x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 9 - KULU

  • 24001 words
  • 27000 words
  • Out of 28650 words

Category: Tale Stories

Views 153

29 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
jininka a cikin Masarautarmu to yau ga shi mun bincikota in har kana son ta rayu ya zamar maka wajibi da dolenka na lallai ka dawo a ƙasammu mu mulki masarautar ku,"


wata ajiyar zuciya ya saki brain ɗin shi ta cunkushe ya rasa gane me suke nufi "ƴa fa suke magana to shi yana da wata ƴa ne bai sani ba? baya ga ƴaƴansa ukku mata kuma biyu sunyi aure ɗayar na waje tana karatu wacce ko a yau sunyi waya, me suke nufi wane babban tuggun suke ƙullawa masarautarsa?" Ya tambayi kansa yana mai jin wani sabon ta shin hankali na lulluɓesa na jin cewar PRINCE ABIODUN ya shigo masarautarsa ya naɗar masu sirrukan Masarauta Ubangiji ne kaɗai ya san abin da zai wakana da kalar ta'adin da za suyi masa ya zamar masa wajibi ne shi ma ya fara shiri



cikin ƴan kwanaki sosai rukuni ukku ke shiri yayin da Rukunin ƙungiya ke na su na son kawar da Arush haka zalika Itama matar take bincikenta na gano Yarinyar da aka ce mata rana raye, sosai ta hau bincike,


Bishiyun jejin take kallo wan ta kafe Babbar ceɗiyar da idanuwa mai ƙullin jan ƙyalle wannan ya tabbatar mata da cewar Duna na wajen "na tabbatar da kana jina kana ganina a yau kace na dawo domin ganin fuskar yarinya na dawo da ƙwarin guiwata ka gwada man fuskarta" ta furta da sauke numfashi


Faran takarda ce ta faɗo a tafin hannunta ɗagawa tai tana dubawa tamkar T v haka take ganin yarinyar tun daga kanta take kallonta har izuwa ƙwayar idanuwanta wan da sak ta Mahaifinta haka zalika fuskanta ta Mahaifiyarta tamkar anyi copy na Arush haka yarinyar take babu abinda ya bambanta su illa ƙwayar idanuwansa da ba kala ɗaya bace da ARUSH wannan ko tantama ba tayi tabbatas ƴar Arush ce da ta ɓatar tsayin shekaru , sai dai Babban burinta bai wuci ta gano asalin ina take zaune a halin yanzun


"Duna na riga da naga fuskanta saura sanin in da take ko dan tunkarar in da take naga bayanta" ta furta da murmushin ganin nasara ta gabatota

Cikin dakakkiyar murya aka furta "tabbas na riga da na gano a inda take zaune za kiyi matuƙar Mamaki idan kika ji cewar tana zaune MasarautarHandaash,shiga masarautar ba zai miki wahala ba muddin kika shirya tuggu" wani murmushi ta saƙi mai nuna tsantsagwaron makirci tana furta tabbas zan yi hakan a halin yanzun zan dakatar da masu son kashe Arush matakin farko da ya kamata nabi shi ne fara ɓatar da hankalin ARUSH sannan na bi shirin dana ƙulla



*ARUSH*


Cikin bacci ta fara jin kamar sheaheƙar Kuka wacce ta fara hautsina mata lissafi, da brain a hankali ta buɗe idanuwanta tana saukewa a kan narƙeƙiyar macijiyar da ta kafeta da idanuwa tana zalzalo da harshe haka idanuwanta suna wani kalar shuɗewa


A hankali Arush ta sauko daga kan gadon tana zuwa akan mucijiyan da nufin dafata sai dai ɓat ta ɓace, a dai dai lokacin ne kuma taji dirar wani abu a gabanta yayin data ɗago idanuwanta tana ƙarewa Mutum ɗin dake tsaye gabanta yayin da aka lulluɓe fuska da jiki kafin tai wani ƙwaƙƙwaran motsi aka murƙusheta tare da shaƙa mata wani abu nan take brain nata ya juye hannayenta take son kaiwa ya zuwa Yaronta amma sam ta gaza hakan bakinta ya fara rawa da son magana amma ba hali nan take idanuwanta suka fara jujjuyewa





*MASARAUTAR HANDAASH*


*KULU*


Kwance take yayinda taji cikin baccin ana fara shasshafata da wani abu mai sulɓi a ɗan firgice ta buɗe idanuwanta tana saukewa a kan narƙeƙiyar macijiyar data kafeta da idanu wacce ko tantama ba tayi mucijiyan data gani a waccan kari ne, baki take so ta buɗe ta fasa ihu ko za taji sassauci amma sam ta gaza haka jikinta ya fara karkarwa idanuwanta suka fara kakkafewa tana son somewa wata tsawa taji an daka mata wacce ya sa ta yin laƙwas ta buɗe idanuwan nata tana haɗiyar wani mugun yawu jin muciyar na magana "ban zo wajenki da niyyar cuta miki sai ma taimakonki da nake so nayi tabbas rayuwarki na a haɗari babba, yanxu ne taskar mabuɗin ƙaddararki za ta fara buɗe wa tamkar yacce ta Mahaifiyarki ta buɗe tun a matakin shekarun da kike, ina son dukkan abin da kika gani ya haye miki karki fitar da rai da matakin nasara a baya, rayuwarki lulluɓe take da cutuwa , wacce muddin baki cire tsoron dake ranki ba ba zaki taɓa ci gaba ba, ba lallai idan kin ganni yanzu ba ki sake ganina a karo na gaba ki amfani da kalmomin da na faɗa miki cikin hikima da basira, ki cire tsoro ki fuskanci ƙalubalen rayuwarki ƙaddararki yanzun ne za ta soma a baya ba komai bace" tana gama faɗin hakan ta kafeni da idanuwanta waɗan da idan nawa idanuwan ba gizau su kayi ba kamar har hawaye naga suna zubarwa, a hankali ta saka wutsiyar ta tana shafa mun kai tana furta "ki gazgata zancen da kika ji ana faɗi na cewar ke jinin Masarautar JOHAAN ce ba ƙarya aka furta miki ba" tana gama faɗin hakan ta ɓace yayin da ni kuwa zufa ke ƙara tsatstsafo min ina mayar da mugun numfarfashin na gaza tantance tsakani ruɗu da tsoro wane ne yafi yawa haka maganganunta na fara aunasu a ma'aunin lissafi,


Waje guda na makure ina ƙara jan dogon numfashi tare da bin mutane dake kwance ɗakin da kallo,

Na daɗe a zaune har gari yai haske Bintu ce ta buɗe idanuwa ta ganni zaune ina ƙarewa Mutanen ɗakin da kallo kallona tayi tana furta "kulu mai ya hanaki shiryawa ki fita?"


"Ba komai" na furta a taƙaice sbd yanda nake jin kaina ,Azalzala mata da ake ta taho shi ke bai bani damar ci gaba da magana ba, haka ta fice

Ganin sun fita ya sakani miƙewa nima jikina sam ba ƙwari na shirya ganin har rana ta fara fitowa


Kamar yanda na saba sashen sa na nufa in da na tarar bai nan alamar ya fita game samu nai na gyara ko ina na ajiye masa break fast nashi ganin bai dawo ba ta sakani yin Arwallah a gurguje ina na kabbara sallah wan da nake roƙon Ubangiji yafiya kan jin hutarkirin da nayi


Motsin da naji a bayana ne ya bani damar juyowa gabana na wani irin bugawa zuciyana na wani irin harbawa da sauri _sauri da wani kalar mugun kallo da kuma tsananin tashin hankali yake kallona bakinsa na rawa ya furta "You Are a Muslim?"


Hawaye sosai suka cika man idanuwa ina ɗaga masa kai hankalina a matuƙar tashe ,bai iya furta magana ba illa fatan Allah ya sa shine kaɗai ya ganta wani bai ganta ba cikin zubar da hawaye na furta "na tabbatar ban cancanci yafiya ba ƙaddara ce ke bibiyar rayuwana kai mun rai kar ka faɗawa kowa"


a mamakina murmushi naga ya sakar mun yana furta "Josmie ko kaɗan ba wan da zai sani fatana dai ace ni kaɗai ne ya ganki kina salla,dan duk wanda aka kama Musulmi a masarautar na kashesa ake, abin da bana fata kenan,"


Ajiyar zuciya na saki ina ƙara godewa Ubangiji, "Thanks" na furta a hankali, hannayena ya kama yana kallon idanuwana da murmushi cikin wani salo ya fara murzawa da son kawo fuskarsa a tawa saurin kaucewa nai ina kwace hannuna "pls ka daina ni sam Addinina bai bada damar wan da ba muharramina taɓani ba"


mamadin naga damuwa ko ɓacin rai sai naga akasin hakan yana murmushi "idan na aureki fa?"


"Shi ma auren ba zai yiyu ba" na furta a hankali

Annurin dake fuskarsa ya ɓace yana mai jifana da kallon son karin bayani "Josmie ban gane me kike nufi ba "


"Ina nufin Addinina bai yarje mun auren wan da ba Musulmi ba, ba zan taɓa aurenka ba har sai ka kasance kai ɗin musulmi ne wan da na tabbatar ba mai yiyuwa bane, na sha gaya maka cewar ni dakai ba zamu taɓa mallakar juna ba, sbd nasan ba aure a tsakanina dakai har sai ka karɓi musulunci wan da abu ne mai wahala" na furta


"Ko kaɗan Josmie akan na rayu dake zan iya aikata komai kin tabbatar mun da sai na musulunta zan iya mallakarki to tabbas zan musulunta sannan na mallakeki a yau zan tabbatar maki da abinda kike ganin ba zai faru ba tabbas zai faru a yau ɗinna" ya ƙarashe zancen cikin sanyin murya

Ni kuwa sosai nake kallonsa da mamaki wasu hawayen farinciki na sake wanke mun fuska ina ƙara jinjina girman ƙaunar da yake mun, kafin nayi mashi wani magana ya fizgi hannuna, wata ƙofa naga ya nufa wacce ban san da zamanta a dakin ba, ta ita muka fito wata farfajiya wacce ba kowa a wajen sai manyan motoci cikin sauri ya jani muna shiga ɗaya daga cikin motocin umartana yai dana kwanta a back seat don kar a ganni, kwanciyar nai ina mai jin zuciyata na harbawa da sauri, tayar da motar yai inda muka dumfari get ɗin ba tare da sanin shi bane aka buɗe masa wanda sosai yai tafiya before mu fita get ɗin masarautar

Hankalina a masifar tashe nake kallonsa ina furta "what are you planning to do?"

"I will marry you I tried for you, I'm not ready to live a little breakup I will assure you of the war that you think will not happen "naji saukan furucinsa Wanda yai dai dai da bugawar zuciyana


"Aurena fa kace za kayi baka tunanin matsalar da zata biyo baya kayi haƙuri ka mayar dani zan zauna a matsayin da nake" na furta


Ba tare da ya ƙara mun mgn ba ya ci gaba da tafiya, munyi tafiya mai tsayin gaske before yai parking mota a wata unguwa wacce kai da ka gani ka san ta maras ƙarfi ce p cap ya saka da face masks yanda ba za a iya ganeshi ba umartana da na zauna a mota yai, ya fita a hankali yake bin unguwar da kallo zuciyarsa na buga masa haka zalika yana mai jinjina girman kasadar da zai yi,sai dai zai iya komai a kan ya mallaki kulu


bakin wani gida yaje yana mai tsayawa yana tunanin yanda zai fara gabatar da maganarsa, gyaran Muryar da yaji anyi ita ce ta mai do sa daga tunanin daya tafi

ɗago da idanuwansa yai yana saukesu akan Dattijon dake tsaye gabansa wan da da alamu shine mai gidan


hannun Ya miƙa masa sukai musabaha, before ABIODUN ya ɗan nisa yana furta "na san da cewar ba ka Sanni ba sai dai ganina kawai da kayi da wata babbar buƙata nazo maka domin na sha jin cewar kai ne babban Malamin Musulunci a garin nan, na zo maka da maganar cewar ni ma a yau ina son ka musuluntar dani tabbas zan shiga a jerin sahun Musulmai"


"Allahu Akbar haƙiƙa na tayaka murna da har ka gane addinin gaskiya za kabi sahummu"dattijon ya faɗa


Ɗakin soron gidan ya ja ABIODUN suka zauna nan take ya karɓi musulunci , sosai mutumin ke murna in da duk wani abu ya fara koya masa ganin bai da lkcn koyon ya saka shi samun biro da littafin ya rubuta dukkan Abinda Ya dace Musulmi yayi kama daga wanka da banbance su Arwallah sallah,haka zalika yace ya zaɓi sunan da yake so, cikin sunayen da aka bashi zaɓi sosai yaji sunan ALIYU ya kwanta masa dan haka ya zaɓeshi


"Sai dai har yanzun ina da wani Abun da zaka min shine aura mun wacce muke tare da ita" ABIODUN ya faɗa


"Ba damuwa ina ita yarinyar" Dattijon ya faɗa ba tare da ya bashi amsa ba ya je ya taho da kulu wan da idan banda zuciyana dake bugawa babu abinda yake haka zalika ɓangare guda na tsinci kaina da faruncikin musuluntar da ABIODUN yayi

"Tabbas kina da Babban rabo a duniya da lahira, tun da ki zamto musuluntar sa, kika kawo shi ya zuwa addini gsky a halin yanzu ya zo min da maganar aurenku," Dattijon ya furta yana mai kafeni da idanuwa

Ba tare dana bashi amsa ba ya ci gaba da cewar "sai dai ina da tambayar ke ina mahaifanki suke duk da nasan ba lallai shi iyayensa sun sani ba"


"Ban da kowa nima sanin iyayensa ba za su amince ba ya samu zuwa nan"


Jijjiga kansa yai yana furta, "ma sha Allah na ɗauki nauyin biyawa Aliyu sadaki"

Jinjina da godiya mu kayi masa wan da ba tare da ɓata lokaci ba ya tara shedu aka ɗaura mana aure akan sadaki 30k,

Sosai yai mana nasiha ya ƙara tunatar dani kan koyawa ABIODUN abubuwan Addini


Sallama mu kai masa da godiya muka bar wajen,koda muka dawo mota sosai yake zuba murmushi da farinciki hannayena duka ya kama yana ma ƙara narkar da idanuwansa a cikin nawa "na tabbatar ba sunanki Josmie ba ko za ki iya gaya min sunanki na zahiri yanzu"


Murmushi na saki ina furta "HAUWA'U amma wan da aka fi kirana da shi shine KULU"

murmushi ya saki yana mai furta "Hauwwa"
Murmushi nai, a hankali ya saka hannayensa yana mai rungumeni tsam a jikinsa tare da sauke ajiyar zuciya tallafo da fuskana ya yi yana haɗe bakimmu waje guda yana tsotsa, cikin wani kalar salo da ya haifar mun da shiga cikin wani yanayi na daban, sosai na muka ɗan sha soyayya before mu tsagaita mu dumfari Masarauta wanda ƙirjinanmmu ke ci gaba da bugawa


Lkcn da muka shiga ciki sosai gabana ya tsananta faɗuwa ina mai jin jikina ya sauya mun yadda muka fita ba tare da an gammu ba haka muka dawo ba tare da wani ya gammu ba,



ɗakinsa na koma ina mai zama tare da mayar da numfarfashi zuciyana fal cike da tsoro, da ƙarfi aka buɗe ƙofar Falon wan da dukkammu sai da gabanmu ya faɗi sakamakon ganin Uwar gidan sarki wacce ke bina da tsinannan kallo tana bin ABIODUN tare da furta "Where did you enter? It's been a while since you've been home. and you let someone know that you are not going out"


ɗan yatsina fuska yai yana furta "Awujo I am a small child and when I go out I have to announce"

Ba tare da ta mashi magana ba ta juyo wajena tana kallona wan da muka haɗa idanu, a masifance taxo kaina tana ɗaga hannayenta tana sakar min marin da sai dana fasa ihu tsabar zafi ga wajen da ya ɗan fara fashewa, "I am your generation and you will make eye contact with me and get out of here and you will be punished badly"


Sosai ABIODUN yaji marin wan da har sai da ya rintse idanuwansa yana mai jin zuciyarsa na mashi zafi,

"Son" yaji saukar muryan Mahaifiyarsa wacce ke shafa masa kai, zuciyarsa a cunkushe ya amsa da "Yes"

Cikin ɗan damuwa ta dubesa tana furta "ko kasan goben nan Mateo zai dawo sbd umarnin da Mahaifinka ya bayar kan ya dawo ya saka maka ido akan bai yarda da kai ba sbd gujewar mu'amalantar jinin JOHAAN "


Shiru yai na lokaci kaɗan yana mai jin wani yanayi a tattare dashi haka za lika idanuwansa sosai suka tara ruwan hawaye na tuna cewar ya karyawa Mahaifinsa Arqawalin daya ɗaukar masa,

Da mamaki Maman nashi ke kallonsa tana furta "Abio kukan me kake hakan?"

"Ba komai idona ne dake ɗan ciwo , Awujo ina da buƙatar keɓewa ni kaɗai" ya furta a hankali wanda ranshi da zuciyarsa sam ba daɗi



Ɗan ɓata rai tayi tana kallonsa "Abio ba gsky ka faɗa mun ba dole da akwai dmw a ranka ka faɗa Mani me ke damunka"


shiru yai yana furta "Awujo ba komi ki bani maganin ciwon kai nasha"


Ba tare da ta sake magana ba itama ta ɗauko masa Box ɗin maganin sanin ba zai ƙara mata magana ba sbd shi kaifi daya ne

ba shi tai yasha tana fita ranta cike fal da damuwa,


ABIODUN kuwa sosai ya ke son sake keɓewa da kulu Babban ta shin hankalinsa shi ne bai wuci jin cewar gobe Mateo zai dawo wan da sam bai ji daɗin hakan ba, ya tabbatar da ba zai dinga samun damar keɓewa da kulu ba,


Wankan shiga musulunci yayi tamkar yanda aka koya masa,abubuwan daya rubuta ya fara koyo wan da cikin hukuncin Allah dandanan ya iya wasu abubuwan


Har yai Sallar La'asar har zuwa ishsha'i wan da har lokacin bai sake ganin Kulu ba wan da sosai ya ɗan shiga damuwa


*KULU*

Tun lokacin dana fita na wuce ya zuwa sashemmu hawaye na zuba, ɗakin na dumfara wan da wajen yake a kulle

Sama_sama na fara jin ihu da nishi na tashi wan da ya sakani ɗan tura ɗakin a tunanina ko wani ne ba lafiya

Sai dai abinda na gani ne ya sakani ja da baya ina ambatar sunan Allah wan da idanuwana suka kafe kan Ochuchuwa da Febo da suka danne Bintu suna shirin cimma manufarsu, hankalina a matuƙar tashe na nufi wajensu, mamadin naga shakku ko nadama sai naga sun sheqe da dariya, suna nufoni rufe idanuwana nayi sakamakon ganin jikinsu haihuwar uwarsu,. Hannu Febo ta saka tana fizgoni wan ɗa ko kaɗan ban yi motsi ba illah raina da ya fara ɓaci zuciyata ta fara sosuwa, zanenta Bintu ta rufa tana zuwa bayana ta ɓoye, wan da idan ban da kuka babu abin da take, ihun da naji Ochuchuwa ta saki ne ya sakani kallonta muna zaro idanuwa ganin yanda jinin ke zuba a gabansu ga kumfan daya fara fitowa a bakunansu hankalina a tashe naja hannun Bintu muka fita don na tabbar da cewar Diyana ce kuma tabbas sai ta kashesu yanda ta fitar musu da kumfa a baki ta sakar musu dafi


Waje na samu ina zama, a matuƙar tsorace Bintu ke kallona tana furta "Kulu me ye hakan waye ya fitar musu da jini"

"Manta da babinsu Bintu naji da abinda ke damuna," na furta da hawaye


"Wace damuwa?" Ta tambayeni da son jin qarin bayani


Sosai na zauna na bata labari wan da take kallona da al'ajabi da kuma jinjina wa lamarin Ubangiji,sosai ta bani baki da rarashi kan na kwantar da hankalina,


Mun dade sannan muka fara jin
End Ads