An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
(The legendary story)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟
SANARWA
Wannan littafin kirkirane, domin babu abububwan dasuka ci karo da rayuwar zahiri acikinsa.Amma idan kinga ko kaga yaci karo da rayuwarka dan allah amin afuwa yanayine yasa .Sannan wannan littafin kirkira tace,kuma dan allah akiyaye kwafa ba da yaddata ba.NAGODE sosai makaranta harma da marubuta,domin bazamu cika burinmuba saida yardarku.Ayi karatu lfy.
,
(01)
Mafari......(Garin BARDUGU).
BARDUGU garine wanda yake boyayye a duniyar ta mutane,sanadiyyar surkukiyarsa cikin daji dakuma duwatsu,garin bardugu ya kunshi mutane masu wani irin hali mai wuyar sha'ani a tsakanin mutane,a sanadiyyar halayyarsu har yakai mutane basa son yin mu'amala dasu,sannan kuma basason zuwa inda suke .Aduk inda akasamu abu marar kyau a waje to za'asamu kuma abinda zai burge ko yadauki hankalin al'umma,to hakane yakasance a garin bardugu domin garin na dauke da kyakykyawan muhalli harma da kyawun yanayi wanda ba'a samunsa a wannan duniya tamu,saidai yana dauke da dumbin kabilu masu matukar hadari dakuma tsafi,sannan babban abinda yake bawa mutne tsoro a garin na bardugu shine ;akwai daukar hukunci mai tsauri ga duk wanda ya aikata laifi a a garin sannan yafewa wanda ya aikata laifi tamkar haramunne a garin,wannan shine kadan daga cikin hallaya na mutanen dake cikin garin bardugu,kubiyoni acikin littafin na WATA RAYUWA zakuji abubuwan mamaki harma dasu ban sha'awa ban tausayi dakuma ban haushi acikin wannan littafin,karku manta tare da marubuciyar sadi-sakhna(the legendary novelist)
Faariya! fariya!! fariya!!!,shaine abinda wata mata take fada daga bakin wain daki cike da masifa,matar bazata wuce shekara hamsin ba a duniyarmu amma yanayin garin na bardugu dayake dauke da abubuwa dasuka yi sabani da hankailnmu,matar na dauke da shekara darine harda yan kai a rayuwar ta bardugu.Yarinyar da'ake kwalawa kirane tafito daga daki fuskarta cike da tsoro dakum fargaba,tsayawa tayi agaban matar duk ilahirin naman dake jikinta rawa yake yi,karar marin data kwadawa yarinyar ne ya firgitar dani matuka ,domin ko babban mutum ya karbi wannan nau'in marin to lallai zaiji ajikinsa ballanta yarinya sannan cikin karfin yanayin irin na mutanen,tagataga tayi tamkar zata fadi kana ta tsaya "menene ya tsaidake ga barin zuwa wajena harkika bari namiki kira uku baki zoba?iyee ba magana nake miki ba ?kuma ai waccar uwar taki bata nan na aiketa deban ice bare ki ce a wajenta kike ko?shine abinda take fada cikeda masifa,cikn kuka yarinyar take bata amsar tanbayarta "kiyi hakuri baaba aryana,na tsaya karisa cinye guntun abincin da maamam tabarmin ne ,kuma idan nabarshi ban cinyeba beraye zasu cinyemin,"shine abinda tafada wa aryana nan "dallah yimin shiru ki tashi kije debomin ruwa a rafi "marin da aryana ta zubawa fariya bai firgittataba kaman sunan rafin da ta ambata,(domin kowa dayake garin bardugu yasan hatsarin dayake dauke da rafin anguwar tsaraunin,saboda halittun dasuke dauke a wajen,wanda ko acikin garin na bardugu ba kowa ne yasan dasuba.Acikin halin na bayanda zatayi ta tashi ta dauki tulun deban ruwan ta nufi hanyar kofar fita waje wanda aka daure bakin kofar gidan da tsumma.
WACECE FARIYAH sannan menene dangartakarta da wannan matar wato aryana?
Ainihin sunanta shine FARIYATUL SHARMEELAH,sannan takasance mutumce daga duniyarmu wanda hakan ya samo asline sanadiyyar zuwan mahaifinta garin bardugu.
Ashekarun baya da suka shuade anyi wani zamani da mutane dasuke garin bardugu suka fara zalintar mutanen da suke doron duniya,sanadiyyar karfinsu daya zarta na mutane ,inda suka fara kama mazaje da mata suna maida su bayinsu karfi da yaji,ganin hakn yanason wuce gona da irine yasa masarautar SARDAHAM (daular da take mulkar dukkan nahiyoyin wannan zamanin karkashin jagorancin sarki HURUDDEEN dan SHAMAM,bayan daidaita matsalar dake tsakaninsu sai yazamana mutanen da yan garin bardugu suka kaisu dan su musu bauta sun samu yancin komawa kasarsu,sannan hakanne ya yanke duk wata alaka ta sanayya atsakaininsu.Saidai babban kuskuren daya faru shine rashin komawar SHURAIM gida sanadiyyar fadawa soyayya dayayi da yar gidan uban gidansa,domin kuwa duk da kangin bautar daya shiga bai saka shi komawa garinsuba saboda wata makauniyar soyyaya daya afka cikinta marar billewa.Ganin da baban HUDA yayi nacewar bawansa yaki komawa ga kasarsa dukda damar da'aka basu na komawa ga iyalansu sai abin yabashi mamaki matuka harya fara bincike akan hakan,lamarin yagirgizashi sosai dayagano cewar soyyaya suke da yarsa HUDA,duk wani aiki dayake bashi na wahala sai yazamto cewar ya ninka akan wanda yake masa a baya,duk wannan wahala da shuraim yake fuaskanta daga wajen baban huda hakan bairage koda kwayar zarrah na soyayyar huda azuciyarsaba,al'amarin ya bakanta ran iyayen huda harma da sauran yan'uwanta,sannan aduk sanda sukayi kokarin kawar da rayuwarsa sai yazamana tamk
ar yarsu suke kokarin kashewa,ana ckin hakanne huda taja saurayinta shuraim akan su gudu subar nahiyar tasu,saidai basukai ga cimma nasara ba mahifinnnata ya fahimci nufinta,inda ananne aka yanke mata hukunci tsinuwar kaskanci a rayuwarta,yazamana duk inda zata shiga a fadin duniya bazata kasance mai mtsayi ba kaman yanda tkae a da ba ,sannan hukuncinta bazai taba barta ta tsallaka nahiyar suba.Wanan abinda yasamu huda yasa shuraim jin tausayinta matuka inda yagudu da ita aanguwar tsarauni ,domin shine anguwar dazasu zauna batare da angane hukuncin dake jikintaba.
Saida shuraim suka dauki wasu shekaru suna rayuwar farinciki inda yazage tukuru yana aiki domin ciyar dasu abinda yasmu,bayan wani lokacine huda tasamu ciki ta haifi yarta mace inda aka sama suna fariyatulsharmilah domin shine sunan datake mafarkin sakawa yarta da ta haifa,inda ake kiranta da farkon sunanta wato fariyah.Fariyah yarinyace da tataso cikin gata sannan kuma da abubuwa mabanbanta da rayuwar mutanen wajen sanadiyyar debo kashi 90 na jinin mahaifinta,sannan kuma dagatan datake samu daga iyayennata.Wargajewar rayuwar farin ciki na rayuwar su fahriya yasamo asaline da mutuwar da mahaifinnnata yayi,saiyazaman ya bada amanr iyalansa a wajen wani abokin aikinsa,saidai bai dade da mutuwaba abokinnasa yagano cewar huda tana dauke da tambarin kaskanci da iyayenta suka mata a matsayin hukuncinta,inda yaci amanar abokinnasa shuraim ta hanyar sayar da ita da yayi a bangarennasu ga wata hamshakiyar yankinnsu wanda kowa yasanta da hulda da manyan mutanen dasuke cikin garin wato ARYANA, matace datake bukatar ta dinga mulkar mutane saidai batasamu hakn ba,hakan yasa lokacin da abokin shuraim din yaci bashinta ta matsa masa daya biyata sai,yashiga damuwa,amma lokacin daya gano hukuncin huda sai yabada ita ga aryana a matsayin bashinsa ,sannan shikuma yatashi yabar anguwar.
Rayuwar huda itada yarta ta yashiga cikin kunci sosai a wajen aryana,amma dukda haka huda bata taba nadamar biyewa soyayyartaba domin indai fariyah na gefenta ji takeyi babu ya ita a duniya,saboda kama da tayi da mahaifinta ,dakuma zallan kayunsa data debo.Duk wani kunci da huda take fuskanta hakan bai hanata farantawa yar ta taba da kuma yimata duk wani abu data ke bukataba,saidai lokacin da fariyah tayi shekara goma aduniya sai yazamana hakalin aryana yadawo kan ta,sannan kuma da wani buri data dauka wanda ita kadai tasanshi akan fariyan.
CIGABAN LABARI.........
SADI-SAKHNA Aka the legendary novelist next chapter loading......
(The legendary story)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟
💎💐 ..... WATA RAYUWA....💎💐
Telegram https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0
written by sadi-sakhna
(02)
Daukar tulun tayi cikin sanyin jiki ta fita izuwa ga rafin tana sake-saken yanayin rayuwar tasu itada umminnata,da i0rin halin matsin da ta ta
so ta tsincesu aciki,duk da karanci shekarun fariyah amma takasance mai kaifin tunani dakuma basira,sannan tanada sanyi dakuma hakuri,yarinyace mai son taga tana da abokai dazata dinga wasa dasu ,saidai a yanayin data tsinci kanta yasa ta fuskantar tsangwama da kyama daga wajen su ,wanda hakan yasa sha'awar wasa da yaran yafara fita mata akai sai yazamto rayuwanta yazama tamkar ita kadai takeyi ,sanaddiyyar aiki da mahaifiyartata takeyi bata samun lokacin ta sai sanda zasu kwanta,a lokacin kuma yanayin gajiya yashiga jikinsu basu da lokacin tattauna matsalarsu.Dahaka tana cikin tunanine har ta iso ga babban rafin dayake nesa kadan da muhallinnnasu na tsarauni,zaunawa tayi a bakin wani dutsi gefe da rafin tana karewa wajen kallo,zuwanta baifi a kirgaba wajen saidai bata tba cinkaro da abinda ake cewa na hatsarin wajenba wanda hakan yasa wajen yake bata sha'awa matuka ,domin wajen nadauke da wasu irin tsuntsaye masu kyan gani harma da yan dabbobi dasuke kiwo a wajen ,sanadiyyar kyawun wajen dakuma iskar dake kadwa a wajen ga kuma ruwa sai hakan yafara kwantar mata da hankali sabanin da da ko ambatar sunan waje ake sa hantar cikinta ta kada sanadiyyar zuzuta hatsarin wajen datake ji daga bakin mutane daban daban,ta dan debi dakika a zaune wajen kana daga bisani ta tashi tanufi wajen deban ruwan da tulun a hannunta,tsugunnnawa tayi a gaban ruwan amma saita dagata da diban ruwan sanadiyyar ganin wata yar halitta mai matukar kyau na linkaya acan nesa da ita a wani bangare na kogin,shagala tayi da kallon wajen wanda har batasan lokacin data fara murmushiba,abin yadau hankalinta sosai sanadiyyar yanayin halittarsa data bata dariya sosai(abin na dauke da idanuwa manya kaman idanuwan yaro idan aka tsoritashi ,sannan jikinsa kuma mai kalar shudi da kore a hade,yana daukar hasken rana ,juyawa yakeyi cike da wasa acikin ruwan yayinda itakuma ta shagala sosai da kallansa,tashi tayi ta kara matsawa kusa ganin yagama wasa da ruwan dayakeyi,ganin ya nufi wani hanyane zai bacewa ganinta yasa ta binsa a hankali batare daya gantaba,basu yi tafiya mai nisaba taga yayi wata kwana inda itama tabishi da sauri,saidai yin kwanar nata keda wuya ta nemeshi tarasa.Juyowa tayi cikin rashin jin dadin bacewar tasa tadawo wajen gun tulunta,deban ruwan tayi da sauri ta nufi gidannasu zuciyar ta nadukan tar-tara,tun daga bakin kofar gidan taci karo da aryana na wani harkar tata daban,saidai ganin dawowar fariyahne ya tuno mata da ta aikata ma deban ruwa,sai asannane tafara masifar rashin dawowarta dawuri,idan da sabo tasaba da masifa dakuma azabar aryana wanda takasance tamkar abincin ta ,batare da taace kaala ba tawuce ta juye ruwan a randar uwar gidan tasu,kana tajuya tanufi dakinnasu da na kare yafishi kyan gani a ta fuskar fasali.A zaune take a dakinnasu tayi tagumi tana tunanin rayuwar tasu sannan dakuma kyakykyawar halittar da idanta yai arba da ita a rafi,tambayar kanta tafarayi kamar haka "ita a yanda ake mata bayanin jejin wajen da kuma halittunsa a tabbatar mata dacewa wajene mai hatsari da kuma abin tsoro,amma sabanin haka ita wajen ya birgeta matuka,wanda har tana sha'awar gobe tayi domin ta koma kozata hadu da hallitar datayi arba da ita a yau,duk tana tunaninne ita kadai harda murmushi akan fuskarta mahaifiyar tata tadawo daga aikin da aryana tasakata take mata akowane rana,tsugunnawa huda tayi tana kallan murmushin dake kan fuskar yar tata wanda a take ya wanke duk wata gajiya da ta dawo da ita,duk da batasan menene yasaka yar tata farin cikiba amma tayi na'am dashi matuka azuciyarta,daga kai tayi wanda sai a sannan takula da mahaifiyartata a gabanta tana tayata murmushin data gani a fuskarta,"ummi"shine abinda tafada kana kuma tace"sannu da dawowa ya aiki ummi?" "lafiya kalau fahriya ya kema aikinki da kuma rayuwar hakuri?nasan kina cikin WATA RAYUWA DA bazata ta ba yimimki dadi ba ,sannan kuma kuskuren mune nida mahaifinki,dakuma nawa laifin dabansan asalin danginsaba dana turaki wajensu,duk da suma ina tsoran dakyar su karbeki sanadiyyar keba cikkeken irnsu bace,sannan nikuma bani da ikon barin wannan kasar sanadiyyar abinda yafaru dani,amma kiyi hakuri fahriya cinaji ajikina dasannu rayuwarki zatayi kyau bakamar tawa ba kinji"da haka huda ta kai karshen maganarta cikin kuka wanda hakan yasa itama fahriya yin kukan,sannan tafara maida magana ga mahaifiiiiyar tata"ahahhh ummi ki daina fadar hakan domin ba laifinkubane kaddararkune hakan dakuma sanadin samuna ,sannan nima hakan kaddarata ce kuma na karbeta hannu bibbiyu,sannan koda kinsan inda dangin mahaifina suke bazan taba tafiya nabarki ke kadai ba ummi,zan zauna dake BAZAN BARKIBA,"bayan gamam magananr taane huda tajawo yar taata ta rungume suka cigaba da kukannasu da ba wanda zai rarrashesu.
To haka rayuwar su fahriyan takasance cikin dadi da babu dadi,wanda rashin dadin yaninka dadin yawa,a bangaren fahriya kuwa tun lokacin da taga wannan halittar sai yazaman kullum sai taje gefen inda ta taba ganinsa domin dubashi,saidai ko mai almaar kamarsa bata sake ganinba tun ganinta na farko dashi,tun tana damuwa da hakan har ta fara mntawa da batunsa amma hakan ba wai ya fita a zuciyartaba.
,
Shekaru har guda biyu sun ja a inda fahriya takai shekara yanzu 16 a duniya,sai yazamana rayuwar ta yakara wuya sosai domin yazamana aikin gidan aryana kaso 80%itane takeyi,domin a ganinta yakamata mahaifiyar ta tahuta a yanzu tunda ta taso,saidai huda kwakwata bata son barinta yin aiki sosai domin ita hakan a ganinta zata shiga hakkin yarinyarne sosai.Yanzunma hudane a tsugunne tana wanke kayan hidimar gidanna aryana da baya rasa mutane dasuke ziyar tar wajen,kwalamata kira ta taji uwar gidannata tayine yasata juyowa,kyawuntane yatafi dani matuka,wai hakanma cikar budurcinta bai gama fitowa ba sannan gakuma wayewa da wuya daya dafar da fatarta,amsawa tayi kana ta tafi inda kiran yake fitowa,zuwa tayi tatsaya agabanta dan taji yanzu kuma dame tazo,karkada hannu tafarayi tana yatsina fuska wanda a jikin mutanen na bardugu ma ita fuskarta da yanayinta abin tsoro ne,"maza kije ki debomin ice a jeji kuma kidawo da wuri kafin uwarki ta dawo ta min girki,dan ku tamkar karnuka na ne ,naciyar daku kumin aiki baku da wani amfani bayan hakan,wuce kiyi sauri kitafi da wani fari da jar fuska kaman fatalwaa,"takarisa maganarta tan nuna mata hanya cikin fada.Kama hanya tayi cikin kunar zuciya na maganr da aryana ta fada mata,hakika duk da tana kokarin jure duk wata magana da ta zuba mata to wannan din daban ne da sauran domin ya shigeta sosai,saida gama kukanta sannan ta kama hanyar zuwa deban icen wanda batasan takamamai hanyar ba domin lokacin da mamarta ta bari ta koma yin hidimar dukkan gidan kuma da zuwa saye da siyowar sana'ar aryanar,wani yarone shima datake azabtar dashi ya cigaba da aikin deban icen,tashi daya su fahriyah suka nemeshi suka rasa kuma basu da ikon tambayar inda yake.
Bayan fitarta daga gidane ta kama hanyar wani jeji nesa da anguwar tasu,wanda take da tabbacin zata samu icen a wajen,tafiya takeyi tana kara kallon wajen sosai ,har takai ga wani waje da take tunanin zata samu icen a wajen,har ta juya zata cigaba da tafiya sai hankalinta yakai ga wani waje a gefe mai ruwa akwance zuwa tai domin kallon kyawawan tsuntsayen dake wajen sai kuma idonta ya kallo abinda yafi komai ba ta mamaki ,wato halittar da ta dade tana neman inda take tsawon shekara da shekaru,karisawa wajen da take tayi a hankali domin jin tsoron kar ta sake bace mata irin na ranar data ganta,saidai abinne yabata tsoro matuka ganin halin da abin yake ciki...........
written by SADI-SAKHNA AKA the legendary novelist