x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 9 - HANYAR RUWA COMPLETE

  • 24001 words
  • 25515 words
  • Out of 25515 words

Category: Romance Story +18

Views 182

09 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
ƙasumba yayi baƙi ya rame, da badan sanin da FAISAL da Hajiya Lubabatu sukai masa ba to babu yadda za'ai su gane shi.










Hajiya Lubabatu kuwa tuni hawaye ya jiƙa fuskarta, bai kula dasu ba saida ya fara waige-waige cikin sa'a ya hangesu fuskarsu cike da farin ciki da kuma tausayinsa, shima ƙwallar ce ta tarar masa sai dai ya hanata zuba, ƙarasowa sukai Faisal kuwa da sassarfa ya tawo ya faɗa jikin Dad ɗin tare da sakin kuka, bayansa Dad yake bugawa alamun lallashi, ya kasa magana, Hajiya Luba ma gefe ta raɓa ta rumgumo shi, hakan yasa ya hade su ya rumgume hawayen da yake ɓoyewa suka gangaro, sosai Khaseem ya ji tausayinsu ya kama sh, shima saida ya goge tasa ƙwallar,












"Barka da fitowa Dad", cewar Khaseem daya matso wajen, da murmushi ya gyaɗa masa kai, dan kunyarsa sosai yaji yana ji, hakan yasa ba shiri ya ɗauke idonsa dan wata muguwar kunya ce ta baibaye shi, tir yake da rayuwarsa ta baya yana jin dama a tariyo masa ya gyara kuskurensa, gaba ɗaya ji yayi walwalarsa ta kau, danasani ya maye gurbin farin cikinsa, Hajiya Lubabatu ta nazarce shi haka FAISAL, barin wajen sukai suka nufi motocinsu, direct katafaren gidan da FAISAL ya dandatsa musu suka nufa, dan dama basu jima da dawowa nan ɗin ba.
















Gida ne mai kyau da ƙawa, gida ne wanda daka ganshi kasan masu gininsa sun san me suke, sannan suna da ilmin abin, dan gida ne kamar an ɗakko daga turai an kawo shi, part biyu ne dana su Dad da na FAISAL wanda idan yayi aure anan zai zauna da Iyalansa, sosai Dad yayita kallon gidan kamar ɗan ƙauye.






kamar yadda gidan FAISAL yake haka na Khaseen yake dan gini iri ɗaya akai musu.






Suna shiga Mom takai Dad ɗakinsa wanda ya wadatu da kayan alatu, ruwa ta haɗa masa masu sinadaran ƙamshi, ta taimaka masa yayi shaving ɗin duk wani gashi na jikinsa, dana fuskarsa, sannan ta taya shi yayi wanka, nan take ya fito fes dashi, sai dai ramar da yayi, kaya ta taya shi ya sanya, tama lura dashi duk yayi sanyi, muryarsa ta tsinkaya yana faɗin "ki yafe min Luba, na kyare ki na baƙanta miki, na cutar dake, dan Allah ki yafe min sannan ki ƙara nemar min yafiyar Yarinyar nan, wallahi kunya da danasani ne yake ɗawainiya dani, wani iri nake ji", ya faɗa cikin ɗacin rai.






"Alhajina, wallahi na yafe maka dama ban riƙeka ba na yafe maka tin randa aka yanke maka huƙunci, kuma nayi farin ciki matuƙa da ganin Allah ya amshi roƙona mijina ya dawo mutum na gari, wallahi wannan kaɗai ya ishe ni, sannan Dota ta yafe maka dan da ita mukai maka girke-girken tarba dan mijinta ya kawo ta da kansa dan ta taya ni aiki", rumgumeta yayi yana ajiyar zuciya.












Bayan sun gama cin abinci, Khaseem kuwa tafiya yayi, su Twince da Amal da Aiman suka shigo suna ƙiran Granny wato Hajiya Luba, "Granny zanci tuwo", cewar wata Kyakkyawar Yarinya, tana cuno baki, Amal kenan, shi kuwa Aiman cewa yayi "ni dai kunun Gyaɗar nan zaki bani nasha", su Miema kuwa zama sukai suna cire takalmansu ko uffan basu ce ba dan da alama aun gaji, basu kula da Dad dake zaune ba, Dad kuwa ƙura musu ido yayi, dan sosai yaji Yaran sun shiga ransa, dan dama ya taɓa ganin hotunansu a wajen FAISAL, yana ƙaunarsu har ransa, katse tunaninsa yayi jin Amal da Aiman sun matso inda yake suna cewa "Laaaa Grandfa oyoyo, dama Momma ta ce mana ka kusa dawowa daga tafiyar da kayi, ashe yau zaka dawo bamu sani ba?", suka faɗa suna faɗawa jikinsa, wata ajiyar zuciya ya sauke ya ƙara rumgumesu, "ƙwarai na dawo Yarana bazan kuma barin ku ba", cikin murna suka ce "yawwa Granfa kaga sai mu dena kallon hotanka tinda gaka", da murmushi ya ce "ƙwarai kuwa tinda gana cikin hoton ya zo da kansa ba", dariya suka sanya har su Miema da suka taso cikin farin cikin ganin Kakan nasu da suka daɗe suna ganinsa a hoto, rumgumo Dad sukai ta baya "am happy to see u my Granfa, we missed u so much, kullum Momma da Granny suna ce mana ka kusa dawowa sai yau ka dawo, sai dai muyita ganin hotanka, pls karka kuma tafiya ka barmu", suka faɗa cikin shagwaɓa, ƙwalla Dad yaji ta tawo yayi saurin maidata, sannan ya girgizawa Hisham kai alamun bazai kuma barinsu ba, haka ranar ya lalace wajen wasa da jikokin nasa, fatansa ya ga na FAISAL haka.












Ƙaunar da Faisal yake nunawa Yaran Abokin nasa ne yasa kusan duk weekend anan gidan suke yinsa, sun saba sosai da Hajiya Luba dan ILHAM ta nuna musu itan Kakarsu ce, haka Khaseem dan yana jin daɗin yadda suke nunawa Yaran nasa ƙauna ta haƙiƙa, gashi Khaseem yayi-yayi da FAISAL ɗin yayi aure amma yaƙi, ya rasa abinda abokin nasa yake jira, ga shi dai babu abinda ya nema ya rasa kuɗi kyau da nasaba, ya dai ƙyale shi yaga iya gudin ruwansa, Hajiya Luba har ta gaji da yi masa zancen aure.












Wannan dalilinne yasa su twince suka shaƙu da Hajiya Luba, kamar yadda suke son Umman Ilham haka suke son Hajiya Luba, Dad kuwa a hoto suka sanshi, hakan yasa da suka tambayi waye, ILHAM ta basu labarin kakansu ne, kuma yayi tafiya ne ya kusa dawowa su dinga masa addu'a, hakan yasa suka dage yi masa addu'a tare da tambayarsa koda yaushe, hakan yayiwa FAISAL daɗi, ganin yadda ILHAM ta cusawa Yaranta soyayyar mahaifinsa duk kuwa da abinda yayi mata, hakan yasa ta ƙara ƙima da daraja a idonsa,












Bayan dawowar Daddy da sati har gidan ILHAM tazo tayiwa Dad ɗin sannu da zuwa, har kuka yayi yana neman yafiyarta, kuma ta ƙara jaddada masa ta yafe masa.














Lokacin da ALHAJI BELLO yaji FAISAL yaje har Bichi ya gyara ɓarakar da ya tafka, har kuka yayi yana godiya ga Allah daya albarkace shi da FAISAL a matsayin Ɗa, har Bichin FAISAL ya kaishi ya ƙara neman yafiyarsu, kuma alhamdulillah yafiya ta samu saura ta Ubangiji.


















Mama tayi aure inda ta aure Abokin Alhaji BELLO RABE, ya ganta ne lokacin da ake shari'ar ILHAM, daƙyar ta amince saida ta tabbatar ba halinsu ɗaya da Alhaji Bello Raben ba, sannan ta yarda, mai kuɗi ne sosai, matarsace ta rasu tabar yara biyar duk manya, kuma suna girmamata sosai, Mama da Hajiya Luba sun zama ƙawaye na ƙut da ƙut, har gida Alhaji Sale da Mama suka zo sukaiwa Dad jaje tare da murnar dawowarsa, sosai yaji kunyar Mama kuma yayita bata haƙuri, da neman yafiya, kuma ta yafe masa.














ILHAM ta saki jikinta fa Dad tana zuwa ta gaida shi, tana kuma girmamashi a matsayinsa na mahaifin wanda ta mayar kamar Yayanta.






"FAISAL ina neman Alfarma a gare ka, akwai wata Ƙaramar Yarinya da aka kai Kurkuku bata fi shekara goma sha biyar ba, wai tayi kisan kai, kuma da ganin yarinyar nan bata aikata abinda ake tuhumarta dashi ba, dan kana gani kasan sharri ne, wallahi abin tausayi, bakaga yadda ake cin zarafinta ba, dan Allah ina so ka tsaya mata dan idan bata samu adalci ba, zata ƙare rayuwarta a kurkuku tana ƙaramar Yarinya",










Sosai FAISAL ya ji tausayin Yarinyar, kuma yayiwa Mahaifinsa alƙawarin zai je dan ganawa da Yarinyar, kuma yayi mamaki da yaji kurkukun maza aka kaita bana mata ba, kuma a matsayinta na mai ƙananun shekaru, dole akwai wata sarƙaƙiyar.










Alhamdulillah, yau muka kawo ƙarshen Book ɗinmu na haɗaka wato *HANYAR RUWA*






Ina fatan Ubangiji ya ya abinda muka rubuta ya zama izina ga masu aikata wannan lamari a duniya gaba ɗaya, wato cin zarafin Ɗan adam da yin rufda ciki akam abinda ba naka ba, cin zarafin Ƴaƴa mata ta hanyar fyaɗe ba tausayi babu jinƙai, da kuma tsanar talaka wanda bashi ya tsarawa kamsa kasancewa talakanba, ya kamata masu hali irin wannan su gyara saboda dama sau ɗaya take zuwarwa mutum, wallahi ya mutu bai tuba ba to ya kuka da kansa dan Allah bazai barshi ba.












Abinda mukai dai-dai Allah ya bamu lada abinda mukai ba dai-dai ba Allah ya yafe mana.
















Sabon Littafin ƘANWAR SOJA wanda zata fara nan bada jimawa ba, wato *BANIDA HUJJA*

Wato Yarinya ce Ƴar kimanin shekara sha biyar zuwa sha shida aka kawo gidan yari da laifin kisan kai, kai da ganin yarinyar kasan bata san koda kisan kiyashi ba balle mutum duk da ance mutum mugun icce ne, sai dai na wannan Yarinyar akwai lauje cikin naɗi, akwai lamari mai ban mamaki da zallar chakwakiya a ciki, dan a ƙa'ida ma shekarunta bai kai a kaita kurkuku ba, amma sai gata an kawo ta, hatta gandirobobi, birsinoni mamakin hakan suke kuma ba komai ne abin mamakin ba shine magarƙamar maza aka kawo ta ba ta mata ba, wannan duk yana cikin littafin *BANIDA HUJJA* na ƘANWAR SOJA, karku bari a baku labari, labarin yazo da sabon salo cakwakiya, firgici da rikita-rikita, tausayi da dai sauransu, ku bibiyi wannan book mai tarin abin mamaki.










By Rumyn Royal
















*Alƙalamin mu Ƴancinmu✍️*
End Ads