x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 7 - HANYAR RUWA COMPLETE

  • 18001 words
  • 21000 words
  • Out of 25515 words

Category: Romance Story +18

Views 183

09 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
ALHAJI BELLO RABE bisa zarginsa da yiwa Ƴar ta ILHAM ƴar shekara 15 mummunan fyaɗe bayan yayi amfani forcid poison, wanda ya fitar da ita daga hayyacinta", yana gamawa ya miƙawa alƙali takardar sannan ya zauna.










Wani Lauyer ne ya miƙe baƙiƙƙirin da shi ya ce "Sunana barrister Usman, nine lauyern wanda ake ƙara", bayan ya gabatar da kansa ya koma ya zauna, FAISAL ne ya miƙe cikin jarumta da haiba ya ce "Sunana Barrister FAISAL, nine Lauyern wanda yake ƙara, tare da abokin aikina", ya nuna Barrister Khaseem, tashi yayi shima ya ce "Batrister Khaseen", sai suka zauna gaba ɗaya.✍️














*By Rumaisa Aliyu Inuwa(Rumyn Royal Star🌟)*












Sharing fisabilillah👏⚖️💧HANYAR RUWA⚖️


💦The way of water💦






Together
By


ƘANWAR SOJA


RUMYN ROYAL


ZAHRA ROYAL.




A heart toching story💔say No Rape❌








In the name of Allah, the beneficent the merciful.








After the successful of
(FARASHIN SO, RABI DANJA) & (FANSAR MACIJIYA), now we are back with (HANYAR RUWA).










🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*






*Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai*








PAGE 3️⃣0️⃣➡️3️⃣1️⃣











Wani Lauyer ne ya miƙe baƙiƙƙirin da shi ya ce "Sunana barrister Yusuf , nine lauyern wanda ake ƙara", bayan ya gabatar da kansa ya koma ya zauna, FAISAL ne ya miƙe cikin jarumta da haiba ya ce "Sunana Barrister FAISAL BELLOH RABE, nine Lauyern wanda yake ƙara, tare da abokin aikina", ya nuna Barrister Khaseem, tashi yayi shima ya ce "Batrister Khaseen", sai suka zauna gaba ɗaya.








COURT ce tayi shiru nan aka fara maganganu 'kasa jin cewa Barrister FAISAL Yana kare wacce uban sa yayi fyad'i ganin COURT ta rikichi Al'kali ya buga guduman sa anan akayi shiru kamar ruwan sama ya d'auki.





Maga takadda ne ya mi'ki ya karanta laifukan da ake tuhuman Alhaji BELLOH RABE dashi tsaff ya rikicin sai uban gumi da yakiye "BELLOH RABE Court ce ke tambayar ka , shin ka aikata laifin da ake tuhuman ka dashi ," girgiza kai yayi "magana zakaye " cikin rawar murya '" ya mai girma mai Shari'a wanan 'kazafi ne da sharri ne ban aikata ba".








Al'kali ne ya gansa da kyau ya karkace yayi rubutu a takardar sa " ko lawyer wanda aka kai 'karan sa yana da magana " Barrister Yusuf ne ya mi'ki cikin zaguwa da Murmurshi " thank you my lord " an kawo wanan 'karar ne domin cin zarafin Alhaji BELLOH RABE ganin cewa kaff fad'in Kano arzikin sa ne a gaba yana daga cikin manyan manyan masu kudin mu, idan ba'a samu sunan sa a number one ba to zaisu a two..








Idan ka lura da wanan babo irrin sharrin da baza'a mai ba ganin yadda yake samun chigaba a harkokin sana'o'in sa , wanan mugun 'kazafi taya Alhaji BELLOH RABE zai wa wanan yarinyar mai shikkaru goma sha biyar fyad'i , ina neman court da ta duba zance na nasu aiki nawa ne a gidan ALHAJI BELLOH RABE ?











Akwai zawarawa akai 'yan mata harda tsoffin hakan bai ta'ba faruwa ba sai akan wanan yarinayr? shin itta goal ce da Alhaji zai neme t meye a ganganr jikinta " wane irrin kukka mai taffasa zuciya iliham ta fashe dashi wacce ta zauna akan keken marasa lafiya, "wanan shine abinda zance ya mai girma mai Shari'a"





,


Al'kali ne ya kammala rubutun sa ya daura da cewa. "shin ko lawyer wanda ya kawo 'kara yana da abin fad'a akan abokin takarar sa ?" a nitse Barrister FAISAL BELLOH RABE ya mi'ki " Thank you my lot " wato shi daman duniya juyin d'an wake ne watarana ya juya anan gobe a Chan " Barrister Yusuf be ' ya buga table ya mi'ki ," objection ya mqi shari'a abokin aiki na yana amfani da wasu kalmomi don yin gugan zana akan wanda nake karewa ya kawo abinda zai shafe Shari'a..."








Al'kali ne ya rubuta abin da zaiye " 'kirafi ya amso" sorry my lord "abinda Barrister FAISAL yace kinan " ya mai girma mai Shari'a wanda takawo 'kara ta shigar da 'korafin ta akan ALHAJI BELLOH RABE wanda ya kira mata haddin ta ta hanyar tursasawa kuma tayi attempt na kashe ta ta hanyar amfani da sa ta cikin buhu ya jiffa da itta a Chan bayan gari ,muna da shaida da zai tabbatar mana da cewa a wanan ranar Alhaji BELLOH yana gida da yamma alhali baya dawowa sai dare,"..











Barrister Yusuf ne ya mi'ki "my lord Barrister FAISAL yana sa magana a baki ta hanyar d'aurawa wanda nake karewa laifin da bai aikata ba " Barrister FAISAL ne ya amsa da cewa " am on my feet Barrister Yusuf wanan hurumin na ne magana akan cutar wa da akawa housemaid ta hanyar fyad'i baka da ikon dakatar dani"..








"Barrister YUSUF 'korafi bai amso ba " a kunya ce ya zauna da takaice , murmurshi Barrister Khazeem yaye nan FAISAL ya gama jawabin sa da duk abin da ya faru , duk zu'kata sun raunana wasu harda hawaye , a inda wasu suka ce kawai FAISAL ya amshi case nan ne don ya nema wani dukiya a gun babban sa ya hana sa don haka ya shirya wasan kwaikwayo..








Al'kalin ne yayi shiru yana nazari chan yayi rubutu da cewa " wanan court mai Albarka da a dalchi ta d'aga wanan Shari'a r zuwa 2 gawatan August ,2022, da fatan duk lawyer wanda ake 'kara zai kawo shidan cewa Alhaji BELLOH RABE bai aikata wanan laifin ba don ya wanke sa daga wanan zargin sa , "...











Nan ya buga guduman sa dukka aka watse daga court Umma ce ta zaro ido a gaban Faisal " tabbas yanzu kam naga abinda Ilham take sanar min daman kai d'an ALHAJI BELLOH RABE ne?"














Al'kalamin ƙanwar sojah-----------ce ✍️💞








⚖️💧HANYAR RUWA⚖️


💦The way of water💦






Together
By


ƘANWAR SOJA


RUMYN ROYAL


ZAHRA ROYAL.




A heart toching story💔say No Rape❌








In the name of Allah, the beneficent the merciful.








After the successful of
(FARASHIN SO, RABI DANJA) & (FANSAR MACIJIYA), now we are back with (HANYAR RUWA).










🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*






*Da sunan Allah mai rahama mai jink'ai*






Page3️⃣2️⃣➡️3️⃣3️⃣




Nan ya buga gudumarsa dukka aka watse daga court Ummah ce ta zaro ido a gaban Faisal "tabbas yanzu kam naga abinda Iliham take sanar min daman kai d'an Alhaji BELLOH Rabe ne?".






Sosai ta ta cika da d'unbin mamaki tana girgiza kai da sauri Faisal ya ce "kware da gaske Ummah amma kar hakan yasa kuji cewa wai bazan iya tsaya muku ba in..... Dakatar dashi Ummah tayi tana sharewa Iliham hawayen dake zuba na tsananin tsoron wannan shari'a kana ta ce "lallai na tsorata anya kuwa bazamu hak'ura ba yaro kana ganin bazaka samu matsala da dashi Mahaifinka ba kar hakan yaja muka babbar matsala akamu bazan so hakan ba daga taimako kai kuma abun ya zamema matsala" ta idasa maganar iya gaskiyarta tabbas ta tsorata yadda Mahaifin nasa yake masu kallon k'ask'anci.




Sauke ajiyar zuciya yayi ya ce "Ummah please koma naida wannan tunanin na fasa shari'a dashi dan kuwa babu gudu babuja da baya" kamin Ummah tayi magana harya fice daga wajan cikin tashin hankali Ummah take kallon barrister Khaseem dake kallon ta itama tace "anya yaron nan kuwa Mahaifinsa fa zai iya komai ina gudun abinda zaije ya dawo ni kam nayi mamakin cewa d'an sane" d'an gyara zama barrister Khaseem yayi ya ce "hakane Ummah karki damu Faisal yana da kyakkyawar zuciya kinsan Allah yana fidda rayayye a cikin matacce to kamar hakane tsakanin Faisal da Babansa shi Faisal ya kasance mutunan kirki ne sab'anin mahaifinsa", sosai kwantar ma da Ummah hankali dan gaya yadda suka tsorata ya k'ara cewa "Ummah saifa kun kwantar da hankalinku kun ba shari'a had'in kai duk abinda kuka sani kuyi k'unk'urin sanar da court kar wani abu ya baku tsoro ta hakane zaki kwato ma d'iyarki y'ancinta", sosai ya k'ara nusar da ita.








A wajan Faisal kuwa yana shiga gida ya tadda Dad d'in sai masifa yake ma Hjy Lubabatu inda yake shiga bata nan yake fita ba sai hawaye take na bak'in cikin mijin nata Faisal na shigo ya nufi wajan mahaifiyarsa zuciyarsa na tafartasa Alhaji BELLOH cikin masifa ya ce "yauwa ai dama kai nake jira harni zaka rink'a jayayya dani a cikin court harni zaka tsaya kana tuhuma a bainar nasi ni Faisal?", Ya idasa maganar yana nuna kansa a hargitse Faisal zanyi magana rantsa a jagule da sauri Hjy Lubabatu ta girgiza mai kai cike da masifa Alhaji BELLOH ya k'ara cewa "barshi bana ya zage ni ai ke kika bashi k'ofar raina Mahaifinsa wallahi wallahi akan wannan shari'ar Faisal zan iya tsine ma" wata irin masifaffiyar bugawa zuciya ce ta sami Hjy Lubabatu dafe k'irji tayi ta ce "Alhaji tsinuwa fa kace", ta idasa maganar hawaye na bin k'uncinta Faisal kuwa baiji wani abu ba dan shi akan gaskiyarshi yake ko Allah ya ce koda iyayanka sun tsine ma indai wajan gaskiya ne da bin umarnin Allah kwata-kwata Allah bazai amshi wannan tsinuwar ba bare shi da yake ubane ba uwaba.




Cike da k'unar zuciya ya ce "kware kuwa yadda kika ji kai kuma wallahi karna fito na taddaka kai cikin gida na tunda ka zab'i wasu banzaye a kaina kuma mu zuba muda ku muga wa zaiyi nasara karna fito karna fito na sameka a cikin gida na kaji na mai-maita maka inba haka ba wallahi billahil azim zanma abunda baka tab'a tsammani ba zan cire sani na wai kai d'ana ne na shinfid'a ma rashin mutumcin da sai ka zubar da hawaye". Yana idasa maganar ya haura sama yabar su sake da baki........✍️














*ZAHRA ROYAL STAR CE*🌟✍️










Comment and share Fisabilillahi🥰🙏⚖️💧HANYAR RUWA⚖️


💦The way of water💦






Together
By


ƘANWAR SOJA


RUMYN ROYAL


ZAHRA ROYAL.




A heart toching story💔say No Rape❌








In the name of Allah, the beneficent the merciful.








After the successful of
(FARASHIN SO, RABI DANJA) & (FANSAR MACIJIYA), now we are back with (HANYAR RUWA).










🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*










PAGE 3️⃣4️⃣➡️3️⃣5️⃣


HAJIYA LUBABATU kuwa tsoro da firgici da tashin hankali ne ya ziyarce ta, mamakin mijin nata take tana ƙarawa, FAISAL kuwa ido yabi Mahaifin nasa da shi dan dama yasan za'a zo wannan wajen, cikin ƙunar zuciya Hajiya Lubabatu ta ce "nima bazan zauna ba FAISAL tare zamu bar masa gidan, banga amfanin zama da mutum irin wannan ba, dole na barshi bazan tsaya ina kallo kabar gidan nan ba, ƙafa ta ƙafarka", kallonta yake tare da haɗiyar abinda ya tokare masa wuya ya ce "Mom kiyi haƙuri ki zauna bazan so akaina kibar gidan nan ba, zan tafi kuma kinsan ina tare dake ba zanyi nisa dake ba, dan Allah ki kwantar da hankalinki, addu'a zaki taya Dad da shi na tabbata wataran zai gane ba akan gaskiya yake ba, kuma duk abinda yake faruwa zan dinga sanar dake", ya faɗa cikin lallashi da son kwantar mata da hankali, cikin rawar murya ta ce "to ka gaya min inda zaka je ko hankalina zai kwanta", ta faɗa da sanyin murya, tausayi ta bashi ya ce "Mom ina tare da Khaseem", abinda ya faɗa kenan ya nufi side ɗinsa, bai jima ba ya fito ɗauke da troly a hannunsa,










gaban Mom ya tsaya ya sumbaci goshinta tare da kwantar mata hankali da idonsa kana yabi hanyar fita, cikin murya dashashshiya ta ƙira sunansa, juyowa yayi ya kalle ta dan shima idonsa ya kawo ruwa, "ka ci abinci FAISAL karka dinga zama da yunwa, zan masa magana in sha Allah zaka dawo gida", kai kawai ya gyaɗa mata kana ya ja jakarsa ya fice.












Khaseem ne ya maida su Umma gidansa, sai kwantar musu da hankali yake, Umma dai jinsa kawai take dan jikinta gaba ɗaya yayi sanyi ƙalau, ILHAM kuwa banda ajiyar zuciya babu abinda take jerawa, hawayen idanunta ma sun ƙafe sai kukan zuci take, suna isa wanka sukai suka yi sallar azahar kana ya gabatar musu da takeaway ɗin da ya siya musu, ILHAM kasa ci tayi dan ko kaɗan Abinci yanzu ba shiga yake ba a gare ta, sai Umma ta tsawatar mata tukunna take ci.




















Fitowar Khaseem kenan daga wanka bayan ya shirya wayarsa tahau ƙara, isa wajen da take yayi ya ɗauka ganin FAISAL ne yasa ya ɗaga yasa ta a handsfree "kana ina?", cewar FAISAL, jin muryarsa da Khaseem yayi yaji shi sai a slow hakan yasa ya ce "what going on?", ya tambaya ba tare da ya bashi amsar sa ba, numfashi ya sauke ya ce "Dad ya kore ni a gidansa, yanzu haka ina Raihan Hotel", hankalin Khaseem ya tashi ainun, cikin wani irin yanayi ya ce "FAISAL ta bakin Umma anya ba zamu haƙura da wannan shari'arba, ka duba fa ka fara samun matsala da Dad, anya ba zamu canza shawara ba?", ya faɗa fuskarsa da alamun tsoro, murmushin takaici FAISAL yayi ya ce "no going back Abokina, kasan bana iya haƙuri da abinda na fara, dan haka ka cire duk wannan musa abinda yake gaban mu da muhimmanci, yanzu dai ya Umma da ILHAM?", cikin yanayi na ba yadda ya iya ya amsa masa da "suna lafiya, sai dai gaba ɗayansu jikkunansu is so cool", cikin ƙarfin gwiwa FAISAL ya ce "encouranging them please", ya faɗa, sun tattauna magana kana suka datse ƙiran.
















Cikin ɓacin rai Hajiya Lubabatu ta nufi sama zuwa ɗakin Alhaji Bello, tana shiga ko sallamar da ta saba batai ba ta ce "yanzu abinda kayi ya dace kenan BELLO!, Ɗanka na cikinka ka kora saboda son zuciyarka, wallahi ina danasanin saninka da nayi a rayuwa, da ana komawa baya dana gyara kuskuren da nayi na aurenka, ka cika mugu azzalumi BELLO bansan halayyarka ba saida na aureka, ashe kai ƙungurmin macuci ne azzalumi murakkabi kuma mazinaci, wallahi idan baka tubarwa Allah ka nemi waɗanda ka cuta su yafe maka ba wallahi kai ɗinnan abincin wuta ne kai, kuma....", bata kai ga ƙarasa maganarta ba taji saukar wani bahagon mari a fuskarta, bata gama jure zafinsa ba ya ƙara mata wani gigitacce wanda yayi sanadin faɗuwarta ƙasa, dukanta ya shiga ji kamar ya samu jaka, saida ya tabbatar ta daku kana ya nuna ta ya ce "har kinyi zarrar da zaki zo gabana kina jifa na da maganganu irin wannan har kina ambatar sunana kai tsaye, to bari kiji wallahi koda wasa kika ƙara zuwa gabana kina gayan magana ba tare da kin tauna ba saina kusa kashe ki, kuma tabbas ni macuci ne kuma mazinaci kamar yadda kika sani, sai dai zama dani dole tinda har muka aje ɗa a tsakanin mu, kinga kuwa zama da mazinaci dole", yana kammala faɗa ya rushe da dariya ya fice ya barta hancinta da bakinta duk jini, banda kukan takaici babu abinda take.




















Rana bata ƙarya aka ce sai dai uwar ɗiya taji kunya, yaune Alƙali ya bada damar dawowa Kotu domin cigaba da gabatar da shari'a, kowa ya halatta kamar wancen lokacin, sai dai yawan mutanen na yau na daban ne, dan Kotu ta cika tayi maƙil babu masaƙa tsinke.✍️
















*By Rumaisa Aliyu Inuwa(Rumyn Royal Star🌟)*⚖️💧HANYAR RUWA⚖️


💦The way of water💦






Together
By


ƘANWAR SOJA


RUMYN ROYAL


ZAHRA ROYAL.




A heart toching story💔say No Rape❌








In the name of Allah, the beneficent the merciful.








After the successful of
(FARASHIN SO, RABI DANJA) & (FANSAR MACIJIYA), now we are back with (HANYAR RUWA).










🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*

















3️⃣6️⃣. ➡️. 3️⃣7️⃣.


Rana bata ƙarya aka ce sai dai uwar ɗiya taji kunya, yaune Alƙali ya bada damar dawowa Kotu domin cigaba da gabatar da shari'a, kowa ya halatta kamar wancen lokacin, sai dai yawan mutanen na yau na daban ne, dan Kotu ta cika tayi maƙil babu masaƙa tsinke.✍️











End Ads