x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 4 - HANYAR RUWA COMPLETE

  • 9001 words
  • 12000 words
  • Out of 25515 words

Category: Romance Story +18

Views 182

09 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
wa inna iallhin raji'oun cewar mutumin dake tsaye a kan dutsen da sauri ya juya domin fargaba da tsoron abin da ya gani.....











Umma da ke tsaye mai unguwa ne yace ,"ku suturta mata tsiraichin ta akai ta gidan su abin tausayi wanan shini babban matsala aika yarinya aikatau gidan masu kuɗi don samun abun duniya ga sakamako nan" ai duk wanda ya shiga motar kwad"ayi a tashar wulakanchi zai sauka tun yaushe Yusufu yace yana son yarinyar nan mai unguwa," cewar wani mai adaidaita sahu...













Hannu biyu biyu Umma tasa ta tallafo kan yarinyarda 'kuda suka fara zaryaa akan ta ganin ta mai kyau yasa ta tabbatar 'yar ta Iliham ce hijjabinta ta cire ta lullu'bata ganin hannun ta ke motse wata mata ce ta dafa da "kiye haƙuri ke kamata ga mai mashin a kaita gida Allah bata lafiyata " fad'a tana shari hawayin ta , cikin tausayawa.











Ruwan zafi Umma tayi ta mata wanka sai nan Iliham ta bud'e idon ta ,ganin 'barnar da akawa Iliham yasa Umma saki fashewa da sabon kuka ga jinin yake tsayawa kamar maza biyar ne suka mata fyad'i Iliham dake ganinta sai hawaye ba ummm ba ummm da ido taki ganin Umma nan ta tunanin ta ya tsaya akan me yasa bata mutu ba ta dawo gida a raye?








Dubu biyar ce Umma ta samu ta d'auka "sannu Iliham bere naji shagon mai maganin asibitin nan na sayi miki magani da zai tsayar da jinin nan ya rage miki rad'ad'i 'yata " Kai ta girgiza mata har yanzu hawaye kawai kibin kumatun ta duk idon don sauya sunyi lu'bu'lub'u dasu ko yatsar ta bata iya d'agawa duk abinda Umma zata mata tayi mata tass harda gunzuko tayi mata ta fita gidan.....











"Iro gata chan mai shud'in himmar koren nan itta ce uwar yarinyar kasan Bara sukiye daga baya ta tura yarinyar gidan masu kud'i a cikin gari ne na manta sunan mai gidan ma , kaga yanda aka wa yarinyar daga daga kuwa Mallam kwaɗaye a bin duniya da ace ittace zata yi aikatau ne da sauki amman ta tura yarinya mai shikkaru sha biyar fa, kai amman anyi azzaluma mata ", haba don Allah bani labari nawa ai ance uwar ta ce 'yan gudun hijira " dariya sukayi su dukka biyu ..














Duk abinda suka ce akan kunnen ta hawaye ta shari kamar zata wucce su ta dawo " kusani ban zallunchi 'yata ba iri irin kune masu zaluntar ta ,duk wani bawa mai numfashi a doron 'kasa Allah na jarabtan sa da jarabawar rayuwa namu jarabawar kinan ,sanan Iliham na da gata a duniya domin Allah subhanahu wata'ala ne yace " .








Duk wani tsanani yana tare da sauk'i sanan shi mai jin'kai mai rahama a tsakanin bayin sa, sanan kunce zaku ga waye gatan ta a duniya, tabbas Iliham na da gata don ta yarda da cewa Allah d'aya ne dashi kuma muka dogara mu ka kai 'karar wanda suka zallunchi mu a gaban sa."











Da sauri tabar gun tana matse hawayen ta "me mutane suka d'auki matsalar fyad'i , alhali kai baka fi "karfin jarabawar ka ba, wanda ya faru da su bada son 'ra'ayin su ba , kuma ba da gangan ba, babo wanda yafi 'karfin 'kaddarar rayuwa sa . duk abinda ya faru mai kyau ko mara kyau already an rubbuta cikin littafin ƙaddarar tabbas wanan ITTA CE 'KADDARA TA," littafin sister Zahrah Royal Star ce..




















AL'KALAMIN ƘANWAR SOJA ✍️💞⚖️💧HANYAR RUWA⚖️


💦The way of water💦






Together
By


ƘANWAR SOJA


RUMYN ROYAL


ZAHRA ROYAL.
# %


A heart toching story💔say No Rape❌








In the name of Allah, the beneficent the merciful.








After the successful of
(FARASHIN SO, RABI DANJA) & (FANSAR MACIJIYA), now we are back with (HANYAR RUWA).










🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*










PAGE 1️⃣6️⃣➡️1️⃣7️⃣




Mutane ne suka taru a kanta suna salati, dan babu wanda yake tunanin wannan matar zata rayu.








Cikin kiɗima drivern da yake tuƙa wani matashin Saurayi ya tsaya yana salati iya ƙarfinsa, shima matashin salatin yake gami da fita daga motar kamar yadda drivern yayi, Saurayin daka ganshi zaka hangi kyau da hutu a tare da shi, bashida tsawo sosai amma ba gajere bane, yana da ƙirar gwarazan maza, kana ganinsa kasan ko waye ya tara ko kuma nace Iyayensa sun tara masa, kyakykyawa ne duk da bashida hasken fata amma ba baƙi bane hutu ya fito a ainihin kyan fatarsa,






"maza muje mu ɗakkota mu kaita Asibiti", cewar Saurayin, da gudu suka kutsa kai cikin dandanzon mutanen da suka zagaye Umma, ba ɓata lokaci aka kaita mota da taimakon wasu mutane, jan motar sukai suka nufi Asibiti, kasancewar private ne suna zuwa aka karɓesu aka shiga bawa Umma taimakon gaggawa, hankalin matashin ya tashi fatansa dai kar yayi silar mutuwar matar nan.
















Wajen awansu Uku a tsaye yana tsaye gefansa driver ne yaji wayarsa tayi ƙara ganin mai ƙiran ya sanya shi ɗauka da sauri, Mahaifinsa ne yake tambayarsa yaji shi shuru kuma tin ɗazu jirginsu ya sauka, amsa masa yayi da gashi nan zasu ƙaraso, bayan ya gama biyan komai suka bar asibitin, saida yaje gida yake sanarwa Iyayensa hatsari suka samu a hanya, sai dai bai sanar dasu komai ba kasancewar bamai yawan son surutu bane, duk da sun tambaye shi amma bai sanar dasu gundarin abin ba ya dai ce babu matsala.














Sai dare ya koma kuma alhamdulillah, likita ya sanar masa buguwa ta ɗanyi a kafaɗarta sai ciwukan da taji kuma zasu warke nan bada jimawa ba, shiga yayi ya ya ganta bacci take, kallonta yake da tausayi, dan ya fahimci tana cikin halin rayuwa kasancewar kayan da yake jikinta ba sai an faɗa masa ba, yana tsaye wayarsa tayi ruri, fita yayi ganin mai ƙiran yayi murmushi ya ɗaga "Barrister Khaseem howfar?", ya faɗa yana zama a kujerun da suke farfajiyar wajen, "bakada mutunci ace ka dawo amma baka sanar min ba?", cewar Barrister Khaseem, "sorry Abokina ban samu nutsuwa bane sai yau, amma ina nan zan shigo", "ok kana ina yanzu", Khaseem ya tambaya, kallo yabi harabar asibitin da shi ya ce ina Asibiti", nan ya labartawa Abokin nasa abinda ya faru jiya hanyarsa ta dawowa gida daga filin jirgi, ya jajanta masa kana sukai sallama har yana masa alƙawarin zuwa asibitin idan ya gama abinda yake.










A daren Umma ta farka da sunan ILHAM a bakinta, abin ƙarin ruwan da yake jikinta ta fuzge, tasowa yayi ya ce "baiwar Allah kar ki jiwa kanki ciwo", kallonsa take ta ce "ILHAM" bai fahimceta ba ya ce "ki zauna bari na ƙira likita, "Bawan Allah ina ne nan?", "Asibiti" ya bata amsa, maiya kawo ni Asibiti bayan Yarinyata tana can bansan halin da take ciki ba, na baro ta bata da lafiya", tambayar ta yayi a wace unguwar take, sanar masa tayi har inda suke, ganin tana buƙata likita ya ƙara duba ta yasa shi fita, tana zaune likita ya shigo , "ki koma ki kwanta har yanzu jikinki baiyi ƙwari ba", cewar Likita, "a'a gida zani na bar Yarinyata batada lafiya", ganin zatai gardama yasa likita yi mata allura bacci, aikuwa nan take baccin ya sure ta, gida Saurayin ya tafi dan dama rasa inda zashi yayi ya zauna a ɗakin da Umman take.








ILHAM kuwa shuru taji Umma bata dawo ba hankalinta ya tashi ga shi wani irin dishi-dishi take gani ƙasanta idan banda zugi babu abinda yake mata, kuka take mai cin rai tana ƙiran sunan Umma da muryarta wadda bata fita, ga faɗuwar gaba da take riska a kowace daƙiƙa, da rarrafe taje ta ɗaura alwala ta zo ta tada sallah a zaune, bayan ta idar ta ɗaga hannunta sama "ya Allah kai kaɗai ne gatana banida kowa sai kai sai Ummana, ya Allah ka saka min, ya Allah kamar yadda ya ɓatamin rayuwa Allah ka ɓata masa tasa, Allah ya saka min ya rabbi, ya cutar dani cuta mafi tsanani, ya rabbi kana gani ka saka min", kuka take sosai hakan ya hana ta ƙarasa addu'ar, har dare ya fara sosai babu Umma wannan karon kukanta ne ya ƙaru, har soro ta rarrafo tana leƙe amma bata hango ƙurar Umma ba, zama tayi a soron tana jajjera ajiyar zuciya, ganin dare yayi sosai ILHAM ta saddakar ta kuma rasa Ummanta kuka take wanda ya haddasa mata tsananin ciwon kai, ga zazzaɓi daya rufe ta, a soron ta kwana wanda baccin wahala ne ya ɗauke ta.












Yau kwanan Umma ɗaya a asibiti, farkawa tayi da sunan ILHAM a bakinta, da sauri ta sakko a gadon ta fice daga ɗakin direct hanya tabi burinta ta koma gida, aikuwa ba wanda ta haɗu da shi a hanya, wajen gate ɗin ta nufa napep ta tare ta gaya masa unguwar da zai kaita, aikuwa ba jimawa suka iso, sai a lokacin ta tuna batada kuɗi a jikinta, roƙarsa tayi akan bari ta je ta ɗakko masa yana ta masifa wai zata ɓata masa lokaci, a soro taci karo da ILHAM tana kwance saurin zama tayi ta janyota jikinta tana ƙiran sunanta, a firgice ILHAM ta farka ganin Umma yasa ta fashe da kuka ita ma Umman kukan take, "Ummana ina kika je?", ganin ciwuka a fuskar Umma yasa gabanta faɗuwa gami da tallafo fuskarta tana cewa "Umma meya same ki?", "tashi mu shiga ciki, a hankali ta ɗaga ta suka shiga, zaunar da ita tayi ta shiga inda kayansu yake ta ɗakko wata daƙunanniyar ɗari biyu ta fita ta bawa nai napep, daƙyar ya karɓa yana mita, ita dai bata bi tasa ba ta komo ciki.










Da safe ya dawo Asibitin sai dai me babu Umma babu dalilinta, Likita ne ya shaida masa ya zo dubata yaga bata nan da alama kuma ta tafi ne, sosai Saurayin yaji babu daɗi, magungunanta Likitan ya rubuta ya ce tinda yasan inda take ya siya ya kai mata, haka kuwa akai bayan ya siyi magungunan ya ƙira Khaseem dan yayi masa rakiya, tare suka tafi Unguwar da Umma take dan kai mata maganinta.✍️


















*By Rumaisa Aliyu Inuwa(Rumyn Royal Star🌟)*














*Alƙalamin mu Ƴancin mu✍️*⚖️ 💧HANYAR RUWA💧⚖️
💦The way of water 💦






Together 💪
BY


'KANWAR SOJA


RUMMY'N ROYAL





ZAHRA ROYAL ,


A heart toching story 💔 say NO to rape❌








In the name of Allah the Beneficent the Merciful




_After the successful of (FARASHIN SO &. RABI DANJA ) & ( FANSAR MACIJIYA), now we are back with ( HANYAR RUWA )_






🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*








PAGE1️⃣4️⃣➡️1️⃣5️⃣






DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN K'AI






________________✍️Babo wadda yafi k'arfin k'addara a rayuwarsa tabbas wannan *ITA CE K'ADDARATA* (my now book),






Koda ta isa gidan ta tadda Iliham sai uban kuka take ba k'ak'k'autawa ga wani irin rad'ad'i da take ji da sauri ta rungume Iliham magana takewa Iliham d'in tana aikin rarrashi amma ina ba bakin magana domin kuwa taga alama Iliham bata iya cewa komai rungume ta k'ara ta durzar kuka mai tab'a zuciya,






Iliham kuwa wani irin take ji kamar ba'a duniya take ji take kamar kwakwalwarta ta juye ne wai mike faruwa da ita wannan duniyar ba abinda ke cikinta sai rud'e da tashin hankali inba kai wani bane a cikin k'asar, kallonta Umma take ganin tana kallon sama hawaye na shatata a idonta ba k'ak'k'autawa kamar an bud'e faffu da kyar Umma ta samu ta ciccib'eta takai ban d'aki cikin ruwan zafin ta sata wata irin y'ar k'ara ta saki mai cike da azaba duk da gashin da Umma tayi mata tafa gano anjamata rauni ne dan kuwa jini ne keta fita har yanzu,




Cike da tashin hankali ta fita domin zuwa asibiti da kyar ta samu ta d'akko ta sai asibiti Iliham da har yanzu hawaye take bata uhum bata uhum uhum koda suka isa asibitin kin karb'ar su akai dan kuwa sun fahimce mike faruwa cike da tashin hankali Umma ke masu bayani su taimakawa tilon d'iyarta ta wata Dr dake kallon a wuk'ance tace "kinga Malam dole fa sai kun tahu da dan sadda anba haka sai dai ku kwana a nan aikin banza kawai hala kin aika d'iyar taki ne tallah taje ta zubar da mutumcinta in..... Kamin ta ida maganar Umma ta wanke ta wani mari tana huce nunata tayi da yasa tace "wai miya sa mutane da yawanku baku da tunani ne wai ku baku san k'addara bane baki da tarbiyya ki kalli tsabar ido na kike gaya min wannan maganar" tana nunata da yatsa hawaye na shatata a idonta likitar data mara kuwa da sauri ta kila masu tsaron asibitin tana cewa "baza baza ku fitar min dasu" da sauri Umma tace "a'a y'ar nan basai an fitar damu ba zamu fita ai na Allah basa k'arewa ke kuma kije Allah ya shirye ki" ta idasa maganar wasu hawayen tausayin su na zubawa Iliham dake kallon komai ji take inama ta mutu kawai da wannan bala'in ji yadda har an fara nuna masu tsana inaga nan gaba mi yasa mutane suke hakane haka suka koma gida cike da mawuyacin hali da Iliham d'in take ciki zuciyar Umma har wani zafi take.


Kai tsaye batai magana da Iliham dake kwance rai hannun Allah ba dan kuwa wani irin rad'ad'i take ji a ko ina na jikinta kai tsaye Umma gidan Hjy Lubabatu ta nufa,




Tana shiga ko sallama bata samu tayi saboda tashin hankali a porlon gidan ta taddasu Hjy Lubabatu nama Alhaji BELLOH nasihar cewa yafa ji tsoron Allah ganin shigowar matar da sauri Hjy Lubabatu ta tashi tsaye gabanta na dukan uku uku da sauri tace "anga Iliham d'in in..... Kamin ta idasa Umma ta tareta rai a b'ace tace "na ganta mana tunda mijinki bunsuru ne shi wallahi nasan cewa kai ka aikata mata wannan tanyan aikin kuma ka sani cewa..... Tunkan ta idasa Alhaji BELLOH a hargitse yace "ke da'alla dakata sai mi inni nayi ai baki da wata shedar cewa ni nayiwa d'iyarki fad'e dama can d'iyarki y'ar iska ce in..... Kamin ya idasa maganar Umma ta fashe da wani irin kuka mai tab'a zuciya cikin kuka tace "wallahi y'ata ba y'ar iska bace kuma wallahi ka shirya SAKAYYAR na nan tafe" cike da zafin rai Alhaji BELLOH "ke har kin isa ki shigo gida na kina gaya min wannan maganar to kije duk inda zaki kikai k'ara ta kuma daga yau karna sake ganinki a cikin gidan nan inaba haka ba wallahi sai nayi miki rashin mutumcin da baki tab'a tsammani ba fice min daga gida nace" ya ida maganar yana nuna mata k'ofa Hjy Lubabatu itama kuka take kawai saita fara hawa sama da sauri Umma da zuciyarta take jin wani iri rad'ad'i kamar zata buga tace "zan fita mana ai basai kace" sai kuma ta d'aga kanta tana duban Hjy Lubabatu tace "ke kuma kinsan ko miye da mijinki yake aikatawa saboda wani dalili naki zaki nemi rufa mai asiri to ki sani AKWAI ALLAH" tana gama maganar ta fice daga gidan.






Umma na tafiya a kan titi tana hawaye yanzu ina zata sa kanta wannan wacce irin masifa ce harta zo tsakiyar titi bata sani ba motoci nata mata hon amma ina hankalinta yayi gida wajan Iliham tada baro cikin mawuyacin hali wata motaci ta taho a guje tayi ciki da Umma sai dai taji anyi sama da ita mutane sai sallalami suke duk mutane sun yayyame ta motar data bigeta kuwa ko tsayawa batai ba...............
















*ZAHRA ROYAL STAR CE*✍️








Comment and share Fisabilillahi🥰🙏⚖️💧HANYAR RUWA⚖️


💦The way of water💦






Together
By


ƘANWAR SOJA


RUMYN ROYAL


ZAHRA ROYAL.




A heart toching story💔say No Rape❌








In the name of Allah, the beneficent the merciful.








After the successful of
(FARASHIN SO, RABI DANJA) & (FANSAR MACIJIYA), now we are back with (HANYAR RUWA).










🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*










PAGE 1️⃣8️⃣➡️1️⃣9️⃣








Kaka kuwa akai bayan ya siyi magungunan ya ƙira Khaseem dan
End Ads