x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 7 - MINISTER ASHRAF

  • 18001 words
  • 21000 words
  • Out of 42082 words

Category: Romance Story +18

Views 266

22 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
wallahil azim kome zaki yau akwatunan nan bazasu fice daga wannan gidan ba".

Wani banzan kallo Laraba tai mata tana sakin dariya tace "zamu fita dashi zuwa gidan yayana Alhaji Tajuddeen idan isa ke 'yar iskar kanki ce dan Allah kizo ki tareni ko ki hana fita dashi zan nuna miki cewa kura ba farkar kare bace zaki gane kin min rashin kunya bari Alhaji Mukhtar d'in ya dawo gidan ai Ina nan har gobe sai an yita ta kare kinsan wace ni bana d'aukar raini" juyawa tai tana kallon Hajiya Hindu da Saudat wadanda suka sake baki suna mata kallon ikon Allah tace "muje Hajiya idan mun kai ta nan zamu dawo kowa ba gidansa zai wuce ba saina tabbatarwa da Alhaji Mukhtar wannan abinda ya faru muje" tana fad'in haka suka fara fita da akwatunan zuwa harabar gida Hajiya Salmah tana tsaye ba'kin ciki ya gama cika mata ciki har suka gama d'ebewa tana jin tashi motoci guda da bud'e gate da ficewar wata iriyar zazafar ba'kar ajiyar zuciya ta sau'ke tare da zama jagwaf akan kujera tana dafe kanta da hannu biyu jin juwa na d'ibanta zama kusa da ita Hajiya Suwaiba tai tana dafe kafad'arta tace.

"Hajiya karki damu ki daina damun kanki kar kiji komai bata Isa maganganun da suka fad'a miki suyi tasiri ba dan wallahi nima zan taya ki ya'ki da fad'a na ganin cewa Sultan bai auri wannan yarinyar ba naga alamar wadannan dangin mijin naki basu da mutunci ki dage idan sun dawo shima Alhaji Mukhtar d'in ya dawo kada ki bari su samu ke6ancewa ta fad'a mata karya da gaskiya ki tsaya ayi komai a gabanki karta jawo auren ki ya mutu dan naga wannan matar da kukai musayar yawu da ita har wani zaro harshe take ko mayya ce oho".

D'agowa Hajiya Salmah tai tana cewa "ai wallahi Suwaiba ko baki fad'a ba bazan kyale suba domin Nima ba kanwar lasa bace nafi karfin dukkan su hud'un zasu dawo su same ni" cikin zuga Hajiya Suwaiba tace "tabbas karki yarda ki nuna musu tsantsan fushin ki karki yarda ni bari dama yana shigowa ko tare dasu ko shi kadai kawai ki fashe masa da kuka sannan ki 'kuga musu sharri a gurin kice haka kawai suka saka ki gaba sukai miki tas ta uwa ta uba babu lefin tsaye bana zaune ni bari na tafi karsu dawo su sameni hayaniya ta tashi nasan zasu iya yimin sharrin nice na zuga ki tunda naga ba 'yan arziki bane" ta fad'a tana mi'kewa tayi mata sallama har harabar gida ta rakata suka sake sabuwar tsewa tana sake 'kulla mata abubuwa daga baya ta shiga motarta tabar gidan Hajiya Salmah kuma ta koma ciki tsaye tay a parlor ta kasa zama tayi nan tayi can gabadaya zufa ce ke tsattsafo mata a jiki har mamaki ne ya kamata meyasa take zufa sai kace mara gaskiya shiru tai cikin dagulewar lissafi jira take Rasheedat ta taso daga school ta aiketa gashi Amrat tana bedroom bata jin dad'i huuuuuuhh ta sau'ke ajiyar zuciya tare da nufar kofar part d'in su Amrat danta gano yaya jikin nata ta tashi ko har yanzun tana kwance.

***✍️✍️✍️Duk abinda ya faru a gidan Alhaji Mukhtar saida Laraba ta mayarwa Alhaji Tajuddeen komai domin ta fahimci kamar har yanxu Hajiya Salmah bata sauko ta sauya halinta ba badan dai Sultan ya riga ya gama gidansa ba tare zai zauna da mahaifiyar saba da tace a fasa auren Nabilah dashi domin maganar gaskiya ta hango wata irin 'kiyayya da Hajiya Salmah takewa Nabilah tunda har aka zo wannan lokacin bata daina ba tofa baxata daina d'in ba da ace zasu yarda toda data basu shawara kawai Nabilah tayi ha'kuri da Sultan ta auri wani duniya tana da fad'i ba dole sai ta auri Sultan ta zauna dashi ne zata iya rayuwa ba a'a duk gidan wanda Allah ya kaita zatai rayuwar farin ciki me cike da 'yanci bata da yadda zatai ta hana auren amma xatayi ta addu'a idan har babu alkhairi tsakanin Nabilah da Sultan Allah ya rana abun ta ruwan sanyi idan kuma 'kaddarar Nabilah ce auren Sultan nan ma tana ro'kon Allah yasa ta iya cinye jarrabawar ta.

Har bayan sallar isha suna gidan Hajiya Fatima suna ta hira anan Laraba ta kira Alhaji Mukhtar yaxo ya dauke su ya mayar dasu gida ya dad'e acan gidan Laraban suna zance da mijinta bai bai ankara har lokacin ya fita sai kusan karfe sha d'aya ya dawo gida Hajiya Salmah harta gaji da zaman jiransa a palor ta koma bedroom barci ma ya fara d'aukarta kamar a mafarki yaji tsayawar motarsa wani irin wuntsulowa tai daga kan bed tayo kasa da sauri ta mi'ke jiki na 6ari ta suri hijab ta fita a bedroom d'in hijab d'in na hannunta bata samu damar sakawa ba saida ta kusa shiga part d'in sa sannan tasa tare da banka kofa ta shiga ko arzikin sallama babu yana zaune bayan ya cire kaya sai ganinta yayi ta fad'o masa cikin bedroom tana huci baiyi mamaki ba tunda Laraba tayi masa bayani yasan komai kawai ya shareta ko d'agowa baiyi ya kalleta ba balle tasa ran zaiyi mata magana ganin haka yasa tace.

"Alhaji yanxu tsakani da Allah abinda Laraba tai min ta kyauta irin cin mutumcin da tazo har gidana tayi min tayi daidai kenan wallahi badan darajarka ba yau batai kwanan gidan ta sai nasa an rufe min ita akan me zata zo har cikin gidan aure na ta tada min husuma kawai ta gayyato wasu mata 'yan bariki masu wari haya'ki sunzo sun cika min gida to wallahi bazan yarda ba nice na haifi Sultan ba ita ba dan haka bata da iko dashi sai abinda nace ka samu 'yar uwar ka kaja mata kunne ba ruwanta da lamarina zance nane da d'ana baza'ai min dole ba ha'kuri na yazo karshe ta gama kaini bango ka taka mata burki kafin nad'au matakin da kowa bazai ji dad'in saba".

Kamar gunki takewa magana haka Alhaji Mukhtar yai bala'in d'auke kai daga saitin ta ya manna mata hauka wanda taji matukar zafi da ciwon abun ta fad'a masa maimakon yayi magana saiya baiwa iska ajiyarta? Kuka ta fashe dashi tana cewa.

"Gaskiya Alhaji kana da abun mamaki wanne irin son Kaine da rashin adalci wannan ka nuna min dan kawai ita jininka ce ni Kuma barenka ce ka fad'a maka tazo har gida tayi min zagi na tsamar nama har kakanni na saida ta ambato ta saboda batasan inda mutumci yake dama na sani tunda dad'ewa Laraba bata kaunata kuma nafi 'karfin ta haka zata ganni ta barni tunda naga bakin ka d'aya da ita gashi tazo tayi min abinda ranta yake so na fad'a maka kayi banza dani ba matsala ta faru ta 'kare tunda har Allah yasa ka sani nan gaba xan dau'ki doka a hannu na wallahi tallahi duk 'yar matar data sake xuwa gidan nan ta kawo min raini saina 6are mata kai mu zuba ni dasu d'an halak ka fasa" tana gama fad'in haka fuuuuu ta juya kamar zata tashi sama ta fice daga bedroom d'in kai Alhaji Mukhtar ya jinjina cike da tsananin mamakin maganganun rashin arzikin da Hajiya Salmah ta iya tsayawa tserere a kansa kamar zata rufeshi da duka ta fad'a lallai ya jinjinawa rashin hankali irin nata amma yana daidai da zamaninta zaiyi maganin gaba-gaba dai zatai dana sani indai bata canxa halinta ba zai bata mamaki zanyi abinda bata ta'ba tunani ba.


✍️Mrs Äl'ämëëñ Ähmäd çë mai tambarin yma dutse new world sabuwar duniya kuzo kuyi kallo dad'i yana Jigawa garin ilmi garin addini zaman lafiya Jigawa.


💃Da anyi kiran Jigawa har wani tunkaro nake yi ana maganar Jigawa har wani canza salo nakeyi Jigawa jiharmu ce abar faharin muce an sanmu akan zaman lafiya ba'a sanmu da rigima.🌹


Tnks for ur supports 🔥 nagode sosai masoya godiya sosai sosai godiya 🌺🥀 ana tare 🤝 insha Allah YÚSRÃHMS CE.

8~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Hamidinah.


Mrs Äl'ämëëñ Ähmäd çë 😘
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹


TYPING📲 FRI, JAN3/25 8:25pm YUSRAH MUSA ABUBAKAR🤘💓.


💕MINISTER ASHRAF💕


WHATSAPP NO:+234 8160983083
yusrahmusa65@gmail.com


ÀÑÑÙRÌ WRITER'S ASSOCIATION 💫
Home of hospitality and harmony gidan kar'bar mutane hannu biyu da zaman lafiya ÀÑÑÙRÌ haske le'ka gidan kowa koda ma'kiya na kallon ka ramin kura sai'ya'yan ta.


We love our NABI SAW no success without him he's the light of every darkness he's the answer to every question he's the mirror of our life he've no limits ya rasulullah muna sonka fiye darai da iyaye da dukiya.


•••••••••••••••••••••••
•••••••••••••••••••••••••••••••••••
•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••


9~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Salihinah.


💦Yüsëëñ Sïr Äl-ämëëñ çë💦
PG____09&10
Abu kamar wasa tun Hajiya Salmah tana ganin kamar bada gaske bane abun bazai faru ba har taga a zahiri dai ga bikin nan ya tunkaro sosai har 'yan uwanta na nesa sun fara kiranta a waya suna sanar mata cewa suna nan suna shirye shiryen tahowa damuwa ta gama damunta batai komai ba fuska babu fara'a haka gabadaya ta sauya zaman gidan ko gaisuwar Sultan bata amsawa balle Alhaji Mukhtar tayi masa yaji ta daina zuwa part d'insa Amrat kuwa da taga murna take saida tayi Mata shegen duka harda fasa mata baki Rasheedat ce me sake tunzurata tana zugata cewa har numbar wayar Nabilah ta kar'ba kullum sai sunyi waya itadai Amrat batace komai ba ta bari Allah ya saka Mata sharrin da Rasheedat d'in tayi mata akan haka Alhaji Mukhtar yayi mugun 6ata Mata ranta yayi mata tas har saida taji dama bata daki Amrat ba haka ta d'au fushi da ita kamar abokiyar gabarta ta dawo ba sosai take kulata ba da'kyar take amsa gaisuwarta ba yabo ba fallasa Hajiya Salmah ta zama haka take zaman gidan bata shirin komai balle Rasheedat da take jin kamar ta kama da wuta tsabar ba'kin cikin Sultan ba Hajeer zai aura ba hatta lallen da Amrat tayi lalle da saloon akan haka saida sukai fada karshe suka raba d'akin kwana.

Haka a 6angaren amarya Nabilah ma shiri take sosai kullum suna tare da Husnah tana taya ta wasu abubuwan bata komawa gida sai dare itace ta tayata suka raba invitation card da komai a lokacin bikin ya rage saura kwana goma sha biyar Nabilah tana gidan wata qanwar Mamin ta acan ake mata gyaran jiki me kyau da kayayyaki a 'kan'kanin lokaci duk kamaninta ya sauya ta sake wani irin kyau da haske acan akai kiran me lalle tayi mata ba'ki da ja akai mata saloon batai kitso ba tabar gashinta a sake ta tajeshi yayi kyau ya zuba akan jikinta ba'ki wulik yana she'ki saura sati d'aya d'aurin aure da dare Hajiya Hauwa ta dawo da ita gida domin akwai wasu abubuwan daya kamata su tattauna tsakanin ta da mahaifanta.

°°°°Washe gari Nabilah tana bedroom a kwance har kusan sha biyu na rana bata tashi ba tun bayan sallar asuba data koma barci bata farka ba bud'o kofa Hajiya Fatima tai ganin har lokacin Nabilan barci take yasa ta karaso tana yaye bargon tsaye tai cike da mamaki take kallon Nabilah ganin yadda ta qara kyau da haske kamar ba ita ba gashi ta d'au lalle da saloon duk kamaninta sun 6ace sauke ajiyar zuciya tai tana sake qare mata kallo kafin tad'an girgiza ta tana cewa.

"Nabilah Nabilah ki tashi haka".

Ta fad'a tana sake girgiza ta da'kyar Nabilah ta bud'e ido tana kallon Hajiya Fatima da idonta wanda yake cike da barci tace "Mami lafiya"? Kaita d'aga mata "eh lafiya ki tashi haka rana tayi baki breakfast ba kuma gashi Daddyn ma yazo yana nemanki" tashi zaune Nabilah tai tana cewa "Daddy Ash"? Ri'ke ha6a Hajiya Fatima tai tana kallon Nabilah wacce ta mi'ke tana d'aukar wani siririn mayafi ta yafa a kanta tace "Nabilah dama baki daina cewa Daddy Ash d'in nan ba"? Nabilah dake shirin fita jin tambayar da Hajiya Fatima tayi mata yasa tayi dariya tana cewa "ayya Mami na riga na saba saidai ha'kuri" ta fad'a tana bud'e kofa fita Hajiya Fatima tai ita kuma tabi bayanta.

A parlon Alhaji Tajuddeen ta samesu suna ta hira da dariya irin ta abokai da sallama ta shiga tana zama a kasan carpet tace.

"barka da zuwa Daddy ina kwana" kallonta Alhaji Ashraf yayi yana cewa.

"lafiya kalau Baby fatan kin tashi lafiya"?

"Eh Daddy ina lafiya".

"Masha Allah Baby lokaci yayi an kusa tafiya d'aki ko? Muma kwanan nan zamu girma zamu fara tara jikanu" ya fad'a yana juyawa ya kalli Alhaji Tajuddeen wanda shi kuma Nabilah yake kallo yace "amma dai abokina ni za'a baiwa wali ko"? Juyo da kallonsa kan Alhaji Ashraf yayi yana jinjina kai yace "eh me zai hana insha Allahu fatana dai Allah ya sanya alkhairi cikin lamarin ya shige mana gaba".

"Amin, Baby me kike so na kawo miki a matsayina na uba wacce kyautar kike so nayi miki wacce bazaki manta da ita ba"? Alhaji Ashraf ya tambaye ta daidai ta d'ago suka had'a ido lokaci guda zuciyar kowannan su ta buga da mugun 'karfi da sauri Nabilah ta d'auke idanunta tare da d'an dafe'kirji a hankali ta runtse ido tana cewa.

"Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un me yake faruwa haka"?.

Shima Alhaji Ashraf a nata 6angaren wani irin abu yaji da yanayi me wuyar fassara haka kawai yaji wani abu ya soki zuciyarsa wanda baisan ko menene kuma baisan me hakan yake nufi ba sai sabon kallo da zuba ido dayai mata batare daya ankara ba hankalin Alhaji Tajuddeen baya kansu yana ga TV baisan me suke ko a wanne hali suke ba tunda magana suke a tsakanin su shi bai shafeshi saida yaji sunyi shiru sannan ya juyo yana cewa.

"Uba da 'ya harkun gama maganar ne naji kunyi shiru"?.

Sauke numfashi Alhaji Ashraf yayi da'kyar cikin son fisge abinda yake neman hanshi sukuni ya samu ya janye idonsa daga kan Nabilah yana d'an girgiza kai yace "eh mun gama saidai bata fad'a min kyautar dazan bata ba amma ni nasan abinda zan bata wanda ya dace da ita zan kawo mata gifts guda biyu wanda ba wanda yayi zato" ya karasa maganar da murmushi akan fuskarsa da fara'a Alhaji Tajuddeen yace "alhamdulillah Allah ya baka iko abokina"

"Amin insha Allahu zan cika alkawari ai nina d'auka"..

"Ok Nabilah tashi kije dama kiran kenan Ashraf ne yake son ganinki aiki ya hanashi samun lokaci ya jima baku had'u ba shiyasa da Mamin ki tace kina barci nace ta taso ki jeki" to Nabilah tace tana mi'kewa ta fita haka nan taji lokaci d'aya jikinta ya mutu kamar wanda akai mata allurar kasala ko wacce rashin lafiya ke shirin kamata hatta yanayin kuzarinta da tafiyar jikinta ta sauya bata tsaya a parlor ba ta kama hanyar shiga part d'inta Hajiya Fatima data fito tana waya ganin inda ta nufa yasa ta kalli dinning yadda yake haka yake da alama Nabilah ko kallon wurin batai ba dakatar da ita tayi da cewa.

"Nabilah ina zuwa kizo kiyi breakfast man zaki koma bedroom".

Juyowa Nabilah tai muryarta a sanyaye ba kamar koda yaushe ba tace "ina zuwa Mami brush zan yi yanzu zan dawo" ok kawai Hajiya Fatima tace tana samu guri a d'aya daga cikin kyawawan manyan white and blue cushions d'in dake zagaye a parlon tana sake danna kiran Hajiya Zainab qawarta.

Tana cikin wayar Nabilah ta dawo ta sauya har kayan jikinta zuwa wasu kayan kanti 'kanana masu kyau tasa qaramin talhat bule black Hajiya Fatima na zaune tazo ta wuce ta karasa dinning tare da zama ta fara bubbud'a dishes dake gurin ganin akwai faten wake da bushasshan kifi yasa tayi serving d'insa ta zauna ta fara ci Hajiya Fatima tana gefe can nesa da ita amma duk abinda takeyi hankalinta nakai sai taga kamar bata cikin walwala akwai wani abu dake damunta so take yi ta gama wayar nan ta tambaye ta.

POV ALHAJI ASHRAF
Tunda ya dawo gida ya rasa me yake masa dad'i daya rufe ido Nabilah kadai yake gani da sauri zai bud'e a zabure yana maimaita innalillahi wa Inna ilaihi raji'un wannan wanne irin abun kunya ne wai meke damuna ne meyasa daga ganin Nabilah zanji hankali ya tashi me ya jawo hakan? Ya tambayi zuciyarshi amma baida amsa shiru yayi cikin rashin sanin madafa yanzu wazai tunkara da wannan tambayar wazai tara ya fad'a masa abinda yaji ya same shi a lokaci d'aya mene fassarar hakan maganar gaskiya yana son sani shidai ya sani bai d'au Nabilah matsayin komai ba sai 'yarsa bayan haka bayajin akwai wani abu game dashi a kanta amma ya kasa yarda da iya wannan hujjar daya samu tabbas akwai dalili, to kodai na fad'a son 'yar abokina batare dana ankara ba? Yaji zuciyarsa ta sharta masa haka wanda a razane ya bud'e idonsa dake rufe yana mi'kewa tsaya ya goya hannunsa a baya ya soma zaga parlon daga nan yayi can a fili ya soma cewa.

"Wacce irin 'kaddara ce wannan na rasa wacce zuciya ta zata kamu da ciwon so sai 'yar abokina? Subahanallahi wannan abun kunyar har ina Allah kasa ba haka zuciyata take raya min ba" ya fad'a yana cike hular dake kansa gashinsa ya ji'ke shakaf da zufa tsabar rashin nutsuwar da yake ciki d'ora hannunsa biyu tayi tun daga kan goshinsa har zuwa fuskarsa ya shafa yana sau'ke zazzafan numfashi me kama da zafin wuta tabbas yau ya shiga matsala da yasan idan yaga Nabilah wani abu zai gifta a zuciyarsa daya ha'kura da 'kara ganinta har karshen rayuwarsa baisan wanne irin tsautsayi ne ya fad'a masa ba a yau wacce irin damuwa ce take tunkaro shi taya zai samu mafita Alhaji Tajuddeen shine abokin shawarar sa baiga ta yadda za'ai yaje masa da wannan maganar ba a yanzu haka yana ji a ransa zai iya aure sa6anin da can daya sa a ransa cewa ba lallai yayi ba abun tambayar anan shine wanne dalilin ne yasa lokaci guda yaji hankalinsa ya karkata ga yayi auren bayan da ba haka yake ba ko maganar mace baiso ayi masa tun shekaru ashirin da biyar daya wuce lokacin da Alhaji Tajuddeen ya auri Hajiya Fatima yayita matsa masa shima ya nemi mace yayi aure
End Ads