dark brown colour , d'inkin half jamfa ,kalar kayan ya dad'a haska fatarshi.
Hannayenshi duka biyu ya zura cikin aljihu yana kallon wani wajen .
A hankali ta juya ta kama tafiya tana jin wani irin yanayi a tattare da ita.
Ajiyar zuciya ya sauke snn ya bita da kallo, a ranshi cewa yake ashe da gaske suke cewa saiya yi da gaske zai iya yi mata magana, dole ma ya cire fargabar da yake ji ya mata magana.
Binta yai a baya har ta shiga cikin makarantar.
Yana kallonta ta zare babban hijabin da ke jikinta, 'ya karamar farar hijabi ta bayyana ,tsawonta iya kirji.
Wani irin takaici yaji ya rufe shi.
Yanzu a haka zata tsaga cikin mutanen ajinsu ta shiga.
Yanzu haka kullum take yi ,kuma tayi yawo cikin makarantar kowa yana gane masa ita.
Take yaji wata matsananciyar kishinta lullub'eshi.
Tsaki yaja lokacin da yaga ta shige cikin class.
A bayyane yace "Meye amfanin irin haka."
Ya kuma jan 'yar guntuwar tsaki.
Ya jima tsaye gun yana ta sak'a da warwara daga k'arshe dai ya bar gurin ya tafi sabgoginshi.
Haka ta wuni da tunaninshi da mamakin abinda ya yi d'azu.
Duk abinda takeyi yana manne cikin zuciyarta ,hotonshi ke mata yawo cikin idon zuci.
*** *** ***
Napep ne ya sauketa kusa da masallacin kofar gidansu.
Hanyarta ta shiga gida jikinta ya bata ana kallonta ,hakan ya sa ta d'an dubi gefenta.
Karap suka had'a ido a tare kuma suka kawar da kansu.
"Inna lillahi "tace tana dafe kirjinta dake bugawa da sauri.
Sauri ta kara ta shige cikin gida tana maida numfashi.
Mutuminnan fa yana so ya mata illa.
Dan baisan yadda takeji idan ta ganshi bane da ko da wasa bazai rika zuwa kusa da inda take ba.
Bata ankara ba taji an amshe jakar hanunta ,dubawan da zatayi taga Nusaiba ce tsaye a gabanta tana kallonta tamkar maison jin wani abu daga gareta.
D'aure fiska tayi snn tace "Ya dai."
"Ke zanma wnn tambayar aunty Salma, kin shigo kamar an jefo ki ,snn kuma kika tsaya kika kurawa waje d'aya ido, me ya faru."
Nuna kanta tayi da yatsarta "Ni d'in?"
"Muje ki huta da alama gajiya tayi miki yawa likita."
Nusaiba tace ba tare da ta amsa mata waccar tambayar ba.
Tare suka shiga d'akin ta tub'e uniform ta shiga wanka amma zuciyarta fal tunani.
Bayan fitowarta Faty ta shigo mata da abincinta na rana ,duk da yamma tayi amma ta saba takan d'an tab'a kafin taci na dare.
Amma yau ko sha'awar cin abincin batayi.
Tsura mata ido Nusaiba tayi can tace "Aunty meke damunki sam ban gane miki ba."
Basar da tambayar tayi tace "Ina Ummi Faty."
"Tana d'akinta "tace gami da ficewa dan itakam ba mai yawar magana bace Nusaiba ce mai surutu ,ga san jin kwakwaf.
Ganin da tayi baza ta samu bayanin da takeso gun auntynta ba yasa "Allah ya baki hakuri ."
Ta tashi ta fita itama.
Binta Salma tayi da kallo snn ta d'an murmusa ,a hankali ta ce,"Kusasu."
Jingina tayi da jikin gado taci gaba da tunaninta.
*** *** ***
Tsaye yake yana mamakin kanshi da kanshi.
Wannan wace irin yarinyace haka?
Kwarjininta yayi yawa.
Shawara ya rikayi da zuciyarshi.
Shin ya aika ta fito ne ,ko ya hakura sai gobe.
Dafe kanshi yayi yana magana shi kad'ai.
"kada kuma na aika ta fito na gagara yi mata magana.
Gaskiya da naji kunya yarinya karama."
Shi kad'ai ya kuma cewa kanshi "Ka tabbata zata fito d'inne tukuna."
Murmushi yayi ya kuma cewa tunda na ganki ma yayi ba sai na aika ba.
Shiga motarshi yaja ya tafi zuciyarshi fal tunanin yadda zai b'ullowa al'amarin.
*Mmn Abdul &Noorain.*
[17/12 06:24] Hajara: *ππIN SO CUTANEππ*
*Fasaha Online Writers.*
*F.O.W.*
*By Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*
4.
ππππππ
Halima Auwal .(Mmn Aysha)
Maryam A.I Gital.
Teemerlurv.
Khairat Up .
Mamyn Najma.
Fashuna.
Hawwer (Autar Fasaha.)
Aysha Ali Garkuwa.
Raheenat.
Aisha s.Bayero (Kalar Gayu.)
Rahmat Nalele (Samareen Bana)
Xaynab π€(Rouky Pinky.)
Ummin Weedyan .
Dss.
*Fasaha grp nvl members muna alfahari daku ,Allah ya kara baseera fasaha da zakin hanu.*
**** **** ****
Har Ummi ta shigo d'akin ita a tunaninta ko Salma bata jin dad'ine dan tasan ko yaya in ta dawo sai ta nemeta sun gaisa. Amma yau shiru.
"Ummulu yau kuma lafiya kika zauna cikin d'aki shiru."
Kakaro murmushi tayi snn tace "Lafiya lau Ummi sannu da gida."
"Yauwa sannu ,amma me ya ajiyeki cikin d'aki kikayi shiru haka."
Ta tambaya tana naxarin 'yar tata.
"Ba komai Ummi yau munyi wani practical ne mai wahala, na gaji da yawa ne."
Hhhhhh Practical indeed Aunty Salma."
"Sannu ,Allah ya albarkaci karatun ,yasa ya amfani al'umma."
"Amin Ummina ."
Tace tana murmishi dan sosae take jin dad'in addu'ar da Umminta ke mata ko wace rana.
Kiran sallar Magrib da taji anayi ne ya tayar da ita daga inda take zaune.
Abincin daren ma dan kada Ummi tayi tunanin wani abu yasa ta daurewa taci.
Ga kuma 'yar sa ido Nusaiba.
Haka yau ma ta kwana mafarkinshi .
Har mamakin kanta take ji ,wai ita ce ta fad'a ,ta tsunduma cikin kogin son wani wanda bai furta mata kalmar so ba.
Dauriya kawai takeyi kada a fahimci halin da take ciki har ta shirya ta fita dan tafiya makaranta.
Ko da ta fita sai da ta tsaya ta tsurawa inda ta ganshi jiya ido kamar an ce mata zai b'ullo ta ganshi.
Abinda bata sani ba shine yana daga nesa yana kare mata kallo.
Ganin tsayuwar bazata k'areta da komai ba yasa ta kama hanyar tafiya inda zata samu abin hawa.
Kokari takeyi ta yakice damuwar da ta take ciki.
Shi yasa da ta dawo daga makaranta bata yadda ta zauna ita d'aya ba gudun kar tunani ya addabe ta.
Sa hanu tayi aka karasa aiki da ita kamar yadda ta sabayi kullum.
Washegari ma haka da ta fita take ta tsammanin ko zata ganshi amma shiru ,kwana biyu kenan take ta zuba ido bashi ba labarinshi.
Hakan yasa ta dage lallai sai ta yakiceshi daga zuciyarta,dan wasa wasa tunaninshi yana so ya zame mata matsala.
Kamar yadda ta saba yauma haka ta sauka dadai masallacin kofar gidansu .
Kallon inda ya zame mata kamar jaraba tayi dan duk lokacin data fita sai ta kalli wnn wajen .
Abin mamaki shi ta gani jingine da jikin motarshi ya zuba mata idanu.
Sanye yake cikin shigar yadi mai laushi ,milk colour ,d'inkin tazarce ,kanshi ba hula sai kwantacciyar bakar sumar shi irin ta asalin fulani,wanda ya dad'a k'awata mishi fiskarshi.
Wannan karo murmushi mai narkar da zuciya da gabb'an jiki ya sakar mata.
Tuni kuma jikinta ya amshi sakon .
"Ya Ilahi."
Ta furta tana jin yadda zuciyarta ke bugawa .
Da sassarfa ta shige cikin gidansu tamkar ana hankad'a ta.
Bata yi gigin tsayawa wani tunani ba gudun kada 'yar sa ido ta gano ta .
Da saurinta ta shige d'aki, ta jefa jakarta kan gado snn ta jinginu da jikin bango ta runtse idanunta ,jikinta har rawa rawa takeji yakeyi.
Murmushi ne ya sub'uce mata da ta tuna killer smile d'in da ya sakar mata d'azu.
Dafe kirjinta tayi tace a hankali "Ahmad zaka kashe Ummusalma."
Still idonta a rufe ,ta kuma sakin wani murmushin.
"Akwai good news kenan auntynmu."
Ta tsinkayo 'yar sa idonta tana fad'a.
Saurin bud'e idonta tayi ta watsa su kan Nusaiba ,take kuma ta daidaita nutsuwarta ,ba tare da tayi magana ba ta zare hijabin jikinta snn ta zauna bakin gadonsu tana maida numfashi a hankali.
Binta da kallo Nusaiba keyi can ta tab'e baki tace "Yau kuma da abinda aka dawo kenan."
Ganin bata kula ta ba yasa tayi sum sim ta fice daga d'akin.
Washegari kasancewar weekend ne babu inda Salma taje tana gida suna wankin kayansu dana Ummi dana khalil, dan duk weekend suke had'a kayan su wanke.
Sosae ta sake suna ta zuba hira cikin raha da kannenta dan ta kore duk wata tunanin Ahmad daga zuciyarta, saboda taga Nusaiba gab take da ganota .
Kwance take kan sallaya bayan sallar magrib ,cazbaha rike a hanunta amma kuma ba abinda takeyi dashi sai fiskar Ahmada dake mata gizo , idan ta tuna murmushnsa sai itama ta murmusa.
Ganin abin yaki barinta yasa ta d'an daki kanta tare da cewa "Wai meye haka ne."
Nusaiba da Faty da suke ninke kayan da suka wanke duk suka juyo suka kalleta.
"Me muka yi miki aunty."
Cewar Nusaiba.
Harara ta zabga mata "Ke kuma waya kasa da ke."
"Au da Faty kike , me tayi to."
Faty tayi saurin cewa "Ni kuma?"
Karamar tsaki tayi ta juya musu baya taci gaba da kwanciyarta, tunani ta shigayi ,lallai asirin zuciyarta ya kusa ta tonuwa .
"Me yasa Ahmad ya shiga zuciyarta haka .
Me takeji wnn game dashi."
Ni ko nace Na love ohhh my sisi.
Tsaki ta kuma ja wanda ya tilastawa su Faty kallonta snn suka kalli juna.
Aunty Salma dake hana su yawar tsaki yau ita ke da kanta take ta zabgawa.
Lallai akwai matsala.
*Mmn Abdul &Noorain.*
[17/12 06:24] Hajara: *ππIN SO CUTANEππ*
*Fasaha Online Writers.*
*F.O.W.*
*By Anty Rukie "Mmn Abduljalal.)*
5.
ππππππ
Haka ta karaci kwanciyarta da tunaninta har taji an tada sallar Isha'i snn ta tashi ta bada farali.
Karatunma yanzu idan anayin shi rabi karatu rabi tunani.
Wani lokacin tana cikin karatu sai ta lumshe ido ta kama murmushi ita kad'ai.
Ah lallai abun azeemun.
Ranar sunday da dare bayan sallar isha'i tana kwance ta tashi taci abinci taki firr, ko da Ummi ta matsa mata sai cewa tayi batajin dad'in jikinta , ciwon kai zazzab'i ,ciwon ciki .
Hhhhhh kodai ciwon zuciya Madam Salma.
Ita kanta ta rasa takamammen wanda zata ce yake damunta.
Ummi ta matsa mata dakyar ta tab'a kad'an ta cire hanu ta koma ta kwanta.
Yanzu abinda take ji yafi karfin tunaninta .
Zuciyarta nauyi yake mata, ji take kamar ta fitar ta huta.
Ummi tace ta tashi su tafi asibiti nan kuma tace abin baikai haka ba.
Taje ko chemist ne su Nusaiba su rakata a bata magani nanma ta dad'a narkewa bata son zuwa.
Dama kuma sun san halinta sarai bata son magani bare uwa uba allura.
Dama haka likitocin suke ?π€
Ga tsoron allura su kuma sun iya tsirawa mutane.π
Ko k'arya nayi Mmn al-Mustafa?π
Sallamar yaro ne ya dakatar da Ummi daga fad'an da takewa Salma na kin magani.
Dukansu suka amsa sallamar yaron suna maida hakulansu gareshi.
"Ana sallama da Salma inji wani a waje."
Rass Salma taji gabanta ya fad'i.
A ranta tace Allah yasa Ahmadunta ne.
"Kace batanan ."
Ta tsinkayo Nusaiba tana fad'a, dan tasan amsar da zai samu kenan daga Salma.
Abin mamaki sai sukaji tace a hankali.
"Bari inje in duba inga ko wayene."
Zuruf ta ta mike taje tana zura hijabinta.
"Kai."
Nusaiba ta kwala wa yaron kira dan har ya fara tafiya.
"Kace tana zuwa."
Galala Ummi tayi tana binta da kallon mamaki.
Suma kannenta matan da mazan duk haka abun yake a wajensu.
Salma da lafiyarta ma yaushe ta fita ta saurari wani bare kuma ba lafiya.
Sumi sumi tazo ta wuce su tayi hanyar kofar gida.
Tsayawa tayi tana leka ta kafar gate d'in
"Hmmmmmm" ta sauke doguwar ajiyar zuciya.
Wanda take fata da muradin gani shi ta hango tsaye ya zubawa kofar fitowa ido.
Dafe kirjinta tayi ta lumshe ido tana murmushi .
Wani sanyin dad'i taji yana ratsa ko wani sassa na jikinta.
Minti biyu ta d'auka tsaye a wajen ,tunanin yadda zata fita takeyi tunda bata saba ba.
A hankali take takowa cikin nauyi da kunya .
Shiko gogan ido ya zuba mata kamar ya jawota ta iso da wuri.
Ma k'asa yace "Faruk fito gatanan zuwa."
Tana isa Faruk yana fitowa daga cikin mota.
A kunyace ta gaishesu ba tare da ta d'ago ta kallesuba.
"Malama Salma sai kika ga bak'i ba zato ko?"
Cewar Faruk.
"Hmm " kawai ta iya cewa.
"Laifi kika mana muka biyo ki fa."
"Laifi kuma ?"
Tace a hankali tana mai d'ago kanta.
Caraf suka yi 4 eyes da gogan ,ai a d'ari ta sauk'e kanta.
"Laifi babba ma kuwa malama Salma."
Cewar Faruk.
"Kin sace min zuciyar aboki , kin hana mishi sukuni ,ya gaza samun nutsuwar zuciya. Da fatar za'a taimaka a agaza a maida mishi zuciyarshi ta koma daidai."
Dad'a sunkuyar da kanta tayi tanajin ni'imtacciyar iska na shiga jikinta.
"Salman, fili dominka sai ka kokarta ka amso zuciyarka.
Faruk ya sake cewa .
Kan su ankara har Faruk ya bar wajen.
"Kaji min d'an iska ,zai tafi ya barni da ita."
Ahmad yace a zuciyarshi yana mai bin Faruk da kallo.
Haba Ahmad kamar ba namiji ba?π€
Salman kuma?
Ta maimaita sunan da taji Faruk ya kirashi dashi a ranta.
Ita dai da Ahmad tasanshi to ya akayi yau kuma aka kirashi da Salman.
"Uhm uhm" Ahmad ya d'anyi gyaran murya yana gyara tsayuwarshi tare da daidaita nutsuwarshi.
Yau ga dama ta samu ba sanya.
Kallonta yai still kanta a k'asa ,so take ta d'ago ta kuma kallonshi amma nauyinshi da takeji ya hana ta yin hakan.
Kokarin bud'e baki takeyi tace mishi su shiga daga ciki dan bata saba tsayuwa haka ba ,amma bakinta ya gaza bud'uwa. Gaba d'aya kunya ya gama mamayeta.
*Mmn Abdul &Noorain.*
*Wnn shafin naku ne.*
Reederh Malaysia
Mmn sadeeq
Zaa princess
Foulani cerdia.
[17/12 06:24] Hajara: *ππIN SO CUTANEππ*
*Fasaha Online Writers.*
*F.O.W*
*By Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*
6.
ππππππ
A tsanake yafara gabatar da kanshi snn yaci gaba da bayanin abinda ke tafe dashi.
Nishad'i suke ji dukansu hakan yasa basu gaji da tsayuwar dasukayi a wajen ba.
Fitowar kannenta ne ya ankarar da ita abinda ta aikata ,sai yanzu ma ta tuna cewar bata da lafiya.
Abin al'ajabi kuma ko alamar ciwon bata ji ayanzu.
Sallamar shi tayi da cewar zata shiga gida dare yayi.
Shikam ta biya shi a hakanma tunda ta tsaya ta saurare shi, ga dukkan alamu kuma ya samu karb'uwa duk da ba sakewa tayi da shi sosae ba amma ya fahimci kunya ce ta mata yawa.
Al-amin ne ya zo shigewa yaga abinda ya bashi mamaki ,wato Salma tsaye da wani da gani kuma zance sukeyi .
Baiyi k'asa a gwiwa ba ya nufi inda suke.
Sallama yayiwa Ahmad tare da mika mishi hanu suka gaisa.Mamaki yake da kuma jinjinawa sa'a irin na wnn bawan Allah.
Bayan ya wuce Ahmad ya tambayeta "Wannan shine yayannamu?"
Kai ta gyad'a mishi alamar eh.
Snn ta kuma cewa zata shiga dare nayi.
Sallama sukayi har ta fara tafiya ya dakatar da ita.
"Gimbiya a taimaka min da phone no. Ko zan samu bacci mai dad'i."
Ya fad'a yana zaro wayar shi daga aljihu.
Dawowa tayi ta amshi wayar ta saka no. Snn ta juya ta nufi gida.
Har ta shiga yana tsaye a gun yana kallonta.
Sai bayan ta shiga ne tukun ya nemi layin Faruk yace mishi yazo su tafi.
Rufe kofar gate d'in tayi ta juya zata shige ciki taji an riko hijabinta.
A tsorace ta kalleshi.
"Yayanmu ka bani tsoro wlh."
Ta fad'a a shagwab'e.
"Sorry Ummulun Ummi, wani baban sa'a ne wannan ,har aka fita mishi da darennan."
"Kai yayanmu ai ka bari mu shiga ciki ko?"
Ta fad'a tana yin gaba.
Binta yayi a baya yana cewa "Abinne ya ban mamaki, lallai wannan gaye mai sa'a ne."
Suna shiga ciki ta ga Ummi zaune tare da khalil tana k'ara mishi karatun Qur'ani.
Binta Ummi tayi da kallo ,ita kuma duk kunya ya gama cikata da tuna a yadda ta fita daga gidan daga cewa barin je inga waye.
"Ummulu ya jikin ?"
Ummi ta tambayeta.
"Jiki kuma ?"
Ta mayar wa ummi tambayar.
"Dama bata da lafiya ne Ummi."
Cewar Al-amin.
Kwance take anan tana kukan ciwon kai, ciki, da zazzab'i aka aika kiranta, kaga yanzu har tambayata take wai jiki kuma?"
Cikin zolaya Nusaiba tace "Ita tama manta bata da lafiya fa Ummi."
Al-amin ya cab'e zancen da cewa "Maganin ciwon ne dai yazo."
Yauwa al-amin ka canka dadaiπ
Itakam tuni ta shige d'aki dan kunyar Ummi taji da gaske.
Shi kuwa al-amin sai ya k'ara da cewa "Meye sunan sirikin namu."
"Lucky."
Nusaiba ta bada amsa har da d'aga murya yadda Salma zata jiyo ta.
"Kuma fa hakane."
Al-amin ya fad'a yana dariya."
Cikin farin ciki da annashuwa Ahmad ya koma gida ,yau jinshi yake kamar ya sauke wani kaya mai nauyi, jinshi yake sakayau.
Ji yake tamkar babu kamarshi babu kuma wanda ya kaishi sa'a.
Saida ta gama juyinta kan gadonsu cikin farin ciki snn ta d'au litattafanta ta fara dubawa.
Har su Nusaiba suka shigo karatunta take yi hankali kwance cikin nishad'i ,ta kwana biyu bata karatu mai dad'i irin na yau ba.
Karar wayarta ce ta katse ta , dubawa tayi taga new no.
Jikinta ya bata cewar Ahmad ne ,sbd haka fiskarta d'auke da murmushi ta d'aga wayar.
"Na kira nace miki na isa gida lafiya ne, na kuma miki mu saida safe."
Murmusawa tayi snn tace "Na gode ,mu kwana lafiya."
Ci gaba tayi da karatunta tayi bayan ta ajiye wayar, su Nusaiba duk sun kwanta.
Can tayi nisa da karatunta ta sake jin wayar na ringing.
Dubawa tayi taga shi d'inne.
"Bakiyi barci ba?"
Tambayar da ya jefo mata kenan bayan ya amsa sallamar da ta mishi.
"Yanxu zanyi."
"Me ya hana kiyi tun d'azu."
"karatu nakeyi ."
"Karatu kuma da darennan ,taimakeni dan Allah kiyi baccin yanzu."
"To ai kaima bakayi yi baccin ba."
"Jikina ne ya bani bakiyi ba shi yasa na kasa yi."
"Hmm, Mu kwan lafiya ."
Tace tare da kashe wayar kamar ita ta kira.
*Mmn Abdul &Noorain.*
[17/12 06:24] Hajara: *ππIN SO CUTANEππ*
*Fasaha Online Writers.*
*F.O.W*
*By Anty Rukie (Mmn Abduljalal.)*
7.
ππππππ
Kamar yadda yace hakan kuwa tayi dan rufe littafan tayi ta adana su a ma'ajiyarsu.
Alwala taje ta d'auro ta yi addu'oin da ta saba yi kafin ta kwanta.
Soyayya mai karfi ya shiga tsakaninsu har ya zamanto basa iya yin kwana d'aya basu sa juna a idanunsu ba.
Sau d'aya ya tab'ayin tafiya ta harkar kasuwancinsa .
Hhh wnn lokacin sun ji a jikinsu dukansu biyu.
Kwana biyar kacal yayi amma ji suke kamar sun shekara basu had'u ba, duk da cewa basu d'aukan lokaci mai tsawo sai sunyi waya.
Daga nan kuma yace bazai kuma tafiya irin haka ba ,koma me ya taso zai tura yaranshi .
waya kuma ako da yaushe cikin yinshi suke kamar ba ita ke jin haushin Nusaiba idan ta ishe ta da amsa waya ba.
Snn kuma duk dare sai yayi ta kiranta yace ta kwanta ta huta baya so ta wahalar mishi da kanta ,baya kuma barinta sai ya tabbata ta kwantan.
Karatu kam yanzu tab'a shi dai ake sama sama ba kamar yadda ta keyi da ba.
Ita kanta ta rasa abinda yasa take biye mishi yake hana ta isasshen karatu duk son da takewa karatun kuwa. Da gaske zuciyarta ke mishi biyayya akan duk abinda yakeso ko da bata so hakan ba.
Zaune suke k'asar bishiyar mangoro dake cikin gidansu suna shan iska.
Ummi, Fati, sai kuma Salma , Ummi da Fati tsintar shinkafa sukeyi ,itako Salma jan lalle take zana wa yatsunta.
Nusaiba dake cikin d'aki tana gyara ne ta fito rike da wayar Salma ta zo ta kara mata a kunnenta .
Da hanu ta tambayeta wayene.
Kamar tana jira tace "Waye kuma banda Lucky."
Sallama tayi ya amsa ,suka gaisa tana satar kallon Ummi , Ummi ko kallonta batayiba ,idonta na kan trayn shinkafarta.
Bayan sun gaisa tace mishi yayi hakuri aiki take yi zuwa anjima zata kirashi.
Cire wayar Nusaiba tayi daga kunnen Salma ta nemi waje ta zauna.
"Yauwa aunty Salma ya kamata ki d'an takawa yayannan namu birki hakanan.
Kiran yana yawa ,atleast da dare kam ya bar ki kiyi karatu ,amma bini bini kira ,gaskiya