x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 8 - KULU

  • 21001 words
  • 24000 words
  • Out of 28650 words

Category: Tale Stories

Views 149

29 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
ita ba, ba tare da manufa aka turo ta masarautarsu ba, duk da ta kasance jinin masarautar JOHAAN ce wato ƙaddara ita ce sanadin turota, taya zai fuskanci wannan al'amari???" Yaiwa kansa wannan tarin tambayoyin wan da ba shi da mai bashi amsa



A hankali ya buɗe idanuwan nasa yana zuba su a fuskarta cikin gazgatar da zancenta ya furta "na yarda dake da abin da kika faɗa man, ina son daga yanzu ki cire ran cewar ba za ki mallakeni ba, ki sa a ranki na zama naki,duk da ni kaina nasan ko zan haɗiyi zuciya na mutu ba lallai iyayena da masu mara musu baya su amince ba"


"Ni kaina na san da hakan sannan ko da ace sun Amince bai zama lallai ni na mallakeka ba, Addinina bai yarje min ba" na furta


Murmushin takaici ya saki yana furta "har iyanzu na rasa gane wane Addinin ne kike magana da har bai yarje miki da aurena ba, Josmie na gaza gane kanki ko dai ba sona kike ba iƙirari ne kawai a baki, ko dai kin shigo masarautar nan dan ki uzzurawa rayuwata da soyayyarki, Why kike son cutar da rayuwata ta hanyar sanyaya man jiki da kalamanki, kin san kalmar da nafi tsana naji ta fito a bakinki na cewar ba za mu mallaki juna ba tsakanina dake" ya faɗa da idanuwansa waɗan da suka fara canza launi

hannayensa na saki ina mai miƙewa ba tare da nai masa magana ba har sai da na ɗaga ƙafafuwana da zummar tafiya "kayi haƙuri da abinda nake faɗa maka na san da cewar kai ma ka san da gsky nake faɗa sai dai hangen ka na son cimma ƙudirinka ya hanaka gane abinda kake son cimmawa," Ina gama faɗin hakan na wuce zuciyata na mai sake buga mun na tabbatar da nayi gangancin faɗawa soyayyar ABIODUN wan da ban lura da illar hakan ba sai a yanzun




Manyan idanuwansa ya rufe yana mai gazgata zancenta but why he will do it is not their fault, it is his heart's fault da har ya gaza yarda da gaskiyar da yake gani, "Soluwole ka taimakeni" ya furta a hankali



*Adewale Femi*


Duk yan da yaso hankalinsa ya kwanta akan ABIODUN sam ya gaza hakan har a ƙarƙashin zuciyarsa ya gaza yarda da in har ABIODUN bai bar Masarautar sa ba ba zai tsallake tarkon JOHAAN ba,


Zazzzafan iskan dake bakinsa ya furzar yana mai lumshe idanuwansa zuciyarsa na sake buga masa a duk tsawon daƙiƙa ya tabbatar da ba zata daina buga masa ba har sai Jinin JOHAAN ya bar masarautar nan, da kanshi yake son gano wace ce ita da har ta sake a masarautar sa ba tare da wani yaga alama ba zai yi shiri sosai,dan tabbatuwar ganota


Wani wahalallen numfashi ya sauke yana kallon Wazirin nasa wanda ya kasance jininsa ɗan uwansa Chubandoo " na san da ba ka san dalilin da yasa nake nemanka akan maganar da za muyi da kai mai muhimmanci ba , na san da cewar ka san da tun a wancan ƙarnin da ya shuɗe dubar masarautar nan ta tabbatar da cewar Jinin JOHAAN zai shigo a masarautar nan ya gusar da farinbcikin cikinta da nasarori sannan duba ya tabbatar da ba ko wane bane zai shigo face mace, wacce ita ce za ta auri Yariman Masarautar nan, a kwanakin baya da suka wuce tabbas jinin JOHAAN ya shigo a cikin masarautarmu wan da tun ranar data tsallako ƙafarta a masarautar nan zuciyana ya fara bugu sannan duban Boka OChucco ya tabbatar da lallai ta shigo wan da bana fatan wannan mummunar baƙar ƙaddarar ta faru" ya ƙarshe zancen da sauke nannauyar numfashi

Sosai Waziri ke bin Mai martaba da kallo bakinsa ya gaza furta komai idan ban numfarfashin da yake saukewa tamkar wan da yai gudun tseral zuciyarsa na wani irin masa zillo da bugawa sai da yakai kusan Ten Minutes a haka sannan ya furta "Your Highness, surely there are many problems that will happen in this emirate where there is blood in the emirate of Johaan,dan tabbatas da manufa su kayi haka sannan da shiri da ƙulli nake ga me zai hana mu tasarwa Yarima tsaye sannan mu turawa KINGDOM OF JOHAAN da saƙon cewar mun ɗaro tarkonsu tabbas ƴarsu da suka turo za mu kashe, idan har ba su fito sun bayyanawa duniya manufarsu ba"

Ajiyar zuciya ya sauke yana ɗaya kansa alamun ya gamsu da shawarar da Chubandoo ya bayar "amma sai dai kuma sbd ƙara kiyayewa ina son *MATEO* ya dawo daga ƙasar US sbd sakawa ABIODUN Ido dan a halin yanzun sam shi ma na gaza yarda dashi" mai martaba ya faɗa jinjina kai waziri yai alamar ya amince duk da ya tabbatar da yaron nasa MATEO ba lallai yaso zuwa masarautar ba sai dai komai da dalili



*Masarautar JOHAAN*


Bayan haihuwar ARUSH sosai aka sha hidima ta ban mamaki da kuma bajinta, haka zalika hatta da Manyan Ƴaƴan Sarki wato Ƴaƴan Gimbiya Josmie dake ƙasashen waje suna aure sai da suka hallara taya murnar samuwar Yarima a masarautar su wan da sun riga da sun fitar da rai da kuma tsammani,

A ɓangaren ARUSH ma sosai take kula da Yaronta wan da abubuwan dake faruwa da ita ya sakata ƙara dagewa da kulawa dashi,babban abin da ke tayar mata da hankali shi ne bai wuci cewar shima an ce mata tabbas tamkar yanda ake ɗaukar mata kingin ƴaƴa to a wannan karim ma shima ba lallai yasha ba



Tamkar yanda ta saba ko wane dare idan za su kwanta yaron na a jikinta yau ma haka ta kasance wan da a hankali ta fara jin wani nannuyan bacci na son fixgarta ƙoƙarin hana kanta tayi amma hakan bai yiyu ba, jikinta dake maƙalƙale da jaririn aka kama da ƙarfi yayin da ake son rabata da yaron sai dai amma sam ta ƙi bada damar hakan bcox riƙo ba na wasa tai wa yaron ba, cikin huci da zafin rai Matar dake tsaye a gabanta ta daka mata wani ƙaƙarfan ƙarfe a hannu wan da yai sanadiyyar sakin yaron tana ƙwalla ƙara mai firgici "me yasa kuke son cutar da rayuwata ku ƙyaleni da azabtarwar da kuke man na roƙeƙu a wannan karin kar ku rabani da gudan jinina tamkar yanda kuke rabani da kingin ƴaƴana Azabtarwar taku ta isa haka har yanzun ban mance da sauran Yarana ba na san ko wacece ke za ki san ciwo da zafin da Mahaifiya za taji yayin data rasa Yaronta ,zan iya baku komai dana mallaka muddin za ku ƙyale mun Yaro, ku sani shi fa bai san komai ba idan laifi nai muku nice da hukuntawa ba shi ba, ko wace ke kin san da cewar ke ce mai nasara da galaba a kaina tun lokacin da ƙaddara ta shigo dani Masarautar nan nake haɗuwa da manyan abubuwan da har yanzu tabonsu bai bar zuciyana kunyi nasara ku ƙyaleni haka nan" ta faɗa tana mai sake fashewa da wani kuka mai ciwo wan da ke fitowa har a ƙarƙashin zuciyarta


shedaniyar dariyar da taji an fashe da ita before a tsagaita ana furta "ARUSH har yanzun ba muyi nasara a kanki ba kin tsere min kin min fintinkau taya kike tunanin zan iya barin rayuwarki ki huta ke ce silar shigowa rayuwata ke ce rusa dukkan wani farincikina taya kike tunanin zan ƙyaleki kaɗan kika gani" Ana gama faɗin hakan aka fashe da dariya yayin da matar ta zuro hannu da zummar ɗaukar sa sai dai caraf Arush ɗin ta riƙe "a gabana da ba za ki ɗaukar mun Yaro ba sai dai idan rayuwana kika fitar ki san........" Bata idasa ba sakamako wani abu da matar ta watsa mata a fuska wan da ya sakata sakin wani wawan ihu mai cike da hargitsi da azaba wan da har lokacin yaron na a hannunta riƙe ƙam haka za lika idanuwanta na a rufe

Jin shiru na wasu ƴan daƙiƙu ya sakata ware idanuwanta jikinta sharkaf da zufa yaron na maƙale a jikinta wata wawauyar ajiyar zuciyar ta saki tana mai bin ɗakin da kallo ganin Josmie da kuma Mai Martaba wan da yake kallonta da damuwa fal a ranshi a hankali yazo wajen ta yana rungumeta luf tai a jikinsa tana sauke numfashi da ajiyar zuciya tare da fashewa da kuka mai tsanani

Bubbuga bayanta ya fara yi yana furta "ARUSH what's going on you're yelling ?" ɗago da fuskarta tayi tana girgiza kai tare da faɗin "whatever happened to me da ake son ɗaukar mun Yaro baya ga waɗan da aka ɗauka ba zan iya ci gaba da zama Masarautar na ba muddin kuwa aka ci gaba da yunƙurin ɗaukar mun Yaro"


hannayenta Josmie ta kama tana furta "ARUSH me kike faɗi ne haka? kin san harda sawa ranki da kikayi har ya saka kike mafarki yanzu haka fa ihunki da kururuwarki ya saka Hadimai sanar damu, ki cire komai a ranki babu abinda zai faru dake da Yaronki,ki mance abubuwan da suka faru dake a baya..........



*Hmmmm na gaji da rashin comments naku ɗaiɗaiku ne masu so nima zan daina takura kaina akan dole sai nayi,masu yi man ina godiya sosai*

*Musamman ƴan Amanar,Rahina Aminu, Ummi Suraj, Aunty Hauwa Safinabala,Mariyanbaba ngd ssoaii Allah ya bar zumunci*


*RIAMCOOL ce*


Writer of

RUSHEWAR RAYUWA

*BAYAN WUYA*

*ANYA UBA NE*

And now

*KULU*
[10/23, 9:05 PM] CUTIE~RIAM: *KULU*


*BY RIAMCOOL*


*MIKIYA WRITER'S ASSO.....*


P.29&30



Wani zazzafan iska ARUSH ta furzar yayin da har lokacin hawaye ba su daina tsiyaya a idanuwanta ba, A hankali mai martaba ya saka hannayensa yana ɗauke mata su wan da har lkcn bai yi mgn ba tsabar damuwa da lamarin matar tashi,an ɗau kusan 10 minutes ba tare da wani yayi mgn ba sai bubbuga bayanta da yake wan da ya saka ta yin shirun tana mayar da ajiyar zuciya "ARUSH why are you still refusing to calm down"King Velentino ya faɗa yana mai janyeta a jikinsa tare da ɗago da fuskarta

girgiza masa kai tayi tana furta "sam bana tunanin da akwai ranar da zan iya kwantar da hankalina muddin abubuwan da suka faru basu gushe a zuciyata ba sannan ba a daina bibiyar rayuwata ba, bcox of what da ake zaluntana tsawon shekaru kana kallo da idanuwanka ko su waye ina tare da su sannan sun fito fili a zahirance sun bayyana ko tantama ba nayi a cikin su sune masu ɗaukar........" bata idasa ba sakamakon wata gigitacciyar tsawar da ya buga mata yana jifanta da manyan idanuwansa waɗan da suka janza launi tsabar ɓacin rai na lokaci guda

"ARUSH babban kuskuren da za kiyi shi ne saka ƴan uwana da dangina a cikin lamarin ki haka zalika babban da nasanin da za kiyi shi ne kuskuren ƙara ambatar cewar Sune silar sace miki yara, ki sani sam ba za ki taɓa haɗani da ƴan uwana ba haka zalika ƙullinki bai isa ya sakani rabuwa da su ba ko kuma aminta da zantattukanki ,ki gyara kalamanki" ya faɗa cikin tsantsar ɓacin rai tare da hankaɗa Arush ɗin gefe guda tana faɗuwa da ita da yaron hannunta a hanzarce Josmie tazo tana ɗagata wanda idan ban da kuka babu abinda take haka zalika zuciyarta na azalzala da zafi da kuma raɗaɗi


"Sai yaushe ne za ka dawo hanya ka fara gane abinda nake furta maka,gsky ne na tabbatar ɓatar maka da hankali akai....." bata idasa ba sakamakon rufe mata baki da Gimbiya Josmie tayi tana girgiza mata kai Alamar tai shiru, shirun tayi tana ci gaba da kuka wanda har muryanta ya dishe,wan da bata damu da hakan ba dan idan da sabo yaci ace ta saba tun ɗaura ƙafarta a gidan ya zame mata kurkuku, shine mafarin buɗe mata ƙofofin ƙaddararta, wan da ba tasan ranar rufesu ba


Share mata hawayen Josmie tayi tana karɓar yaron hannunta tare da furta "ARUSH ki yi shiru ki mance komai a halin yanzu ki kwanta ki bacci ni zan riƙe maki yaron na tabbatar ba wani baccin kirki kike samu ba,"


ba ta iya furta komai ba illa ɗaga mata kai da tayi tana kwanciya kanta na wani irin sara mata ita kuma Josmie ta fita tare da rufe mata ƙofar ɗakin



misalin ƙarfe 3 na dare yayin da ba ka jin sautin komai idan ban da bugun zuciyoyin mutane da kuma fitar numfarfashinsu, Babban Hall ne dake shaƙe da mutane, wan da ko wane ya rufe fuskanshi da baƙin kyalle haka zalika jikunnansu sanye da baƙaƙen kaya


ɗaya daga cikinsu ne yai gyaran murya da alamar shine shugaban wannan kungiyar nasu da wata kalar shaƙaƙƙiyar murya wacce duk nacinka baka isa ka gane ko waye ba "na tabbatar kowa da kowa ya san dalilin da yasa muka taraku anan, shin ko kunsan muddin ba mu fara aiwatar da aiki ba rayukammu na cikin babban haɗari, yanzun babban abin da nake so a fara aiwatarwa shine kawar da Arush wan da shine zai ida bamu damar tunkarar Mai martaba, ba na son ko kaɗan wannan masarautar ta wanzu a ci gaba tamkar yanda aka bamu umarnin wargaza ta da ɓatar da tarihinta dole ne mu fara shirin yaƙi, ba nason wani ya saka yaƙini da duba cewar Masarautarsa ko wane ya manta da babinta da babin cewar ya taɓa rayuwa a cikinta sannan Mahaifarsa ce abin tunƙaho,mu mance da wannan dukkammu mu fara shiri"

shiru su kai na lokaci kaɗan before su sauke numfashi ɗaya daga cikinsu na furta "dukkammu mun Amince sannan mun saka yaƙinin cewar za muyi wannan aikin tamkar yanda ƙungiya ta bukata,a halin yanzu wane mataki za mu fara bi?"


wata dariya shugaban ya saki daga bisani ya tsagaita yana furta "matakin da za mu bi Akan ARUSH ne da Yaronta sune za mu fara kawar da su" na'am su kai da maganar ta shi yayin da lokaci guda ta shiga matsanancin ɓacin rai da damuwar ganin akwai masu son rusa mata daɗaɗɗen mafarkinta, da burinta ta cikin ƙyallen data rufe fuska take ƙare musu kallo yayin da take ƙara jijjiga kanta,zuciyarta na buga mata


Bayan ta fito daga Hall ɗin taron a hankali take bin wajen da kallo,kai tsaye wani babban farfajiya ta samu ta tsaya wan da ke cike da itatuwa, sosai kanta ya kulle ta rasa me za tayi,


Idanuwanta ta rufe tana furta wasu maganganu, ta ɗauki tsawon lokacin ta nayi before ta tsagaita, tana buɗe idanuwanta, dai dai ƙafarta ta ɗaga tana duba wajen yayin da ta saka hannaye tana ƙaƙular wajen harta tone wajen , Babbar laya ce duƙunƙune a cikin hannu ta saka tana ɗauka tare da warware ta ta fito da takardar dake ciki, a hankali ta fara magana da kirari "Babban Sheɗani DUNA magaucin jinin mai taken DUNA sha jini kaci hanta babban shaiɗani mai ƙahonni Babban makirin Aljani mai saka munaƙisa kaine Daba idan baku harka ta ɓaci kaine Ubana maganin kukana mai ilimin sanar dani tuggu a yanzu nazo ka warware mun abinda ke tunkaroni ka sani tsayin shekaru ina da burin hawa karagar Mulki muradina na Mulki masarautar JOHAAN na kafa tarihin da ba a taba kafawa a Africa ba"


tana gama faɗin hakan tai shiru yayin da ita kaɗai ke jin maganar da ake mata, a hankali ta sauke ajiyar zuciya tana furta "na san da wannan sai na kawar da yaron Arush ɗin da ita wannan ba zai min wahala ba"

Dariya taji an fashe da ita wacce har cikin dodon kunnenta, ake yi "Makirar mace ke har kina tunanin idan kika kawar da yaron Arush da ita kin gama da babunsu ina, da akwai wata jinin tata wan da wannan kuskurenki ne wan da kika aikata tsayin shekaru" aka ƙarashe maganar da wata shaiɗaniyar murya mai amo da zallar nuna taƙadaranci


Wata masifaffiyar zufa ce ta yanko mata ta lokaci kaɗan haka jikinta ya ɗauki kyarma da zafi kanta ya fara zafi da sara mata "Duna me kake nufi? Ka yi man bayani yan da zan gane"


"Abin da kikaji na furta na cewar Jinjirar da kika ɓatar tsawon shekaru Ashirin a yanzu hakan tana a raye, wan da in dai kina son cimma burinki da ƙudirinki to tabbas ya zama dole ki ganota ki fara kawar da ita sannan ki koma ya zuwa mahaifainta da ƙanenta, kiyi harmar ganota" ana gama faɗin hakan ta daina jin komai yayin da numfashinta ke fita da sauri_sauri zufa ta sake wanke mata jiki tana jin wani mugun zafi na ratsata duk iskan da Ubangiji ya wadata a wannan daren ita sam ta gaza jinshi tsabar bala'in da take ji


sulalewa tai a bishiya tana zama tana ƙara harhade numfashinta, tun da take bata taɓa jin bala'i kalar wannan ba kenan shirin da tayi na tsayin shekaru bai faru ba,gujewa masifar tsayin shekaru da tayi bai yi,ba wannan wace kalar yarinya ce wacce ta tsallake tarkon ta???, ta kai ta ne inda babu wani mahaluƙin da ya isa yaje wajen ba tare da ya mutu ba ta kaita ne inda ƙara ace mutuwa taxo maka lokaci guda bisa ga inda ta ajiyeta,wane ya ceceta harya reneta yaushe hakan ya faru bata sani ba??? tai wa kanta waɗannan tarin tambayoyin





*King Velentino*

tun lokacin da ya baro Arush ya ke zaune sosai abubuwa suka jagule masa, yan zun ne ya tabbatar da mulki bala'i ne masifu da dama sun afkar masa tarkuna da dama ake ɗala masa daga masarautu da dama sosai zuciyarsa ta jagule masa zuciyarsa na ci gaba da bugawa yayin da yazo buɗe saƙon da Masarautar Handaash ta aiko masa rufe idanuwansa yai ya fara karanto Addu'ar su ta Christian sannan ya buɗe ya fara karantawa



"Saƙo daga Masarautar Handaash tabbas ka cika kai cikakken mai wayo ne ka ɗana mana tarkon da ba lalle ya kamamu ba, ka sani har a gobe mune da riba, domin sirrukan da ka daɗe kana ɓoyewa mu na lokaci kaɗan mun ganosa ko kasan da Yariman Masarautar Handaash ya shigo masarautarku yayi rayuwa ya naɗar mana sirrukanku wan da ba tare da anga wata sheda ba ya fito ya dawo ya zuwa Masarautarsa, na tabbatar da cewar da munaƙisa ka turo
End Ads