kwafah .
Dayake kowa yasan aikinsa babu wani bata lokaci huda ta fara shirye shiryen dora abinci yayinda fahreeyah ta dauki tulunta tayi hanyar rafi .
Tafiya take tana kalle kalle har ta kai ga wajen deban ruwan ,jikinta ne yayi dan sanyi ganin ba babu saheel shida fonee a wajen ,har tajuya zata tafi saikuma suka duro a gabanta suna dariya ,da alamar yimata bazata ,itama dariyar tayi tare da rungume fonee a jikinta ,kallonsu saheel ya tsaya yana yi fuskarsa dauke da murmushi ,ya ayyana wani abu a ransa dashi kadai yasan manufar sa .
fahreeyah ce takatse masa tunanin daya ke ta hanyar cewa ,
"yah saheel kaga fah fonee ya dauke min gyalena ya gudu koh "
"zama yayi a wajen da take zaune ,ta cunoo baki gaba ita a dole ta kai kara ,murmushi yasake yi kafin yace ,
"idan kina wani abu FARYAH ,kaman y'ar karamar yarinya ,idan kika barshima a zai dawo da shi ko ?"
shiru tayi amma babu alamar ta yadda da abinda yace din ,saidai kuma ko me ta tuna ?,sai kuma ta dawo da murmushi kan fuskarta tareda cewa ,
"uhmm dama zancen mu na jiya yahh saheel ,menene mafitar dakace kana da ita akan rayuwar tawa ?"
"kin yi magana da mahaifiyarki kaman yanda mukayi ?"
"ahah bamuyi magana da ita ba "
"tohh miyasa ?"
"babu komai ,kawai dai bansan yanda zan yimata zancenka bane ,kuma danaji kace idan inason rayuwata ta sanja ,dole sai nayi nesa da ita ,sai hakan ya sacemin gwiwa ,banason rabuwa da ita yah saheel ,ita din rayuwatace "
"ba rayuwarki bace ,da rayuwarkice kaman yanda kika fada to hakika zaki sanja wannan rayuwar taki faryahh ,kowa da kika ganshi akwai wani abu dayake yaki da shi a rayuwarsa,karki kasance mai jiran sai anmiki yaki a rayuwarki keda kanki zaki sanja komai faryah ,keda kanki ,sannan hakan bazai yiyu ba sai kin jure kinji ?"
jikinta ne yayi sanyi da kalamansa ,haka kawai takejin kaman akwai abinda yake shirin faruwa da ita ,batare da tace masa komai ba ta tashi ta dauki tulun ruwanta ta dora a kai ,kafin tace ,
"na gode da kulawarka da kuma bani shawara a kullum yah saheel ,sai gobe ,bari natafi karna dade "
"yau bakisan rakiyanne ?ko akwai abinda yake damunki ?"
"ahah bakomai ,zan iya tafiya ma "
"shikenan ki isa lafiya "
"tohh "
tafiya ta ke kwata kwata bata kallan gabanta ,saida tayi tuntube da dutsi kafin hankalinta yakai kan abinda dake ,ba komai ne yake dawowa cikin kwakwalwar ta ba illah maganganun da saheel ya fada mata ,tunani take a ranta to taya ne zata sanja rayuwarta ?.
Dahaka ta isa gida ta juye ruwan data debo a randar aryanar ,dakinsu ta shiga inda mahaifiyar ta ta ke zaune tana dan lashe kwanon da saka musu kanjon abincin datayi ,dagowa tayi da idonta ganin y'ar ta ta a tsaye a bakin kofar ,saida ta shigo ta zauna kafin ta miki mata nata abincin a wani dan kwano dayake gabanta ,dauka tayi itama tafara ci ,dan dama yunwace a cikin cikinta .
Bayan sun gama cine ,sukaji muryar aryana tana kiransu daga waje ,fitowa sukayi suna kallonta kafin tace ,
"yawwa inaso na fada mukune cewar ,anfara neman bayi a kasuwar shekarar nan,dan haka ke fahreeyah ki shirya dan nasa ka sunanki a cikin wad'anda za'a sayar min ,banaso nakara ganinki kin yi wani aiki ,sonake a ganki bulbul ko zakiyi daraja ,da daga gani za,a samu kudi ,hungo nan abincine kidinga ci kina koshi "
tafada tana mika mata kwano cike da abinci aciki ,da taga bazata karba ba dangwara mata a gabanda tayi gaba ,tana kara tabbatar musu da jawabinta ,.
Har tagama bayaninta tabar wajen fahreeyah basuyi ko motsiba saboda wata irin razana data bugi girjinsu saboda jin furucinta ,huda ce taja wani dogon numfashi mai karfin gaske ,wanda duk kamewar da fahreeyah tayi saida tazuya da kallonta zuwa ga mahaifiyar ta ta .
(The legendary story)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟
💎💐 ..... WATA RAYUWA....💎💐
phone number:09035784150
telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0
whatpad :@SAKHNA03
......Dedicated to proficient writer association........
chp(12)
"wayyo ummaaaaaahhh ki tashi kar ki barni a wannan kuncin nikadai ummah ,kinji "
gunjin kuka take mai cike da ban tausayi tana jijjiga ummannata wanda take kwance kamar matacciya ,wani tunani yazomata ,aikuwa batare da bata lokaciba ta nufi dakinnasu ta dauko ruwa a kofi ,watsa mata take tana cigaba da kiranta .
Wani irin numfashi ta saki tareda ajiyar zuciya ,can kuma saita kalli y'ar ta ta ,tareda tunanin abinda yafaru ,al'amarin daya farune ya dawo musu a kwalkwal warta ,zawo fahreeyah tayi tareda matseta a jikinta tana sakin kuka mai tsuma zuciya ,
"ahah fahreeyah bazan bari ta dauke min keba ,bazan bari ta zefaki cikin wani kangin bautar ba ,bazai yiyuwa ba fahreeyah "
"ehh ummah bazata rabamu ba ,kidaina wannan kukan umnah ,yana sakani cikin tashin hankali "
"shikenan fahreeyah allah yana tare damu ,tashi "
tafada tareda tashi daga inda take zaune ,kama hannun ta tayi sauka tashi kafin suka shiga daki .
Kwanaki sun karu kuma abubuwa sun faru ,saidai duk da abincin da aryana take bawa su huda hakan bai saka fahreeyah tayi kiba ba ,saima sake ramewa datayi saboda tashin hankalin data kara shiga ,ga shi kuma dadin karin abun tahana ta tafita koda nan da wajene ,a ganinta tadaina aikin wuya saboda tasamu kudi dayawa idan akazo siyan bayi .
A bangaren saheel kuwa abin yabashi mamaki dayaga fahreeyah ta daina zuwa diban ruwa tsawon kwanaki ,hakan yasa yafara tunannin anya kuwa lafiya take ?baidai saka abin a ransa ba ,sai yabarshi akan cewar watakila sun sanja mata aikine ,ta koma yin na cikin gida .
Yau ne takama saura kwana uku masu sayen bayi sudawo kaman yanda suka ambata , yayinda fargabar bayin allah wato huda da yar ta ,takaru fiye da mai tunani ,dan har yakai bacci ma kaurace musu yake ,yanzunma zaune suke a tsakar dakinnasu suna tunanin mafita ,huda ce ta kalli yar ta ta kafin tace ,
"tabbas yanzu nafara nadamar aikata kuskuren dana yi ,dana ga yana shirin shafar rayuwarki ,nayi tunanin cewar idan muna cikin wannan bautar in kin girma ke zakiyi aure ki samu sabuwar rayuwa ba irin wannan ba ,ban taba kawo kaina ba ,nidai burina shine ke kisamu ingantacciyar rayuwa ,amma gashi sanadiyyar gangancinmu zaki tsinci kanki a WATA RAYUWA ,wacce tafi wadda muke ciki muni ,wayyo ni da wannan rayuwar"
"ahah ummah kidai na fadin hakan da sannu hakan zaizo da sauki "
"hmm meyasa zakice haka bayan kinsan bamu da mafita "
"akwai mafita ummah ,yacemin akwai mafita "
"shi wa ?wanene shi ?"
"uhm yaya saheel ne ,yacemin akwai mafita ,kuma wai ke da kanki da kuma ni zamu samo mafita ,in muna son hakan yakasance kuma wai ,sai mun daina tsoron rabuwa ,ko nesa da juna "
"a ina kika hadu dashi ?"
"a inda nake zuwa diban ruwa "
shiru huda tayi kaman mai nazari kafin tace ,
"inaso gobe ki saci hanya ki kira minshi ,zamuyi magana nidashi "
"ammma umm ........."
"karki ce komai kiyi yanda nace "
"tohh ummah "
haka kuwa akayi da safe su fahreeyah suka fito fuskarsu babu damuwa mai yawa akan fuskarsu kaman wanda aryana tace ta janye gudurin ta daga kansu ,ayyukan dasuka san aikinsu ne suka fara ,har huda ta fice domin debo itace ,sai kuma tasaki kara ta zauna ,tana shure shure ,fahreeyah ce ta taho da sauri dan ganin abinda yasamu umman na ta sai kuma taga mamar ta ta gigicewa tayi tana mata sannu itakuma tana kara narkewa ,ganin abinda yake faruwane yasa aryana zuwa kansu tatsaya dan ganin mai yafaru ,
"hmm munafukai ,saiki tashi kiban waje ai ,ke kuma (tafada tana nuna fahreeyah )sai ki tashi ki debomin itacen ,kuma idan kinga dama karki dawo nasa abi bayanki ehe "
kallon mahaifiyartata tayi sai gani tayi ummah nata tayi mata alama da ido ,hakan yasa tagane duk shirine domin taje ga inda ta aiketa jiya .
Juyawa tayi ta fita daga gidannasu ,batare da tsoron hukuncin da aryana zatayimata ba ,tayi hanyar gidan saheel domin isar da sakon mahaifiyartata ,domin tasan wannan aikan yanada alaka da rayuwarta ,tafiya take tana tunani a zuciyarta har ta iso ga gidan saheel din ,tsaywa tayi a bakin gidan tana tunanin tashiga ko ta tsaya .
Tana tsayenne taga fonee yafito daga gefenta ,nufarsa tayi tana tambayarsa dauke da murmushi akan fuskarta ,tana tsugunne ne ,taga saheel shima yafito daga inda fonee ,kallonsa take batace komai ba yayinda shima yake kallonnata ,ganin hakan zai ja musu lokacine yasa ta fadin ,
"uhm ya saheel ina kwana ?"
"lfy kalau ,da wata matsalane ?"
"ehj dama umma ce tace nafada maka tanaso kuyi magana da ita "
tafada fuskarta tana fitar da hawaye ,matsowa yayi kusa da ita kafin yace ,
"menene yake faruwa faryah ,kifadamin ?"
labarin abinda yafaru ta fadamasa tana share hawayen daya fito daga idonta ,jijjiga kai yayi dauke da damuwa akan fuskarsa kafin yace ,
"shikenan kice mata zan zo da daddare saboda idon mutane tunda batason a sani "
"to 😩"
"ki kwantar da hankalinki kinji komai yana zuwane yanda aka tsara shi "
"shikenan ya saheel nagodee "
juyawa tayi ta tafi zuciyarta cike da kunar rai ,sauri tayi ta hada itacen da aka aiketa kafin ta dauka tatafi gida .
Aikuwa batayi mamaki ba saida tasha na kullum wato zagi ,shigatayi wajen mahaifiyarta datake kwance a daki sannan ta fada mata yanda sukayi saheel din .
bayan gari yafara duhune haske ya fara daukewa daga kallon mai kallo yayinda fahreeyah suke zaune suna jiran tsammani ,fonee ne yashigo dakin yana shafa kansa a jikin fahreeyah ,huda ce ta zabura zata gudu ganin abu yashigo ,saidai kuma abin ya bata mamaki ganin yanda fahreeyah ta shagala tana shafashi ,daga kai tayi ta kalli mamar ta ta kafin tace ,
"ummah ya zo ,yana waje "
tashi sukayi suka fita wajen gefen dakinsu , samunsa sukayi yajuya bayansa ,fahreeyah ce ta fara magana ,
"ya saheel "
juyowa yayi tareda gaisheda da ummar tata ,wato huda ,shirune ya wuce a tsakaninsu kafin huda tace ,
"ina so kubiyoni muje wani waje yanzunnan "
binta sukayi batareda musu ba ,sunyi tafiya mai nisa cikin garin kafin suka zo wani gida mai dan rufin asiri ,saidai kuma kaman gidan mutum dayane .
Juyawa tayi tana kallonsu dauke da murmushi yayinda suma ita suke kallo dauke da mamaki ,kallontane ya koma kan saheel ,
"saheel ina so ka ............"
(The legendary story)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟
💎💐 ..... WATA RAYUWA....💎💐
phone number:09035784150
telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0
whatpad :@SAKHNA03
......Dedicated to proficient writer association........
chp(13)
"saheel ina so ka auri y'a ta fahreeyah "
kallonta sukayi duk a razane ,kamar basuji mai take fad'aba ,
"umma me kike cewa haka ne ?"
"bazaki gane ba ke ,amma ina tunanin idan shiya ji zai iya fahimtata "
"ahah ummah kituna fah mai kikace "
sukad'ai suke maganarsu ,shidai tunda ya ji abinda yafito daga bakin huda bai sake magana ba ,sai binsu da ido dayake ,saida HUDA tazo gabansa tareda karyar da kai tana kallonsa ,
"bawan allah nasan a idonka zan kasance mai wauta wacce take yarda da wanda batasanshi ba ,sannan zan kasance mai san kai saboda yanayin abinda narokeka ,amma kasani kodaya bayanda kake ganiba ne ,ni uwace mai son tseratar da yar ta daga kangin dayake tunkarota ,ni uwace da banida wani buri sai ganin yata cikin kwanciyar hankali ,nasan fahreeyah ta baka labarin rayuwarmu ,haka kawai na tsinci kaina da yarda da kai bawan allah ,dan allah amincemin da auren y'a ta ,sannan ka tabba tarmin da cewar zaka kulamin da ita a wannan RAYUWAR ,narokeka "
tafada tareda sakin wani kuka mai tsuma zuciya ,wanda duk wanda yaji yasan ma'abocin kuka nacikin wani irin yanayi ,ganin kukan bazai mata bane yasa ta tsugunna akan gwiwoyinta tareda kama kafafunsa .
Ganin abinda mahaifiyartata takeyi kuma wai,duk akanta yasata sakin itama kukan tareda durkushewa ,wai saboda tsabar kunci da rashin daraja ,mahaifiyarta ce take rokon wani ya aureta,ba dan so ba ,saidai dan ya taimakata ,
tana cikin wannan tunaninne ta ji muryar saheel yana fadin ,
"shikenan ummah na amince zan auri fahreeyah ,kuma nayi miki alkawarin riketa da amana ,matukar ina tare da ita kuma ina numfashi ,da sannu babu abinda zai sameta "
"nagodee d'annan allah yayimaka albarka ,yakumasa albarka a rayuwarku ,bazan taba mantawa da abinda kamin ba har abada "
fahreeyah ce itama ta share nata hawayen ganin ummah nata ta dora murmushi akan fuskarta .
Hudace ta zuya tare da shiga cikin gidan da suka tsaya a bakinsa ,binda sukayi suma har zuwa cikin gidan ,gidane karami mai dauke da dakuna guda biyu madaidata .
Suna cikin kalle kalle ne ,wani matum mai dan shekaru yafito daga dakin tareda amsa sallamarsu ,fuskarsa ce ta nuna almar mamaki kafin ya iso gabansu ,
"huda dama kina raye ?"
"ehh baba HASHEEM ,ina raye,yanzu ma nazo neman alfarma ne gunka "
"allah yasa ba wajen zama zaki bukata ba,domin kinsa duk wanda yasaukeki a gidansa to hukuncin dake jikinki ne zai hau kansa shima "
"ehh ina neman wata alfarma ne daban ba wacce kake zatoba "
"shikenan ku shigo naji da mai kuke tafe "
shiga sukayi ciki ,tareda shaida musu abinda yake tafe dasu gabadaya ,jinjina kai yayi kafin yace ,
"shikenan zamu taimaka ,sai su zauna zuwa da safe za'a daura amman ,inaga kekam ki tafi saboda kar a samu matsala zamanki anan"
"ehh nasani baba hasheem indai zaka taimaka min dahakan banida matsala da wani abun "
karisa maganar tayi fuskarta dauke da damuwa ,da kuma dana sanin abinda ta aikata .
Bayan ta tafine yazuyo da kallonsa izuwa su fahreeyah kafin yace ,
"shikenan na amince zan taimaka muku da abinda mahaifiyarki ta bukata ,inajin tausayinta matuka ,saidai banida ikon bata muhalli a wajena,yanzu ga can daki ki kwanta kafin muga mai gobe zatayi "
A wajen huda kuwa tana isa gida dakinsu ta lallaba ta shiga zuciyarta na dukan tara- tara cike da fargaba .
"KEEEE d'iyar fatara da tsiya maza ki fito za'a fara ciniki ,ai in fada maka kyakykyawace ta fad'a a taro ,nasan zaka sayeta da daraja ina fadamaka ........"
zancen tane ya katse ganin huda tafito daga dak'i ita kadai batare da fahreeyah ba ,
"kee kuma ina take ?ai kinsan bake na kira ba ko ?"
"eh fahreeyah bata nan ,dana tashi bangantaba nima "
"kutt mekkike nufi kinsaka baiwa ta ta gudu kenan ?"
"ahah tashi nayi bangantaba nima a dakin "
"DUK'ANA !!! maza kabimin sawun waccer tsinanniyar yarinyar ,kuma ka tabbatar ka nakasata kafin ka kawomin ita ,ke kuma ki saurari mummunan hukuncina ,dan nasan da hannunki akan hakan "
A can kuwa wajen su fahreeyah bayan sun tashi da safe sun shirya ,sai kuma baba hasheem yakirasu zuwa wajen majalisar sa.
A zaune take a gefe a daya bangaren kuma saheel ne shima a zaune saikuma wasu mutanen suma masu yawan shekaru.
Shirye shirye aka farayi na daurin aurensu ,inda aka nemi amincewarsu gabadaya ,bayan sun gama shiryawa ne aka fara da bayar da sadaki ,zoben hannunsa yamik'a mata batareda yace komai ba ,yayinda waliyyinta baba hasheem yakrb,a tareda shaidawa sai kuma aka fara siiga ............
Haka lamarin yakasance har aka gama abinda za'a yi ,baba hasheem ne ,yashiga cikin gidan yafito da wani kaya a hannunsa na mata ya mika mata tareda cewa ,
"ga wannan kayan al'adane da'ke bawa kowace y'a a wannan dangin ,duk da abinda yafaru, yafaru ,dole kina da jinin wannan dangin ,ki kula da kanki ,allah ya baku zaman lafiya "
Yana fad'a yajuya yakoma cikin gida ,daga kanta tayi tana kallon fuskar saheel hannunta dauke da kayan da baba hasheem din ya bata .
Juyawa yayi yafara tafiya batareda yace mata komaiba ,itama ganin haka yasata binsa a baya tana tunanni a ranta ,
""to yanzu tare zamu dinga rayuwa kenan dashi ,meyasa naga kowa yatafi an barni dagani sai shi to ?,gidansa zan koma da zama kenan ? au ashe aure akamin nida shi ko ?""
jin irin abinda take fada arantane yasata sakin murmushi ita kadai ,shima anasa bangaren tunanin yake akan ,
""kai anya kuwa nine ?wai na amince da auren ta ,nidai banajin wani abu mai kama so a gameda ita ,sannan banji haushiba da'aka dauramin aure da ita ,to me yake shirin faruwane haka ?""
dahaka suna cikin tunaninsu da basu da mai basu amsarsa suka iso kofar gidan saheel din ,tsayawa suka yi kowa yana kallon kowa ,lokaci daya suka dauke idonsu a tare kuma ,.......
😊😊😊,rayuwar gidan saheel zai zo muku a gaba shida matar tasa fahreeyah kuci gaba da bani goyon baya ,domin nasamu na dinga suburbudo muku shi 😊,.
A dunga taimakawa da bamu
#comment
#vote
(The legendary story)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟
💎💐 ..... WATA RAYUWA....💎💐
phone number:09035784150
telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0
whatpad :@SAKHNA03
......Dedicated to proficient writer association........
chp(14)
Wuceta yayi ya bud'e dakin ya shiga ,ganin bai mata maganaba itama ta bishi cikin gidan .
bata sameshi a cikin falonba ,sai tasamu waje ta zauna akan kujera kalle kallen cikin gidan ,sai yanzune take karewa cikin gidan kallo, ba kaman zuwanta na farko ba ,
""a zagaye dakin yake ,anyi masa shafe da farar kala ,ga kuma kujeru guda uku a cikin dakin ,sai wata hanya dazata kai mutum wani dan karamin d'aki inda ake girki ,dakin da saheel ya shiga kuma shine wajen kwanansu wanda yake dauke da gado dakuma dan karamin shimfid'a a gefe ta fonee , a bangaren hagun kuma a akwai kofa dazata fitar da kai inda bandaki yake .
Gidane dan karami amma mai kyau da ban sha'awa ""
tana cikin nazarinne taga saheel ya fito daga dakin daya shiga lokacin da ya dasuka shigo cikin gidan ,yanzunma bai mata maganaba kawai ya wuce inda yake dafa abinci ,ta dan dade a zaune yasake fitowa hannunsa dauke da kwanon abinci ,a