bana so ka auri wacce Umma tace domin Hajeer school d'in mu d'aya na santa sosai kuma kyakkyawa ce itama mukam ita meke so hum'um Nabilan banz........................
Tana rufe baki taji saukar zazzafan mari a fuskarta wanda yasa a gigice ta saki 'kara tana mi'kewa tsaye da gudu ta shige part d'insu a fusace Sultan yabi bayanta domin ya tsani raini shi mutum ne me zuciya tunda har ta taso masa da 6acin rai Hajiya Salmah ko tayi magana saiya kai kandaminsa da gudu Rasheedat ta shiga bedroom d'insu tana kuka domin Marin yayi mugun shigarta gashi da zafin hannu humm batasan ya biyota ba sai gani tayi ya banko 'kofa ya shigo 'kara ta fasa tana d'ora hannunta aka cikin kuka tace "dan Allah Yaya Sultan kayi ha'kur............
Bai bari ta karasa bashi ha'kurin ba domin bashi yazo nema ba idan da zai iya ha'kura tofa da bai biyota ba belt d'in dake d'aure a wandonsa ya zare cikin 6acin ran da ya riga ya taso masa akan lamarin ya soma shimfid'a mata a jikinta ihu take sosai tana bashi ha'kuri ko sauraron ta baiyi Hajiya Salmah dake parlor ranta yayi mugun 'baci amma ko matsawa batai ba jin ihun Rasheedat ya'ki 'karewa yasa 'kanwarta Amrat ta mi'ke tana nufar bedroom d'in gabadaya ya hargitsa musu d'akin tsayawa tai a ba'kin kofa tana kallonsu ba damar da zata bashi ha'kuri domin ganin yadda ya d'ame da dukkan karfin sa yake sakarwa Rasheedat belt d'in sauke ajiyar zuciya tai tana karasa shiga da karfi tace.
"YAYA SULTAN".
Da sauri ya juyo had'e hannuwanta Amrat tai tana cewa "dan Allah Yaya Sultan kayi hakuri dan Allah ka 'kyale ta dan girman Allah insha Allahu Allah bazai hanaka za'bin ranka ba bansan meyasa Nabilah bata yiwa Umma da Aunty Rasheedat ba amma nikam a nawa 6angaren bana jin komai kuma ina sonta domin koba komai 'yar uwata ce dan Allah kayi ha'kuri ka daina dukanta" ta karasa maganar tana dur'kusawa a kasa ganin haka da jin furucinta yasa Sultan bai sake kallon koda inda Rasheedat take kwance tana rusa kukan azaba ba sai belt d'insa daya mayar yana fita daga bedroom din mi'kewa Amrat tai tana zuwa inda Rasheedat ke kwance ta d'agota tare da zaunar da ita a bakin gado ta shiga toilet ta d'ebo ruwan d'umi da karamin towel ta dawo a kusa da ita ta zauna tana d'und'uma mata duk inda taga shacin belt d'in ya fito domin ansha allura da mai kamar jiki ya tsage jini ya fito saida ta gama ta mayar towel d'in ta dawo daidai Rasheedat ta mi'ke tana jan 'kafa ta nufi gaban wardrobe kai Amrat ta girgiza tare da cewa.
"Aunty Rasheedat kin gani ko kiga yadda kika jawowa kanki matsala kema kinsan Yaya Sultan baya d'aukar wargi meyasa zaki shiga cikin maganar su ki bari dai Umman data isa dashi ta fad'a masa amma ke mene naki a ciki ba shine yaga yana sonta ba zai zauna da ita meye matsalar ki da hakan idan ke batai Miki ba shi kuma yana son kayarsa saiki rabu dashi ya auri za'bin ransa ba gara Nabilan ba akan ita wancan Hajeer d'in da kike cewa kin santa school d'inku daya idan kin santa kinsan halinta ne"? Jin abinda Amrat take fad'a yasa Rasheedat ta sakar mata wata uwar zazzafar harara batare datai magana ba ta'be baki Amrat tai tana ci gaba "yanzu tsaya nayi miki misali a kanki yadda kike son Mustapha sai ace ki rabu dashi ko Kuma ace mahaifiyar sa bata sonki kamar yadda Umma bata son Nabilah zaki ji dad'i haba Aunty Rasheedat kema ki tuna fa gidan wani zaki tafi ba'a gidanku zaki tabbata ba kuma bakisan halin dangin mijin da zaki aura ba ko tanan bai kamata ki ri'ka sukan Nabilah ba a rubuce yake abinda kaisai anyi maka shin ke bakya tsoron hakan wacce irin rayuwa ce wannan"?.
A fusace Rasheedat ta juyo tana cewa "fita min a d'aki dan bura ubanki idan nayi auren kije kisa ayi min abinda nayi mtwwww" taja dogon tsuka tana sauya kayan jikinta tare da nufar gado ta kwanta tana lullu'ba domin lokaci guda taji wani irin sanyi me yanayi da zazza'bi nason kamata taji ya fara rufeta jikinta ya dau'ki zafi Amrat tana tsaye tana kallon ta bata sake cewa komai ba Kuma bata fita daga d'akin ba sai gaban mirror data nufa tana zama tare da d'aukar wani book da yake aje ta fara karantawa.
Hajiya Salmah tana zaune Sultan ya fito zai fice wata uwar harara ta sakar masa cike da jin haushin dukan da yayiwa Rasheedat akan Nabilah kuma tasa a ranta indai tsautsayi yasa Nabilah ta aureshi sai tasa Rasheedat ta rama dukanta ganin yana shirin fita tace "Sultan zo min nan" dakatawa yayi yana sau'ke numfashi kafin ya juyo yana dawowa har gabanta ya zauna a kasan carpet cikin ladabi yace "gani Umma kiyi hakuri idan na 6ata miki rai" wani kallo Hajiya Salmah tayi masa tana cewa.
"Oh Ashe kasan kayi min lefin? Lallai Kam Sultan wai kana hankalinka kuwa ko Kuma asiri sukai maka domin wannan son da kake nunawa 'yar yarinyar nan ba 'kalau ba yanzu tsabar rashin hankali kaga irin dukan da kayiwa Rasheedat akan wata banza can gefe dan kawai kin hada kakanni dakyau Sultan yayi maka kyau tashi kaje ka auri Nabilan Allah ya baka sa'a".
Jin abinda tace yasa Sultan girgiza kai yana cewa "dan Allah Umma kiyi hakuri abinda ya faru idan hakan danai ya 6ata miki rai ki yafe min" ta'be baki tai tana kau dakai tace "ka tashi kaban guri nace ko? Idan kaga dama karka sake kwana a gidan nan daga yau ya tattara ka koma gidan su Nabilan" humm matsalarta kenan auren Nabilah da zaiyi ya sani shine yaja duk wannan damuwar bai sake cewa komai ba ya mi'ke yana fita 'kwafa Hajiya Salmah tai jin tashin motarsa alamar hospital zai tafi yasa ta mi'ke tana shiga part d'inta ta Kira 'kawarta a waya tana d'agawa ta soma magana.
"Hello Hajiya Suwaiba wai ya batun mu na auren Hajeer da nace miki Ina nemawa Sultan nifa gaskiya yaron nan yana neman d'ora min hawan jini shiyasa nace ki barta tazo ko sati d'aya tayi min su had'u dashi ya ganta tad'an ri'ka shige masa da haka maybe kinsan mace tuni zata juya ra'ayin sa ya fasa auren wancan matsiyaciyar yarinyar".
Daga can 6angaren Hajiya Suwaiba tai murmushi tare da jinjina kai tana cewa "ayya 'kawata kiyi hakuri wallahi Hajeer yanzu bata da lokaci ne Daddyn ta yana gari idan har ba komawa yayi ba bazai ta'ba bari taje wani gu tayi koda kwana bane shiyasa kikaga bata zoba amma ki qara ha'kuri zuwa wani lokaci idan ya koma insha Allahu da kaina zan kawo miki ita har gida ya ganta haba kawata wazai 'ki hada jini dake saidai idan ma'kiyin ki" sauke ajiyar zuciya Hajiya Salmah tai cikin jin dad'i tana cewa "yauwa 'kawata nagode sosai saina ganki".
"Ok saina zo".
Sauke waya Hajiya Salmah tai tare da fitar da huci tana cewa "kai jama'a har naji dad'i wallahi Kai Kuma Sultan zan nuna maka matsayin karfin girman ikon uwa kaje ka auri za'bin naka nima zan tilasta maka ko baka so ka auri za'bina sannan nasa ta wulakanta Nabilan mu had'u mu 'kutata Mata wanda da 'kafarta zata gudu daga gidan wallahi tallahi sai tayi nadamar aurenka dani suke zancen muje zuwa" ta karasa maganar tana fita ta shiga part d'in su Amrat ta gano ya yayiwa Rasheedat da jikinta domin tana parlor tana jiyo 'karar belt d'in idan ya sauke Mata a jiki.
***
Tafiyar Hajiya Sadiya Dubai ita da 'kawarta Bilkisu Basu dawo ba sai saida sukai sati uku abin ya baiwa Husnah haushi ranta ya 6aci ganin kullum lamarin mahaifiyar tata kara ta6ar6arewa yake ranar data dawo ko zama basuyi ba Hajiya Bilkisu ta qara janta suka tafi wani gurin inda bata san ko ina bane Saida suka qara kwana biyu sannan ta dawo Husnah tayi kuka da halin Hajiya Sadiya tayi ba'kin ciki ta ha'kura addu'ar ta kad'ai Allah ya shiryeta ta daina wannan yawace yawacen tayi aure tssha ganin manyan mutane da alhazawa suna zuwa gurin ta amma ta'k za'bari d'aya ta aura kawai ita duniya ne a gabanta.
Yau weekend ne bataje ko'ina ba tana gida sakamakon Husnah ta fad'a mata zata zo tare da 'kawarta su gaisa da kanta ta shiga kitchen ta had'a kayan ciye-ciye na alfarma ta gyara dinning table tsaftace parlor taci wanka itama ta d'au kwalliya ta kashe d'auri kamar zata muhimmin ba'ko ta hakimce akan kujerar parlor tana kallon yadda less d'in jikinta yake walwali da she'ki da dubban kud'ad'e,, waya ta d'auka tana bud'e data tayi sa'a kuwa Alhaji Ashraf yana online murmushi tai tana kiransa video call amma harta katse baiyi picking ba ta sake kira bai d'aga ba dama tasan za'ai haka ha'kura tai ta katse datar tare da mi'kewa tsaye ta saita wayarta ta ri'ka d'aukar zafafan salfie saida ta gama sannan ta sake bud'e datar ta tura masa photunan tare da cewa.
"Ina sauraron amsa please Ashraf idan ka samu lokaci dan Allah kazo gidana idan bazaka samu dama ba ka fad'a min inda zan sameka ina so zamuyi magana" ta tura masa sending tare da zuba ido taga ya bata amsa amma shiru ga alamar ya gani nan amma baiyi Mata reply ba zazzafan numfashi ta sau'ke tare da mi'kewa ta goya hannunta a baya ta fara zaga parlon cikin tarin tunanin taya zata shawo kan Alhaji Ashraf ya sota ya aureta itakam tana matukar sonsa kuma tana burin aurensa sannan tana fatan mafarkin ta ya zamo gaskiya agogo ta kalla ganin kusan awa uku da tafiyar Husnah d'auko Nabilah amma har yanzu shiru komawa ta tana zama akan kujerar data tashi kawai tayi tsam domin ta gaza gane meke damunta a halin yanzun kawai kiran Husnah ta danna taji itama idan bazata zo da 'kawar tata ba ita zata fita domin hankalinta ya tashi da shariyar da Alhaji Ashraf yayi Mata yanzu so take ta fita su had'u ko zata samu taji salama a ranta.
Husnah tana zaune a gefen gadon Nabilah tana kallon yadda take kwalliya a shafa nan a shafa can d'an murmushi tai tana mi'kewa tace "please Nabilah ki tashi muje kinga Momy tana kirana taga dad'ewar tayi yawa gashi ke Kuma kin 'ki gama kwalliyar kamar zakije gano shugaban qasa gashi banga komai a fuskarki ba banda lipstick" juyiwa Nabilah tai tana kallon ta kafin ta mi'ke tana d'aukar mayafinta da handbag d'inta tace "na gama muje" hanyar fita suka nufa Husnah na cewa "yauwa sis ko kefa kullum ina fad'awa Momy ke shine yau tace tana so na Kai mata ke ta ganki muje" ta karasa maganar suna ri'ke hannun juna kowa da murmushi a fuskarsa suka fita parlor zaro ido Nabilah tai ganin wanda yake zaune yasa tace.
"Daddy Ash dama kazo gidan nan ban sani ba"?.
D'agowa Alhaji Ashraf yayi ganin Nabilah yasa yace "Baby dama kina nan amma shiru banji motsinki ba sanda nazo ko kina barci ne"? Murmushi Nabilah tai tana kallon Hajiya Fatima datayi mata da'kuwa tana cewa "wato Nabilah fad'ar Daddy Ash d'in nan ya shiga bakin ki ko zaki iya kiran naki uban da Daddy Taj"? dariya tai tana d'an rufe baki tai tana cewa "yi hakuri Mami na sha'afa ne Daddy ina kwana"?.
"Lafiya kalau Baby ya kike"?.
"Ina lafiya Daddy ranar na dawo daga school na tarar ka kawo min kaya nagode Allah ya qara arziki".
"Amin Baby ina zuwa wannan 'kawar kice"?.
"Eh Daddy 'kawata ce sunanta Husnah Sahah".
Jin abinda Nabilah tace yasa Alhaji Ashraf kallon Husnah yana sake maimata Husnah Sahah a ransa oh kodai yarinyar Hajiya Sadiya Sahah ce ita? Ko ba'a fad'a ba ga kama nan ya gani bai sake cewa komai ba ya jinjina kai kawai daidai Nabilah ta mi'ke tana yiwa Hajiya Fatima sallama cewa zata je gidansu Husnan kumà ba jimawa zatai ba,,, suna fita Alhaji Ashraf yace.
"Amma Fatima ya akai kukai sake har Baby take mu'amala da yarinyar Hajiya Sadiya Sahah"?.
"Meya faru kasan mahaifiyar tane"? Hajiya Fatima ta fad'a cikin fargabar me Alhaji Ashraf d'in ya hango bayan taga sha'kuwa a tsakaninsu kaiya d'aga Mata yana kallon Alhaji Tajuddeen yace "kwarai Fatima nasan mahaifiyar ta Hajiya Sadiya Sahah ba mutuniyar kirki bace ai kai ka santa Tajuddeen Kuma kasan halayenta meyasa ka bari har Nabilah take 'kawance da 'yarta baka tsoron abinda zai biyo baya"? Kai Alhaji Tajuddeen ya girgiza yana cewa "wallahi Ashraf ban sani ba ko a mafarki bansan suna zumunci da wata 'yar gidan Sadiya Sahah ba sai yau da na gansu tare Kuma bansan ita bace sai yanzu data fad'i sunanta badan haka ba ban wani ganeta ba tunda bata kama da mahaifiyar ta".
Huci Alhaji Ashraf ya fitar yana cewa "Gaskiya banji dad'in wannan al'amarin ba bana so ace Nabilah wani abun rashin dad'i ya faru a kanta saboda haka dole ne a tari abun tun wuri da zafi ake dukan 'karfe sannan ice tun yana d'anye ake tan'kwasa shi yanzu abinda ya kamata idan Baby ta dawo ka sameta cikin nasiha kayi mata magana ba cikin zafin rai ba dan na sanka da saurin hawa kabi a hankali kayi mata bayani yadda zata fahimci manufarka sai ta ri'ka ja baya a sannu da haka da haka saita janye jikinta daga na wannan yarinyar kafin wani abun muniya wanda bama fata ya faru" ya karasa maganar yana kallon Alhaji Tajuddeen wanda ya jinjina kai cike da gamsuwa domin maganar gaskiya ya san Hajiya Sadiya Sahah yasan halinta ba ba'kuwarsa bace dole ya dakatar da Nabilah tunda yaji wacece Husnah daga Ina ta fito sauke ajiyar zuciya yayi yana mi'kewa yace.
"Shikenan na fahimta muje zan dau'ki mataki bari saita dawo".
Mi'kewa Alhaji Ashraf yayi yana kallon Hajiya Fatima da itama ta mi'ke yace "ok Fatima na wuce gida daga can" kaita d'aga tana cewa "baza ka dawo kayi lunch anan ba"? "Eh tacan zan wuce gidan munyi magana da wani mutum jiya zaizo daga government house zamu gana shine dalili bari muje kinga kira ma yake yi maybe ya sauka kuma baisan inda zamu had'u ba" ya karasa maganar yana juyawa 6angaren Alhaji Tajuddeen yace "muje" fita sukai yana d'aga kiran Hajiya Fatima kam shiru tayi cike da tunani da rashin jin dad'i domin Nabilah ta matukar sha'kuwa da yarinyar nan rana d'aya ba lefin tsaye ba na zaune ace ta rabu da ita ta daina yi mata magana ba fad'a ba komai bayan school d'insu d'aya sun saba gaskiya abun baiyi daidai ba bari Alhaji Tajuddeen ya dawo ta sameshi ta bashi wata shawarar Allah yasa zai yarda.
***Husnah da farin ciki a fuskarta suka shiga parlon Hajiya Sadiya har lokacin tana zaga kujerun dake parlon da waya a hannunta tana sake Kiran Alhaji Ashraf amma bai d'aga ba idonta yayi ja ranta yakai 'kololuwa wajen 6aci ganinsu yasa ta sassauta fushin dake cin ranta tana d'an sake fuska da murmushi tace.
"Sannu da zuwa bismilllah zauna" ta fad'a tana bin Nabilah da kallon cike da mamaki ta zuba Mata ido zama Nabilah tai cikin ladabi ta gaida ita amsawa Hajiya Sadiya tai tana kallon Husnah wacce bakinta ya'ki rufuwa tace "ki kaita dinning Ina zuwa" to Husnah tace suna mi'kewa suka tafi can domin itama Nabilan taji dad'in hakan sai tafi sakewa akan suna gaban Hajiya Sadiya ga wani kallon 'kurulla da take mata sunan zaune suna hira da dariya abinsu Hajiya Sadiya itama ta karaso gurin ta samu guri ta zauna tare da cewa Husnah tai serving din'ta mi'kewa Husnah tai ta had'a Mata komai kafin ta koma ta zauna amma me Hajiya Sadiya ta kasa nutsuwa taci abincin yadda ya kamata haka kawai ganin Nabilah ya tada Mata hankali kuma batasan dalili ba aje spoon d'in hannunta tai tana kallon Husnah tace.
"Husnah wannan yarinyar daga Ina kuka taho tare a wanne gidan take gani nake kamar nasan wani me kama da ita a cikin manyan mutanen mu kuma wanin ba kowa bane sai professor Alhaji Tajuddeen"? ta karasa maganar tana sake qarewa Nabilah kallo cike da mamaki.
Itama Husnah kallon Nabilan tai tana cewa "eh Momy kin fad'a daidai wallahi 'yarshi ce sunanata Nabilah Tajuddeen".
Murmushin ya'ke Hajiya Sadiya tai tana cewa "ayya Allah sarki ai jini baya 6uya kallo d'aya nayi mata na gani, ashe itace qawar taki"?.
"Eh Momy qawata tace sosai banda kamar ta kaf cikin qawaye na munfi shakuwa da ita".
Kai Hajiya Sadiya ta jinjina tana cewa "Masha Allah gaskiya kinyi dacen qawa naga itama kamar ba ruwanta irin yadda kike dama haka kike so" 'yar dariya Husnah tai tana kallon Hajiya Sadiya tace "ai Momy yadda kika san 'yan biyu idan mukai abu wani lokacin haka muke a school kuwa ba d'alibai ba hatta malamai sun gane mu saboda bama rabuwa saidai idan tashi akai har twins ake ce mana" ta karasa maganar suna had'a ido da juna sukai murmushi wanda akan idon Hajiya Sadiya haka kawai taji gabanta na fad'uwa lokaci guda ta tsinci kanta cikin wata iriyar fargaba to meya faru meke damunta meyasa daga ganin wannan budurwar ta nemi nutsuwarta ta rasa?sauke wani kalar zazzafan numfashi tai tana sake kallon Nabilah a karo na ba adadi ganin yadda suke hira a tsakanin su lallai akwai so da shaquwa mai karfi runtse ido tai jin yadda zuciyarta ke harbawa kafin ta mi'ke tana barin wuri domin tasan ganin Nabilan ne ya jawo Mata haka to amma akan wanne dalili shine tambayar dake cin ranta harta shiga bedroom da sauri ta rufe kofa tana d'auko waya ta kira numbern Hajiya Bilkisu tare da fatan Allah yasa tana kusa tayi sa'a kuwa tana d'agawa cikin 'kaguwa tace.
"Ke Hajiya Bilkisu kin ta'ba ganin 'yar gidan professor Tajuddeen ne ko a wani wuri"?.
Daga can 6angaren hajiya Bilkisu dake zaune tare da wata hajiya suna lissafin manyar ma'kudan kud'ad'e tace "eh bana ce ba kona taba ganin nata na manta kinsan 'ya'yan manyan nan ba barinsu ake suna fita ba saida 'kwak'kwaran dalili a Ina zan ganta ked'in had'uwa kukai"?.