daga ni har kai, dan yayi alƙawarin saki na idan maganar nan ta fita?", ta faɗa muryarta na rawa, wani murmushun takaici yayi ya ce "I hate U Dad, hate u somuch, Yarinya ce ƙarama, kuma basuda shi talakawa ne why ba zaka tsaya a tsanar su kawai ba saika keta musu haddi, Mom mijinki ba shida imani ko kaɗan, na tsani mutum mara imani wanda baisan komai ba sai kansa, Mom Dad ya ɓata wayonsa, yanzu da wane ido zan kallo Barrister Khaseem wanda tare da shi muka ji komai, kuma ya zanyi da Alƙawarin da nayi zan ƙwatowa Yarinyar haƙƙinta, Mom idan ni na janye kina tunanin Khaseem zai janye, kuma kina tunanin zai rufawa Dad asiri, kuma koda mun rufa masa asiri mu duka uwar Yarinyar kina tunanin zatai shuru, kowa yasan waye ALHAJI BELLO RABE a wannan gari?", mom kallon yadda yake hawaye yake sosai, bata taɓa ganin kukansa ba da wayonsa dai, sai yau cikin ƙasa da murya ta ce "Son ka nutsu, abinda yasa bazan tona asirin Mahaifinka ba abu ɗaya ne ya min kashedin zai sake ni, nima banji daɗin abinda ya faru ba FAISAL ka yarda dani", tashi yayi yabar wajen tana ƙiransa ko juyowa baiyi ba dan kansa zafi yake masa.✍️
*By Rumaisa Aliyu Inuwa(Rumyn Royal Star✍️)*
*Alƙalamin mu Ƴancin mu✍️*⚖️💧HANYAR RUWA⚖️
💦The way of water💦
Together
By
ƘANWAR SOJA
RUMYN ROYAL
ZAHRA ROYAL.
A heart toching story💔say No Rape❌
In the name of Allah, the beneficent the merciful.
After the successful of
(FARASHIN SO, RABI DANJA) & (FANSAR MACIJIYA), now we are back with (HANYAR RUWA).
🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_
*Alk'alaminmu 'yancinmu*
PAGE 2️⃣4️⃣➡️2️⃣5️⃣
" Son ka nutsu, abinda yasa bazan tona asirin Mahaifinka ba abu ɗaya ne ya min kashedin zai sake ni, nima banji daɗin abinda ya faru ba FAISAL ka yarda dani", tashi yayi yabar wajen tana ƙiransa ko juyowa baiyi ba dan kansa zafi yake masa.
Dafa kanta tayi dake sara mata "inallillahi wa inna iallhin raji'oun , ya Allah ka taimaka min wai me yake shirrin faruwa da iyalai na ne na tabbatar Alhaji BELLOH yaji labarin nan komai zai iya faruwa ne duk tunani na ma ta ya akayi ya had'u dasu oh my God"..
"ka ganni kaga wanda zai tsaya abakin 'kofa ne to ne ma'akachi ne d'an sa'ko daga area court 3 dake nan Bichi takadar sammachi na kawo wa Alhaji BELLOH RABE " dariya Iro ya fashe dashi "aikin banza kinan ko dai kullum baku gajiya da akawo 'korafi ko kawo wa Alhaji BELLOH mutumin da take juya A'lkalai da lawyoyi ,"tsaki yaja ya amshi ya bud'e masa gate har office ya rakasa tura.door nin yayi ko knocking baiyi ba.
"Iro ashe baka da hankali ko kad'an bansaniba bance kar ka shigo office Nan ba har sai na kiraka ,"bai idda maganar da zaiye gaba ba ya hango wane saurayi cikin shigar ba'kar wando da farar riga mai tambarin judge of appeel , zuciyar sa ce ta buga ya saba da kallon irrin hakan amman me yasa a wanan karon yaji abun ya sauya mai linzami, "kai kuma daga uban wane court ," murmurshi yaye "Alhaji kenan yanda aka saba an kawo 'kararka ga takardar "ya fad'a yana mi'kamai ,"
"Aikin banza kinan " zaro kudi yayi bundle biyu da zai kai dubu d'ari Ukku "ga wanan a watsalar da 'karar a kore shari'ar" murmurshi mai ciwo gayen yayi "ya'laɓai wanan karon ne na tabbatar bazaka tsira da zuwa court ba domin ne kaina bansan waya kawo 'karar ba sai dai abin mammaki shine ranar zama ka tanadi babban lawyer da zai kare ka " aikin banza matsiyace kawa kanka ,ai wallahi bbao mahalu'ki da ya isa yasa na tsaya gaban wanan kurtun a'kaw'kin don amsa wasu munanan tambayoyi , karanta min 'karar"...
"Alhaji bana da hurumin sauraren banayan nan ko karanta maka yanzu mu haɗu a court ya fad'a Yana tafiya da sauri sauri ," tashi hankali kam Alhaji bai gani ba sai ya tsaya yasan cewa d'an sa ne ya kai 'kararsa don yayi wa haosemaid fyad'i" cewar yaron a zuciyar sa "tabb akaiw kallo a wanan lokacin"...
"Alhaji BELLOH ne ya bud'e takardar nan ya fara karanta wa kamar bai iya karatun ba , Iro dai tsaye akan sa kamar bishiya yana ganin irrin tashi. hankalin da Alhaji ya shiga ga wani gumi da ke kitto mai a jikin sa kamar wanda basir ya kama bai warke ba.
JUDIGAL FORM 3,
SECTION'S 131 and 141 ACJL ADS 2000
IN THE BICHI AREA COURT NO 89 KANO STATE,
Case number CRW 232
between the complainer BARRISTER SUHAIMA ABUBAKAR , And BARRISTER KHAZEEM YUSUF , AND BARRISTER. FAISAL BELLOH RABE
DEPENDER
ALHAJI BELLOH RABE
Tsayawa yayi da kallon rubbutun don jire ne yake barazanar d'auke buguwar zuciya sa, dafa table nin yayi Iro ye maza ka kira min Abdulsamad a office nasa " cikin minti biyu so ga sunan ga wanan takardar karanta min da kyau don Ba fahimci komai ba da mammaki a fuskar Abdulsamad ya chigaba da karanta wa "a tai'kaice Alhaji an shigar da 'karar ka bisa zargin ka da aikatawa yarinya 'yar shikkaru goma sha biyar da fyad'i da kuma tuzartarwa ga mahaifiyar yarinyar kasancewar 'yar aikin gidan ka ne..
Da kuma cin zarafin da tilasta wa da barazanar kissan kai ta ta hanyar sanya mata a'l forced acid reflux domin samun damar kitta mata haddi , ... wanda suka shigar da wanan 'karar kuma , Sune dai wanda ka gani a saman nan cikin su harda D'anka wato Barrister Faisal da kuma 'korarriyar wacce tasan bakin aikin ta duk Nigeria an santa a matsayin jajirtaciyar Barrister Mai aiki da fasaha da haza'ka da aiki tu'kuru wato dai Barrister Suhaima Abubakar ( ta cikin littafin DUHU CIKIN HASKE MY BOOK) ,,
"ALHAJI BELLOH kasan cewa kwana nan ma tayi wining case na matsalar rape a birnin Kaduna abin da yaban mammaki ta ya akaye tazo nan don wanan case nin don gaskiya ba'a samun ta da saukii, amman " kai don Allah rufe min baki kazo ka gayyamin wacce ce itta ne kai bakasan tashin hankalin da na shiga ba ko get out please , " Bindigar sa ya zaro ya Shiga mota a gaggauce sai hanyar gidan sa da gudu mai gadi ya bud'i 'kofar don ganin Alhaji a wanan Lokacin ba 'karamin tashin hankali ba ne mussaman ma da yaga ko takalimi babo a 'kafar sa ......
"LUBABATU ! LUBABATU!! LUBABATU!!! wai ina kike munafuka maciya amana algulguma mayaudariya ina kike kizo nan ke gayyamin waye asalin uban Faisal a duniyar nan !!!?
In the name of Allah, the beneficent the merciful.
After the successful of
(FARASHIN SO, RABI DANJA) & (FANSAR MACIJIYA), now we are back with (HANYAR RUWA).
🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_
*Alk'alaminmu 'yancinmu*
PAGE 2️⃣6️⃣➡️2️⃣7️⃣
"Lubabatu! Lubabatu! Lubabatu!!! Wai ina kike munafuka macijiya amana algunguma mayaudariya ina kike kizo nan ki gayamin waye aslin uban Faisal a duniya nan?".
Cike da tashin hankali take sakkowa daga saman bene ta ce "haba Alhaji wanne irin kirane wannan haka in..... Tunkan ta rufe baki ya d'auke ta marin daya sata dafe k'uncinta tana kallonsa cike da mamaki ta k'ara cewa "Alhaji anya kana cikin tunaninka kuwa?" Wata irin ashar ya danno ya ce "gidan mahaukata ne a kaina baki ji mi nake cewa bane ni zaki rainawa wayo waye uban Faisal ne?", cike da d'unbin mamaki take kallon sa da kyar ta bud'e baki ta ce "kamar ya ban gane waye ubansa ba bayan kai", "rufe min baki na ce to inba nina haifesa ba ni zai tozarta ni Faisal ki gaya min gaskiya waye ubansa?", Ya idasa maganar a tsawace.
Tunkan ya k'ara wat maganar Faisal ya shigo rai a b'ace yana cewa "karka sake dakar min uwa kuma shari'a kamar anyita dakai ni dama ace ba kaine mahaifin nawa ba miye ka aika haka Dad why dan Allah?", ya idasa maganar yana sakin kuka kamar k'ara min yaro.
Tsaki Alhaji BELLOH yayi yana wani makirin murmushi ya ce "mu zuba mu gani nida ku shege ka fasa", ya gama maganar ya haura sama a zuciye da sauri Faisal ya ce "Mommy please kice min Dad ba shine ya haife ni ba" kallonsa take hawaye na wanke mata fuska kwata-kwata ta kasa magana rungume d'an nata tayi tana buga bayansa alamar rarrashi.
A wajan Alhaji BELLOH kuwa koda ya shiga d'aki waya ya kira yana cewa "ku tabbatar kunje har gidan su yarinyar kun k'arasa min ita har lahira bana son ta kai safiyar gobe" daga cikin wayar naji wata murya bud'and'iya irin ta gaggun y'an iska ya ce "an gama oga umarni naka cika aiki namu", katse wayar yayi kwata-kwata ba imani a ransa shifa indai kan a tab'a mutumcin sa ne to kuwa zai iyayin komai tabbas shi anma zai tab'a mutumcin wasu ai.
Cikin dare y'an daban Alhaji BELLOH suka haura gidan su Iliham sai dai sunyi rashin sa'a dan kuwa suna asibiti har yanzu jikinta bai wani samu sauk'in kirki ba sosai sukai watse da kayan gidan suka babbaza komai suna kiran Alhaji suka ce "ranka ya dad'e bafa kowa a cikin gidan nan" wata irin tsawa ya buga masu ya ce "kamar ya ba kuwa ina zasu tafi to ko wani munafikin ne ya sanar dasu shirin mu kun duba sosai kuwa?", Y'an daban ya ce "an duba ko ina Oga ba wani halitta dake rayuwa a cikin gidan yanzu".
Sosai Alhaji ya shiga tashin hankali dan kuwa Monday ne za'a fara zama k'otu.
Sosai Iliham ke k'ara samun kulawa sai dai har yanzu bata wani magana sosai dan kuwa da an kira sunana Alhaji BELLOH firgita take har tana neman shid'ewa sosai abun ya d'aga su Faisal hankali harda Ummah da kyar da zub'in goshi ta fara basu baya nan duk abinda ya faru sai dai ana zuwa wajan daya keta mata mutumci kawai masuyi aune ba ta tafi luuuuuu ta suma dan kuwa wani irin masifaffan bugawar zuciya ne da b'aci ran tuna abun sosai take tsoron Alhaji BELLOH in aka kira sunan shi kamar an mata Albishir da mutuwa sosai Ummah ke kuka tana cewa "kun gani ko tabbas ya dasa mata tsoron sa taya za'ai yarinya bazata tsorata ba ya tashi ya afka mata da k'arfin tuwo" ta idasa maganar tana shashshakar kuka......✍️
*ZAHRA ROYAL STAR CE*🌟✍️
Comment and share Fisabilillahi🥰🙏⚖️💧HANYAR RUWA⚖️
💦The way of water💦
Together
By
ƘANWAR SOJA
RUMYN ROYAL
ZAHRA ROYAL.
A heart toching story💔say No Rape❌
In the name of Allah, the beneficent the merciful.
After the successful of
(FARASHIN SO, RABI DANJA) & (FANSAR MACIJIYA), now we are back with (HANYAR RUWA).
🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_
*Alk'alaminmu 'yancinmu*
*Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai*
PAGE 2️⃣8️⃣➡️2️⃣9️⃣
Likita aka ƙira ya fara bata taimakon yadda zata farfaɗo, aikuwa tana farfaɗowa ta sa kuka, kukan da babu ranar da zata dena shi, dan ko fuskar ALHAJI BELLO bata son sake tunawa, da za'a bata damar kisa da babu abinda zai hana bata kashe Alhaji BELLO RABE ba.
Har kawo wannan lokaci Umma da ILHAM basu san cewa FAISAL ɗa ne ga ALHAJI BELLO RABE ba sa bo da bai sanar musu ba haka bai bari Khaseem ya sanar da su ba, ya ce ya bari lokaci ne zai nuna hakan, sosai Khaseen ya jinjina jarumtar FAISAL dan ya shirya tinkarar Mahaifinsa a kotu, hakan ya ƙara masa ƙwarin gwiwa shi kansa Khaseem ɗin, sai dai yana tausayawa FAISAL matuƙa dan ya tabbatar Kotu zata yanke hukuncin daya dace ga ALHAJI BELLO RABE, da tunanin shari'ar yake kwana yake tashi.
Umma tana jin daɗin yadda suka tsaya tsayin daka wajen ƙwatarwa ILHAM haƙƙin ta, in banda albarka babu abinda take sa musu, da tayi tunanin masu tausayi da imani sunyi ƙaranci a duniyar nan, ashe suna nan suna shawagi a cikinta kawai yawa ne da basuda shi, Allah kuma ya dube su ya haɗa su da su, takan godewa Allah akai-akai.
ALHAJI BELLO RABE daya haɗa tagumi da alama yayi nisa a tunani, dan tinda FAISAL ya riƙe wuta ganin sai ya kaishi kotun nan yake cikin wani hali, da wani ne ba FAISAL ba da babu shakka saiya kashe shi idan yaso idan gawa tana shari'a sai tasa ya fara, amma son da yakewa FAISAL wanda shi kaɗai Allah ya bashi ba zai taɓa bari koda ƙwarzane ya samu ba, Hajiya Lubabatu ce ya shigo tin ɗazu amma baisan ta shiga ba, zama tayi ta riƙo hannunsa cikin nata, a firgice ya kalle ta dan ya tsorata ainun, ganin ita ce ya ɓata rai ya fizge hannunsa ya ce "ki gaggawar tashi ki bar ɗakin nan kar na ci mutuncin ki", da mamaki ta kalle shi dan kwana biyu baida aiki saina hantararta da tazo guri zai tashi, "Alhaji wai me kake haka ne, me nayi maka da zafi zaka dinga wulaƙanta ni kamar ba matarka ba", ta faɗa cikin takaicin abinda yake mata,
"Ai billahillazi Luba idan har ba zaki sa ɗanki ya janye ƙarar daya kai ba bazaki taɓa samun yadda kike so dani ba, kuma ki rubuta ki ajiye wallahi idan har aka ci galaba a kaina kin shiga uku daga ke har ɗanki, kuma duk yadda zanyi sai nayi lamarin nan ya lalace", cewar Alhaji.
Murmushin takaici tayi ta ce "Alhaji kenan, wallahi wani lokacin kana bani mamaki, ka aikata abu kuma ka juye shi akan waɗanda basu ji ba basu gani ba, shi yasa ai aikin danasani baiyi ba, da ace alkhairi kake aikatawa a rayuwarka da baka furgice haka ba, daka zauna lafiya kamar kowa, amma ka kasa zaune ka kasa tsaye yanzu wa gari ya waya, ni dai banida hurumin hana FAISAL aikinsa wallahi",tana gama faɗa ta tashi ta barshi yana buɗe da bakinsa yana mamakin abinda Luba ta faɗa masa.
Duk wani bayani an haɗa su, ILHAM ta sanar dasu duk abinda ya faru, sun haɗa duk wani bayanai ranar shiga Kotu kawai suke jira, ranar da Khaseem ya ɗauki Umma ya kaita gida dan ɗakko wa ILHAM kaya nan ta taradda yadda aka hargitsa musu gida da kaya, da alama an shigo gidan, sai dai babu abinda suka ɗauka, toma me zasu ɗauka banda tsummokara Umma ta faɗa a ranta, ganin haka Khaseem ya fahimci akwai matsala, shi yasa bayan an sallame su ya kaisu gidansa, tinda dama shi kaɗai ne, da Umma taƙi sai da yayi mata bayanin ALHAJI BELLO zai iya komai dan yaga ba'ai wannan shari'ar ba, jin haka tsoro ya ƙara kama su Umma, hakan yasa suka bishi gidansa, FAISAL hakan yayi masa daɗi dan dama yana zargin Daddyn nasa.
MONDAY
Kotun cike take da mutane, wasu sunzo ne dan tasu shari'ar wasu kuma sunzo kallo ne kamar yadda aka san kotu da haka, can na hangi Umma da ILHAM da tayi zuru-zuru, dan jikinta har wannan lokacin babu ƙwari dan riƙe da ita Umma take, ta lafe a jikin Umma, Barrister FAISAL da Barrister Khaseem suna zaune a kujerun da aka tanada domin lauyers, sai Alhaji BELLO RABE da shima yana zaune fuskar nan babu alamar rahama tattare da ita, sai wurga ido yake yana jin kamar ya kashe kowa dake cikin kotun, zuwa wani lokaci Alƙali ya bayyana cikin kotun kowa tashi yayi alamun girmamawa tare da faɗin "Kotuu!!", cikin muryar gardawa da matsakaita, sai bayan ya zauna sai kowa ya zauna, mai karanto ƙara ne ya tashi ya karanto ƙara kamar haka, "a yau Alhamis 14/9/2023 zamu saurari ƙarar da Khadija Hassan ta shigar a wannan kotu ranar 1/9/2023 akan