Da sauri ta girgiza kai tana cewa "a'a wallahi ko kulashi bana yi idan yayi min magana ko Husnah zatai min sheda wallahi ba ruwana dashi kawai yace yana sona na fad'a masa akwai wanda zan aura ya rabu dashi ya'ki".
"Ok mubar wannan maganar fad'a min da yazo kofar gidan nan d'in bayan kin fita meya faru me yace miki sannan taya kike tunanin zan yarda bayan baki kwana a gida ba jiya a Ina kika kwana"?.
Jikin Nabilah ne ya dau'ki sabuwar rawa da tsuma tsoro yana lullu'be ta da'kyar tace "dana fita cewa yayi na shiga motarsa muje ya sai mun wedding gown nace masa a'a na gode sai yace akwai maganar da zamuyi dashi idan munje can yanzu zan dawo dake nan ma ban amince masa ba...................
Shiru tai tare da d'agowa tana kallon Alhaji Tajuddeen wanda ya d'aga kai yana cewa "Ina jinki fad'a min meya faru" kuka Nabilah ta saki cikin damuwa da takaici ta soma fad'a masa dukkan abinda ya faru tsakanin ta da Sir Ahmad da kuma zuwan da Husnah tai ta d'auketa zuwa gidansu ta d'ora da cewa "dan Allah Daddy ka yafe ni wallahi tsoron irin tashin hankalin da zan zo gida na tarar yasa na kasa dawowa gida jiya ban kwana a gidansu Husnah da wata niyya ba sannan ban amince sir Ahmad ya yaudare ni ya samu nasara a kaina ba kayi hakuri Daddy" ta karasa maganar tana kneeldown a gabansa tare da had'e hannuwanta guri d'aya alamar neman yafiya kai Alhaji Tajuddeen ya jinjina yana cewa.
"Kin tabbata haka ne abinda ya faru tsakanin ku babu son ranki a ciki dole ya d'auke ki"?.
"Eh Daddy wallahi babu yarda ta".
'Ok shikenan a wacce anguwa yake da zama"?.
Kai Nabilah ta girgiza tana cewa "ban sani ba Daddy kawai a iya makaranta nake ganinsa Kuma dama tare damu zai bar school d'in shima zai koma state dinsut".
"Ba d'an nan garin bane"?.
"Eh ba anan haka yake ba yare ne shi sannan bansan ranar dazai tafi ba ko yau ne".
Mi'kewa Alhaji Tajuddeen yayi jin abinda tace ya kalli Mukhtar yana cewa "tashi muje zan shigar da report a baza jami'an tsaro a yau d'in nan sai an nemo shi ba state d'insu ba ko ramin gyare yake wallahi saina fito muje" mi'kewa shima Alhaji Mukhtar d'in yayi suna fita yayim da Nabilah ta tashi daga inda take dur'kushe ta karasa tare da fad'awa jikin Hajiya Fatima ta fashe da sabon kuka shafa bayanta Hajiya Fatima keyi batare datai magana ba domin bata da abun cewa kanta ya gama kullewa da wannan al'amarin fatan ta Allah yasa ayi nasarar kama wannan lecturer d'in gaskiya ta bayyana a fahimci komai.
📝✍️🌻Mrs Äl'ämëëñ Ähmäd çë.
See you tomorrow morning tnks for ur supports 🔥 be with me at always my lover's.
Ya cikar cikakku alhamdu ka dayantu kai kad'ai Allah yake so Annabi 💕 yabo zanyiwa baba gashi Kuma ban iya ba bansan Yaya ake ba dan Wanda kaiwa maraba rannan a fadarka rabba yazam madubin ka rabba yarda inmar nasan kana so ya dad'e.
🌹Baya goya marayu mekai dakai ya rayu dakai kan kowa ya wayu dan Kai ka koyar da gayu abinda bai yuwu ya yuwu madarar kyau sai wanda muke so Annabi SAW 💓💯.
10~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Raki'inah.
***
TYPING📲SUN, JAN5/25 10:20AM YUSRAH MUSA ABUBAKAR🤘💯.
💕MÏÑÏSTËR ÄSHRÄF💕
ANNURI WRITER'S ASSOCIATION 💫 home of hospitality and harmony gidan kar'bar mutane hannu biyu da zaman lafiya ÀÑÑÙRÌ haske le'ka gidan kowa koda ma'kiya na kallon ka ramin kura sai'ya'yan ta.
In the name of Allah the must benefits and the must merciful ALLAH THE MOST HIGH DOESN'T SLEEP ALLAH THE MOST HIGH IS PURE HE ACCEPT ONLY WHAT IS PURE we love our NABI MUHAMMAD S.A.W💓 (May the blessings and the peace☮️ of Allah be upon him Amin🙏🙏🙏.
11~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Sajidinah.
💦Yüsëëñ Sïr Äl-ämëëñ çë💦
PG____11&12
Humm duk nisan turin da akaiwa lilo zaije ya dawo inda yake manya maganin karagar 'kasa tun ba'aje ko'ina ba a ranar komai ya kammala dukiya me yawa Alhaji Tajuddeen ya bayar domin yayi matukar fusata da abinda sukaiwa Nabilah tuni aka baza jami'an tsaro wanda gabadaya gari ya zama an rufe lokaci guda yanayin tafiye tafiye ababen hawa suka canza duk abinda ake yi Sir Ahmad bai sani ba yana gidansa inda ya kama haya yana holewa tare da Nazzi Danual ya shiga a gigice yana sanar dashi abinda ke faruwa tare da bashi shawarar a yau suyi gaggawar bakin garin nan kafin hukuma ta damke su sun ta'bo 'yar manya sun d'auko damin daba saukewa, in hankalin Sir Ahmad yayi dubu ya tashi jiki na rawa ya mi'ke ya soma hada kaya yacewa Danual da Nazzi suma suje yanzun nan su d'ebo kayansu subar garin tsautsayi ne yasa bai tafi ba harya d'auko trolley yakai cikin motarsa ya fitar mayar yana mayar dashi ciki yace sai gobe zai tafi maybe tausayin za'a kamashi ne.
Da yake ita 'karya fure take bata 'ya'ya idan har baka da alhakin mutum ya cutar dakai Allah yana saka maka cikin gaggawa tare da Nazzi da Danual suka d'ebo trolleys d'insu suma kamar zasu tashi sama da yake akwai 'yar tafiya tsakanin su yasa suka taho a 'kafa a hanya suna tafe suke sake maimata abinda ya faru a jiyan caraf a kunnen wani jami'i cikin azama ba zato suka ga yasha gabansu tare da nuna musu bindiga alamar su d'aga hannaye a firgice suke kallonsa tare da tsoron Allah yasa baiji maganar da suke ba zubar da akwatunan sukai suna she'kawa a guje rufa musu baya yayi da yake an sanar ko'ina gari fal yake da ma'aikata tuni suka dam'ke su a gurin tare da sanya musu ankwa jami'in daya ji akan me suke maganar yace.
"Waye d'ayan da kuke magana a kansa"?.
Shiru Danual yayi cike da taurin kai alamar bazai fad'a ba marin da jami'in ya kifa masa har saida bakinsa ya fashe jini na fita cikin tsawa yace "zaka fad'a ko saina tashi kanka da bullet"? Ya fad'a yana d'ora masa bindiga a saman kai tare da d'ana kunamar kamar zai saki a rud'e Danual yace.
"Zan fad'a kayi hakuri zan fada" dan Allah".
Janye bindigar yayi yana mi'kewa yace ina jinka yanxu kayi magana fad'a min".
"Ba laifi na bane wani ne yasaka mu aikin kud'i ya biya mu".
"Waye ya saka ku ina yake"?.
"Yana gidan sa".
"Ina ne gidansa"?.
"Wajen can haka ne gaba da nan".
"Ka tabbata yanzu yana gidansa za'a sameshi"?...
"Eh yana gida jiran mu yake".
"Ok kira mana shi".
D'ago hannu Danual yayi yana nuna musu ankwar da suka d'aura masa yace "bazan iya daukowa ba tana aljihun wando na".
Jin abinda yace yasa jami'in zura hannu a cikin aljihun Danual ya d'auko waya yace "mene securityn"? Fada masa yayi ya rubuta bayan ta bud'e ya fad'a masa number ya kira tana shiga Sir Ahmad ya d'aga yana cewa "hello Danual me kake har yanzu baku taho mun tafi ba"?.
Datse kiran jami'in yayi yana kallon Danual yai qasa da murya yana cewa "ka amsa masa idan ya kira kuma kada ka kuskura ka nuna masa mun kamaku kuna hannun mu kayi masa magana a nutse kai Danual ya d'aga yana cewa to daidai kiran Sir Ahmad ya shiga karawa Danual a saitin bakinshi yayi bayan ya d'aga daga can 6angaren sir Ahmad yace.
"Hello Danual ina jiranku fa a ina kuka tsaya ne harna fito da mota waje kuyi sauri mana".
Kai Danual ya jinjina yana cewa "am kayan namu ne yayi yawa bazamu iya kawowa ba kazo da motar saika d'auke mu" ok kawai Sir Ahmad yace yana katse kiran wayar jami'in ya mayar masa yana kallon sauran 'yan uwansa yana cewa "yanxu abinda zai faru kowa ya samu guri ya 6uya ku kasance cikin shiri amma kada kuyi harbi" amsa masa sukai tare da bazuwa a gurin kowa ya la6e agu me duhu can hasken fitilar motar Sir Ahmad ya tunkaro gurin ganin motocin jami'an tsaro kusan guda uku a gurin yasa jikinsa ya bashi akwai wata matsala karya kwana yayi da sauri ya juya yana baiwa motar giya aguje jami'an suka fara fitowa tare dabin bayansa da gudu suka fara harbin tayar motar tuni iskar tayun suka sace amma bai daina gudu ba har saida yaje ya daki bishiya kan motar ya mokad'e sannan ya tsaya a bisa dolensa cikin azama ya bud'e murfin motar ya fito daidai sun karaso zai zuba da gudu suka ri'ke shi batare da sunce masa komai ba suka saka masa ankwa shima cikin tsaurin rai da karfin hali yace.
"Yalla'bai me nayi muku"?.
Wani irin kallo ya watsa masa yana hankad'a 'keyarsa suka fara tafiya zuwa gurin motocin su yace "ban sani ba ka idan munje zaka ji abinda kai" shiru Sir Ahmad yayi bai iya cewa komai ba sai gabansa daketa dukan d'ari d'ari cike da fargabar ya zaiyi ya kare kansa yanzu hankalinsa bai sake tashi ba saida aka jefa shi cikin mota yaga Danual da Nazzi saidai ba damar yayi musu magana yana ji yana gani aka tafi dasu zuwa bayan kanta aka rufe,, a daren akai Kiran Alhaji Tajuddeen aka sanar dashi an samu wadanda ake zargin da saka hannunsu a sharrin da akaiwa Nabilah kasa nutsuwa Alhaji Tajuddeen yayi a lokacin ji yake bazai iya bari sai gari ya waye ba a take ya tafi Saida yaje yaga Sir Ahmad da Danual da Nazzi ji yayi wani irin 6acin rai ya rufeshi yaso ace anyi musu shegen duka tun a daren amma wani tunani yaxo masa tunda ba'ai bincike ba Bari ya barwa gobe.
Gida ya koma amma bai iya runtsawa ba har nisan dare ya gani tsabar 'kaguwar da yayi gari ya waye asubar fari ya fita masallaci bayan anyi sallah bai dawo gida ba tare da Alhaji Mukhtar da Alhaji Ashraf suka tafi gurin wancan case d'in.
Alhaji Ashraf yafi kowa fusata da tozarcin da sukaiwa Nabilah shine ya bada umarnin a nad'a musu mugun dukan da azaba zata saka su duma wuya ta farfad'o dasu sannan baice a sassauta musu ba ko mutuwa zasuyi kafin azo kan dalilin kama sun da akai.
Danual akwai bala'in tsoro tun dukan bai gama tsara masa jiki ba ganin ana neman hallaka shi ga tsawa da barazana shine ya fara fad'ar gaskiyar aikin da Sir Ahmad ya sashi yayi masa Nazzi ma ta fad'i cewa ba Nabilah bace wacce akai wannan abun da ita itace fuskar Nabilah kawai tasa domin biyanta Sir Ahmad yayi.
Amma abun daya baiwa kowa mamaki da aka tambayi Sir Ahmad sai yayi tsalle ya dire yace sam sharri sukai masa bai bai sasu aiki ba baisan komai ba yin duniya ya furta cewa shine yaiwa Nabilah haka amma ya'ki amsawa yace shi bashi bane an d'auki kusan sati biyu ana yiwa Sir Ahmad tambayoyi da Kuma shedu 'karara hatta Husnah da Nabilah saida suka zo sannan suka fadi abinda ya faru yace ina shifa bai aikata ba abu kamar wasa harya tafi wata guda sir Ahmad yana kan bakarsa shi baisan komai ba karshen wasan da yaga azaba da mutuwa 'kiri-'kiri ana nemam hallaka shi da'kyar aka samu ya bud'e baki ya fad'i gaskiyar lamarin da yadda komai ya faru tun daga ranar daya fara ganinta har zuwa ranar da yazo kofar gidan su Nabilan da sigar yaudara ya d'auketa zaije ya keta mata mutuncinta kuma bata amince ba ta fice a d'akin bayan ya cire mata hijab......................
Yana gamawa ko baki bai rufe ba Alhaji Tajuddeen ya kifa masa mari tare da mi'kewa ya dam'ki wuyansa idonsa jawur ya soma aika masa naushi cikin tsananin 6acin rai ganin xaiyi masa illa yasa da'kyar Alhaji Mukhtar da Alhaji Ashraf suka 6am6are shi jikinsa na sewa yake kokarin 'kwacewa amma basu sake ba domin idan ransa ya 6aci yana da wuyar dawowa daidai kawai janyeshi sukai suna fita dashi daga gurin sir Ahmad kam yana yar6e a kasa ya kasa tashi tsabar nuna da jikinsa yayi da azabar duka sai zuwa akai aka daukeshi ana mayar dashi aka rufe Alhaji Tajuddeen bai bar ofishin ba saida ya tabbatar an gama komai ya yanki takardar sammaci wacce zasu shiga kotu alkali ya yanke musu hukunci sannan suka koma gida.
Ganin irin ba'kar azabar da Sir Ahmad yasha yasa da aka zo gaban alkali gudun abinda zai sake faruwa dashi ana tambayarsa gaskiyar mene abinda ya faru tsakanin sa da Nabilah ya fad'a komai baiyi 'karya ba sannan aka tambayi Nabilah haka ne tace eh Danual da Nazzi ma suka fad'i iya aikin dayasa su sukai masa ya biyasu kud'i me yawa nan ma aka tambayi Sir Ahmad haka ne gaskiyar abinda ya faru yace eh haka ne yayi kuskure amma dan Allah a yafe shi a take Alhaji Tajuddeen yace babu wanda zai yafeshi idan ma yana tunanin Nabilah ce zata yafe masa to yayi hauka dan wallahi baiga dalilin da zaisa Nabilah ta yafewa Sir Ahmad ba dole sai an yanke masa hukunci kowa haka yake cewa tabbas ayi masa hukunci shine daidai yanxu idan aka sakeshi ba'a dau mataki a kansa ba an bashi damar yaje ya sake aikatawa wata budurwar haka ko wani a gefe wanda yaga abinda Sir Ahmad d'in yayi Kuma ba'a d'au mataki ba yaji sha'awa shima ya aikata gara a bashi hukunci daidai da lefinsa bashi ba wani ma saiya kiyaye daga shi har Nazzi da Danual babu wanda aka sake dukka aka kaisu gidan maza su zauna daidai da lefinsu da kuma rubutacciyar takarda me nuni da cewa ba Nabilah ba Sir Ahmad har abada kotu tayi musu iyaka sannan a gaban jama'a kowa da kowa aka wanke Nabilah daga zargin da ake mata na watsi da tarbiyyar da aka bata sai lokacin hankalinta ya dawo jikinta abinda ta dad'e batai ba wato murmushi a ranar shi tayi ta rungume Alhaji Tajuddeen da kukanta na murna tana yi masa godiya sannan taiwa Husnah godiya itama wacce ta tsaya tsayin daka har saida ta kawo karshen zaluncin da Sir Ahmad yayi mata tun daga wannan ranar shikenan aka rufe babin Sir Ahmad Nabilah ta d'auke hankalinta a gurin ta manta da abinda ya faru tsakanin su gudun ta ri'ka tunawa tana d'orawa kanta damuwa hakan baida amfani.
Duk wannan gwagwarmaya da ake ta kashe case d'in Nabilah Sultan baice 'kala ba kuma koda wasa bata sake ganinsa ba tun daga ranar kamar wanda yabar garin haka yanzu ya dawo babu inda yake zuwa saboda damuwa da d'acin dake cin ransa daga hospital sai gida kullum hatta magana ya daina yi ba sosai ba.
Yauma kamar kullum da yake weekend ne baije ko'ina ba tunda gari ya waye har kusa sha biyu na rana ko breakfast da yake fita yayi yau baije yayi d'in ba yana kwance idonsa na kallon pop d'in d'akin bud'e kofar bedroom d'in akai ana shigowa amma bai d'ago ba balle yasan waye ya shigo.
Tsaye Hajiya Salmah tayi a bakin kofar shiga tana kallon yadda gaba daya yabi ya rame akan abinda ya faru ji tai takaici ya rufeta 'bacin rai ya baibaye mata zuciya karasowa tayi tana zuwa kansa ta tsaya tana cewa "Sultan yau ko breakfast baka fita kayi ba saboda da tunanin wannan tsinanniyar yar iskan yarinyar ko? wai me yake son mayar da kanka akan wata banzar mace mara kamun Kai kana ganin fa yadda ta bayyanar da tsiraicinta ga wani tsinannan idan har ka aureta mene ribarka taya kake zaton zaka manta da haka?.
Ganin har lokacin yayi shiru kuma bai motsa ba yasa Hajiya Salmah fitar da huci me turiri tana jinjina kai a ranta tace "amma gaskiya su Alhaji Tajuddeen sun cuceni babu abinda zance saidai Allah ya isa tsakani na dasu indai dalilin wannan bankad'addiyar yarinyar tasa ka zama haka ni fatana ma Allah yasa kada hawan jini ya kamaka" a fili kuma juyawa tai zata fita daga bedroom d'in ranta a 'bace har takai bakin 'kofa ta dakata batare data juyo ba tace.
"mahaifin ka na nemanka nasan akan maganar wannan 'yar iskan fitsararriyar yarinyar ne Nabilah maybe zaice kayi hakuri ne ka d'au kaddara baza'a fasa ba a rufawa juna asiri hum'um to wallahi bari kaji kada ka yarda ka amince idan kuwa ka yarda sai mun raba hanya dakai wallahi tallahi kaji na rantse ko? Karka amsa zaka aureta domin naji yana cewa "komai ya wuce wai wani anyi bincike an gane sharri aka had'a mata wani saurayi ne lecturern su a school ya biya wasu kud'i aka 6ata mata suna ba ita bace wata arniya ce tasa fuskarta humm ma'karyatan banza duk da haka ni dama dan ka nace ne amma wannan yarinyar Nabilah batai min ba bata cikin kalar 'yan matan da nake so su zama surukai na ka gane muje yanxu ni dama haka nake so kullum fatana Allah ya kawo silar wani tsautsayi ya gifta wanda xai hana yuwuwar auren nan Ashe zanga wannan ranar gashi Allah ya kawo mu burina ya cika dan ko mutuwa zatai bazaka aureta ba wallahi kaji na rantse muje" ta fad'a tana yin gaba mikewa yayi yana saka takalminsa yabi bayanta fuska a had'e babu walwala har suka je parlor inda Alhaji Mukhtar yake zaune su Rasheedat yasa su tashi su bar parlon zasuyi magana saida ya rage su uku ya kalli Sultan yana cewa.
"Abdul-azeez kasan abubuwan da suka faru damu kwanan nan na damuwa da tashin hankali da fituttunun da sukai ta afkuwa wanda yasa gabadaya duniyar ta canza mana cikin 'kanqanin lokaci sakamakon kallon da mutane suka koma yi mana akan Nabilah da wani 6ata garin yaro yaso yi mata sharri kai kasan komai tunda kaima ya baka waya ka kunna ka gani to amma yanxu alhamdulillah domin hausawa sunce ciki indai gaskiya wuka bata huda shi kamar yadda ya faru