarda ni mai laifi ne amma hukuncin da kike mini ya min tsauri da yawa, kiyi wa Allah ki sassauta min."
Cikin sassauta murya idanunta sun cicciko tace "Ahmad me yasa kamin haka?
Me yasa ka turo magabatanka ba tare da sanina ba."
"Kiyi hakuri ban yi tsammanin abin zai miki zafi haka ba.
Na d'auka ko don so da yardar dake tsakaninmu sun isa susa ki hakura da abinda nayi, ki kuma amsa tayin neman auren da nayi miki, ban sani ba ashe nayi kuskure ,ni kad'ai ke ta haukana.
Ko ban fad,'a kin san sonki da k'aunarki suka sani yin hakan.
Ya karashe maganar cikin rawar murya dan zafi biyu ne ya had'e mishi, ga barazanar yayanshi gareshi ga kuma salma tana faman juya mishi baya.
Bata san sanda ta durk'ushe kusa da shi ba ,muryarta a shak'e alamar kuka ke shirin kufce mata tace "Tsoro nakeji Ahmad."
Katse ta yayi da sauri "Tsoro ? Tsoron me?"
"Ahmad Jikina na bani idan na shiga gidanka baza ka barni na cika burina ba."
"Ai kam jikinki ya baki gaskiya dan akwai k'alubale babba ma kuwa."
Yace a ranshi .
A fili kuma ce mata yayi "Idan ba gaskiya jikinnaki ya baki bafa, idan zan barki ki cika burinnaki fa?"
Kawar da kanta tayi dan bata son kallon kurillar da yake mata yau, tamkar me mata kallon bankwana.
"Ina shakka akan haka Ahmad ,dan ban ga alamun haka ba."
"Salma ,zanyi iya kokarina naga burinki ya cika ,idan nace miki nayi alk'awari zaki aureni."
Gyad'a mishi kai tayi a sanyaye tana goge hawayen da suke zubo mata.
Shi d'inma a fakaice yake goge nashi ,sbd yana tunanin yadda za'ayi ya mata alk'awarin da cika shi ba tabbas, kuma shi duk abinda zai zubar mishi da mutunci a idon salma da 'yan gidansu baya so,dan ita d'in 'yar mutunci ce 'yar gidan masu mutunci.
Rab'a shi tayi ta wuce dan bazata iya tsayawa wani dogon zance ba ,duk jinta take wata iri jikinta yayi mugun sanyi.
Nusaiba ko saida tayi wa Ahmad sallama tabi bayan auntynta .
Suna shiga nusaiba mai bakin reza tace "Wlh lucky ya ban tausayi Fati ,har kuka fa yayiwa aunty."
"Ungo nan."
Ummi ta fad'a tana mata dakuwa .
"Dama abinda ya kaiki kenan dan ki kikawo rahoto."
Hhhhhh wa yaga BBC.
"Allah ya duba miki mama nusai ,da ya sani ma ni ya kira babu wanda zai san yayi kuka."
Cewar Fati.
"Kwa dai ji dashi ."
Salma ta fad'a a hankali snn ta shige d'akinsu.
Cikin zullumi ya koma gida yana ta tunanin yadda zai shawo kan yayunshi su amince da auren Salma.
Hakan kuma bai hana shi kiran ta ya dad'a kwantar mata da hankali ba, saida yaji ta saki jiki snn ya kyaleta, ya d'ora daga inda ya tsaya (tunanin kenan.)
Itako salma duk da ta yarda da Ahmad da k'aunar da yake mata ,wani gefe na zuciyarta yaki yarda cewa ahmad zai iya cika mata alk'awari.
Daga k'arshe dai tayi wa kanta add'uar fatan alkhairi tsakaninta da ahmad.
Shawarar da zuciyarshi ta bashi yayi niyyar aiwatarwa, dole ne ya saki jiki da yayanshi ya daina wnn fushi da yakeyi dashi ko Allah zaisa ya dace.
Washegari ya shiga gurin yayanshi dan ya fara aiwatar da kudirin shi.
Saidai me.....?
[17/12 06:24] Hajara: *ππIN SO CUTANEππ*
*Fasaha Online Writers*
*F.O.W.*
*By Anty Rukie (Mmn Abduljalal)*
12.
ππππππ
*Wannan shafi zai tafi ne direct zuwa gareki my kakus (Amina Sale Muri)*
Mmn Baba, Allah ya barminke π
*Masoya na gode da addu'oinku ,ina alfahari daku , ina qaunarku fiye da yadda kuke qaunata.*
Yana isa yayanshi ya fara zazzaga mishi masifa, "Wato ahmad, ni ban isa da kai ba ko? kafi k'arfin in sa ka ko in hanaka kenan.
Tun yaushe nake binka kaje wajen Asiya ku zanta kaki saurarona ,kai gaka isasshe, to bari in fad'a maka da kaje da kar kaje duk sammakal aure dai ba fashi, idan yaso dan tsabar kiyayyar da kake mata idan an kawo maka ita kayi gunduwa gunduwa da ita ka kawo min ,kaji ko?"
Amma yaya da ka barni na zab'i wata ko ba salma ba akan da ka min auren dole yanzu watakila yarinyar ma tilastata za'ayi kaga idan akayi mata hakan ba'a yi mata adalci ba."
Ahmad ya fad'a cikin sassauta murya.
"Ahmad, ba shawara ko ra'ayinka nake nema ba ,umarnine nake baka a matsayina na babban wa wanda nake mazamin uba .
Ita yarinyar da yake 'yar arziqi irin albarkace batayi musu ko ta nuna wata matsala ba sai kai da kake mai bushasshen ido."
"Ahmad bishi a hankali ka samu biyan buqata."
Zuciyarshi ta raya mishi.
"Allah ya baka hak'uri ,yaya zanje anjima da yamma."
Ahmad ya fad'a cikin tausayawa kanshi.
"Kada ma kaje in ka dama Ahmadu, gwara ka nunawa aminina da duniya cewar ban isa da kai ba ,itakam asiya ta nuna an isa da ita tunda tayi wa mahaifinta biyayya ,ba irinka ba marar jin magana da rashin sanin ciwon kai."
"Oh Allahna."
Ahmad ya fad'a cikin ranshi.
A fili kuma yace ,
"Zanma je in sha Allah."
Daga ya tashi ya fice yana jin kanshi na juya mishi.
Wato yayanshi so yake ya d'ura mishi hawan jini, idan ba haka ba meye na cewa sai yaje zance bayan ya san ba son yarinyar yakeyi ba snn qiri qiri yanaso ya raba shi da masoyiyarshi,abar qaunarshi, hasken idaniyarshi.
Zuciyarshi a cunkushe ya tafi gidan abokin yayanshi, aka yi mishi iso .
Zaune yake yana tunanin me ma zai cewa yarinyar.
Nazo zance?
Yayana ya turo ni ?
Oho ni banma san me zan ce mata ba.
Itama mai matacciyar zuciya ,ace mutum bai ce yana sonki ba a had'aki dashi ki yarda.
"Mtss ."
Ya ja tsaki a bayanne dan sauran zantukan a zuciya yake yinsu
Ni ko nace "Amma ahmadu ka cika d'an rainin sense ,me kake cewa Salma idan kaje wajentaπ
Yana zaune yaji sallamar Asiya ta ,ciki ciki ya amsa dan sanin muhimmancinta.
Shigowa tayi hanunta d'auke da trayn silver , kwalin juice , robar ruwa sai kananan cups a kai.
Sanye take da atamfar cote d voir ,kalar brown ,ta yafa gyale wanda ya shiga da kayan ,fiskarta tasha kwalliya ,sai kamshi ke tashi a jikinta kamar anyi b'arin turare.
Gabanshi taje ta duqa ta ajiye snn ta d'an koma baya kad'an.
"Sannu da zuwa Bappa ahmadu."
Ta fad'a da 'yar siriryar muryarta kamar ta asiyarmu.
Sunan da yaran yayunshi suke kiranshi dashi kenan.
"Kaji 'yar banza ,wai baffa ahmadu kamar wani tsoho."
Ya fad'a a zuciyarshi.
π€£π€£π€£ haba ahmad tunda ake kiranka da sunan baka jinshi kamar na tsofi ba sai yau, kar kayi dai nima na soma kiranka da wnn sunan.
Bata damu da kin amsa mata gaisuwarta ba duk da ba haka ya saba mata ba idan sun had'u ko in taje gidansu, amma ita kanta tasan wnn had'uwa ta dabance.
Matsawa tayi ta jinginu da jikin kujera snn ta kuma cewa "Ina yini Baffa ahmadu."
Baisan sanda yace "Ke ni baffanki ne, ta ina muka had'u na zama baffanki."
Shiru tayi kanta a kasa.
"Hindatu kike ko wa?"
Da sauri ta d'ago ta kalleshi .
Yana nufin ya mance sunanta ma kenan, lallai abin nashi da gaskene.
A hankali tace "Asiya."
'yar karamar tsaki yaja ,snn ya kalleta a yatsine, shi sai yanzu ma ya tuna da sunan 'hindatu 'yar yayanshi ya kirata.
A ranshi yace "Ji rashin kunya wai ita nan zatazo gurin saurayi har da cab'a kwalliya idan an barta tayi abin burgewa."
Nace ina ruwanka mal. Ahmadu indai ba burgekan tayi ba, kai ka saya mata kayan kwalliyar.π
Asiya ko tace min gane min hanya Mmn Afrah.π
*Gaisuwa gareki masoyiyar gaskiya Maryam A.I Gital, Allah ya bar min ke.*
luv all my fans.ππ
[17/12 06:24] Hajara: *ππIN SO CUTANEππ*
*Fasaha Online Writers.*
*F.O.W*
*By Anty Rukie (Mmn Abduljalal)*
13.
ππππππ
*Dedicated to my sister ,Asiya muhammad.*
Asiya kyakkyawar yarinya ce fara tass ,don ko shi Ahmad bai isa ya nuna mata farar fata ba.
Jikinta d'an daidai, dirinta daidai jikinta baiyi yawa ba baiyi kad'an ba, karyanka kace ka ganta bata burgeka ba , bama kamar idan ka kalli kwayar idonta ,dan manyan idanune da ita farare tass, kamar dai na asiyarmu.
Ga bakinta d'an dadai mai d'auke da fararen qananan haqora.
Amma shifa ahmad duka wnn ba burge shi tayi ba, shi a gurinshi babu macen da ta kai salmarshi.
"Wai ke baki da wanda kike so yake sonkine zaki buge da auren baffan qawarki?"
Ya fad'a tare da tsare ta ido sai muzurai yake mata dan yasa mata tsoro.
Jin tayi shiru bata ce komai ba sai wasa da yatsunta da takeyi ,yasa shi yace .
"Ke duba, idan har kinsan ba san aurennan kike ba ki fito kifad'a musu bakiso kinada wanda kikeso ,dan kar ki cutar da kanki ,yanzu an daina yayin irin wnn auren na takura, kina jina?"
"Hmmm."
Tace kawai tayi shiru.
"Ki bud'i baki kiyi magana ba kiyi ta "Hmmm ba, hmmm kam sai ta iya kasheki babu wanda yasan abinda ke cikinki."
Dariya maganar tashi ta bata wai hmmm zai kasheta.
Lallai ma baffa
ahmadunnan.
Murmusawa tayi snn tace "Nikam bazan iya bijire wa iyayena ba ,bazan yi musu dasu ba ,duk abinda suke so shi nakeso."
"Kaji wawiyar yarinya zata b'ata min shiri , tana nufin tana sona kenan ,lallai iska na wahalar da mai kayan kara.
Zancen zuci.
"To ni kuma ina da wacce nakeso ba ke ba ya kenan?"
Shiru ta masa tamkar bata jishi ba.
"dake fa nake."
Ya fad'a tsawace.
A razane ta kalleshi snn cikin rawar murya tace.
"Ka bar wa Allah komai zai zab'a maka abinda yafi alkhairi."
Shiru yayi na d'an lokaci dan ta so ta kashe mishi jiki.
Can dai yace.
"Ke ma kiyi addu'ar Allah baki miji maisonki."
"Aini na dad'e da neman zab'in Allah akan samun miji managarci ,mai addini, sanin ya kamata, mai mutunta d'an adam , snn wanda zai riqe ni da amana."
Harararta yayi "To kin tabbata nine wnn mijin da kika roqarwa kanki, kina da tabbacin zan riqe ki da amana, bayan kuma hankalina nakan wata?"
Kanta a k'asa tace "In sha Allah ,dan nasan addu'a bata fad'uwa qasa banza, nikam nayi na'am da zab'in da Allah ya min."
"Kinfa kawo point yarinya addu'a bata fad'uwa qasa banza ,nima dashi na riqe tuntuni Allah ya mallaka min salmata cikin sauqi."
Zancen zuci.
Niko nace zab'in alkhairi akace ba abinda kakeso ba mal.ahmadu.π
Basu wani jima ba ya musu sallama ya koma , yana komawa gida ya tarar yayanshi yadawo daga kasuwa.
Gurinshi ya wuce dan ya sanar da shi ya je gurin Asiya ya dawo.
βΉwa yaga notice me.
Duk da yaji dad'in zuwan da ahmad yayi bai nuna ba, saima ce mishi da yayi, "da fatar ba rashin mutunci kaje ka musu ba."
Shafa kanshi yayi tare da cewa "A'a wallahi."
"To yayi kyau."
Yayannashi yace atakaice.
Zama yayi kamar zaiyi magana sai kuma wata zuciyar tace mishi "Bi a hankali ahmad kar ya gano ka."
Sbd haka ya tashi yayi waje danjin an dara k'iran sallar maghrib .
Yanzu daga yayannashi har salmar lallab'asu yakeyi, ya rasa wa zai tankwasa a cikinsu ya zubar da makaman yakinsa.
Sai da ya kuma zuwa wajen asiya dan ya tabbatar wa yayanshi ya mishi biyyaya.
Bayan kwana biyu yaje ya same shi da maganar.
Bayan ya gaisheshi a ladabce yace "Yaya dama nazo ne batun maganar salma."
Sai kuma yayi shiru yana d'an sosa kai tare da kallon yayannashi k'asaΒ².
"Ina jinka."
Yayan ya fad'a yana had'e fiska.
"Dama nace tunda zan auri asiyar me zai hana itama salmar a nema min aurenta , kaga ko tana aikin tunda asiya tana nan ba wata matsala, zata kula da gidan."
Kallon banza yayan ya bishi dashi snn yace "da yake ga maigaidin gida ka samu kenan, kai ka fita ,matar so ta fita ita ku barta da gadin gida ko?
To ban amince ba.
Ashe baka fita harkar yarinyar nan ba dama.
To daga yau kar ka kuma kawo min zancenta dan har abada ba amincewa zanyi ba, gwara ka rik'e wacce muka zab'a maka hanu bibbiyu ya fi maka alkhairi.
Ba kaje ka nacewa mai vakkugo boro (Mai rataya jaka.) tazo tana juya ka yadda taga dama ba ,dan irinsu ba imanine da su ba."
Shiru yayi yana kallon yayanshi yadda ya fitittike yake zuba mishi masifa yaki ya saurareshi sam.
"wani irin kallo kake min haka ahmadu, dan ina guje maka fitina shine zaka tsaya kana min irin wnn kallon rainin .
Akwai abubuwa da dama da muke guje maka wanda kai baka sani ba, ire iren wad'annan mata masu zuwa aiki fitina ne, sai kaga ana haifa maka yara masu kamanni dabanΒ² sai kayi sa'a kasamu d'aya mai kama dakai, kuma a jibge maka su a ce duk naka ne, babu kuma yadda ka iya kayi ta d'awainiya da shegu.
To ni dai ba da ni za'ayi wnn kafurci ba kaji na gaya maka."
*Mom Sadeeq ce*π
[17/12 06:24] Hajara: *ππIN SO CUTANEππ*
*Fasaha Online Writers*
*F.O.W*
*By Anty Ruky (Mmn Abduljalal)*
14.
ππππππ
Takaici da bakin cikine suka cika ahmad jin irin qazafin da sharri da yayanshi yake faman d'orawa salma , sbd haka ya tashi ya bar mishi wajen ba tare da ya kuma mishi magana ba.
Lallai yayanshi baisan wacece salma ba da har yake tunanin zata iya aikata irin wnn hali.
Tunani ya Shiga yi a yanzu ga irin abinda yake fad'a akanta inaga in ya aureta ,lallai akwai yaqi a gabansu daga shi har salma ,dole su fiskanci matsaloli, shi kuma ba hak'ura zaiyi da ita ba.
Haka ya ci gaba da zuwa wajen salma ,bai sake kawo mata zance turo magabata ba ,ita kuma hankalinta kwance ,gani take kamar ya hakurane sai ta k'are karatunta.
Shi kuwa yayanshi da sauran yan uwa shirye shiryen biki suka fara yi dan gani suka idan suka sake zai botsare musu yak'i auren asiya .
Tunda yaje gurinta sau biyu bai kuma zuwaba ,ita kuma bata damu ba tunda tasan ba sonta yakeyi ba.
Bai tashi sanar da salma zancen bikin shiba sai ana saura sati biyu baikin nanma dan kada taji a bakin mutane ne ta ga kamar ya munafurce ta.
Sosai ta shiga tashin hankali dan lokaci da yasanar da ita labarin k'ura mishi ido tayi ko motsi babu sai aikin kallonshi takeyi cikin razani da mad'aukakin mamaki.
Shima kanshi ahmad cikin fargaba na yadda zata d'auki al'amarin da kuma abinda zai biyo baya yake.
Ba karamar dauriya yayi ba wajen yi mata zancen , ita ma kuwa yaci ace ta fahimci hakan ko daga yadda yake in ina wajen fad'a mata maganar.
Bata anakara ba taji hawaye na mata sintiri a kan fiska.
"Subhanallah, salma kuka ? Dan Allah ki daina zaki sa na karaya, kinsanfa nace miki ba san yarinyar nan nakeyi ba ,auren had'ine,
me zaisa ki tada hankalinki, dan Allaj ki daina."
Cikin sarkewar murya tace "Me yasa baka sanar dani tun wuri ba, saida ya rage saura kwanaki kad'an?"
"saboda nima ba'a sanar dani da wuri ba tunda sunsan ina da wacce nakeso ba zab'insu ba."
Ya shararo mata k'arya.
girgiza kanta ta shiga yi "Bazan iya ba ahmad ,bazan iya ba, dole na hakura da soyayyar ka koda zata kashenine."
Cikin firgici yace "Haba salma ,me yasa zakice haka, me yasa zaki yanke wnn hukunci ."
Katse shi tayi da cewa "Saboda danginka basa sona suna da zab'insu, kuma nikam..."
Sai kuma ta fashe da kuka.
"Wa ya fad'a miki basa sonki salma, suna sonki mana tunda ai kinga da kansu suka zo nema min aurenki, da ba don kin nuna bakyaso yanzu bama da yanzu an kusan gama komai ,dan Allah kada ki min haka salma."
Cikin kuka tace "nikam bazan iya ba ahmad kishi ma kad'ai ya isa ya kasheni ,bazan iya ba."
Innalillahi to ce miki nayi ina sonta da zakiyi kishi da ita ,uumm?"
"Ko baka santa ina dai zaka zauna da ita ."
"Ni dai ki bar wnn magana na fad'a miki ba son aurennan nake ba , idan kika ce zaki hakura dani kinaso na mutu kenan."
"Ba wani mutuwa da zakayi ."
Ta fad'a tana jan hanci.
Ganin abinnata da gaskene ya dage da rarrashi ,dakyar ya samu ta bar kukan ,shi ma d'in daurewa yakeyi, ji yake haushin yayanshi da na asiya suna dad'a cika mishi zuciya.
Bai bar gidanba saida yaje har wajen mal.ya sanar dashi maganar aurenshi , snn ya nuna mishi yana kan bakanshi game da maganar su da Salma.
Nasiha sosae mal.ya mishi daga karshe ya mishi add'uar Allah ya bada zaman lafiya da zuri'a d'ayyiba.
Ita ma ummi da kanshi yaje ya mata bayani, addu'ar zaman lafiya ta mishi itama, tana mai tausaya musu dashi da salma.
Tun daga ranar salma take jinta wata iri.
Sosae take jin zafin abin a ranta.
Wai yau Ahmad ne zaiyi aure kuma wata zai aura ba ita ba , gaskiya abin na ci mata tuwa a qwarya.
Ranar tashin hankali.
Ranar da aka d'aura auren ahmad da asiya , daga ahmad d'in har salma cikin tashin hankali suke.
Tun safe yake neman layinta taki d'auka ,qarshema kashewa tayi.
Kwance ta wuni a ranar dan zuciyarta ke mata ciwo.
Dakyar ummi ta sata a gaba taci abinci da rana.
Ganin yadda ta sawa kanta damuwa ,ummi ta sanar da mal.halin da salma takeciki.
Nasiha ya mata mai ratsa jiki, duk yadda ta so ta daure saida tayi kuka.
Daganan ta shige d'akinsu ta kwanta tana jin yadda zuciyarta ke bugawa tamkar zata fito waje.
Har dare bata kuma fitowa ba, bata qara cin wani abinci kuma ba, fati da nusaiba duk sun shiga damuwa, sosae suke tausayawa auntyn tasu.
Har dare yana neman layin baya samu ga rashin kwanciyar hankali, dan duk wata hidima da akeyi kallon abokan shi kawai yakeyi.
Layin nusaiba ya gwada kira,ya kuwa ci sa'a ta shiga.
Bayan sun gaisa ya tambayeta salma.
"Gata kwance tun safe bata jin dad'i."
Abinda tace mishi kenan.
"Taci abinci?"
"Kad'an taci tunda rana bata kuma ci ba."
"Ina zuwa "
Kawai yace ya kashe wayar.
[17/12 06:25] Hajara: *ππIN SO CUTANEππ*
*Fasaha Online writers*
*F.O.W*
*By Anty Rukie (Mmn Abduljalal)*
15.
ππππππ
Ba da jimawa ba sai gashi yana sallama, har cikin gidan ya shigo ya gaisheda ummi snn ya nemi ganin salma.
Kwance take bisa katifar su fati ta lumshe ido tamkar maiyin bacci amma ba barcin take ba.
Muryarshi taji