godiya bayan ya bata maganin da yanda za tayi amfani dashi
Washe gari jin da kanta tai masa girki da magungunan da Boka Olesegun ya bata, bayan ta gama shirya komai ta Hakimce a kujeran Falon tana jiran shigowarsa
Ƙamshin turarensa ya sanar mata da shigowar ABIODUN cikin wani kalar farinciki da ya fito tsantsa a fuskarta ta miƙe tana faɗi"Welcome my beloved son"
Murmushin ganinta yayi yana mai ware hannayensa ya rungume ta tare da faɗin "thanks" ya faɗa tamkar wanda bai son magana
A fuska kawai wannan murmushin da annurin fuskarta ke fita amma a ƙarƙashin zuciyarta ƙuna take, kukan zuci ne fal a cikinta ƙiyayyarsa tai mata ninkaya ta dabaibaye dukkan wani loko nata, rugumarsa da tai ji take ƙara acce garwashin wuta ne ta taɓa da da hali tabbas babu abinda zai hanata ɗaukar rayuwar Abiodun ta yadda gawarsa ma ba zatai kyan gani ba
Cire jikinta daga nashi tai tana ƙara ƙaƙalo masa murmushin da dauriyar yinsa kawai take, tsabar iya makircinta, ya saka ba zaka taɓa cewa ba a zuciyarta yake ba
hannayensa ta kama ta zaunar dashi tana ta masa maraba, a zuciyar ABIODUN kuwa sosai yake jinjina girman ƙaunar da Boluwatife ke masa yana mamakin yanda Awujonsa ke son rabashi da ita
Maganar ta ce ta
katsesa tana furta masa da yaci abinci girgiza mata kai yayi alamar ba zai ci ba cikin dmw tace " My son, what do you mean you don't eat food I prepared this food with my own hands" ta faɗa da dmw
Murmushi yayi yana faɗin "I ate food in Awujo, that's why my stomach was full and I couldn't put any food in it"
Ba don taso ba ta kyalesa amma a zuciyarta ta ayyana dolensa yaci Abincinan "tohm shikenan amma ka tabbatar girkin dare a wurina za kaci tun da kaci na wajen Awujenka"
ɗaga mata kai yayi alamar to, yana tattaro dukkan nutsuwarsa ya mayar da ita a gunta tare da faɗin "Mama Bolu,wani abun ne ke faruwa da masarautar nan ne da har Daddy ya gaza faɗa Mani, sannan naga tsantsar tashin hankali a wajensa wan da ban samu damar tattaunawa dashi ba, amma nasan dukkan wata damuwa na Daddy ke kin sani ki faɗa mani babban dalilinsa na cewar na baro London nasan ba lafiya ba" ya faɗa cikin harshen turanci
murmushi tayi tana mayar da hankalinta gunshi tare da shimfiɗa damuwa a fuskarta tana faɗin "Son tabbas dan dmw da akwai ta a masarautar nan abin da Mahaifinka ke gudu a tsayin shekaru yau gashi yana shirin faruwa a masarautar nan sbd jinin JOHAAN na a cikin masarautar nan"
Sosai maganar ta dake shi amma yai ta maza ba tare da ya iya mgn ba, miƙewa yayi ya fita zuciyarsa sam babu daɗi
Kai tsaye sashensa ya nufa yana kwanciya yi tare da lumshe idanuwansa Oba Adewale Femi kawai yake jira ya dawo daga fada domin ya ƙara jin ba'asin zancen
Da ƙyar ya samu baccin gajiya na ɗaukar sa, wan da ya daɗe yana before ya farka wanka ya sake yi yana son nufar Mahaifinsa wanda ya tabbatar a yanzu ya dawo daga fada
Zaune yake yana sauke numfashi jin mahaifinsa ya gama kora masa jawabi tamkar yanda Boluwatife ta faɗa masa, "wane shiri yanzu ake ciki" ABIODUN ya faɗa
shiru Oba Adewale Femi yai yana
kallon itama Mahaifiyar ABIODUN ɗin wacce take sauraronsu, "ABIODUN a iyakar bincikena tun kafin abun ya faru an sanar damu ba wata mafita mafita ɗaya ce mai tsauri ita ce barinka a Masarautar HANDAASH"
Daga shi har Maman nashi kallon Oba Adewale Femi suke cikin tsantsar mamaki da zallar razani bakinsa na rawa ABIODUN ke furta
Dad, you know what you're talking about" ABIODUN ya faɗa cikin kodai mahaifin nasa ba a hayyacinsa yake ba sai dai maganar da yaji ya furta ne ya saka shi gazgata lallai yana hayyacinsa "ABIODUN, I am aware of what I am saying that you should leave this kingdom" ya faɗa da hawayen dake biyo kuncinsa wanda tun da suke basu taɓa ganin koda ɗigon hawaye a idanuwansa ba sai yau da ya furta ABIODUN yabar masarautar sa da bakinsa akan wani dalilin da ba lallai ya faru ba hasashe ne kawai cikin masifa da tujara Maman ABIODUN ta fara faɗin "ABIODUN has nowhere to go, he will never leave this kingdom, on what is an illusion, there is no war about it."
hannu ya Adewale Femi ya ɗaga mata yana mai mata kallon takaici da rashin hankali ƙofa ya nuna mata ta fita, wan da cikin fushi ta fita tana mai zazzaga masifar ɗanta ba zai bar masaurar nan ba
ABIODUN kuwa ya gaza furta komai wanda numfarfashi kawai yake fitarwa ,
*KINGDOM OF JOHAAN*
Wani kalar zafi da huci ke fitowa daga jikinta sosai take mayar da numfarfashin azabar da take ji a duk lokacin da zata haihu sai dai na wannan karin daban yake , Azababben zafi ne ke ratsata tun daga kanta har izuwa tafin ƙafarta dalilin haka ya haifar mata da karkarwa tamkar wacce taji kiɗan gangi wanda haka ne ya haifar mata da gumin dake tsatstsafowa daga ko wane loko na jikinta
A hankali ta ƙara lumshe Manyan dara daran idanuwanta tana ambata Jesus a hankali wan da a fatar bakinta ne kaɗai za ka gane, Gimbiya Josmie dake tsaye kanta tuni idanuwanta suka cicciko da ruwan hawaye tana faɗin "Ki daure za ki iya da amincewar Jesus" ta faɗa da harshen turanci
cikin dakiya da jajircewa Matar dake naƙudar ta buɗe idanuwanta tana kallon Josmie tare da buɗe busasshen leɓenta tana girgiza kai hawaye na biyo kuncinta ...............
*RIAMCOOL ce*
Writer of
RUSHEWAR RAYUWA
BAYAN WUYA
ANYA UBA NE
AND NOW
*KULU*
[10/23, 9:03 PM] CUTIE~RIAM: *KULU*
*BY RIAMCOOL*
*Mikiya writer's Asso.....*
*Bismillahirrahamanirrahim*
P.21&22
"Josmie ba zan iya ba na tabbatar a wannan karon ma Abinda zan haifa ba lallai ya tsira ba, shima halakar man dashi za ayi, na roƙi Yesu Jesus da in har za a halakar man da wannan yaron na cikina to na fi son mutuwa taxo ta ɗaukeni ba zan tashi ba kawai" wanda duk wannan maganar da take ta nayi ne cikin ƙarfin hali ba fita take sosai ba, iya fatar bakinta dake motsi kawai za ka gane abinda take cewa
girgiza kai Josmie tayi ruwan hawaye na ƙara ambaliya a kwarmin idanuwanta, "Za ki tashi da yardar Jesus sannan ki reni yaronki da hannunki a wannan karin babu abinda zai faru da yaron cikinki"
dukda azabar da take ji hakan bai hanata mayarwa Josmie amsa ba, "da gaske wannan karin ba za a halakar man ya yaro ba, kamar yanda aka halakar man da ƴaƴana ba ɗaga mata kai Josmie tayi tana mai murmushi wan da yake haɗe da kukan tausayi,
yayinda da lkc guda kuma tai wani nishi mai ƙarfi daya haddasa fitowar jariri wan da ya canyara kuka a lkc ɗaya, lamo tayi tana mai lumshe idanuwanta tana jin wani bacci bacci na niyyar fixgarta sai dai tai ƙoƙarin hana kanta sbd wannan baccin dake fixgarta shine sanadin duk halakar ƴaƴanta, a wannan karin ba zata bari hakan ya faru ba, don haka tayi ƙoƙarin ware manyan idanuwanta masu matuƙar kyau akan yaron dake hannun Josmie yana canyara Kuka
Murmushi mai haɗe da sautin kuka ta saki "Josmie yau nice na ware idanuwana akan abinda na haifa wan da hakan bai taɓa faruwa ba"
iya ɗaga mata kai kawai Josmie tayi tana murmushin farinciki, cikin lkc ƙanƙani Masarautar JOHAAN ta san da cewar Gimbiya ARUSH ta haihu sannan ɗa Namiji
Tun lokaci da. Mai martaba ya shigo ya zuwa ɗakin da ARUSH ɗin take ya kafeta da idanuwa yayinda shima hawayen farinciki ke fita "na haihu a wannan karon ba tare da banga fuskar abinda na haifa ba, nayi farinciki da godiya ga Yesu domin shi ne ya bani damar ganin wannan yaron ina son ku tabbatar man da cewar tabbas zan rayu da yarona, ku bashi kariya daga halakakkun gidan sarautar nan, ku tsare shi daga makircin maƙiya" ta faɗa da ƙwalla cike taf a idanuwanta wanda murmushi da annurin ke akan bisa kyakkyawar fuskarta
shima murmushin ya saki yana kama hannayenta duka tare da saka idanuwansa akan nata "ARUSH I can assure you that this time our child will not perish" murmushi mai haɗe da dariya ta saki tana rungume sa, wanda duk abinda suke Gimbiya Josmie na kallo tana sakin murmushin farinciki yayin da ta kaiwa mai martaba Yaron sosai ya riƙesa yana kallonsa wan da murna ce fal a ransa ganin ya samu Magajin masarautar Handaash, a daren ranar sosai akai shagali yayin da farinciki ya ninkaya a masarautar Handaash
yayinda a gefe ɗaya na munafukai da kuma maƙiya ba haka suka so ba, baƙi ciki ne fal cike da zuciyoyinsu,
sosai take haki da furzar da iska mai zafi tana mai sake jan wani numfashin tana fitar dashi yayinda idanuwanta sun kada sun yi ja kai kace gauta, "ina ina da hakan ya faru me ya saka a wannan karin Yaron ARUSH ya tsira?? tun bisanin shekara Ashirin nice ke galaba akanta mi yasa a wannan karin banyi galaba ba akanta, ga shi abinda nafi tsana ne shine samuwar wani ɗa Namiji a gidan sarautar nan kayi duk yanda za ayi kaga ka halakar da yaron nan" ta faɗa da dakakkiyar murya ta tsofi wacce har kyarma take
Mutumin da tsawon shekaru yake tare da ita but har a wannan lkcn bai taɓa ganin fuskarta ba idan banda yamishashsun idanuwanta wan da tsabar tsufa ya saka su yamushewa, itama a nata ɓangaren bata nuna masa cewar ta ganesa ba, duk da kalar ɓadda kamar da yake hakan ba zai hanata ganewa bcox makira mace ce mai haɗarin gaske
Jijjiga kansa yai yana shaƙe murya"in dan wannan karki damu ki saka a ranki tamkar anyi an gama ne duk da na dan ba mu kaɗai bane masu harar yaron nan ba" dariya mai nuna zallar jin daɗi tayi tana furta "nayi Alqawarin ARUSH ba ke babu jin daɗin haihuwa haka zan ci gaba da ɓatar miki da yara" sosai suka tattauna yan da ɓatar da yaron zai kasance
a ɓangaren ARUSH kuwa duk da kalar tsaron da aka bata amma sam taƙi ta kwantar da hankalinta tai bacci gani take idan har tayi bacci a wannan karon ma zata rasa yaronta tamkar yanda take rasawa, har yanzun tana jin ɗaci da kuma raɗaɗin abinda ke faruwa da ita
*KINGDOM OF HANDAASH (Masarautan Handaash)*
Tun lkcn da KULU dana bar wajen ABIODUN zuciyarna ke mani dukan Uku uku ban nutsu ba har sai da naga n abar sashen na koma ya zuwa namu, ni kaɗai ce a cikin ɗakin namu yayin da kowa ya kama gabansa, a hankali na fara ganin wulgawar haske wanda ya sakani rufe idanuwana ana fatan Allah ya sa Abinda zuciyans ke raya mani gsky ne
Ina buɗe idanuwana hasashena ya faɗa mani gsky domin kuwa Diyana ce a gabana fuskarta ɗauke da murmushi, faɗin kalar yanayin farincikin da na shiga ba zai musultu ba,jikinta na faɗa ina mai fashewa da kukan farinciki tare da faɗin "Diyana a ina kika shiga? kika barni ba kya son ziyartana"
Kaina ta shafa yayin da take kafeni da idanuwanta wanda tsabar kaifinsu sam bana iya saka nawa a cikinsu, "KULU masarautar nan shigowarta da aiki ni kaina ban shigo ba sai da na shirya, akwai haɗarurruka da dama a cikinta,da dalilin shigowana a ciki"
"Diyana ban gane ba ki fahimtar dani yanda zan gane" na faɗa da tsoron dake raina fal
Murmushi ta saki tana furta "a halin yanzu ba zaki gane ba amma nan gaba kaɗan za ki fahimci abinda nake son sanar dake,a halin yanzu na fara sani wacece ke a sanadin masarautar nan da kika shigo na san Ahalinki a halin yanzu"
da mamaki shimfiɗe a fuskana nake dubanta "Diyana kin san wace ni? shin su waye iyayena , kina nufin duk kin san wannan???" na jero mata tambayoyi
gefe ɗaya ta kalla tana furta "eh duk na sani"
"na tabbatar kina da hanyar sadani dasu kuma ke mai taimako ce a koda yaushe ina mai roƙonki ki taimaka ki fitar dani a masarautar nan wllhy ina ji a jikina na zauna a cikinta da akwai abinda zai faru dani"
"KULU hakan ba zai taɓa faruwa ba a halin yanzun sbd babu bawan da ya isa ya shallake qaddararsa dole ne ki fuskanceta ƙadaddararki na ata ko ina ba lallai ko kin koma a mahaifarki su karɓe ki ba, ki fahimta da akwai qaddara mai ƙarfi da zata haɗaki dasu" tana gama faɗin hakan ta ɓacewa ganina yayin da ta barni cikin tunani mai zurfi da kuma zubar hawaye waɗanda na rasa na miye
yayinda maganganuta ke ƙara kai kawo a brain nawa "me ce qaddarar da zata faru dani a masarautar nan har ta haɗani dasu?" Naiwa kaina wanna tambayar wacce bani da mai bani amsa
Kuka sosai naci harna gode Allah a ranar sbd tsabar kukan dana sha kaina sai da yai ciwo abinci kanshi dan Bintu ta takura min da naci na ɗan tsakura
*ABIODUN*
Tun lkcn daya gama sauraren ɗanyen hukuncin da Mahaifin nasa ya furta ya rasa kalmomin da zai yi amfani wajen mgn jikinsa a sanyaye ya miƙe yana mai ganin jirin da har ya kusa yar dashi a ƙasa ba don mai martaba Adewale Femi ya riƙesa ba da tuni yasha ƙasa
da rinannun idanuwansa da suka jiƙu da ruwan hawaye Adewale Femi ke kallon Yaron nasa "ABIODUN did not say anything"
"There is nothing I can say to leave me in this emirate, it is the end of my life." ABIODUN ya faɗa with tears in his eyes
Riƙo hannayensa Mai martaba yai yana kallon idanuwan ABIODUN "kar kace haka mana ba zaka rasa rayuwarka ba akan ka bar masarautar nan ni kaina tamkar numfashina zai fita haka nake ji, sai dai idan za kayi man Arqawali ni kuma zan Barka a masarautar nan"
ɗan jimmm ABIODUN yai yana ɗaga kansa alamar ya amince "ABIODUN na san da cewar a halin yanzu mace bata gabanka balle kuma soyayya, ina son Kai man Arqawali ba zaka so wata ƴa mace a masarautar nan, dukda kai ɗin mai na tabbatar mai aji ne sai dai ance ka guji makiri duk inda yake na tabbatar ko wace ita tana nan tana bibiyarka domin ka faɗa komarta ban son haɗa jini da maƙiyammu"
ɗaga kansa ya sake yi a karo na biyu yayin da ya rungume mahaifin nasa yana mai tabbatar masa ya ɗaukar masa Arqawali
lkcn da ya bar sashen Mahaifinsa ya shiga ya zuwa nasa ɗakin wan yanda ya barsa haka yake alamun ba a sake gyara masa ba, a ƙufule ya fita inda yaci karo da securities nasa maza ɗaya daga ciki ya kira ya gyara masa komai da komai Kuku's suka shirya masa abinci, kaɗan ya ɗan tsakura ya kwanta don ya samu relief
ni kuwa washe gari tun da Asuba na tashi mukai sallar mu a ɓoye tamkar yanda muka saba , sai da gari ya ɗan fara haske before na nufin sashen Uwargidan sarki domin gyarawa Yaronta sashensa da kuma yi masa girki, a lkcn bani kaɗai bace dan haka na shiga sahun kingin Bayin muka gyara ko ina tsab, lkcn ƙarfe takwas na safe na shiga kichen inda muka fara yiwa Uwargidan sarki abinci ta da kingin yaranta, sannan mukai wa Prince ABIODUN nashi daban shima inda muka girka masa Rice stew and vegetables stew + pawpaw
Yayin da duk aikin da muke Kuku Mosis na mini fira wani nayi murmushi wani nayi dariya
Wani kalar Cinyan Dabba naga ya ɗauko mai tsoka da mai wan da sam ban taɓa ganin da akwai mai kal
ar naman ba a Akuya rago da sauran naman mu na musulmai
"what meat" zaro idanu yai yana furta "You mean you don't know Pork meat" ɗan sosa kaina nayi ina yatsina fuska cikin wayancewa nace "Awww I know" ok ya furta yana murmushi
A zuciyana kuwa cike yake da ƙyamar da ƙyar na shiga taya shi wanke naman muka gyarasa sosai farfesunsa mu kayi yayinda sai ƙamshi yake zubawa tsab muka kammala, muka jera a Dinning cikin gajiya da aiki na nufin ɗakin ABIODUN zuciyana fal da tsoro
A buɗe ɗakin na sameshi hakan ya bani damar turawa ina tura kaina a ciki tare da gyaran murya shiru naji hakan ya sa na fara gyara parlourn tsab ko ina sai ƙamshi ke tashi cike da gajiya na shiga fara leƙa bedroom nasa sai dai sam babu kowa a ciki ajiyar zuciya na sauke ina shiga tsab shima n gyara na wanke Toilet
Da ɗan sarsarfa yake hawan step ɗin benen jikinsa sanye Da Kayan game, cikin kuzari ya tura ɗakin nashi yana mai lumshe idanuwansa jin ƙamshi ya dokar masa hanci buɗe idanuwansa yai yaga ko ina tsaf alamun an gyara motsi yaji a bedroom nashi hakan ya saka shi tunkarar ciki,motsin mutum naji a bayana wanda ya sani juyowa a hanzarce gabana na dukan ukku ukku ganin wanda nake tsaye gabanshi...............
*Ma sha Allah my Habibties 💖 😻 Ina matuƙar gdy da addu'o'inku gareni much love Habibties 💖*
*A lover from the beginning You can follow my channel*
*KULU*
*BY RIAMCOOL*
*Mikiya writer's Asso....*
*Bismillahirrahamanirrahim*
*Assalamu alaikum ina gdy ga waƴanda ke mun addu'a , sannan masu biyoni pc suna min complain ɗin bana musu Update da wuri waye da miye, na faɗa muku fa ban da lafiya, ne tun da nake Novel ban taɓa tsaitsayawa ba ba tare da dalili ba, akwai wacce tamin mgnr da banji daɗinta ba, gsky mutane ku san kalar mgnr da za ku faɗa dan Allah, Allah ya kyauta*
P.23&24
Shi kuwa ba tare da ya kalli inda take ba ya raɓa ta gefenta yana wucewa tare da ɗan ƙara haɗa rai yana wucewa ta gefena, nannauyar ajiyar zuciya na saki ina hamdala ganin dukkan aikin daya kamata nai masa,