x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 2 - MINISTER ASHRAF

  • 3001 words
  • 6000 words
  • Out of 42082 words

Category: Romance Story +18

Views 256

22 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
farko da zata bashi tace.

"Sir Ahmad nifa Ina da wanda zan aura dan Allah ka rabu dani" ta fad'a tana sake had'e fuska zuba mata ido yayi yana kallon ta har kallon ya wuce misali ganin kawai lokaci zai 6ata mata tace "zan tafi" zata juya ya dakatar da ita "Nabilah" tsayawa tai a fusace ta juyo zatai magana ya girgiza mata Kai yana kara matsowa inda take kamar me shirin ri'ke mata hannu da sauri ta sake matsawa ya kuma binta karo na biyu ganin idan tai sake masa zai iya taba mata jiki yasa kamar walkiya ta juya fiiiii kafin ya farga har tayi nisa yaso yabita a baya amma saiya tsaya yana hard'e hannunsa ya zuba mata ido harta 'kule kafin yayi murmushi yana jinjina kai a ransa yana ji yana son yarinyar nan da aure da zata amince masa amma zai lalla6ata idan ta'ki hummm that mean war kenan dan wallahi bazai iya ha'kura da ita ba dole zaisan yadda zaiyi ko bai aureta ba zaiyi kokari yaga ya samu abinda yake so a wajenta juyawa yayi shima yana barin gurin.

Husnah tana tsaye a bayan block d'in tana jiran Nabilah sai kuma ta ganta ta 6ullo a fusace tana sauri gyaran murya tai mata wanda yasa ta juyo da sauri tana kallon ta tare da sauke ajiyar zuciya ta waiga baya ko Sir Ahmad ya biyota karasowa Husnah tai fuskarta ba walwala tace.

"Wai nikam dan Allah me Sir Ahmad d'in nan yake nufi bake da yake takurawa Beelat ni kaina na fara gajiya da wannan aikin banzar nasa kullum bazai bari kiyi abun arziki ba idan munzo school daga Kira sai Kira tsabar bulkumanci da sakalci Allah daga yau bazaki sake zuwa inda yake ba kome zaiyi domin naga d'anyar kan nasa ya wuce inda nake tunani haba jama'a" tsaki Nabilah tai tana cewa.

"Share sa muje kawai indai yana da zuciya daga yau bazai sake kulani ba wallahi so yake yayi asarar takardar aikinsa domin matukar yaci gaba da matsa min zan hadashi da Daddy kawai ya dauka min mataki" Kai Husnah ta d'aga tana cewa "basai yaci gaba da matsa miki lamba ba kawai ki sanar masa a d'au mataki idan ma za'a bashi transfer lokacinsa baiyi ba saiya sani aikinsa zai 6ata muje kawai kar a shiga mana exam d'in ma muna nan" wucewa sukai kamar sun sani kuwa suna zuwa daidai lokacin shiga ko zama basuyi ba suka zarce cikin class d'insu,,,basu fito daga jarrabawar ba sai kusan karfe d'aya da rabi a ranar suna fitowa kowa ya fara alwala suna tafiya sukai sallah su Nabilah sun jima a gurin sallar domin saida la'asar tazo sukayi sannan suka taso Kai tsaye gurin motarsu suka nufa saida sukai sallama Nabilah harta bud'e mota zata shiga ta tsaya tana cewa.

"Husnah dan Allah karki manta gobe ki fito da wuri tunda naji kince gidan kanwar Momyn zaki tafi" Kai Husnah ta d'aga tana cewa "ok sai Allah ya kaimu gobe ki gaida mun da Mum sosai Beelat" "ok bye" Nabilah ta fad'a tana shiga motarta itama saida ta Husnah ta wuce sannan tabi bayanta ita ta nufi Yalwawa Nabilah Kuma ta nufi Yadi ko a hanya tunanin yadda zata 6ullowa da al'amarin Sir Ähmäd takeyi amma ta bari a ranta tunda yau ta fad'a masa ya rabu da ita idan yaji shikenan idan baiji ba koda za'a 6ata masa paper saita fad'awa Daddy domin ya d'aukar mata mataki irin su Sir Ahmad ba mutanen da za'a zubawa ido bane domin shi mutum ne d'anye kuma ga6o ta tabbata matukar ta share bata fad'a anyi maganinsa ba uhmm tana tsoron abinda zai faru a gaba Allah ma ya kiyaye.

Horn tayi a kofar gate d'insu me gadin dake zaune ta ciki ya tashi ya bud'e mata ta shiga sakamakon tana sa rai maybe zata fita da yamma yasa bata Kai motarta cikin rumfar parking d'in motoci ta barta a baya baya ta kasheta tana fitowa ta shiga ciki tsit parlon kamar ba kowa sakamakon Hajiya Fatima tana bedroom kuma TV ba'a kunne yake ba shiyasa parlon yad'au wani irin shiru shirun ma har yayi waya part d'inta ta wuce domin haka kawai taji jikinta na mata ciwo saida ta had'a ruwa me zafi tayi wanka ta sake sabon shiri cikin dinkin wata kyakkyawar atamfa anyi mata dinkin buba yasha stone yanata walwala ta kashe d'auri ta dau'ki agogo ta saka da takalmi harda d'an kunne da sarka kamar wacce zatai ba'ko ta feshe jikinta da daddad'an turare sannan ta dau'ki phone d'inta ta dawo parlor ganin kiran Husnah yasa tai murmushi tasan abinda zata tambaye ta amma sakamakon yanxu Hajiya Fatima ta fito tana parlon yasa bata bi kiran ba ta bari saita koma part d'inta yadda xatafi yin wayar a sake karasowa tai tana zama ta kalli Hajiya Fatima dake binta sa kallo tace.

"Barka da gida Mami na fatan kin wuni lafiya"?.

Kai Hajiya Fatima ta d'aga tana cewa "lafiya kalau na wuni ya gajiyar school ya exam"? "Alhamdulillah Mami ina Daddy ko bai dawo ba"?.

"A'a ya dawo da wuri ma wanka yayi dai ya fita a gidan" ok kawai Nabilah tace tana d'age kafafunta daga kan carpet ta maida kan kujera ta tan'kwashe su bata sake cewa komai ba hankalinta nakan waya tana chatting d'agowa Hajiya Fatima tai tana cewa "amma Nabilah bakici abinci ba tun breakfast d'in safe shine kin dawo d'inma basaki mayar da hankali kici ba sai ulcer ta kama ki" murmushi Nabilah tai tana girgiza kai tace.

"Ai Mami ulcer bazata ta'ba kama niba".

Da mamaki Hajiya Fatima tace "meyasa bazata kamaki ba saboda da tana tsoron ki"? Dariya Nabilah tai tana cewa "a'a saboda 'kawata ce mun riga mun saba" "uhmmm" kawai shine abinda Hajiya Fatima tace tana kallon Nabilan wacce da gaske bazata ci abincin ba ta sake gyara zama tana mayar da hankalinta kan secreen d'in wayar tace.

"Nabilah d'azu Daddyn ki yazo yana nemanki nace kina school amma ya aje Miki kyautar daya kawo miki gashi can akan dinning banma d'auke sa nasa a fridge ba sai kinzo ki gani da kanki yaso kin dawo kun gaisa har yace zai jira ki taso sai kuma akai kiransa a waya shine suka fita tare da Daddyn naki".

Murmushi Nabilah tai tana d'agowa kalle ta domin tunda taji tace Daddyn ta tasan wa take nufi aje wayar tai cikin zumud'i ta mi'ke tana zuwa ta d'auko kyakkyawar ledar dake she'kin tabuntaka balle kumà abinda yake ciki ta dawo tana zama har lokacin da murmushi akan fuskarta ganin kayayyakin da suke ciki yasa ta sake fad'ad'a murmushin ta cikin walwala tace.

"Wai Mami kina nufin Daddy Ash yazo gidan nan yau? Wayyo gashi bana nan".

Zaro ido Hajiya Fatima tai tana kallon ta da mamaki tace "Daddy Ash kuma Nabilah abokin uban naki guda kike kira da Ash"? Dariya Nabilah tai tana cewa "to Mami ba sunan shi bane"?.

"A'a ba sunan shi bane tunda ba Ashraf kika ce ba shi kuma sunansa kenan".

"Ai Mami da Ash da Ashraf duk d'aya ne".

"A gurinki ba amma ba d'aya bane tunda shifa ba yaro bane da saurayi ne saiki kirashi da hakan amma ubanki guda"?.

"To Mami bakiji akace dakai wasa da baban wani gara kayi da naka ba shiyasa nayi hakan".

"Au haba kenan yanzu zaki iya kiran naki tsohon da Daddy Taj ko? Tunda ai shima Tajuddeen yake".

Hhhh dariya Nabilah tai tana fiffito da kayan zallar chocolates ne kala kala sai yogurts da ice cream da tsadaddun biscuits humm Hajiya Fatima bata bud'a taga mene a ciki ba amma tasan za'a rina kallon Nabilah wacce ta 6are wata babbar chocolate tana sha tayi ta d'an girgiza kai tana cewa "wai mutum ya girma shekara ashirin da yan kai amma saboda babu qani yasa suke shagwa'ba ki yanzu irin wannan kayan za'ki haka kamar 'yar yaye"? Dariya Nabilah tai tana mi'ko mata guda d'aya tace "Mami kema gashi ki sha wadannan chocolates d'in na dabam ne bana yara bane" kai Hajiya Fatima ta girgiza "a'a nikam bazan sha zaki ba kema da kike wadansu abubuwan ganin ba wani sai kene da kina da qani ko qanwa baza kiyi wani abun ba koda kud'i" murmushi Nabilah tai tana hade kayayyakin ta mayar dasu cikin ledar tace.

"Shiyasa ya Sultan yake cewa wai Daddy's dina sune suka 6ata ni dashan abubuwa shiyasa ban damu da abinci ba shikam bazai yarda da wannan shaye shayen kayan za'kin ba dole ya koya min cin abinci".

Jin abinda Nabilan tace yasa Hajiya Fatima cews "oh nina manta ma d'azu da safe kunyi sa6ani kina tafiya school sai gashi ya shigo gidan yana neman ki nace masa kin tafiya makaranta shima a lokacin hospital zai tafi dana fad'a masa haka sai kawai ya juya ya fita ban sani ba ko yaje"?.

Kai Nabilah ta girgiza tana cewa "A yau ya Sultan yazo gidan nan Mami"? ta fad'a da surprise a fuskarta domin jiya da sukai waya ya fad'a mata zaiyi tafiya yau da safe ya akai kuma ya fasa d'an shiru tayi cikin nazari zuwa wani lokaci ta d'ago tana kallon Hajiya Fatima kamar zatai magana sai kuma ta fasa tana mi'kewa ta shige part d'inta ta d'auko hijab ta dawo parlon da mamaki Hajiya Fatima tace "Nabilah ina zuwa haka daga dawowar ki a school ko hutawa baki yiba balle kici abinci"? Kai Nabilah ta girgiza "no Mami na 'koshi zanje gidansu Daddy Mukhtar ne naji Yaya Sultan ya fasa tafiyar".

"Amma me yasa bazaki kirashi a waya ba dole sai kinje kinsan ba jininku ne ya had'u da yaran gidan ba musamman Rasheedat harda ita kanta matar gidan Hajiya Salmahn to me zakije kiyo".

"To ai Mami ba gurin ta zanje ko gurin yaran gidan ba ni gurin ya Sultan zanje".

"Ok gurin Sultan d'in da zakije inace a gidan yake kuma d'anta ne ko asibitin doctor Sambon zaki bishi"? Hajiya Fatima ta fad'a tana qare mata kallo jiran amsa kai Nabilah ta girgiza tana cewa "a'a ba hospital zan bishi ba asalin gidansu zanje ba dad'ewa zanyi ba yanzu zan dawo".

"Humm Nabilah kenan ni harna rasa bakin magana wai da gaske ke a zuciyar ki son Sultan kike bayan kina kallon irin zaman da mahaifiyar sa Hajiya Salmah keyi damu ga fitsara gurin 'ya'yanta amma ke duk hakan yayi miki a haka kike son kije gidan matsayin surukarta bayan kinsan har gobe bata goyon bayan Sultan akan neman aurenki da yake yi haba Nabilah ina kika Kai tunanin ki ya kamata ki tsaya guri d'aya kiyi nazarin abinda kike son aikataw....................

Bata karasa maganar ba akai kiranta a waya dan haka ta mi'ke tana shiga part d'inta domin ta amsa kiran a nutse ba kamar tana parlon ba shiru Nabilah tai bayan wucewar Hajiya Fatima ta fad'a cikin tunani ta sani har gobe Hajiya Salmah bata son ala'kar ta da d'anta Sultan amma tunda ba Sultan d'in ne ya 'kita ba itama bazata watsa masa qasa a ido ba zata aureshi kodan samun farin cikin su ita dashi ai tasan duk tsiya ba gida d'aya zai zauna da Hajiya Salmahn ba balle yawan fitina ta ri'ka tashi, sauke numfashi tana mi'kewa ta dau'ki ledar chocolates da key d'in motarta ta shige part d'inta domin ta samu tayi taga magriba tayi gara taje tayi sallah yau yadda take jinta a gajiyen nan barci zatai da wuri ko jikin nata ta samu ya daina ciwon inta tashi.

***
Da dare har tayi shirin barci ta kwanta ko wayarta bata kashe ba tunanin ko Sultan zai kira kwanciyar ta da mintuna kad'an har barcin ya fara fisgarta kiran Sultan ya shigo da sauri ta bud'e ido tana tashi zaune ta d'auka ganin numbar wanda take tunani yasa saida taiwa secreen d'in wayar kiss kamar Sultan d'in take gani kafin ta d'aga tare da fara ido tana kashe murya tace.

"Hello ya Sultan barka da dare".

Shima a nasa 6angaren yana bedroom d'insa a kwance ya lullu'ba da bargo yana rungume da pillow ya sake gyara kwanciyarsa sosai yana murmushi yace.

"Ya kike Baby na"?.

"Ina lafiya ya Sultan ashe bakai barci ba naga goma ta kusa"?.

"Eh taya kike tunanin zan iya yin barci bayan a yau ban sanya ki cikin idanuwan da zasu barcin ba tunda safe na wuni da kewar ki gashi ban samu na dawo gida da wuri ba dana dawo daga hospital Ina sauri bayan nayi wanka da sallah ko tsayawa cin abinci banyi ba domin kar dare yayi na samu nazo gurinki sai kuma nayi ba'kon bazata abokina Sameer ne yazo min ziyara tun daga Miyetti shiyasa ban samu nazo ba amma ya kike fatan kin wuni lafiya"?.

Kaita d'aga kamar yana ganinta tace "lafiya kalau gaskiya nayi kewarka ya Sultan" ta fad'a a shagwa'be domin ba lefi ta riga data saba bata magana d'aya biyu saita saka shagwa'ba a ciki.

"Nima nayi kewar ki Baby gashi yanzu idanuwa na suna son ganinki ba hali shiyasa nake fatan da naje Indian nan na dawo zanyiwa Daddy magana kawai a d'aura min aure dake ki dawo kusa dani sai hankali na yafi kwanciya dama kullum cikin kishi da fargaba nake kwana da'kyar nake iya barci idan na tuna kullum sai kin fita waje kinje school samari suna ganinki suna kalle mun ke kada wani banzan yaji kinyi masa ya tareki da maganar so ko ya biyoki gidan ku hummm wallahi saina 6alla masa 'kafa na zubar masa da ha'kora" .


Hhhhh dariya Nabilah tai tana cewa "kai Yaya Sultan akwai kishi ji yadda kake magana da fad'a Kuma a misali na tambaye ka a bisa tsautsayi saika ganni tare da wani saurayin ina hira dashi ya zaka yi"?.

Jin tambayar datai masa yasa ya zabura har yana cilli da bargon daya lullu'ba ya soma girgiza kai tare da dafe saitin zuciyarsa dake bugawa yace "nooo Nabilah please dan Allah karki kara fad'ar irin haka idan ba so kike zuciyata ta buga ba" zaro ido tai tana cewa.

"kai ya Sultan ya zuciyarka ta buga kuma ni nayi ya? Kasan irin son da nake yi maka kuwa bana jin zan iya rayuwa idan batare dakai ba".

Kaiya jinjina yana sakin murmushin da saida ta jishi a kunnen ta yace "yauwa ko kefa Baby nagode sosai yanzu ki kwanta kiyi barcinki saboda kada ki makara gobe idan Allah ya tashe mu lafiya maybe kafin na wuce hospital zan biyo ta gidan naku ki kula min da kanki".

"Ok ya Sultan goodnight".

"Shikenan mu kwana lafiya Baby".

Sauke ajiyar zuciya tai bayan ya katse Kiran sai yanxu taji wani irin dad'i da iska mai sanyi tana ratsata sakamakon wayar da sukai amma da ta hana kanta sukuni lokaci guda ta koma kamar mara lafiya ita a zatonta ko laifi ma tayi masa domin ta sanshi da zuciya shiyasa duk abinda tasan zai 6ata masa rai bata yinsa ko menene qara gyara kwanciya tai tana sake rungumar pillow da murmushi akan fuskarta ta rufe ido tun tana tunani har barci ya d'auketa.

✨✨✨✨Saboda tasa abun a ranta ko barcin kirki batai ba sai mafarki iri iri har asuba sannan ta tashi duk jikinta ma ciwo yake da'kyar take takawa kamar mara lafiya ta shiga toilet tayo alwala ta fito tana saka kaya da hijab tai sallah bata tashi a gurin ba ta dau'ki al qur'ani ta bud'e ta fara karantawa a bayyane cikin zazza'kar muryarta me dad'in sauraro kafin gari yayi haske saida tayi izu biyar sannan ta rufe tayi addu'a ta shafa ta mi'ke tana mayar dashi inda ta d'auko kafin ta cire hijab d'in da kayan ta d'aura towel ta shiga wanka shaf shaf ta fito sauri take ta ta kammala shirinta sakamakon ta kwana da cewa Sultan zaizo kafin ya wuce asibiti haka ta tsara kwalliya mai kyau ta d'au wankan ala tsine uwar me 'karya hatta takalmin data saka a ranar yasan yau zatai muhimmin ba'ko d'aukar handbag d'inta tayi tana fitowa daga part d'inta tasan ba kowa a parlor yanzu idan ma ta fita sai iya 'yan aiki dan haka part d'in Daddynta ta shiga suna zaune tare da Hajiya Fatima suna zance ta shiga da sallama duk binta suke da kallo cikin mamaki yadda tayi kyau ta fito d'as da ita zama tai bayan ta gaisar dasu Alhaji Tajuddeen dahar lokacin yake kallon d'iyar tasa ya sauke numfashi tare da godewa Allah sannan yace.

"Nabilah yau ko gasar kyau ake yi a makarantar taku ne? Naga kin d'au wanka kamar zakije gano shugaban qasa"?.

Murmushi Nabilah tana kallon Hajiya Fatima dake mata kallon tasan saboda dawa tai wannan wankan tace "a'a Daddy zanyi ba'ko ne" da mamaki Alhaji Tajuddeen ya sake dubanta yana cewa "ba'ko kuma wanne iri Nabilah da wannan sassafen"? "Eh Daddy Yaya Sultan ne zaizo" ta fad'a tana d'agowa ta kallo Hajiya Fatima wacce ta d'an girgiza kai dama tasan sai shi murmushi Alhaji Tajuddeen yayi yana kallon ta yace "Ok yayi kyau Allah ya taimaka"..

"Amin" Nabilah tace tana mi'kewa zata fita tace "na tafi school Daddy da Mami" ta fad'a tana shirin fita dakatar da ita Alhaji Tajuddeen yayi da cewa "amma bakiyi breakfast ba Nabilah zaki tafi ki jira su dafa Miki ko indomie ce kici kar ulcer ta kama ki" kaita d'aga "to Daddy bari naje kitchen d'in" saida ta bud'e kofa ta fita Hajiya Fatima ta kalli Alhaji Tajuddeen tana cewa.

"Amma Alhaji nikam sai nake ganin abun nan kamar akwai damuwa a cikinsa fa ni Kuma bana son tashin hankali" da alamun tambaya Alhaji Tajuddeen ya kalleta yana cewa "abun me"? "Auren Sultan da Nabilah har yanzu bana jin farin ciki akan haka kuma ba kowa bane sila sai mahaifiyar shi lefin Hajiya Salmah ne domin tun farko itace ta 6ata abun Kuma nasan har gobe tana nan akan bakanta tunda ta rantse ta sake rantsewa ba karo d'aya ba cewa indai itace ta haifi Sultan a cikinta bazata bari ya auri Nabilah ba na rasa me yake damunta".

"Oh akan haka ne hankalinki ya tashi dan ta fad'i wannan aiko tayi 'karya zan nuna mata kuskuren ta a fili ta hanyar aurawa Sultan Nabilah naga wanda zai hana kaf danginta idan basu taru basu isa su juya min ra'ayi ba balle ita maganar rantsuwa kuma tayi a banza idan
End Ads