Ta fice da sauri ta nufi kicin ɗin, duk tsoronta kada Hajiya ta ji abinda ta yi mata.
Tana fita Hajiya da Afreen suka bi bayanta.
"Ba ta kicin ɗin."
Lubna ta faɗa lokacin da ta sami su Hajiya tsaye a tsakiyar falo.
"Ba ta kicin? To, kodai sake fita ta yi ne irin na ɗazu? Kai Afreen tambayo Ɗayyabu, ke kuma duba ɗakin baƙin can."
Hajiya ta basu umurni
Da sauri dukansu suka fita.
Tana buɗe ƙofar ɗakin kuwa ta ganta kwance,
"Har kin tsoratamu, mun duba ɗaki bakyanan ashe nan kika dawo."
Ba tare da ta ɗago ba, ta ce
"Eh!"
"Ki zo Mommy tana nemanki to."
Bata amsa ba, kuma bata tashi ba.
"Na ce, Mommy tana ƙiranki."
Kaɗa kai ta yi, ganin har yanzu tana kwance yasa ta keɓe baki ta juya zuwa falon.
Zaune ta samesu yanzu a kan kujera, Afreen ya sanar mata saƙon Ɗayyabu cewar Abulle bata fita ba.
"Tana kwance a can, ta ce tana zuwa."
Sai da ta ɗau lokaci kafin ta fito, ta tsugunna can gefe.
"Shigo mana ki zauna, kin koma can gefe kin raɓe kamar wata baƙuwa."
Ƙara matsowa kaɗan ta yi,
"Ke dai akwai baƙunta Zainab! Ace mutum da gidansu ba zai saki jiki ba, sai ki ta ɗari-ɗari. Ko ba ki jin daɗin zama da mu ne?"
Girgizar kai ta yi,
"To mene ne?"
"Ba komai."
Ta faɗa a hankali
"To, ki saki jikinki kin ji?"
"To."
Murmushi ta yi,
"Yaya kan naki? Lubna ta ce kanki na ciwo, ta baki magani. Fatan kin ji sauƙi."
Kai ta ɗaga ta kalli Lubna, a zuciyarta kuwa cewa ta yi, 'Makira.' A fili kuma ta ce "Na ji sauƙi."
"To, Allah ya ƙara sauƙi."
Ƙiran sallar da aka fara ne yasa suka watse.
Ko da aka fito cin abincin dare ma, kaɗan Abulle ta ci, don gaba ɗaya tunaninta da hankalinta ya koma gida. Duk zaman gidan ya isheta.
***
Ba laifi, yau kasuwa ta buɗe ma su Hamusu sosai, har takai ga sun haɗa kuɗin ɗaki, sun kuma biya an basu. Yanzu zasu yi barci cikin salama.
***
Ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin a kayi daga waje, daga bisani ya ce,
"In shigo?"
Kanta na kan waya tana kishingiɗe a kan gado ta ce,
"A a, ka yi ta tsayuwa."
Buɗe ƙofar ya yi ya shigo, ya janyo kujerar da ke gaban madubi ya aje kisa da gadon sannan ya ce,
"Ina abokiyar zaman taki?"
Keɓe baki ta yi, ta ce
"Ohho mata ba! Can ɗakin naga ta koma."
Girgiza kai ya yi, kafin ya fara magana.
"Anti Lubna dama magana nake so mu yi."
Sai sannan ta ɗago kai ta kalleshi
"Ina jinka."
"Daddy da Mommy suna son Zainab ta zauna a gidan nan, sai dai kuma abinda kike yi mata naga bata jin daɗinshi. A tunanina zaki jata a jiki ki yi farin ciki da murnar samun 'yar uwa, sai kuma naga akasin hakan. Don Allah Anti Lubna ki sassauta mata ko zata ji daɗin zama da m..."
"Dakata! Mara kunya. Tazarar shekaru nawa ne tsakani na da kai?"
Ta katseshi ba tare da ya kai ga ƙarshen maganarshi ba.
Mamaki ne ya kamashi jin ta ambato shekaru, bai ga zancen da ya yi da har zai kai ga hakan ba.
"Biyar!"
Ya bata amsa
"Ok! Ashe kana sane, kana da shekara ishirin ina da ishirin da biyar. Kenan kaga ba kai zaka gwadamin yadda zan yi rayuwa ta ba, idan ba zaka iya ganina a haka ba ka kau da ido."
Baki kawai ya saki cike da mamaki, daga bisani ya miƙe ya bar mata ɗakin don baida ta cewa.
A yi haƙuri da kura-kuran da ke ciki, ban bibiyaba gaskiya.
*Ummyn Yusrah*
*ABULLE TA MAI UNGUWA*
*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*
_Ummyn Yusrah_
_29_
Yana fita ta miƙe ta ja tsaki, ta sa ma ƙofar makulli ta rufe.
Dawowa ta yi ta fara rage kayan da ke jikinta don shirin kwanciya. Abun hannunta ne ɗaya ya gangara zuwa ƙasan gado garin cirewa.
Tsaki ta ja, da nuna alamar gajiya sannan ta sunkuya da niyyar cirowa. Ba ta ganshi ba, ya yi nisa, sai wani farin takarda ta ci karo da shi.
Hannu ta miƙa ta ciro.
***
Yana fita kai tsaye ya nufi ɗakin da Abulle take, da sallama ya shiga yana faɗin
"Ba dai har amaryar mai unguwa ta yi barci ba?"
Tashi ta yi daga kwanciyar da ta yi tana faɗin,
"Tuni na kwanta, barci ya ƙi zuwa."
Dariya ya yi
"To, yaya za a yi ya zo, bayan lokacin yinshi bai yi ba."
"Ai so nake in tashi da wuri."
"Ai ko ba ki kwanta da wuri ba, gidan nan ba a makara. Dolen mutum ya tashi ya yi sallar asuba da zarar lokaci ya yi, idan ya idar sai ya koma."
'Ya koma barcin asara ba.'
Ta faɗa a zuciyarta
"Mu je falo akwai film ɗin da za a sa."
Kallonshi ta yi, ta ce
"Fin? Meye kuma wannan?"
Dariya ya yi,
"Ba fa fin na ce ba. Film!"
Dariyar da yake ne ya fara ƙular da ita,
"Uhmmm! Koma dai mene ne, ni barci zan yi, so nake gobe in tashi da wuri in shirya."
Ta jingina da gadon fuskarta na bayyanar da murmushi ta ce,
"Gobe kamar wannan lokacin ina gida."
Kallonta ya yi,
"Nan ma ai gida ne, mu da muke so ki zauna ko 'yar diplomar nan ki yi ki karanto mana engineering."
Zaro ido ta yi,
"In zauna a ina? Yasin a a! Kuma waye shi gudulomar da injimiyarum ɗin?"
Dariya ne ya kamashi har da riƙe ciki
"Ba fa guduloma ba! Diploma na ce da engineering, ina nufin ki zauna ki yi karatu anan har a kai ki jami a."
A tsarace ta ce,
"A ina ɗin? Yasin ba ni zama. Har wani jami a ma zani? Taɓ! Ashema so ake mutanen Mai ludaya su ƙirani da 'yar iska. Hu'umm! Ba da ni ba aradu."
Yau wannan yarinyar zata kasheshi da dariya, da zantukanta masu cike da shirme.
"Yau kam nan kuka tare da hirar ne?"
Hajiya ta katseshi lokacin da ta shigo ɗakin
"Yau mun ba falo hutu Mommy! Hirar nan ɗin ma ya fi na falon daɗi."
Ya ba Hajiya amsa
"Ai kam naga alama! Tun ɗazu nake jiyo dauriyarka. Zainab yaya kayin naki?"
"Na ji sauƙi Memi."
"Ankuma!"
Afreen ya faɗa
"Don Allah Mommy ki ji, Diploma fa na ce mata da engineering, ita kuma wai guduloma da injimiyarum. Ance Mommy ta ce Memi."
Kaɗan ya rage itama ta yi dariya, sai dai ta gimtse.
"To, ai bata iya ba ne. A hankali zata koya."
Har ta juya zata fita sai kuma ta juyo tana tambayar,
"Ina Lubnar kuma?"
Take fuskar Abulle ya canza
"Ta kwanta."
Afreen ya bata amsa lokacin da ya lura da sauyin da ya gani a fuskar Abulle.
Matse baki ta yi, ta juya ta yi gaba. Tasan halin 'yar tata na rashin son hayaniya, hala sun dameta ta korosu nan.
Shi kanshi ya sani mai zama inuwa ɗaya da Lubna sai ya shirya, ko kaɗan bata iya zama da mutane ba.
"Zainab! Nasan bakya jin daɗin zama da Aunty Lubna. Haka halayyata yake, duk mai zama da ita sai ya yi haƙuri..."
"Idan zaman ya zama dole ma mutum ba."
Ta katseshi
"Haka ne kam! Ɗazu nima na shiga mu yi magana kan yanda take yi miki, ko saurarata bata yi ba. Sai ma wani maganar shekaru da ta fara jeromin."
Ya faɗa yana jan ƙaramin tsaki. Da alama maganar ta konashi
"A rayuwa ai ba a duba yawan shekaru, abinda aka aikata a tsahon shekarun ake dubawa."
"Haka ne kam, na yi iya ƙoƙarina don ganin na saitata amma abun ya gagara."
Ya faɗa cikin damuwa
"Abune mawuyaci ka iya canza mutum lokaci ɗaya akan wata ɗabi a tashi."
"Haka ne kam! Na tabbata inda hakan na da tasiri da Aunty Lubna ta daɗe da canzawa. Sai dai hakan ya riga ya zama ɗabi arta. Ki tayata da addu'a sannan ki yi mata uzuri Allah ya bata ikon canzawa."
"Uhmmm! Amin."
***
Saida ta juyo taga hoto ne ashe. Ƙurama hoton idanu ta yi, kabanta na dukan uku-uku ganin kyakkyawan matashin saurayin da ke jikin hoton tare da Abulle.
_Goron Jumma a_
_Ummyn Yusrah_
*ABULLE TA MAI UNGUWA*
*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*
_Ummyn Yusrah_
_30_
Ga saurayi har saurayi, sai dai da gani ƙauyanci ya gama yi mishi ƙawanya. Da zai samu ya goge, ba ƙaramin nagartaccen namiji za a yi a wajen ba.
Wurgi ta yi da hoton kan durowar da ke gefen gadonta, da niyyar idan gari ya waye zata ba mai shi. Sai dai maimakon ya zauna kan durowar sai ya faɗa bayanshi.
Bata bi ta kanshi ba, gado ta haye ta ja bargo ta rufu. Ba jimawa barci ya yi awon gaba da ita.
***
Duk wani rarrashi da magiyar da Afreen ya ma Abulle kan ta koma ɗakin Lubna ƙi sauraronshi, sai ma tsalle da ta daka ta ce ita da ɗakin Lubna sai a ƙiyama, ta barmata shi bari na har abada kuwa. Tana iya jure komai amma banda walaƙanci
Ƙarshe dai haƙura ya yi ya barta, nan itama ta bi lafiyar gado cike da ɗokin gobe tana garinsu.
Daren yau ya mata nisa, ta yi barci har ta gaji gari ya ƙi wayewa. Tun tana juyi har dai ta tashi ta zauna.
Agogon bangon da ke manne a jikin bangon ɗakin ta ƙura ma ido, gashi dai sai aiki yake yi, amma ita sam bata fahimtar me yake aikatawar, don ba iyawa ta yi ba.
Ita dai kawai bin ɗan dogon tsinken da ke ta zagaye a ciki take da kallo. Daga bisani ta keɓe baki ta ce,
"Agogo kenan! Sarkin aiki."
Da ta gaji da zaman sai ta sake jawo jakar kayanta ta sake zazzagesu tana kuma yi musu sabon naɗi tare da shiryasu cikin jaka.
Sai da ta gama tas! Ta sake ciro hotunan nan tana sake ƙare musu kallo. Wasu ta yi dariya, wasu kuma haka kawai sai su bata tausayi. Mussaman ma wanda suka yi a wani sallah ita da Inno, Ilu da ƙaninta Muntari. Duk sunci kwalliyar sallah. Ilu da Inno zaune a kan kujera, Abulle da Muntari kuma zaune a ƙasa a gabansu.
Kuka ne ya ƙwace mata wanda bata san dalilin yinshi ba.
Sosai take kewar iyaye 'yan uwa da illahirin mutanen Mai Ludaya. Haka nan kawai take jin wani irin janji a jikinta dama yanayinta. Ita kanta tana mamakin yanda aka yi Lubna ke cin bulus da yawa a kanta.
Duk da kasancewarta mai tsoro, bata lamunci rashin mutunci da raini ba. Da zarar ka ce mata kule zata ce cas!
Share hawayenta ta yi, ta ci gaba da kallon hatunan.
Sosai ta kura ma hoton idanu. Tsaye suke a bakin gona ita da Hamusu, yana sanye da rigarshi 'yar shara mai ruwan bula da na yadi da farin wando, ita kuma tana sanye da atamfarta riga da zani da ɗankwali mai kalar ruwan ƙasa da baƙi yayin da ta tamke kunkuminta da gyalenta.
Dukkanninsu rake suke sha. An ɗauki hoton ne daidai lokacin da suka kai raken bakunansu da niyyar gutsura.
Ta daɗe tana ƙare ma hoton kallo, ƙirjinta na dukan sha uku-uku.
Yau ce rana ta farko da ta fara nadama da da-na-sanin biye ma banzar zuciyarta wajen rabuwa da rabun ranta Hamusu! wanda a baya ko a mafarki basu taɓa tunanin hakan ba.
Yau ce rana ta farko da tayi Allah wadai da ƙin tsayawa ta saurari uzurinshi, sabida baƙin kishi irin nata.
Yau ne kuma ta tuna irin gangancin da ta yi na amincewa da auren Mai Unguwa sabida tsantsar ƙwaɗayi irin nata.
Inama tana da halin hana faruwar auren nan nata da Mai Unguwa? Bakin alƙalami ya riga ya bushe. Ta yi ganganci tun a karon farko, a yanzu bata isa ta je da zance fasuwar auren ba, don tasan hakan babban abun kunya ne, abune kuma da zai iya taɓa kima da darajar gidansu. Abune da zai kafa tarihi tun daga iyaye har jikokin-jikoki a gari. Domin abun kunya ne a saka auren mutum a ce an fasa. Gaba ɗaya gari da maƙota sai zance ya zaga kuma gidan sai ya shiga cikin tarihin garin.
Tunowa ta yi da ranar da zata tafi Mairangwangan ya biyota yana yi mata magiyar ta tsaya ta saurareshi, amma ta ƙi, sai ma maganganu da ta gaggayamishi wacce ya gaza haƙuri shima ya mayar mata. Duk da kasancewarshi mai haƙuri sai da ta kai shi maƙura.
Ta sake ɗauko wani hoto da suka yi a yammacin biyun sallah.
Tarin samari ne da 'yammatan garin, sun taru sun yi layi, mata sun tsaya a ɓangaren gabas, maza kuma yamma, dukkanninsu suna kallon juna.
Tafi aka fara tare da waƙa.
'Yammata a dandali da samari a dandali.
Kowa nata shaggali, yau ranar tamu ce
Abulle zo ki rausaya, Hamusu ne gwaninki ke.
Kowa ya san dashi, kema kin tsayar dashi.
An ɗaukeshi ne daidai lokacin da ta fito tsakiyar fili tana rawa, kai a ƙasa Hamusu ya fito yana tayata takawa.
Kuka ne mai ƙarfi ya ƙwace mata, da sauri ta toshe bakinta da hannayenta duka biyun, ta miƙe samɓal a ƙasa tana kuka mara sauti.
_Ummyn Yusrah_
*ABULLE TA MAI UNGUWA*
*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*
_Ummyn Yusrah_
_To, me ma zance muku ne? Kawai dai na gode. Duk da nasan kalmar godiya ta yi ƙaranci a gareku masoya wannan labari._
_31_
Ƙauyen Mai Ludaya
A wannan daren da Abulle ke kewar mutanen garin Mai Ludaya, a garesu su shaida kawo kayan auren Abulle da Mai Unguwa suka yi.
Yau gidan nasu tun safe ba saka tsinke, hidima kawai ake yi, kai ka ce yau take ranar ɗaurin aure. Da dare bayan sallar isha i ne, jama ar garin mai Ludaya suka shaida kawowar fantimoti mai taya babba guda ɗaya, irin na 'yan burni, na auren Abulle da Mai Unguwa.
Atamfarta guda biyar, shadda ɗaya, mayafai biyu, takalmin ado biyu, silifas ɗin roba ɗaya, sai jakarta guda ɗaya irin ta wanzamai. Sai kayan kwalliya da sauran tarkace.
Duk inda ka gilma ji kake 'Abulle ta yi goshi.' wasu kuma cewa suke, 'Dama ƙaɗayi yasa suka ba Mai Unguwarta.' Zantuka dai iri-iri.
****
Rayuwa ta fara canza ma Hamusu. Daga kwana a rumfar shagunan mutane zuwa kwana a ɗakin haya.
Kwance suke a kan tabarmar Ɗalliti, shikam ya jima da barci, Hamusu ko sai juyi kawai yake yi, tunani fal! Zuciyatasa. Gajiya ya yi da kwanciyar ya miƙe ya nufi ledar kayanshi ya ciro wani riga ya warwareta. Hotunansu ne ya bayyana, ya ɗauka ya shiga kallo da ɗai-ɗai tamkar yau ya fara ganinsu, duk da mafi yawan hotunan shi da Abullenshi ne.
Ji yake kamar ya yi fiffike ya isa garin Mai Ludaya, ya je ya gano Abulle ko zai sami sassaucin ƙuna da raɗaɗin da zuciyarshi ke yi mishi.
****
A hankali sautin kukanta ke fita, zuciyarta ƙuna take, ga kuma shauƙin son Hamusu da ya addabeta a yau. Lallai tayi ganganci da ta biye ma son zuciyarta, akan kwaɗayin Shinkafa ta guje ma masoyinta. Me ya sa tun a lokacin bata gane irin gangancin da tayi ba? Me ya sa bata tsaya sunyi fito-na-fito da Indo ba, ta ƙwace masoyinta.
Sake rushewa da kuka ta yi, a hankali ta fara waƙa,
'Rabuwa da masoyi ba daɗi, wannan cuta ce a zuciya.'
'Zan yi bankwana da kai, ka zamemin rabin jikina.'
'Zuciyata taka ce, kasance mai tallafawa.'
Rayuwata na yi zurfi, kaunarka ce ke sani nishaɗi.'
'Mun yi bankwana da kai, yau gashi raina yana ta ƙuna.'
Ta ƙarashe waƙar tana mai tsananta kukanta, ga zuciyarta da ya yi mata nauyi da zafi.
Inda da yanda zata yi a wannan daren, da ba abinda zai hanata tafiya garinsu ta gano abun ƙaunarta ko zata sami sassauci daga ƙuna da raɗaɗin da take ji.
Ta yi gangancin da batasan hanyar da zata gyarota ba, ba wanda zata iya fuskarshi da zancen canza akalar aurenta daga kan Mai Unguwa zuwa kan Hamusu. Lallai ta makaro, makara mara amfani ma kuwa.
Batasan tsawon lokacin da ta ɗauka a cikin wannan yanayin ba, sai da sanyin asuba ya fara ratsata ne, barci ya yi awon gaba da ita.
A firgice ta tashi, cikin tsoro da fargaba ta shiga ƙare ma ɗakin kallo.
Take mafarkinta ya dawo mata, nan ta shiga tunanin me ke faruwa a gidansu? Me ya sa mutane suka taru da yawa haka? Kodai mutuwa aka yi ne? Da sauri wata zuciyar ta tunatar da ita taron aurenta ake.
Ita har ta manta da wani aure ma. Tunanin Hamusu shi ne a ranta.
Cikin sanyin jiki ta tashi ta nufi banɗaki.
Hasken ranar da ya shigo ta tagar banɗakin ne ya tabbatar mata da rana ta yi batama sani ba, tana ta sheƙa barci.
'Wannan gida ko ina a rufe, ina ma mutum zai gane rana ta yi idan ba fita ya yi ba.'
Alwala ta yi ta fito ta duddungura, tana gamawa ta tattara duk wani shirgi nata a ɗakin ta fito falo.
Tsaki ta ja, haushi duk ya rufeta ganin ba kowa a falon.
Zama ta yi, ta ajiye jakarta a gefe don tasan zaman jira zata sha tunda masu gidan basu tashi a barci ba.
Ita a nata ra ayin ma, zuwa yanzu ta yi nisa a hanya.
_Ku yi haƙuri da wannan_
_Ummyn Yusrah_
*ABULLE TA MAI UNGUWA*
*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*
_Ummyn Yusrah_
_To, me ma zance muku ne? Kawai dai na gode. Duk da nasan kalmar godiya ta yi ƙaranci a gareku masoya wannan labari._
_31_
Ƙauyen Mai Ludaya
A wannan daren da Abulle ke kewar mutanen garin Mai Ludaya, a garesu su shaida kawo kayan auren Abulle da Mai Unguwa suka yi.
Yau gidan nasu tun safe ba saka tsinke, hidima kawai ake yi, kai ka ce yau take ranar ɗaurin aure. Da dare bayan sallar isha i ne, jama ar garin mai Ludaya suka shaida kawowar fantimoti mai taya babba guda ɗaya, irin na 'yan burni, na auren Abulle da Mai Unguwa.
Atamfarta guda biyar, shadda ɗaya, mayafai biyu, takalmin ado biyu, silifas ɗin roba ɗaya, sai jakarta guda ɗaya irin ta wanzamai. Sai kayan kwalliya da sauran tarkace.
Duk inda ka gilma ji kake 'Abulle ta yi goshi.' wasu kuma cewa suke, 'Dama ƙaɗayi yasa suka ba Mai Unguwarta.' Zantuka dai iri-iri.
****
Rayuwa ta fara canza ma Hamusu. Daga kwana a rumfar shagunan mutane zuwa kwana a ɗakin haya.
Kwance suke a kan tabarmar Ɗalliti, shikam ya jima da barci, Hamusu ko sai juyi kawai yake yi, tunani fal! Zuciyatasa. Gajiya ya yi da kwanciyar ya miƙe ya nufi ledar kayanshi ya ciro wani riga ya warwareta. Hotunansu ne ya bayyana, ya ɗauka ya shiga kallo da ɗai-ɗai tamkar yau ya fara ganinsu, duk da mafi yawan hotunan shi da Abullenshi ne.
Ji yake kamar ya yi fiffike ya isa garin Mai Ludaya, ya je ya gano Abulle ko zai sami sassaucin ƙuna da raɗaɗin da zuciyarshi ke yi mishi.
****
A hankali sautin kukanta ke fita, zuciyarta ƙuna take, ga kuma shauƙin son Hamusu da ya addabeta a yau. Lallai tayi ganganci da ta biye ma son zuciyarta, akan kwaɗayin Shinkafa ta guje ma masoyinta.