anyi auren an gama sai tayi azumin kaffara domin indai kinga ba'ai auren nan ba to dama can Nabilah ba matar Sultan bace dan haka ki 'kyale ta shirmen banza take tunda shi yaron yana so an wuce gurin ai duk wani ihu bayan hari da zatai a banza bata Isa hana muyi abinda mukai niyya ba Mukhtar tun kafin yasanta nake tare da d'an uwa na tsawon rayuwar mu kinga sama takai wata bazata zo ta lalata mana zumunci da gur6ata mata ahli ba" kai Hajiya Fatima ta d'aga tana cewa "gaskiya ne shikenan Allah ya bamu ji da gani na gari bari naje naga wadannan sun gama aikin had'a breakfast d'in ne koda saura" mi'kewa tai tana fita domin ta gano.
**Fitowar Nabilah Sultan ya kirata duk zaton ta yana gida saida ta fito main parlor ta ganshi a zaune yasha farar rigar likitoci yana sanye da glass a idonsa hankalinsa yana kan wayar dake hannunsa karasawa tai tana lekawa taga me yake gani har baisan ta fito ba cin karo tayi da photonta cikin mamaki ta tsaya kallon photon domin bata san ma dashi a duniya ba sai yau data gani da alama bata sani ba yayi Mata tunda hankalinta ya karkata xuwa wani gurin dabam murmushi tai tana jinjina kai kafin tasa hannu ta kar'bi wayar tana cigaba da kallon photon yayi matukar kyau d'agowa Sultan yayi yana kallon ta daidai ta zauna yace.
"Gimbiya sarautar mata kin gama shiryawa ne school xaki tafi"?.
Kaita d'aga "eh na gama komai tafiya zanyi" mi'kewa yai yana cewa "ok muje na kaiki da kaina yau dama badan aiyuka sun min yawa ba kullum nine zan ri'ka zuwa ina kaiki amma hakan za'ai saina ri'ka fitowa da wuri yadda bazan makara a hospital ba muje" ya fad'a yana yin gaba mi'kewa tai tana bin bayansa har gaban motarsa ya bud'e Mata ta shiga sannan ya zagaya shima ya shiga yana tada motar suka bar gidan hankalinta nakan waya bata fargaba har suka je kwanar gidan yarima Saida taji ya tsaya ta d'ago ganinsu a inda batai tunanin zuwansu yanzu ba tasan maybe Husnah bata cikin makarantar tunda jiya tace mata Momyn ta tayi tafiya idan an tashi a school gidan 'kanwar Momyn nata zata wuce kafin ta dawo tuna hakan datai yasa ta kalli Sultan tana cewa.
"Ya Sultan please dan Allah muje ka shiga Yalwawa kota sabon titin I.M.G (ai em ji) ne ka d'auko qawata a gidan qanwar Momyn ta" jin abinda tace yasa shi kallonta yace "amma tun da baki fad'a min ba da nabi ta wajen Hasinah hotel sai na 6ullo ta titin gidan man Awajil ai zaifi min sauri saboda karna makara a zuwa hospital yau Ina da aiki sosai gashi saida kika bari na kusa school d'in gaskiya bazan shiga Yalwawa ba" ya fad'a zai wuce ya shiga school d'in cikin shagwa'ba tace "ya Sultan kawai aje ni anan zan karasa cikin school d'in da 'kafata" ta karasa maganar tana shirin bud'e murfin motar ta fita ya dakatar da ita.
"Meyasa bazaki bari na karasa dake ba zaki tafi da 'kafa"?.
Turo baki tai tana qin kallonsa saida ya sake maimata tambayar dayai mata sannan tace "to bakace baza muje ka d'auko qawata ba kuma bani da kamarta fa" dafe kai yayi domin gaskiya idan tace saiya yi mata haka zata takura shi amma baida wani za6i tunda baya son 6acin ranta d'agowa yayi yana kallon ta yadda ta cika ta batse ga hannunta har lokacin yana ri'ke da murfin motar jira take ya bata amsa zai daukota kota fita sauke ajiyar zuciya yayi yana cewa.
"Ok sake murfi ki gyara zaman ki muje na d'auko miki ita shikenan hakan yayi miki koda 'kari"? Sakin murfin tai tana murmushi tace "yauwa ko kaifa ya Sultan shiyasa kake burgeni nake sonka akwai sau'kin hali" shima murmushin yayi Mata suna tafi suna hira kamar ba yanzu ta gama had'e rai ba har suka shiga anguwa bayan sunje kofar gidan yayi parking zata fita yace.
"Nabilah" tsayawa tai tare da juyowa tana kallon sa a marairaice yace "please karki dad'e" yadda yai maganar yasa tayi dariya tana tsokanar sa itama cikin marairaice murya tace "bazan dad'e ba ya Sultan" ta fad'a da sauri ta fita tana dariya ganin yadda ya zaro ido shiga gidan tai da sallama a zaune ta samu Hajiya Maryam a waje tana lissafin kayan da tayo sari bayan sun gaisa tace.
"Momy Husnah fa jiya tace min anan zata kwana yau ko"? Kai Hajiya Maryam ta d'aga tana cewa "eh tana nan shiga wannan d'akin tana ciki" to Nabilah tace tana shiga a kwance ta samu Husnah lullu'be da bargo kamar mara lafiya tsaye tai a bakin kofa tanai mata kallon mamaki kafin ta karaso tana cewa.
"Haba Husnah yada kwance karma kice min baki shirya ba"?.
Murmushi Husnah tai tana gyara kwanciya ta fuskanci Nabilan sosai tana cewa "ban dad'e da tashi ba kin gani tun daga sallar asuba na koma barci sai yanzu na tashi ko wanka banyi ba balle breakfast ki shigo man ki zauna idan na shirya saimu tafi" zaro ido Nabilah tai tana cewa "waye zai karaso ya zauna ya jira kin amma ba dani kike ba kinsan irin cakwakiyar dana had'a a waje ya Sultan nefa yau yaje gidan mu shine yace zai kawo ni school d'in har munje kwanar gidan yarima na rokeshi muzo mu daukeki da'kyar ya amince yana cewa zai makara a zuwa hospital Kuma yanzu nazo baki shirya ba humm yau akwai ya'ki idan muka fita so kike yace bazai sake kawoni school ba saidai idan munyi aure" Nabilah na rufe baki Husnah tai dariya tana tashi zaune tace.
"Yanxu fa ya kika ganni"?.
K'are mata kallo Nabilah tai a shirye take tsaf takalmi kawai zata sa da mayafi tace "oh wato dama kin shirya amma shine kika wani kwanta sad'e-sad'e kamar majinyaciya"? Mi'kewa tai tana d'aukar mayafinta da handbag d'inta ta d'auko takalmi tana cewa "eh man naji lokacin da kike cewa small Mom Ina nake lokacin Ina zaune zan sanya mayafi shine na kwanta da sauri na lullu'ba dan na tsokane ki" "ok taho muje kar ya gaji nasan zai iya tafiya ba karamin aikinsa bane niko da kika ganni ban fito da ko sisi ba" ta fad'a tana ri'ke hannunta suka fita sallama taiwa Hajiya Maryam sannan suka nufi bakin gate suka fita harya gaji da zama a motar ya fito yana jingine ya hard'e hannuwa a 'kirji karasowa sukai Husnah tai gaida dashi bayan ya amsa ya kalli Nabilah ya kalli agogon dake d'aure a hannunsa yana cewa.
"To yanzu kam bazan samu damar kaiku ba ku tare d'an napep ya kaisu school ni zan wuce saboda idan nace saina kaiku zan makara da yawa" jin abinda yace yasa Nabilah shagwa'be fuska tana cewa "kai dan Allah ya Sultan ka kaimu bafa nisa daga nan ko a qasa idan mutum yabi ta cikin maja zai iya zuwa" tana rufe baki yace "ok to kubi ta majar mana ai yanzu zakuje Kinga amsa wannan in tafi" kud'i ya mi'ko mata amma ta had'e rai taki kar'ba ita saidai ya kaisu kaiya jinjina yana mi'kawa Husnah yace "ku tari me napep ya kaiku" kar'ba Husnah tai shi kuma ya bud'e mota ya shiga yabar gurin Nabilah tana kallo yabi ta titin mechanic village har ya 'kule kallonta Husnah tai tana cewa.
"Kiyi hakuri Nabilah nice sila badan kince yazo ku d'auke niba da duk hakan bata faru" kai Nabilah ta girgiza tana cewa "haba Husnah ki daina d'orawa kanki lefi tun kafin mu had'u dake nasan halin ya Sultan saidai na fad'awa wani ko su Rasheedat qaninsa basu isa fad'a min wasu halayen nasa ba karki damu muje" wucewa sukai suna tafe suna hira sun d'anyi nisa suka tsare me napep suka hau ya kaisu daidai ya tsaya sun fita motar Sir Ahmad ta shigo makarantar tsayawa yayi a saitin su yana sauke glass d'in motarsa cikin mamaki daya tabbatar Nabilah d'ince sannan ya mayar da glass d'in yana jan motar yayi gaba saida suka biya me napep sun juya sun fara tafiya Husnah tace.
"Ke Beelat bakiga Sir Ahmad yadda yake mana wani irin kallo ba daga ni har ke to me yake tunani a kanmu"? ta'be baki Nabilah tai tana cewa "oho masa nasan ganin mu dayai a napep ne zaiyi tunanin ko mu irin 'yan qaryar nan ne masu aron kaya da aron mota dan mu burge mutune ace mu wasu ne aina gane manufar sa tuntuni sharesa nai" kai Husnah ta jinjina tana cewa "humm kedai bari kawai Beelat Allah Allah nake gayen nan yabar cikin school d'in nan tunda ranar na biyo ta wani block suna tsaye su uku naji kamar yana fad'a musu zai nemi transfer ya koma yanki garinsu ya gaji da zaman arewaci"
Cikin murna Nabilah tace "ya tafi d'in man da nafi kowa jin dad'i wallahi domin dama ya takura min mtwwww" ta karasa maganar tana jan zazzafan tsaki dariya Husnah tai tana cewa "uhm mutum ne shi me naci sai kace maye amma badan haka ba irin had'e masa ran da kike yaci ya daina kula ki".
"Karma ya daina Ina daidai dashi zansa ayi maganinisa".
Sun kusa shiga department d'insu suka ci karo dashi har yakai motarsa parking space ya dawo tsaki Husnah tai tana cewa "kiga maye nasan ke zaiwa magana tunda naga ya zubo mata wadancan idanuwan nasa" tabe baki Nabilah tai lokacin har sun kusa had'uwa tace "yaiwa kansa magana dai amma bani ba domin bazan sake kulashi ba idan ban fito masa a mutum nace masa mutunci ba bazai gane abinda nake nufi ba" tana rufe baki yana karasowa cikin muryarsa da 'kwararriyar hausa ba yace.
"Nebilah Sir Tejuddeeen".
Had'e rai tayi batare data amsa ba suna kokarin wucewa yace "Nabilah" ko sauraron sa batai ba kamar ma bada ita yake magana ba haka suka manna masa hauka suka wuce tsaye yayi a gurin ya kasa gaba ya kasa baya ganin yadda ta yarfa shi a gaban wasu d'aliban kai ya jinjina yana nuna saitin inda suka shiga da yatsa yace.
"Heyemm Nabilah Nabilah ni kikewa shariya kike wulakanta ni bakisan koni waye ba amma zan sanar dake ta hanyar 6ata sunanki a gari dana mahaifin ki idan nayi haka na tabbata zaki fini jin ciwon abinda kikai min na soki da gaskiya kin 'ki zan karbe abinda kike takama dashi na matantakar taki sannan na bayyana lokacin faruwar hakan a gari muje zuwa kici gaba da mun shariya zan nuna miki ke ba kowa bace a cikin Dutse" ya karasa maganar yana fita daga cikin school d'in ya gangara wani gidan cin abinci dake opposite d'in makarantar domin yayi breakfast.
Yauma jarrabawar da sukai taci lokaci domin har 'karfe uku da rabi suna ciki basu samu damar fitowa ba sai karfe hud'u sannan suka fito a gaggauce kowa yayi alwala sukai sallar azhar da la'asar suka mi'kewa suna fita a gurin humm kamar wanda suka sha maganin gano indai zasu fito su baro department d'insu to zasu had'u da Sir Ahmad abun kamar had'in baki saidai wannan karon ko inda suke bai kalla ba yayi gaba kallon juna sukai bayan wucewar sa suna murmushi kai Nabilah ta jinjina tana cewa.
"Kai alhamdulillah har naji dad'i wallahi da naga ya share ni haba yanzu ne zan sake a school d'in nan Allah yasa ya kusa tafiya ma na karasa hutawa".
"Amin domin Nima nayi mamaki da naga ya wuce wallahi na d'auka zaiyi miki magana humm dama irin su Sir Ahmad saika fito ka nuna musu 6acin ranka a fili suke ganewa ne amma koba komai yanzun ma kin samu salama ko nace mun samu domin nima yana shiga hakki na yana mugun takura min kiranki da yake yi".
"Komai yazo karshe ai tunda yayi fushi nasan na huta Allah yasa bazai sake kwana cikin Dutse ba a yau ya koma yankinsu".
"Amin Beelat Allah yasa" Husnah ta fad'a harda yafa hannu a fuska fitowa sukai bakin titi tuna babu wacce tazo da mota yasa Husnah ta bud'e handbag d'inta tana ciro kud'in da Sultan ya Basu su hau napep d'azu dubu biyu ne wanda ya kawosu d'azu sun bashi d'ari biyu yanzu saura dubu d'aya da d'ari takwas mi'kawa Nabilah kud'in tai tana cewa.
"Kar'bi sauran kud'in nan Beelat" Kai Nabilah ta girgiza"no Husnah jeki dashi" da mamaki Husnah tace "Kuma da me zaki hau napep kije gida"? Murmushi Nabilah tana dafe kafad'ar ta tace "Karki damu kije kawai idan mun sauka zan shiga na amso kud'in a gurin Mami na kawo masa ke kuma kinga Momyn ki bata nan" sauke numfashi Husnah tai tana girgiza kai itama tace "ai kuma a gurin 'kanwarta nake kawai ki karfa Beelat".
"A'a Husnah kije dashi nace" "nifa bazanje dashi ba dan Allah ki kar'ba" "ok shikenan bani iya d'ari biyar tunda kin matsa" dubu d'ayan Husnah ta mi'ko mata bata kar'ba ba tace "ni d'ari biyar nace miki" d'an dafe goshi Husnah tai tasan tunda ta ture akan d'ari biyar d'in nan bazata karbi sama da hakan ba mi'ka mata tayi sannan sukai sallama kowa ya tare napep yayi anguwansu.........✍️Mrs Äl'ämëëñ Ähmäd çë😘.
Mu tsaya mu kwana anan Sai Allah ya tashe mu cikin masu rai da nisan kwana da lafiya insha Allahu zan d'ora muku littafin minister Ashraf amma kafin nan Ina so naga comments masu yawa wanda harsai na gaji da dubuwa.
YUSRAH MUSA ABUBAKAR GIMBA MUHAMMAD KA'ABU.
✨🥀Mukamin ka da girma yake me ka'abu da zahidu ka taka daidai uban gidana ya rasulullah.
✨🥀A baitin sunanka ne ya al Aliyu ina tawassuli da annabin nan almakiyyu sirrin wadatuwa wanda ya zama madaniyyu albarkacinsa nazo kai mini a qawiyyu ka kara bani dama in wake nuru zatullah.
✨🥀Ranar kowa yana kasa kai ko kana buraka ma'iku rundunar Allah na bayanka suna ta gaisuwa da sallamar su a gare ka ranar dukkan annabawa ne fadawanka ashe kwa zamusha kallo matsayin rasulullah💓🌹.
Sai mun sake had'uwa a gaba masoya na masu yabo a gareni godiya sosai sosai godiya🌺.
Tnks for your supports🔥 we will meet again.
#Vote
#Comments
#Share
#Fallow
2~Allahummu salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Mujahidina.
TYPING 📲Fri, Dec 20/24 7:44am YUSRAH MUSA ABUBAKAR ✨✨.
💞MINISTER ASHRAF💞
WHATSAPP NO:234 8160983083.
Mai son magana dani kai tsaye a tuntu6e ni ta wannan numbern.
ANNURI WRITER'S ASSOCIATION 💫
Home of hospitality and harmony gidan kar'bar mutane hannu biyu da zaman lafiya ÀÑÑÙRÌ haske le'ka gidan kowa koda ma'kiya na kallon ka ramin kura sai'ya'yan ta.
STORY WRITTEN ND EDITING
By
✍️Yusrah Musa Abubakar
Mrs Äl'ämëëñ Ähmäd çë maman little Zarahn Aunty.
Bismilllahir Rahmanur Raheem.
Ya rabbana salli ala khairul ala biman ala alal samawatul ula bi izini rabbi him alam.
🕋🕌🕋
It's Friday don't forget to recite suratul al-khaf may Allah open the door of success for us and our family we love our NABI no success without him he've no limits ya rasulullah muna sonka fiye darai da iyaye da dukiya.
3~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Shahidina.
💦Yüsëëñ Sïr Äl-ämëëñ çë💦
PG_____03&04
Hajiya Salmah tana zaune a parlor tare da 'yan matanta Sultan ya fito daga part d'in shi zama yayi yana gaida ita kamar bazata amsa ba saboda haushinsa da take ji akan maganar jiya da sukai da mahaifinsa saida ya sake gaida ita a karo na biyu sannan ta amsa da'kyar yaji amsuwar d'an girgiza kai yai zai mi'ke ta dakatar dashi "Sultan Ina zakaje"? "Umma zanje wani wurin ne" jin abinda yace yasa ta had'e rai tana sake qare masa kallo yadda yaci uban wanka tace "shi gurin da zakaje bashi da suna"? "A'a" "to ina zakaje"? D'an shiru yayi domin ya sani matukar yace mata gidansu Nabilah zaije bayan bala'i dazai least gurin ta saiya sha ruwan ashar iri iri..................
"Sultan ba dakai nake ba amma kayi min banza"?.
Sauke numfashi Sultan yai domin gaskiya Hajiya Salmah irin iyayen nan ne masu mugun takura akan abinda ba sune sukai ra'ayi ba cikin d'an tunani yace "Umma zanje gidansu Nabilah ne" ya fad'a yana d'agowa yaga halin da take ciki da wani irin 6acin rai yaci karo wanda saida yayi dana sanin fad'ar dayai saidai shi mutum ne wanda bai iya 'karya ba kuma baya 6oye-6oye yafi son komai a zahiri "Sultan" yaji muryar Hajiya Salmah ta kira shi amma da yanayi mara dad'i amsa mata yai Kuma yasan mezai faru tunda harya ta'bo wannan maganar.
"Wato Sultan dama da nace maka ka daina son wannan yarinyar nan baka daina ba ko? Wai Sultan uban me ka gani a jikinta ne wanda ya burgeka tun yaushe nake maka maganar 'yar gidan 'kawata Hajeer kaje ka ganta nasan zatai maka ubanme ita wannan shegiyar Nabilan ta fita dashi amma ka'ki saboda maita wallahi Sultan indai Ina raye saika auri Hajeer domin ita nake so ta zama suruka ta uwar 'ya'yanka itace tafi dacewa dakai gaba da baya amma kana sane kake kautarwa, humm to bari kaji tunda ka nace sai tsinanniyar Nabilan ba na 'kyale ka kaje kayi gaban kanka amma bada yawu naba sannan daga yau na cire hannu na a cikin lamarin ka kabi uban naka kuje ku karata tashi ka bani gu"
Jin abinda tace yasa Sultan ya girgiza kai cikin damuwa yace "Umma dan girman Allah kiyi ha'kuri ki fahimce ni wallahi bazan iya goge son da nake yiwa Nabilah bane dazan iya dana ha'kura da ita nabi za'bin naki amma duk da haka idan kin amince zan auri Hajeer d'in bayan na auri Nabilan" ya karasa maganar yana kallon ta tare da jiran amsar me zata ce masa.
Kaita jinjina cikin 6acin rai itama tana kallon shi tace "Sultan nifa bari kaji kwata-kwata auren Nabilah d'in ne bana so kayi na tsaneta bana son koda ganinta balle ta zama suruka ta ka gane idan zaka auri Hajeer ka aureta idan kuma bazakai ba shikenan na amma nidai na fad'a maka babu hannu na babu sanyawar albarka ta" Hajiya Salmah na rufe baki Rasheedat dake gefe ta d'ora da cewa "wallahi Umma bake ba ni kaina na tsani yarinyar nan ko ganinta bana so kina gani fa saboda ita nabar FUD na ha'kura na dawo Poly amma Yaya kake neman d'auko ta ka kawota cikin mu gaskiya