x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 3 - WATA RAYUWA

  • 6001 words
  • 9000 words
  • Out of 27012 words

Category: Love Stories

Views 85

02 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
murmushi gefen baki mai dauke da mugunta.
Ranar da takama ranar nadin sarki huruddeen sai yazamana maimakon wanda za,a nada yayi farinciki sai murnar takoma ga iya matarsa da danginta ,wanda a zahiri kuma kowa zai dauka tamkar basa farinciki da hakan.
Bayan angama nadine a fada ,sarki shamam mai sauka daga kan mulki yafara bayani kamar haka:
"hakika yau ta kasance ranar farinciki a gareni da allah yabani ikon mika wannan mulki ga dana wato huruddeen,ina yiwa daukacin dukkan al'ummata farinciki dasamun sabon sarkinsu wanda zai shigaba da mulkarsu har zuwa yanda allah zaiyi,kai kuma inajan hankalinka daka dora akan adalcin da wannan masarauta tasaba yi harma dakuma kara kokarinka akan yanda kasameta,saidai kafin na rufe jawabina ina mai sanar dakai cewar nayimaka zabin iyali ta biyu wato gimbiya SAFEENAH wanda take ya ga daya daga amintaccen sarkinmu wato sarki URWATU,wanda za'a daura a yanzu ,domin bai kamata sarki kaman na nahiyar SARAHAM yakasance da mata daya ba ,dan haka ina mai tayaka farinciki dasamun wannan dama na auran gimbiya SAFEENAH "
Koda yagama bayaninsa sai a take waje yadauki sautin muryar mutane na taya sabon sarkinsu wato huruddeen samun wannan nasarori a rana daya.
A bangaren waziri uwaisu kuwa har akagama hidimar daurin auren sarki huruddeen da gimbiya safeenah baiyi koda tari ba ,domin abin yazomasa a bazata yanda bai taba tsammani ba.
A cikin gida kuwa gimbiya zulaikah wanda yanzu takoma sarauniya zulaikah kuma mata daya tak awajen sarkinnata zaune take akan kujera tana wani shan kamshi agaban mutanen data gayyata domin su tayata murnar wannan rana ,a inda gefe daya kuma bayinta suke yabonta da kalmomi masu sawa duk wanda aka amdata masa su cewar yafi kowa a fadin duniya.
suna cikin murnar ne wata baiwa tashigo da hanzarin ta ,takai bakinta ga kunnen sarauniya zulaikah tana me rada mata wani abu da mu bamu ji mai aka fada ba,wani irin zabura tayi ta mike daga kan kujerar datake tana wani kumbura kamar maciji, fuskarta kuwa dauke take da wata irin razana kaman an aiko mata da sakon mutuwa,magana tafara cikin daga murya wanda har saida muka razana mu masu rahoto(ummu najma uwar tsoro canna ganta ta buya a bayana tana leko kai kaman kace fittt ta tsere da gudu)...
"hakan bazai taba yiyuwa ba domin nice ta farko kuma ta karshe a wajen sarki huruddeen ,bazan taba yadda wata tashigo gonata ba,idan kuwa har tayi garajen hakan to hakika sai ramin maciji yafi mata kwanciyar hankalin zama fiye da cikin gidana ,kin tafka babban kuskuren shiga gonata ko ke wacece ,inaaaa bazai yiyu ba dole a katse wannan auren dan ban amince dashi ba,bazai yiyu baaaaa"
wani irin numfarfashi take wanda har saida yasa mutanen dake wajen bajewa batare da sun shiryaba ,inda ita kuma uwar gayyar tai cikin turakar ta a fusace....nina ce madallah ,ni gani nasan waje ,harda gayyatar mamar faruqu rakiya ita da ummu najma ,amma ko yar kazar basu yaga musu ba ,tsabar rowa 😊😊😊.
koda ta nufi dakinta,daukar alkyabbarta tayi tai hanyar bata zame ko ina ba sai hanyar wajen inda bayinta da dakaru ke biye da ita a baya ,harara ta tsaya ta daga musu ,wanda har saida tasa hantar cikinsu kadawa dan tsoro ,ja sukayi suka tsaya daga bin bayanta ,yayinda tayi wucewarta zuwa gidansu .
shigarta gidannasu ne ta tarar da mamar ta tsaye ,bude bakinta tayi zatayi magana sai takatse yar tata tahanyar nuna mata daki ,wato ta shiga ciki,shigewa tayi inda tasamu babanta a zaune yayi shiru kaman yadaina motsi ,zama tayi a gabansa fuskarta a jike da hawaye ,tana ayyanawa a ranta kenan abinda aka fadamata gaskiyane,batasan maganar ta ya fito filiba saida taji mahaifinnata yana fadin ,
"tabbas abinda kikaji da gaskene babu karya a ciki ,dan a gabana hakan tafaru ,ban taba tsammanin ko wani ne yace da shamam ya aurawa dansa wata matar zai aminceba bare kuma shida kansa ,hakan yaban mamaki ,nayi tunanin yadauki ya' ta kaman yarsa ashe bahaka bane ,wai to yaushe suka hada baki da wancan sarkin ne bansaniba ?hmmmm ,saidai ki kwantar da hankalinki hakika shamam yasaya wa gidan sa tashin hankali da kansa ,domin kuwa bazan taba bari abinda suke tunani yakasance ba,inaso kibude kunnuwanki ki saurari mai zamu fada nida mahaifiyarki a halin yanzu"............
kuka sance dani a chapter ta gaba 😊😊😊😊


(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

💎💎💐💐WATA RAYUWA 💎💎💐💐


тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_profile&wp_page=user_details&wp_uname=Ayeeshatmuhd&wp_originator=zwWkFi8UrQ15wCJ97IpYA%2BgQnfGX9PzVmleI%2FrEP8a5KYyZPDI3Q6FDITR%2F8c8JH%2Bh4M%2FiYfRaUnBHccl04WBnkR5Lgh%2B6M6I417gK74LZ5o2mKGtm64Fl95iySLrmh8

whatpad username:SAKHNA03

phone number:09035784150

Telegram https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

*BY SADI-SAKHNA*


(The legendary story)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟

💎💐 ..... WATA RAYUWA....💎💐


written by sadi-sakhna

(06)

"Da farko banason kinuna kiyayyarki a fili a wannan auran,inaso ki nuna tamkar baki damu ba ,sai kowa yasake dake akan haka kafin zamu dana tarkonmu akansu wanda basu da ikon fita daga cikinsa"
"shikenan abba zanyi yanda kace ,amma nida burina shine a wargaza aurennan tun yanzu dan har yanzu zuciyata takasa aminta da zancen kishiya,hakan yana kona min rai sosai"
"wai ke bakya jin abinda mahaifinki yacene ?ki kwantar da hankalinki da sannu zamu cimma duk wani burinmu ba karbar ragamar masarautar saraham ,ko baki gani yanzuma cikine dake ? idan kika haifi namiji ai saidai ta biyo a baya kuma bazamu taba barta ma ta haihu a cikin gidanba "
"shikenan mungama magana kitashi ki koma kar wani yazargi wani abu sannan ki tarbeta,cikin kwanciyar hankali ,,kuma ki kula da cikin dake jinki domin a halin yanzu shikadaine damar mu ta gaba"
shine abinda mahaifiyarta tagama fadamata bayan hudubar da waziri uwaisu yagama fada mata,tashi tayi ta fara shirin komawa gidannata tare da damarar aikata duk wani abu daya fito daga bakin iyayennata.
A bangaren amarya kuwa koda akasanar da ita daurin aurenta da sabon sarki huruddeen ,hakan bai wani dameta duk da batada masaniya akan shirin aurennata,saboda al'adar masarautar tasuce aurar da gimbiyo ga duk wanda yadace batare da zabinsu ba.
Zaune take akan dardumar dake dakinta bayinta na zaune a gefenta sai ga kira daga turakar mahaifinta akan yana nemanta,tashi tayi batare da tace wani abu ba tabi bayan jakadan cikin sanyin jiki wanda yakasance tamkar halinta.
Koda ta isa turakar iyayenta ,shiru tayi kaman lbrin daya ke zagayawa a cikin fadar bai iso gareta ba ,hakan yasa sarki uwartu fara magana.
"safeenah nasan bazakice komai ba ,kaman sauran yan uwanki akan abinda yake faruwa wanda nasan cewar labarin ya isa kunnenki ,to ki dauka cewar haka abin yake ,sarki shamam dakansa ya zo izuwa gareni neman iri,saboda kyawawan halaaye irinnaki yasa ni amincewa da zaboki acikin yan uwanki ,duba da dattako dakuma halin kawarai na masarautar saraham ,dan haka in fatan zakiyi biyayya akan hakan"
"inshaallah zan kasance mai yin biyayya akan hakan duk wani zabi daya kasance ya fito daga gareku matukar bai kasance sabon allah bane"
"nagodee da wannan magana taki ,da yardar rayuwarki zatayi albarka saboda wannan biyayya taki ,shikenan ki tashi ki tafi zaku fara bukukuwa na al'ada a sashen mahaifiyarku kafin suzo tafiya dake ,allah ya miki albarka tareda zuri'arki gabaki daya "
Tashi tayi wanda tana fita wani kiran yazo daga sashen mahaifiyarta ,wucewa tayi zuwa ga kiran mahaifiyar tata,tana shiga idan ta ya sauka kan manyan matan da suke zaune akan kujerun turakar mamar tata ,karisawa tayi ta gaishesu da daddaya kafin ta zauna a wajen mahaifiyar tata ,kallon gimbiya safeenah tayi kafin tace.
"nasan mai martaba yamiki bayanin komai akan abinda yake faruwa dan haka inso kidora akan yanda nasanki na halayenki ,duk da bikin yazomana a lokaci kadan saida munne mi alfarmar zuwa daukar amarya nan da kwana uku ,dan haka,akwai wanda aka dauka masu gyara dakuma kwalliya wanda zasu fara yimiki daga yau har zuwa nan da ranar daukar amarya,tashi muje dakin dazaki fara zama domin yin gyaran ko ?"
Tana gama bayanin ta mike suka fara tafiya zuwa wani sashe daban inda za'a fara gyaran jikin gimbiya safeenah ,wanda har suka isa tana yimata karin haske akan sha'anin auren daya hau kanta.

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

💎💎💐💐WATA RAYUWA 💎💎💐💐

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

(The legendary novelist),🌄🌄

(The legendary story)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟

💎💐 ..... WATA RAYUWA....💎💐

phone number:09035784150

telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

whatpad :@SAKHNA03

......Dedicated to proficient writer association........

(07)

Share hawayen daya fito daga idonta tayi ,,kana ta gyara zamanta domin fuskantar sabuwar tafiyar dazasu tsinci kansu a ciki ,duk da dauriyar da zuciyarta ta kudurci niyyar yi ,amma duk da haka hankalinta a tashe yake domin bata san mai zata riska a wannan sabuwar rayuwar ba ,da haka suka yi ta keta garuruwa da kuma hanyoyi har ta kaisu ga isa ,nahiyar saraham,tun daga yanayin kananan garuruwan da suke farko farkon nahiyar ,hakan ya tabbatar musu da cewa tabbas sun shigo babbar nahiyar ,da babu kamarta.
Wasu irin dakarune masu yanayin halittar karfi ,suka fara zuya karafan dake jikin kofar shiga masarautar domin bawa gimbiya safeenah damar shigewa ita da tawagarta ,yanayin yanda kofar take budewa shiya zamo abin kallo ga tawagar ,saboda girma dakuma tsari na masarautar.
koda suka isa masarautar basu zame ko ina ba ,sai sashen da aka tanada a al'adarsu na saukar duk wata amaryar data shigo gidan sarautar.
Tun daga bakin sashen da aka sauke su suka tabbatar wajen ya hadu matuka ,inda aka saukar da amarya daban haka sashen da bayinta yake daban ,shkma maza daban mata daban ,sannan inda masu tsaronta suke shima daban.
Baiwa daya ce a wajenta itace sameerah ,wanda dama tun tasowarta ko yaushe tare suke ,gimbiya safeenah ce ta yaye mayafin dake kanta kafin tace ,"sameerah shin ke wani irin yanayi gameda wannan masarautar ,gaskiya har yanzu zuciyata a raunane take da wannan sabon waje dana tsinci kaina a ciki"
"ya shugabata hakika dole zuciya zata ji rauni kasancewar ta a wajen da bata mafarkin kasancewa ,sai dai duk wanda yadogara da allah to lallai allah yana tare da shi ,sannan dun rintsi mu ma zamu kasance tare dake ,a wannan waje batare da mun juya baya ba inshaallah "
"nasan zakuyi hakan sameerah sai dai ..............." bata kai ga karisa maganar ta ba ,suka jiyo maganar wasu mata daga bakin kofar suna neman izinin shigowa ,sameerah ce ta kalli gimbiya safeenah ,kafin ita kuma tayi mata alamar tace su shigo,ai kuwa kamar jira take ,ta daga murya tare da fadin,
"izini ya karbu daga wajen gimbiya sannan kuma sarauniya a wannan masarauta mai dumbin daraja"
koda jin furucin sameerah dasukayi ,sai suka fara shigowa ,daya bayan daya suna jeruwa a gaban gimbiya safeenah bayan sun gama shigowa ne suka rusuna gabadaya a gabanta su goma shabiyu ,yan mata ne masu kyawun halitta ,gabadaya fatar jikinsu kyalkyali take duba da yanayin halittarsu ,sannan kuma kayan jikinsu dukka iri dayane ,hakika wannan yan mata sun hadu sosai ,daya daga cikinsu ce tafara magana ,kuma da alama itace shugabarsu saboda yanayin shigarta ya fi nasu kayatuwa,
"laleh mar haba ya shugaba ta dazuwa wannan masarauta ta saraham ,kuma sarauniya kana kuma amarya ga mai girma sarki huruddeen,hakika idan za'a bamu dama ,zamu gabatar da kanmu a matsayin wani rukuni na bayin wannan masarauta wanda suke da alhakin kula da duk wani nau'in kwalliya na jinin sarautar saraham ,a yanzu ma idan sarauniya bazata damuba ,mun zone mushiryata cikin kayan ado na al'adar wannan masarauta domin fita da ita zuwa ga sauran bangaren wannan masarauta"
kara sunkuyar dakai sukayi lokacin da shugabarsu tagama jawabinta ga gimbiya safeenah ,uhmmm tunda suka fara bayanin sameerah ta tsiresu da ido ,yayinda gimbiya safeenah kuwa idonta yake kasa tun kallonsu da tayi na farko,sameerah ce ta yi gyaran murya kafin tace,
"shin sarauniyar saraham ta amince da bukatar wannan bayi na kwalliya ?"
sai a sannan ta dago kai ,kafin tace" ba matsala zasu iya fara aikinsu "cikin sanyin muryar ta.
Bayan sun ji abinda tafadane suka fara fitar da wasu abubuwa kala kala ,take yan matan suka rabu gida uku kowanne layi da aikin da zasu aiwatar ,wani rukuni ne suka shiga bandaki ,kafin suka fito ,domin sanar da ita cewar ita suke jira domin fara wankan sarauta ,tashi tayi cikin sanyin jiki ,yayinda wasu acikinsu suka matso domin tayata cire kayan dake jikinta ,saida yazamo daga ita sai farin mayafi iya girjinta ,shiga tayi cikin ruwan da aka tanada domin wankan ,turarene kala kala acikin ruwan wankan banda wanda ake shafeta dashi dakuma wasu fulawoyi da ake mulkawa a jikinta ,sai da wanka ya kammala kafin masu kula da kayan shafe shafe suka fara nasu aikin ,bayan suma sun gama tasu fasahar sai kuma masu kula da ado dakuma sutura ,cikin kan kanin lokaci aka shirya gimbiya safeenah cikin kaya mai matukar kayatuwa ,sannan suka ja dabaya tare da rusunawa suka bar dakin ,sameerah ce tashigo bakinta asake domin ganin irn haduwar data yi ,dama kuma ga ga kyau ba karya ,bayan fitarsu da dan lokaci kadan kuma ,sai ga wasu rukunin bayin suma sun shigo ,saidai su sun fi na baya dan manyanta sannan masu da adon kaya kaman na farkon ,suma gaishe da ita suka yi kafin suka nemi izinin ta wajen fita ,domin ganawa da mutanen gidan sarautar.
Bangaren mahaifiyar sarki aka fara kaita wanda ta manyanta sosai ,kasancewar ta dade kafin ta haifi huruddeen ,basuyi wani dogon surutu ba kasancewsrsu dukka basuda wani surutu ,fatan alkairi tayi mata kafin sukayi sallama ,sashen sarauniya zulaikah suka wuce kasancewar matar sarki shamam ta biyu ta rasu bayan auro zulaikah da lokaci kadan ,tun daga hanya gimbiya safeenah ta jinjina karfin mulki na sashen sarauniya zulaikah ,domin to ko ina dakarune majiya karfi suke aikin tsaro ,kana kuma da bayi kala kala cikin kaya daban daban kowane da aikin da suke aiwatarwa ,bayan isarsu bakin kofa saida aka nemo izini daga wajen hakimar kafin suka samu damar shiga falonta na farko wanda shima tsaruwarsa tafi gaban kwatance ,zama tayi akan kujera yayinda sauran bayi kuma suka zauna a akan shimfida ,domin sauraron isowar babbar sarauniyar .
Can bayan wani lokacine suka ji takunta daga babban falonta tana fitowa ,wanda saboda shanya su datayi ,duk hakurin gimbiya safeenah saida taji ranta yabaci da abinda yayar tata tayi musu ,takowa tayi cikin takama gamida kasaita,tana tafiya bayi na tare mata rigarta saboda kar ta fadi ,saida ta iso har kujerar dake kallon gimbiya safeenah kafin ta zauna ,duk wannan abinda ake sarauniya zulaikah bata kalli inda sarauniya safeenah take ba ,saida tagama gyara zama tare da dora kafa daya kan daya ,kafin ta dago da idonta ta kalli inda sarauniya safeenah take ,zare ido tayi game da razana saboda .............

SADI -SAKHNA ce 😊😊😊

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

💎💎💐💐WATA RAYUWA 💎💎💐💐

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

(The legendary novelist),🌄🌄

(The legendary story)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟

💎💐 ..... WATA RAYUWA....💎💐

phone number:09035784150

telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

whatpad :@SAKHNA03

......Dedicated to proficient writer association........

(08)

Gyara zamanta tayi saboda kar razanar da tayi ya fito fili ,saboda kar bayinta su rainata ,tunani tafara yi ranta cewa "tabbb gaskiya kyawun halitta ya bayyana a jikin baiwar allah nan ,don duk da izzar mulkina da kuma launin fata irin namu na kasar saraham ,tabbas bazan nuna wa wannan fatar kyau ba ,sannan .............tunanin da takeyi ta katse sakamakon muryar gimbiya safeenah da taji a cikin kunnenta ,
"barka da safiya sarauniya zulaikah dafatan nasameki lafiya ?"
yatsine fuska tayi kafin tace "zancen lafiyata ,kalau nake nida magajin masarautar nan dayake cikin cikina ,zuwanki bazai sa nakamu da cuta ba ,sannan ina miki barka da zuwa wannan masarauta wadda take karkashin ikon wata ,saidai mutum ya biyo a baya"
sarauniya zulaikah ce ta karisa maganar ta ,fuskarta dauke da wani mugun murmushi mai dauke da ma'anoni daban daban ,hannunta kuma akan cikinta tana shafawa cike da gadara ,sarauniya safeenah ce ta sunkuyar da kanta kafin tace,
"shikenan nizan wuce nabarki lafiya"
tana gama fada ta tashi kana tayi hanyar fita daga falon ,muryar zulaikah taji a bayanta tana cewa ,
"dama kuma inaso namiki dan tuni akan wani abu ,karki manta da kofar da kika shigo "
zuyowa tayi ,ta kalli zulaikah fuskarta dauke da alamar kanta ya daure da maganar ,ganin halin da ta shiga ne yasa zulaikah yin murmushi kafin ta juya zuwa babban falonta cikin takama.
Sarauniya safeenah ce zaune a gaban wani katon madubi dauke da kayan ado iri iri ,hankalinta ba akan abinda yake gabanta bane ,tunanin maganar da sarauniya zulaikah ta fada mata take ,sai can kuma ta watsar da komai ,ta tashi tana gyara alkyabbarta domin shiga turakar sarki ,jakadiya ce ta rakata inda aka sake shiryata domin jiran isowarsa.
Koda jakadiya ta ji alamun fitowarsa sai tabasu waje domin ganawa,zaune take fuskarta a sunkuye har yazauna a gabanta ,
"to ina miki barka da zuwa sabon waje sannan kuma sabuwar rayuwa "
"ina amsawa ya shugabana"
"hmm shikenan dafatan babu wata matsala da kike fuskanta ?"
"babu komai saidai rashin sabo"
"karki damu sannu zaki saba da hakan ,fatanmu shine allah yasa albarka a zamanmu "
"ameen ya allah ".
Daga haka labarinsu dakuma hirar su ta sanja salo ,nabasu waje domin su gana.
Haka rayuwar cikin masarautar ta cigaba da tafiya a tsakanin matan ,yazamana yanzu sarauniya safeenah tasaba da sabuwar rayuwarta ,wanda sanadin halinta na kwarai yasa da kadan kadan mutanen gidan da kuma bayi suka fara komawa karkashinta.
rayuwa suke ta kowa yayi harkarsa ,domin babu wanda yake shiga harkar wani ,saidai a bangaren zulaikah burinta da kuma tsarin da ta shirya yana nan a cikin ranta .
Abubuwa da dama sun faru a masarautar saraham ciki harda haihuwar sarauniya zulaikah da kuma barin ciki da da sarauniya safeenah tayi ,saidai abu yazo ba yanda aka zata ba .
Bayan doguwar nakudar da zulaikah tayi a dakin karbar haihuwa ne ta haifo yar ta mace ,sak kamarsu daya da ita ,lokacin da zulaikah ta kula da abinda ta haifa sai duk duniyar ta sanja mata ,amma soyayyar d'a da uwa ,hakan bai hana ta daukar
End Ads