ihun mutane da koke koke tunkarar wajen mu kayi wanda muka tarar da gawar su Ochuchuwa,hankalina sam bai tashi ba bcox na saba da kalar wannan abun, bayi da kansu su kai musu al'adar su suka samu wajen aka birne gawarsu
*Washe gari*
Tun da sassafe kake jin sautin bisa wacce ke nuni ana buƙatar ko wane ya hallara ya zuwa Fadar sarki kama daga iyalan sarki har Bayi,mutanen gari
Ban san mi ya sa ba na tsinci kaina da bugawar zuciya haka zalika na tsinci kaina a damuwa
Misalin ƙarfe 8:00am dukkammu muka hallara wajen wan da Babbar Fadar ta kacame da mutane da dama sai dai ko wane da ɓangarensa bayi daban mutanen gari daban, mu dake bayi muka jera layi ,
sosai nake kallon wajen da Sarkin yake da nufin ko zan ga ABIODUN,sosai idanuwana suka sarƙafe da nashi murmushin da ba lallai a gane yana yin sa ba ya sakar mun, wan da nai saurin kawar da kaina gefe
sosai wajen yai tsit yayin da ba ka jin sautin komai sai maganar mai martaba Adewale Femi, wanda yake furta "na san mutane da dama za suyi mamakin yanda akai na buƙacesu, ba komai bane face ina son a yau na gano munafikin ɗan aiken da JOHAAN su ka aiko a yau ɗin nan zan fitar da jinin JOHAAN wan da muddin na kama shi sai na azabtar da ko waye kafin na yanke masa hukuncin kisa,tabbas ko wacece za ta riski mummunan hukunci, ki fito da kanki ko wacece"
Lokaci guda zuciyar Kulu data ABIODUN ta buga sosai ya shiga ruɗu da ta shin hankali "yaushe Mai martaba ya yanke wannan hukuncin ba tare ɗaya sanar dashi ba, ya Allah wace ƙaddara ce ke gabatoshi haka?" ya furta a zuciyarsa
Ni kuwa sosai gabana ya tsananta faɗuwa "ba ƙarya aka faɗa miki ba tabbas ke jinin JOHAAN ce" na furta a hankali ina tariyo maganganun ABIODUN Diyana Mucijiyar data sanar dani harna fara gazgazgatawa , kenan nice wannan jinin da masarautar ke nema, wannan ce ƙaddarar da ake furta Mani za ta auku gareni me zai faru dani ban sani ba a hankali wasu siraran hawaye Masu zafi suka fara saukar mun a kunci ba tare dana bari wani ya gani ba na share ina mai addu'ar neman sassauci
shiru wajen yai kowa kansa na ƙasa ganin hakan ya saka mai martaba umartar da akawo wani zobe wan da ake buƙatar kowa ya saka in har dutsin wannan zoben ya kawo jaaa to kai jinin JOHAAN ne
Ruɗu bana wasa ABIODUN ya shiga ba,bai ida shiga ta shin hankali ba sai da yaga zoben wanda da kanshi ya dauko wannan zoben a JOHAAN ,bakinsa ya gagara furta komai idan ban da jikinsa ɗaya ɗan fara kyarma kanshi ya ɗauki zafi
zoben nan aka fara sakawa Bayi wan da kowa aka saka mawa bai kawo jaa, duk layin wani idan yazo sai zuciyata ta sake bugawa, ga ko ina da tsaro babu damar guduwa, layi ne yazo kan Bintu wacce daga ita sai ni, hawayen dake maƙale a idanuwanta na shanye lokacin da layi yazo kaina hannayena na miƙa ina mai rintse idanuwana, da fatan Allah ya sa ba nice Jinin JOHAAN ba, shirun da naji na ƴan daƙiƙu ya bani damar buɗe idanuwana, wani kalar zaro idanuwa nai ina girgiza kai ganin Zoben ya nuna ja a dutsen, bakina ya fara rawa hawaye suka fara fitowa a ciki
kowa na wajen sosai yake kallona musamman Sarkin dake man da wani kalar tsinannan kallo mai nuna zallar tsana, ban ida dawowa daga ruɗun dana tafi fa naji an wani harɗeni da sarƙa mai masifar zafi wacce tai sanadiyyar faɗuwata ƙasa kaina na buguwa da girkakken dutsen dake ajiye, nan take na ƙwalla ƙarar azaba jini na tsartuwa
Tun lokacin da jan ya kawo a zoben ABIODUN ya rintse idanuwansa bai ida dawowa hayyacinsa ba sai da yaji ƙararta buɗe idanuwansa yai yaci karo da jinin dake tsartuwa a goshinta da bai kasance mai dauriya da wayancewa ba tsab za ka iya karantar yanayinsa na shiga tashin hankali
Bintu kuwa wacce bata da dauriya tuni ta fashe da kuka tana furta "na higa ukku ni Bintu za su kashe Kulu" da mugun gudu ta nufi wajen mai martaba tana faɗuwa " mai martaba kai man rai karka kahe mun ƴar uwa"
ƙafarsa Mai martaba ya saka yana shure Bintu tare da bada umarni a haɗata da Kulu a ɗaure wacce turjejen da take da burburwa ya harduƙa wani Dogari ya bugaa mata babban ƙarfen dake hannunsa a kai wanda ta tafi Luuu ta faɗa a hannun *MATEO* wan da shigowarsa kenan a masarautar da wani kalar kallo yabi ta yana ida yada ita ƙasa tare da yatsina fuska
Ihuuu mai ƙarfi na fasa ganin numfashinta ya tsaya cakk, ga jinin dake zuba tamkar an buɗe famfo,cikin rashin imani wani bafaden ya fara jana da sarƙar a ƙasa wanda duk inda ya ja sai wurin ya kwalje yana tsirtuwar jini
Har akan ƙafar mai martaba aka jawoni wan da a lokacin na fara ganin dishi_dishi bakina ya gaza buɗe wa,cikin rashin imani da tsana Adewale Femi ya saka ƙafafuwansa yana take man wuya tare bubbuga mun sandar hannunsa, hannu ya miƙa aka bashi babban karfen daya tanada a cikin wuta hannayena ya kama yana aza mun ƙarfen yayin daya sake buga mun kai da wani dutsen nan take jinin ya biyo hancina da baki, yayin da naji dukkan wani numfashi da motsi ya tsaya mun
Wata gigitacciyar ƙara ABIODUN ya saki yayin da hankalin mutane ya dawo kanshi a ciki harda mai martaba, dake kallonsa a mamaki ganin yanda jikinsa ke rawa haka zalika hawaye na biyo kuncinsa
"Abinda kake gudu tabbas ya faru me yasa za ka min haka ba ita ya kamata ka hukunta ba ni yadace ka fara hukuntawa kafin ita domin ita ba tada laifi nine da laifi da har na aureta,a halin yanzun ta zama mallakin ita ɗin matata ce ita ce wacce na zaɓa akan rayuwar masarautar .........."
Alhm anan na kawo qarshen littafin kulu Book 1 mu haɗe a Book Two
*To fa yanzun wasan ya fara,yanzun ne lvr kulu da buɗe shafin ƙaddararta zai soma,shin me ke faruwa da masarauta JOHAAN , su waye ke ƙulla tuggu da makircin kashe ARUSH da Yaronta,wace ƙaddara ce ta bibiyi Arush a tsawon shekaru ,wace mai sace Mata yara wacce ita ce sanadin sace Kulu a halin yanzu kuma take neman kawar da ita, shin za tayi galaba wajen haukatar da Arush kuma ta kashe Kulu kamar yanda tai iƙirari shin wai wace gaba ce tsakanin masarautu biyu da har HANDAASH ta tsani jinin JOHAAN shin ya Kulu da Bintu za su kasance kashesu za a yi kokuwa, me zai biyo baya baya ga jin furucin ABIODUN, ku biyoni a Book Two wan da zai baku amsoshinku ya warware muku cakwakiya da sarƙaƙkiyar dake ciki, ku sani fa KULU ba a fara komai a cikinsa ba yanzune lvrn zai fara cike da tarin abubuwa, idan kina son mallakar na biyu za ki biya ɗari Ukku kacal ta wannan Account ɗin 9074759493 Maryam zubairu sani opay bnk idan kuma kati ne za ki turo na ₦400 za ku turu shaidar biyanku ta wannan number 09074759493*
*Mai son tuntubata ga number 09074759493 or 08109554986 *
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng