x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 2 - KULU

  • 3001 words
  • 6000 words
  • Out of 28650 words

Category: Tale Stories

Views 145

29 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
ce a yanzu ya zama dole ki koma bautawa Abin bautar Abiodun ta hakan ne za ki iya nasara akansa"


"Olusegun!!!" ta faɗi sunanshi da ƙarfi yayin da matsanancin ɓacin rai ya bayyana a fuskarta


***************

KULU


tun lokacin data ga macijiyan nan ta kasa sukuni ga shi duk yinin ranar ba taga Diyana ba,ga Mama Khubrah ta kasa ta tsare akan ba zata fita ba hakan ya saka jikinta yin sanyi


Tuwon dake gabanta ta tasa yayin da ta gaza ci "idan ba za kici ba akwai masu ci,ji tsabar iskanci a baki abincin ki ƙici, wallahi dan ma yana na nemowar Malam da ba za kici shegiya ƴar tsintuwa haka za ki ƙare mayyar banza" Mama Khubrah ta faɗa tana kai mata ranƙwashi a kai

hawaye ne suka zubo mata ta saka hannu za ta share taga Diyana a gabanta tana sakar mata murmushi tare da miƙo mata hannu wan da ya sakata miƙa mata itama da murmushi ɗauke a fuskarta miƙewa tayi ta fito ba tare da kowa ya ga fitar ta ba


Kai tsaye cikin jeji suka nufa cikin kogon suka zauna wan da Diyana ta bata Abinci mai rai da lafiya,"Diyana" Kulu ta kira sunanta

kallonta tayi tana faɗin "Kulu mi ya faru ne"


"Diyana dan Allah ni wane ne asalin jinsina naku ko bil'adama ko kuwa Jinsin dabbobi nake??" na faɗa idanuwa cike tab da ƙwalla


"Kulu ke ba jinsimmu bace iya abinda na sani kawai ke ɗin sirki biyu ce"


"asalin wane sirki kenan" na faɗa ina kallonta

Itama kallon nawa tayi tana faɗin "har yanzun wannan ne na gaza ganowa ke wace asalin sirkin jinsi ne dake" Diyana ta faɗa


ajiyar zuciya na saki ina furta "Diyana jiya fa naga wata maciya ta ziyarceni"


da mamaki take kallona tana faɗin "kamar ya KULU?"



dukkan abinda ya faru a daren jiya na faɗa mata wan da naga nan take yanayinta ya sauya...........
[7/19, 5:10 PM] RIAMCOOL: *KULU*


*By: Riamcool*


*Mikiya writter's Association*


*Bismillahirrahamanirahim*


*P.4&5*


"Kulu tabbas ke ɗin rayuwarki lulluɓe take da wani mayafin sirri wan da ba lalle ni na gane alaƙarki da macijiyan nan ba,sai dai tabbas wannan Aljanar macijiya ce kika gani kuma mai ƙarfin iko,ita ɗin ta shafi wani ɓangare na rayuwarki haka zalika ita ɗin sarauniyar Aljana ce" Diyana ta faɗa tana kallona


Kallonta nai ina faɗin "Diyana ni kaina na gaza gane wace rayuwa nake gudanarwa wacce tamkar ba Ƴar Adam ba saboda tsanar da akai man, shin ta ya zan koma rayuwa cikin jinsin jinnu na fita daga jinsin ƴan Adam"



"Kulu hakan ba zai yiyu ba dole ne kiyi rayuwa cikin Bil'adam saboda ke ɗin tushen ki nan yake duk da an haɗa jininki da wani sirki"


Ajiyar zuciya mai ƙarfi na sauke wasu hawaye Masu zafi na zubo man,"KULU ba dai za ki daina kuka haka ba ko? ita fa ko wace rayuwa da kika gani da yadda Ubangiji ya tsara maka ita ya kamata ace idan da sabo kin saba,ki koyi juriya da dauriya Kulu" ta faɗa tana rungumoni jikinta


murmushi na saki ina share hawayen nace "To na daina Diyana"


"Yawwa ko kefa" Diyana ta faɗa


ganin Azahar ta gabato ya sakani miƙewa,Diyana da kanta ta rakani gida kamar yadda ta saba,jikina sam ba ƙwari na shiga ina jin zuciyata ta cunkushe man da wani matsanancin baƙinciki da kuma ƙunci,ina jin wani kaɗaici na mamayeni


Bakina ɗauke da siririyar sallama na shiga wan da ya janyo hankalin Mama Khubrah dake faman sauke tukunyar Abinci, da wani matsiyacin kallo ta bini tana gyara ɗaurin gaban da tayi tace "daga gidan ubanwa kike?"


"Jeji"na furta ina rakuɓewa a bango


"Aw kin san da sarai fa tallah za ki fitar min amma kika kama hanya kika nufi jeji,shin wai ni a jejin nan uwar me kikeyi ne? wanda tun kina ƙanƙanuwa kike zuwansa"



"Yi haƙuri" na furta da tsoro domin nasan idan na bata haƙuri nayi laifi idan kuma ban bayar ba shima laifin nayi,hannu ta saka tana jawoni tare da sakar man ranƙwashin da ya saka kaina sarawa hankaɗa ni tayi tana faɗin "ki tashi ki ida haɗa kayayyakin tallar ki fita da ita" ban musa ba na miƙe na harhaɗa sannan na samu nai Arwallah na gudanar da Sallah, Roban taliyar na aza a kaina sannan Saminu Yaronta ya ɗauki Roban waken da Manja, kai tsaye inda nake ajiye tallan kusa da Baba wanda ke siyar da rake Nan na zauna, ina zama aka fara rurrufe ni masu siyan taliya wan da daman dana fita kamar jira ake haka ake rufeni wajen siyen taliyar, ina yi Baba na tayani siyarwa, harna siyar dukanta tas, nan take kuma naji zazzaɓi ya fara rufeni


kallona Baba yayi yana faɗin "Kulu ya akayi ne naga kaman duk kin sauya"


"ba komai kawai kaina ke man ciwo ne"


"Ayya tashi ki tafi gida, ga wannan ki siyo magani kisha" ya faɗa yana fito da Naira Hamsin sanin ban da kuɗi ya sakani karɓa na bawa yaro ya siyo min nasha anan,ganin ba zan tafi gida ni kaɗai ba ya saka Baban tattara raken yana mayarwa shago, kallonsa nayi ina faɗin "Baba sai ka tafi gida baya ba ka siyar da raken bafa"


Murmushi yai Yana faɗin "Kulu kin saba komawa gida tare dani daga tallah,ba zan barki ki tafi ke kaɗai ba ina da kuɗin cefanen yau,muje" ya faɗa yana kama hannuna


Murmushi na saki ina ƙara jin qaunar Baba wan da yake nuna man soyayya wan da ko ƴaƴan cikinsa bai nuna mawa,haka zalika yake nuna mani zallar tausayinsa a kaina, harga Allah shi ya nake jinsa wani na musamman a rayuwata nake jin nafi son shi fiye dani kaina, "na san ba kici Abinci ba,bari na siya miki ko Awara ne kici sbd nasan kina sonta" tsinkayi muryarshi


"A a Baba ka barta da kuɗin Awaran da za ka siya man a siyi wani abu" na faɗa da tausayinsa


Bai bi ta kaina ba haka ya siya min Awaran mai zafi ya bani, da murna na karɓa ina godiya, ko da muka shiga gidan babu wan da yabi kaina, kuɗin tallan na miƙa wa Mama Khubrah ta karɓa tana irgawa sai da ta irga taga banyi ɓatan ko biyar ba sannan ta barni na wuce ɗaki, ina shiga na taras da ba kowa ajiyar zuciya na saki ina fito da Awaran na buɗe na fara ci ina lumshe idanu saboda daɗin da tayi man, ina cikin ci ne na ji an bankaɗo labulen ɗakin "iyeeee wato ke ba za kici abinda aka girka ba sai dai kici Awara sannu ƴar ƙwai nasan Baba ya siya miki to wllhy ba za kici ba sai kin kawo ta nan tun da ba Ubanki bane tsintacciya" Zainabu ta faɗa tana fizgar ledan Awaran dake gabana



Shiru nayi ban ce mata ƙala ba haka zalika ban ɗago idanuwana na kalleta ba,har ta ƙarashe man zagin cin mutunci sannan ta fita,jingina nayi da bangon ɗakin ina mayar da numfashi hawaye na zarya a kuncina, a daren ranar ma da ƙyar nai bacci zuciyata fal da tunanin abin da zan kuma gani sai dai har nai baccin ban kuma ganin komai ba.




A haka rayuwata taci gaba da tafiya babu wani sauyi ƙalubalen gidammu na ƙara gaba yayin da wajen Baba kaɗai nake samu na raɓa naji sanyi, sannan yake takawa su Mama Khubrah birki ga wani abin da suke Mani






A hankali nake jin hayaniya na tashi a tsakar gidan da kuma Kukan su Mama Khubrah dake tashi cikin gidan, da sauri ta fito "Innalillahi'wa'inna ilaihirraji'un mota ta take Malam ya mutu ya barni ashe Ajali ne ke kiransa harya fita na shiga ukku ni Khubrah" na tsinkayi Muryan Mama Khubrah wacce ban fahimta ba sai da naji ana faɗin "ku shigo da gawar sa" wani Mutum ya faɗa Ban ida gazgatawa ba sai da naga an shigo da gawar Baba wan da jikinsa ke sharkaf da jini, ban san sadda na fasa wata uwar ƙara da kururuwa ba ina faɗuwa nan ƙasa sumammiya



ban ida sani inda kaina yake ba sai da na tashi naga ana min firfita da kuma koke koken dake tashi a gidan , da gudu na miƙe ina nufar inda naga an saka gawar a mankara "Innalillahi'wa'inna ilaihirraji'un Baba bai Mutu ba wllhy ku dawo man dashi, shi kaɗai gareni duk duniya mai sona idan ya tafi wurin waye zan raɓa naji sanyi,fitar da yai a ɗazun ashe fita ce ta har abada babu rabon ya dawo ,yanzu Baba ka tafi tafiya ta har abada wacce babu dawowa, ban san ya zanyi da rayuwata ba ni Kulu ku taimakeni" na faɗa tamkar wata zautacciya yayin da na fashe da wani matsanancin kuka,




Dukammu gaza Magana mu kayi sai kuka tsakanin ni da su Mama Khubrah yayin da su sun sami dangin su masu rarrashinsu ni kuwa babu wan da yabi ta kaina balle har naji sauƙin abinda nake ji a zuciyata,rirriƙe gawar mu kayi yayin da za a ɗaukesa wan da da ƙyar aka ɓanɓaremu nida Zainabu,ina ji ina gani aka fita da gawar Baba Bayan kwanaki sha biyar Mutuwar Baba ba ƙaramin tashin hankali ta jefani ba wan da azabar gidan namu ta ƙara ninkuwa








*Masarautar HANDAASH*


Da rinannun idanuwanta Boluwatife ke kallon Boka Olusegun tana faɗin "Olusegun ba zan taɓa bin Addinin Abiodun ba, dan na yarda da kaine shi ne dalilin da ya saka na baka yarda na a kanka, Ina son ka samo wata mafitar ban da wannan




dariya Olusegun ya fashe da ita yana faɗin "Boluwatife !!!! Mafita ɗaya ce wanda Dodon Bauta ya bani amma zan ƙara roƙon Alfarma a wajensa na tabbatar ba zai kunyatar dani ba, amma kafin nan ina da buƙatar da ki bayar da jinjirin cikin jikinki wan da Abin bauta na tabbatar ba zai ƙasa a guiwa ba wajen cikar muradinki


Duk da tashin hankalin da take ciki bai hanta sake shiga cikin wani ba wan da ya sakata wata zabura tana kallon Boka Olusegun.............



Ayi manage banda charge 🥺nex page zan yi mai yawa in Sha Allah



Love yhu All my Habibties😘
[7/23, 12:27 PM] RIAMCOOL: *KULU*


*BY: RIAMCOOL*


*MIKIYA WRITTER'S ASSOCIATION*



*Bismillahirrahamanirahim*



*P.7&8*



*Jiya nayi mistake ɗin Number page,page 5&6 zan saka na saka 4&5*



Sosai Boluwatife ke kallon Boka Olusegun yayin da mamakinta ya gaza ɓoyuwa da yarensu na Yarbawa take faɗin "Olusegun kana nufin cikin da na daɗe ina so sai da ƙyar abin bauta ya ƙaddara mani samuwarsa,gsky ba zan iya bayar da cikin jikina ba zan san nayi" ta faɗa zuciyarta da alamu karyewa



dariya ya saki yana faɗin "kije kiyi tunani Boluwatife"


Ba tare da ta sake kallon Olusegun ba ta fice a ɗakin, ta ɗan yi tafiya mai nisa before ta isa inda bararonta suke, sai yanzu na ƙare mata kallo dakekiyar macece Choculate color mai manyan idanuwa fuskarta a haɗe,yayin da jikinta ke sanye da dakakken leshi da murjani a wuyanta, tamkar hadarin gabas haka fuskarta ke ɗaure tamau yayin da take tafiyar Barorinta na take mata baya, a haka harta isa inda Motocin Abiodun suke yayinda ake ta miƙo mata gaisuwa da kirari amma sam hankalinta ba anan yake ba ya karkata ne ya zuwa ta ga Abiodun ɗin yadda ya koma, A hankali takai dubanta gun Mahaifiyar Abiodun wacce itama fuskarta ke ɗauke da maɗaukakin farinciki yayin da shi kanshi Sarkin fuskarsa ke fitar da Annuri wan da jikinsa ke sanye da wani dakakken Farin leshi ƴar ciki da babbar riga sai wuyansa dake sanye da murjanan shima yayin da hannayensa ke riƙe da sandar azurfa,



Ajiyar zuciya ta saki tana kai dubanta ga Motocin yayin da ta zuba idanuwa taga fitowar Abiodun,a dai_dai lokacin ne aka buɗe murfin Motar bai fito ba illa ƙafarsa ɗaya daya fara fitowa da ita ya ɗan ɗauki kusan Five minutes before ya ida fito da ɗayar ƙafar ihun da yaji Mutane nayi na farincikin ganinsa shi ya bashi damar ida fitowa Yayin da sai da Boluwatife ta dafe ƙirji ganin cikakken Namiji Abiodun Mahaifansa da ƴan uwansa kuwa bakunansu sun gaza rufuwa sbd farincin ganinsa cikin ƙoshin lafiya,


Yana isowa inda Mahaifin nasa yake ya faɗi ƙasa yana kai masa gaisuwa,ɗagosa Mahaifin nasa yayi yana rungumesa, tare da faɗin
"Kaabo ọmọ-alade mi, Abinabawa tẹsiwaju lati daabobo ori rẹ" nan take busa da kaɗe_kaɗe suka fara tashi,gun Mahaifiyarsa yake yana rungumeta wacce itama ta rungumesa tana faɗin"Kaabo, Alade, O ṣeun, Ọlọrun, ti o dabobo ọ lati awọn ibi ti ijọba yii."(Barka da dawowa Yarima Nagode Abin bauta da har ya cigaba da kare ka daga sharrin Matsafan Masarautar nan) ta faɗa tana jefawa Boluwatife kallo



dukkansu ɗunguma sukai ya zuwa Babban Falon gidan,wanka Abiodun ya shiga yayi, fitowa yai daga Toilet ɗin jikinsa ɗaure da Towel ƙirar nan ta jikinsa tamkar ta doki koda ya fito hadimansa Mata na tsaye na jiran fitowarsa, kansa suka fara taje masa suka ɗaure masa baƙin dogon gashin kansa, sannan suka fara shafa masa haɗaɗdun lotion masu daɗin ƙamshi da tsada, sosai suka shirya sa cikin kayan su na Yoruba masu tsada da jinin sarauta,haka zalika ɓoyayyen kyawun Abiodun ya fito


koda ya fito dukkansu suka ɗunguma ya zuwa Baban wajen da Da aka ɗiba a cikin masarautar yayin da yasha Kaya na Alatu da more rayuwa a ciki,sosai aka haɗa babbar liyafa yayin da wurin ke ɗauke da Abinci kala da kala






*KULU*



Zaune nake a tsakar gidammu yayin da hankalina ya karkata ya zuwa aikin da nake wato tsince shinkafa, sallamar da naji ita ce ta sakani ɗagowa ina kallon Talatuwa wacce ta dubeni tana faɗin " Khubrah na ciki kuwa"


gaisar da ita nayi ina furta "eh tana ciki" wucewa tayi tana shiga cikin ɗakin ni kuwa na mayar da hankalina akan aikin da nake



Tunda Talatuwa ta shiga suka gaisa da Khubrah ta dubeta tana faɗin "Khubrah nazo miki da wata magana ne dama idan har za ki amince"




kallonta Mama Khubrah tayi tana faɗin "faɗi ko wace magana ce in Sha Allah zan amince"


gyara zamanta Talatuwa tayi tana faɗin "nake ga Khubrah tunda ba kece kika haifi Kulu ba sana hasali ma ba ku san asalinta ba mi zai hana ki Kaita masarautar Kudu wacce ake cinikayyar Bayi wanda nima zan kai BINTU a can, wallahi KHUBRAH maƙuddan kuɗaɗe ake samu ni kaina an bani maƙuddan kuɗaɗen BINTU kin gansu anan" ta faɗa tana zaro maƙuddan kuɗaɗen dake cikin kwagirinta



zaro ido Khubrah tayi tana kallon kuɗin tare da faɗin "Haba Talatuwa ai babu abinda zai hanani kai KULU kuwa can ban san da wane baki zan gode miki ba,na kawo man wannan maganar daman gashi kuwa ina cikin halin na rashi,yanzu wa zan bawa KULU ya bani kuɗaɗen"



na tsinkayi maganarta wan da dai_dai nazo shiga a ɗakin, baya naja ina furta Innalillahi'wa'inna ilaihirraji'un, mi Mama Khubrah ke nufi, shin siyar dani za tayi dan Baba bashi da rai ko dan na kasance ƴar tsintuwa marar galibi??? Nai wa kaina waɗannan tambayoyin hawaye na zuba a idanuwana da son ƙara jin zancen nasu na kai kunnena aɗakin ina sauraronsu yayin da Talatuwa ke faɗin "kin ga ki bar komai a hannuna goben nan zan yiwa Shu'aibu magana komai za ayi yi, jibi ki shiryata a Kaita inda za ki karɓo kuɗin"



Sosai Mamah Khubrah ke godiya,jin motsin tahowarsu ya sakani barin bakin ƙofar ɗakin



Bayan ban ɗaki na gewaya ina wanke fuskana don kar a gano wani abun



duk yanda naso ɓoye damuwana ya gagara dole sai da fuskana ya nuna har sai da Mamah Khubrah ta gane man, tsoron ta kar ace na san abinda suka ƙulla ita da Khubrah ya saka ta tambayeni amma sai na ce mata kaina ne ke ciwo,



Kwance nake na ƙurawa kwanon ɗakin idanu inata juye juye yayin da damuwa ce fal cike a raina



Wacece KULU


kulu dai tun tana Ƴar jinjira Malam Hadi ya tsinceta a gona wan da ya ɗauke ta ya kawo ta fadar mai gari tare da neman Alfarma ya riƙe ta duk da ya san mawuyacin abu ne Matarsa Khubrah ta riƙe ta saboda rashin Mutuncinta


Da ƙyar da rarrashi ta amsheta wan da ba wata kulawa da take bata, sai dai rainon Ubangiji da taimakon Aljana Diyana da take tare da ita wacce ita ke ciyar da ita tun tana jinjira, tun tana ƙarama ta buɗi ido ta ganta da Diyana,


Lokacin data fara girma Malam ya sakata makaranta Boko da islamiyya wanda take da ƙoƙari sosai sai da abinda ke damunta bai wuci gorin da take fuskanta gun yaran Khubrah da ita kanta Mama Khubrah na cewar ita ƴar tsintuwa ce, ga ƙarin damuwar ta bai wuci yadda Mutane ke nuna mata kyara da hantara ba,ko cikin yara bata da ikon yin wasa saboda hantara,tun tana kuka harta daina shiga cikin yaran hakan ya sakata tasowa cikin kaɗaici sai dai Diyana ce mai ɗebe mata kewa wacce takewa kallon Mahaifiya



Tun tana shekara goma asalin kyawunta ya fara fitowa wacce ta kasance ita ba fara ba sannan ba baƙa ba wato irin fatar nan ce mai tsada Choculate color sai manyan idanuwanta masu jefa me kallonsu a wani yanayi,bakinta ɗan madai_daici, sai dogon gashin kanta da kuma wanda ya kwanta mata luf luf a gaban goshi, sannan ya fitar mata da kwantaccen sajenta, tun tana karamar ta kasance sam bata da hayaniya, ka ƙoƙari don tana aji biyar ta iya karatun Hausa da turanci wan da yake da nasaba da koyawar da Diyana ke mata sannan hada ƙarin wasu yaririka tana jinsu har larabci tana ji,hakan ya saka Baba ke matuƙar ji da ita sosai yake nuna mata so fiye da yaransa wannan ya sa su Zainabu da Mahaifiyarsu ke nuna mata ƙiyayya


A.lokacin da take shekara sha biyar lokacin ne kuma ta fara gane ganen abubuwa masu ban mamaki wan da take shiga cikin damuwa, sannan a duk lokacin da wani ya ɓata mata rai sai yaji a jikinsa ko kuma yayi ta rayuwarsa lura da hakan dasu Mama Khubrah su kayi suke mata kirari da Mayya har cikin gari shi yasa ko kaɗan bata da wani namiji mai cewa yana sonta duk da kyawunta kuwa,hakan be dameta ba duk da babu ranar da zata zo ta koma ga Ubangiji ba tare da ta zubar da hawaye
End Ads