x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 2 - HANYAR RUWA COMPLETE

  • 3001 words
  • 6000 words
  • Out of 25515 words

Category: Romance Story +18

Views 179

09 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
zuciyarsa ta imani ce."











Marairaicewa Faisal yayi kamar ƙaramin Yaro, Mom ce ta nemi ba'asin abinda ya faru, bai ɓoye mata ba ya labarta mata, taji tsantsar tausayin yarinyar, kuma ranta ya ɓaci akan abinda Dad yayi, goyan baya ta bawa Faisal ɗin akan yaje indai ya gansu ya taimake su kuma ya basu haƙuri, da wannan hankalin Faisal ya kwanta.










Yaje duk inda yake tunanin zai gansu amma bai gansu ba, ana cikin wannan yanayi Visa ɗin Faisal ya fito na tafiya ƙasar Australia, domin cigaban karatunsa na Low, haka ya ɗaga yabar Nigeria ba tare da ya haɗu da su ILHAM ba.










Mom dake zaune a Falo tana waya da alama da wata take "Yawwa Hajiya Talatu, dan Allah ki bincika min, so nake na samu wadda shekarunta basu fi 14 ba zuwa 15, yawwa dan Allah kar aja lokaci", daga haka ta yanke ƙiran,




















*By Rumaisa Aliyu Inuwa(Rumyn Royal Star🌟)*
[2/5, 7:33 PM]


https://chat.whatsapp.com/GlC9QmyuWMG7PmC1vhGp4I






https://chat.whatsapp.com/EkTp0cXsTThKckSR3CG8aW






⚖️💧HANYAR RUWA⚖️


💦The way of water💦






Together
By


ƘANWAR SOJA


RUMYN ROYAL


ZAHRA ROYAL.




A heart toching story💔say No Rape❌








In the name of Allah, the beneficent the merciful.








After the successful of
(FARASHIN SO, RABI DANJA) & (FANSAR MACIJIYA), now we are back with (HANYAR RUWA).










🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*





PAGE 4️⃣













---





Mom dake zaune a parlour tana waya da alama da wata take "Yawwa Hajiya Talatu, dan Allah ki bincika min, so nake na samu wadda shekarunta basu fi 14 ba zuwa 15, yauwa dan Allah kar aja lokaci", daga haka ta yanke ƙiran,





Ɓangaren Hajiya Talatu wato Ƙawar Hajiya Lubabatu suna gama wayar ta ƙwalla ƙiran wata 'yar aikinta, "Asabe!", ba jimawa ta iso tare da faɗin "gani Hajiya", "Yauwa Asabe naji rannan kina hirar yara masu bara, ina son idan babu damuwa a samo min wata, ƙawata ke buƙatar 'yar aiki yarinya amma", cikin girmamawa Asabe ta ce "Hajiya ba za a rasa ba zan nemo ta in sha Allah", sallamarta tayi ta tafi....











Wani 'karamin gida ne kamar ganko sai guntun zana da ake kewaye a tsakiya alamar bayan gida ne a wanan gun yarda babban bishiyar limis dake bisa iska, sallama ake dukawa tunda 'kofar gankon amsawa tayi da siriirin muryarta wanda yanzu nan tagama kuka Ilham ce ta fitto daga 'karamin dakin dako rufi babo d'ankwalin kanta ta gyara ganin Asabe ne ta fad'a fuskarta da Murmurshi sannu da zuwa Adda Asabe " ta fadi"a tana dani damuwar ta amsawa tayi da fara'a,











"Ilham. Umma ke bata nan ne " da sauri ta amsa da cewa tana ciki shigo mana Adda Asabe kanta ke ciwo ," kafin tagama magana ma Asabe ta zari takalmin ta tashiga da takalmin ta kasancewar bata son taka 'kasar dake d'akin wanii yagaggiyar zani Ilham ta shimfiɗ'a mata matsayin abun zama, gaisuwa sukayi sosai da mutuntuwa nan Asabe ta zayyana mata komai shiru Umma tayi "to Asabe ban'ki maganar ke ba tabbas muna bukatar taimako amman ina tsoro kasancewar ILHAM amanar 'yar uwa tace kinsan aiki a gidan masu kud'in nan ,"











"Hadiza kinan ne kam na tausaya miki ne kinsan tare muka zo jahar nan tunda boom ya watsar fa muna 'kauyin mu dake Borno dangi duk sun mutu a wanan lokacin Ni kam kinga na samu aiki a gidan Hajiya Talatu kima dai taurin kai gariki a gidan ALHAJI BELLO RABE zatayi aiki to me matsalar duk sati tana zuwa duba ki tunda Hajiya tace yarinya taki so da ba haka ba aiki ma zakiye ,zaku samu abinchi Amman da bara zaku dogara ne ? Amman ba komai kinga tafiya ta ga ledaer taliya ce dafaffe na kawo miki "











" Asabe na amince tunda kin tabbatar da gaskiyar ke gobe kizo ku tafe zan mata magana " ciki da farinciki ta cire duba d'aya ta basu ta fitta da jin dad'i don hakan zai sa ta saki samun gurbin a zuciyar uwar d'akin ta Hajiya Talatu, da farko Ilham ba taso ta je aiki tabar mahaifiyar ta ba amman ya zatayi a hakan 'kadarrar ta tazo mata kuka yaye sosai nan ta fita da Adda Asabe da Umma ta Hadiza,













Bayan sunje Hajiya Talatu ta karɓe su hannu biyu, biyu, ta ce Asabe tabar mata su taje, aikuwa ranar sun cika timbinsu da abinci wanda rabonsu da suci irinsa kuma su ƙoshi sun manta ba zasu iya tunawa ba,





'Daki tasa aka kaisu, bayan sun huta ta ƙira su ta nuna musu illar bara da kuma irin abubuwan da take janyowa, "ki duba baiwar Allah kinada yarinya ƙarama kamar wannan, wasu mara sa imanin zasu iya ɓata mata rayuwa ko a sace miki ita a neme ta a rasa, kinga mai gari ya waya kenan, da ƙarfin ku da lafiyar ku zaku iya neman kuɗi ba zaku rasa ba, amma bara ba tada wani amfani a rayuwar mata harda mazan ma gaba ɗaya,








Dan haka zan aika 'yar ke zuwa gidan 'kawata HAJIYA LUBABATU dinga taimaka mata da wasu abubuwan duk da akwai masu aiki", nan ta tambayi sunan su ƙaramar ta ce "suna na Ilham wannan kuma Ummana ce", ta faɗa tana nuna wadda bata fi sa'ar Asabe ba ɗin ba, ita kuma ta ce "suna na Hadiza", murmushi tayi sannan ta ce, , farin ciki ne ya baibaye su, nan sukayi ta auno mata godiya babo ƙaƙautawa ,





( Nima godiya nayi amman ga Allah subhanahu wata'ala. )











Bayan kwana biyu ILHAM ta fara aikin ta gidan ALHAJI BELLO RABE inda take wa Hajiya girki girki kawai saboda akaiw wasu ma'aikatan gidan, sosai ta samu nistuwa don tana samun abinchi a inda albashi ta na farko ta saye kayan abinchi ta kai tun Umma kuma takan ziyarci ta a duk ranakon mako, tunda ILHAM tazo gidan ko da wasa bata ta'ba had'uwa da Alhaji BELLO ba kasancewar ma yana Abuja wani contract da ya samu mai tsoka da dole shi zaiji ba dan aiki ba.......








" Wallhi 'karya ne Malam Tanimu ba ka isa ka ja dani a 'kasar nan ba waye kai " wanda aka kira da Tanimu ne ya shafi hawayen sa da Murmurshi " ALHAJI BELLO kayi kuskure a rayuwar ka saboda kazallunchi ruhi da ba'a zalunta akwana lafiya Allah ya isa tsakanina dakai ka cuci rayuwata ka 'kwace min gona ta da ya kasance dukiyar marayu a garini nazo maka da 'korafi kasa an kashi ne kabar yara cikin maraice tsakani na da kai Sai Allah ya isa kuma aka gani tun a duniya sai Allah saka min don hakkin marayu bazai barka ba ,"











Hannu yasa ya tsinka mai mari a gigice ya farka yana had'a gumi "shige Tanimu ka mutu ma bazaka barni na huta ba d'an iska ne har namanta ma na damfari gonar ka ai kasuwanci naki aikin banza to ko nafi 'karfin ka balle fatalwar ka dole na kuma Kano a kwanan nan ....








Al'kalamin ƙanwar sojah-----------ce








[2/11, 2:28 PM] Narnah ƙanwar soja 💝💝💝💝💝: ⚖️💧HANYAR RUWA⚖️


💦The way of water💦






Together
By


ƘANWAR SOJA


RUMYN ROYAL


ZAHRA ROYAL.




A heart toching story💔say No Rape❌








In the name of Allah, the beneficent the merciful.








After the successful of
(FARASHIN SO, RABI DANJA) & (FANSAR MACIJIYA), now we are back with (HANYAR RUWA).










🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*










PAGE 6️⃣




Ta shiga tunani akan inda tasan wannan murya, sai dai sanin hakan babu amfanin tsayawa tana tunani yasa ta cigaba da abinda yake gabanta.




Tinda ALHAJI BELLO ya dawo ILHAM bata sake bari sun haɗu ba dan Talatu ta sanar da ita halin Alhajin na rashin son talaka, shi yasa take taka tsantsan akan haɗuwarta da shi.






ALHAJI BELLO shima ya shiga tunani da son tuna inda yasan fuskar Yarinyar da HAJIYA LUBABATU tace masa ƴar aiki ce, amma ganin zai takura kansa yasa ya kori tunanin, sai kuma mafarkin da yayi da Alhaji Tanimu ya faɗo masa "taya zaka addabeni a mafarki Tanimu?, ka kasa zama a ƙabarinka zaka shigar min rayuwa ka addabeni, to ahir ɗinka wallahi ni nama manta da wani filinka dana ƙwace balle azo ga kai kanka", ya faɗa yana kurɓar Coffee,




HAJIYA LUBABATU ce ta shigo da sallama a bakinta, murmushi ya sauke mata ita ma murmushin tayi kana ta ce "yau fa ka shammace mu Alhajina", kamota yayi jikinsa ya ce "kewar ki ce ta assasa, murmushi tayi ta ce "Alhajina na hango damuwa a tare dakao zanso ka sanar min da ita idan da damar hakan", ta faɗa tana tsare shi da kallo,




"Hajiya babu wata matsala kawai dai lamarin aiki ne" ALHAJI BELLO ya faɗa yana son kawar da zancen dan yasan halinta da bin ƙoƙƙofi, ƙyale shi tayi badan ta yarda ba.












HAJIYA LUBABATU tana yabawa da aikin ILHAM Yarinyar tana burgeta, hakan yasa take taimaka mata sosai dan ta hango Yarinyar tana da buƙatar taimako, hakan yasa take taimaka mata da suttura daga ita har Ummanta, hakan ya ƙarawa ILHAM ganin girman HAJIYAR dan ta fahimci HAJIYAR tan da tausayo ba kamar mijinta da yaƙi jinin talaka ba, Umman ILHAM da kanta ta zo taiwa HAJIYA LUBABATU godiya akan hidimar da take da su.










Yau ALHAJI BELLO yayi shirin zuwa KANO dan yana son zuwa Ƙauyen BICHI, HAJIYA LUBABATU tayi mamakin tafiyar tasa, dan rabon da yaje ba zata iya tunawa ba, haka kurum taji tafiyar bata kwanta mata ba, sai dai bata nuna ba, har farfajiyar gidan ta rako shi ɗauke da breafcase ɗinsa, dai-dai nan ILHAM ta dawo daga kaiwa maigadi Abinsa, cikin rashin sani ta ɗago aikuwa karaf idanunta dana ALHAJI BELLO ya sarƙe ana juna, firgicewa tayi ta rasa inda zata nufa dan ba ƙaramin tsoro mutumin yake bata ba tinda aka bata labarinsa, cikin tsawa ya ce "keeee!!!, ubanme kika tsaya yi anan?", a guje tabar wajen tana rawar jiki, "haba Alha.....", bai bari ta ida ba ya ce "duk laifin kine LUBA ya za'ai ki dinga kwaso min tarkacen mutane irin haka kina kawo min gida, wallahi na tsani ganin irinsu, amma har yanzu baki fahimce ni ba", ya faɗa a zafafe, ita dai haƙuri taita bashi har driver yaja suka bar gidan gaba ɗaya, sauke ajiyar zuciya HAJIYA LUBABATU tayi tana mamakin mijin nata.✍️














*By Rumaisa Aliyu Inuwa (Rumyn Royal Star🌟)*




PLS SHARING 👏
[2/11, 2:28 PM] Narnah ƙanwar soja 💝💝💝💝💝: ⚖️ 💧HANYAR RUWA💧⚖️
💦The way of water 💦






Together 💪
BY


'KANWAR SOJA


RUMMY'N ROYAL


ZAHRA ROYAL ,


A heart toching story 💔 say NO to rape❌








In the name of Allah the Beneficent the Merciful




_After the successful of (FARASHIN SO &. RABI DANJA ) & ( FANSAR MACIJIYA), now we are back with ( HANYAR RUWA )_






🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*








PAGE 5️⃣




Da sunan Allah mai rahma mai jin mai






____________________✍️aikin banza to ko nafi k'arfinka balle fatalwar ka dole na kuma Kano Kwanan nan.






Tashi yayi duk da cika bakin da yake yi hakan bai hana shi had'a zufa ba sharkam wayarsa ya zaro yana bada umarnin ayimai bokin d'in jirgi yau yau d'in nan sai dai cikin wayar akace "wallahi Alhaji yau jirgin dazai tashi zuwa Kano ya riga da ya tafi sai dai zuwa gobe" tsiki yaja yana kashe wayar tashi yayi ya shiga ban d'aki bai wani dad'e ba ya fito yana zama bakin gado wayarsa ya d'akko kamar zaiyi kira kuma sai fasa yana cewa "kai bari kawai inyi mata bazata sai dai ta ganni" (Hjy Lubabatu Kenna),








Washe gari kowa tunda safe ya saboda jirgi sai Kano,






Iliham ce cikin kitchen tana ta fama aiki tunani ta fad'a yau haka nan ta tashi da wata y'ar fad'uwar gaba aiki take tana tunani har bata sani ba saura kad'an ta yanke wadda ke kusa da ita mai suna Talatu tace "Ya salam Iliham tunanin mi kike ne?" Da sauri ta Sauke ajiyar zuciya tana hamdala dan kuwa Allah yayita da tsoron wani abu ta tab'a mata jiki tace "wallahi Talatu yau haka nan nake jin Yar kasala" ta ida maganar cikin y'ar shagwabar data zame mata jiki Talatu tace "ayyah mu maida hankali mu gama kinga Hjy ta kusa sakkowa" kama aikin mukai gadan-gadan saida mukai abu har guda uku kamar an gaya mana cewa mai gidan zai dawo.












Hjy Lubabatu ce zaune kan kujar porlo fitowar ta kenan ta d'aga waya tana video call da Faisal sunata fira yace "Mommy wallahi nayi kewarku sosai" cike da son yaron nata tace "ai gashi harka rame anya yaron nawa bai fara Soyayya ba kuwa wannan ramar ba kewarmu kad'ai bace" da sauri yace "haba Mommy Allah kuwa ba wata Soyayya" dariya ta saki cike da k'aunar yaron nata tace "kai da wasa nake nida nake so kayi karatu sosai",




Suna cikin firar sukaji dirar motaci cikin gidan da sauri Hjy Lubabatu ta kalle Faisal dake cikin wayar tace "anya ba Dad d'inka bane zai min bazata da zuwanshi ba" cikin murna Faisal yace "dama baya gida yau karki kashe Mommy a tarbeni dashi" da sauri ta amsa da to tana tashi ta nufi k'ofa dai dai ya shigo da sauri ta ware idon tana cewa "ashe kuwa kaine rungume sa tayi cike wayewa sai ta d'an sake shi jin Faisal na cewa "Ohh Mommy harkin manta dani Dad ya dawo ko" dariya tayi tace "kai ba dole ba" da sauri Dad yace "Oohhhhh my dear yakake ya school" cike da son iyayan nasa ya amsa dai-dai lokacin Iliham ke fitowa zata aje abinci dai-dai lokacin Dad idonsa yayi tuzali ta ita tunani ya fad'a shin ina yasan wannan fuskar ne,








Da sauri yace "Lubabatu wai bana hanaki kwashe-kwashe ba kinsan bana k'aunar talaka baida wani anfani jiba da Allah duk son cika mana porlo da wari" da sauri Hjy Lubabatu tace "haba Alhaji wane wari kuma sai dai in ni ke warin amma ba wani wari da nake ji ni" ida maganar tana shan mur Iliham kuwa da dama sauran kad'an ta shige kitchen d'in jin muryar da kamar tasan ta cikin tswa-tsawa gata da tsoro dama bata shirya ba ta fad'a kitchen d'in bata samo ganin waye mai muryar ba,






Talatu tace "naso na tsayar dake yanzu ake ce min mai gidan ya dawo kuma in yana nan ba'a fita in yana zaune porlo bai so yaga kowa dan wallahi sai kin kiyaye dan naga kina tafiya kamar marar lakka dan baya k'aunar talaka ko kad'an" ta ida maganar tana ci gaba da aikin ta Iliham kuwa ci gaba da wanke-wanken tayi itama abunda suka b'ata tana tunanin mai wannan muryar...................
















*ZAHRA ROYAL STAR CE*🌟✍️🥰










Comment and share Fisabilillahi🥰🙏
[2/12, 10:16 AM] Narnah ƙanwar soja 💝💝💝💝💝: https://chat.whatsapp.com/GlC9QmyuWMG7PmC1vhGp4I





https://chat.whatsapp.com/EkTp0cXsTThKckSR3CG8aW






⚖️ 💧HANYAR RUWA💧⚖️
💦The way of water 💦






Together 💪
BY


'KANWAR SOJA


RUMMY'N ROYAL


ZAHRA ROYAL ,


A heart toching story 💔 say NO to rape❌
















🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*






PAGE 8️⃣➡️9️⃣



SADAUKARWA


Wanan littafin sadaukarwa ce ga fittaciyyar ƙungiyar nan ta haziƙan marubuta , jajirtattu , ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION, muna
End Ads