ko ga wanene ba, amma koma dai menene, abun na da nasaba da shi. Domin sauda yawa idan wani abu zai faru da shi, walau na farin ciki ne ko akasin hakan yana ji a jikinshi.
Wannan alamar yana jinta ba abu mai daɗi ne ke faruwa ba.
"Inna! Ina hanya gobe, na sani yanzu kina cikin mummunar yanayi. Ina zuwa gareki Innata ka da ki tafi ki barni."
Nan ya yi ta sambatu har yana sharar hawaye.
****
Gaba ɗaya mutanen sun tsorata da yadda suka ga hatsarin. Dukkanninsu babu alamar rai a tare da su.
Cikin sauri aka cicciɓo Idirisu aka sanya a amalanke, aka yi gaba da shi, aka kamo Abulle, wacce saida aka janyota da ƙarfi kafin aka rabata da kakkaifar dutsen da ya shige kanta.
Anan ne fa Malam Ilu ya yi ido biyu da ɗiyarsa Abulle.
Jikinsa ne ya shiga kaɗawa kamar mazari, bakinsa na faɗin,
"Innalillahi! Abuwa ce ta wajena. Ita ce!!wallahi ita ce!"
Abinda yake faɗa kenan.
Sai yanzu suka kula, domin da fari hankalinsu a tashe yake, basu kula da ko suwaye ba.
"Ku taimakamin don Allah! Ku taimakamin a kaita asibiti, wayyo Allah!"
Cikin sauri aka sanyata cikin amalanken da Ilu ke riƙe da shi, duk ya ruɗe ya fita hayyacinsa sai sambatu yake, jikinsa sai rawa yake.
Ganin ya kasa tura amalanken ne aka karɓa, da gudu aka nufi hukumar kiwon lafiya a matakin farko na garin.
Sauran jama'ar suka biyosu a baya da kayansu da kuma mashin ɗin.
Babu likita, sai wata ma'aikaciyar jinya guda ɗaya da aka samu.
Ta dai dubasu, ta tabbatar musu da cikawar Abulle, shi kuma Idirisu buguwa ya yi, shi ya haddasa masa dogon suma, zai farfaɗo, ta sanya masa karin ruwa ta yi masa allurai.
Kasantuwar rashin aikin da ma'aikatan ke yi ya sa ba a wani tsaya dogon bincike da wasu ababen da ya dace ma'aikatan asibiti su yi ba.
Akan yi kwana biyu ko fiye da hakan ma ba tare da an buɗe asibitin ba, yanzun ma sa a suka yi, ma'aikaciyar ta zo karɓar haihuwar 'yar uwarta.
Ba Malam Ilu kawai ba, duk wani mutum da ke wajen sai da ya girgiza da jin mutuwar Abulle, shi kam ya gama yin mutuwar zaune.
Tashi guda ya nemi juriya da jarumtarsa ya rasa. Hawaye ke gangarowa kan ƙuncinsa.
Haƙuri da ban baki aka shiga ba shi, nan suka tura gawar Abulle zuwa gida, shi kuma Idirisu aka tura gidansu don sanar ma iyayensa.
***
Shiru falon ya yi, tibin ma dake aiki rage muryarsa aka yi. Afreen da Lubna dake zaune duk kewar Abulle ta damesu, zaman kwana uku kawai suka yi da ita, yau da ta tafi sai suke ji kamar sun ɗabi shekaru mai tsawo da ita.
Lallai sabo turken wawa ne.
Lubna ce ta kalli Afreen cikin sigar tsokana ta ce,
"Afiriji! Ɗan ɗauko min ruwa a na'urar sanyaya ruwa."
Kallonta ya yi, ya langaɓar da kai,
"Anti Labano ruwa ya ƙare."
Take duk suka sa dariya.
_Ummyn Yusrah_
*ABULLE TA MAI UNGUWA*
*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*
_Ummyn Yusrah_
*ABULLE TA MAI UNGUWA*
*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*
_Ummyn Yusrah_
_43_
Tafiya kawai suke, ko kaɗan Malam Ilu bai san inda yake jefa ƙafarsa ba. Badon riƙe hannunsa da ake yi ba ma da kamar wuya ya iya tafiyar.
Har yanzu bai gaskata mutuwar Zainabunsa ba, ya fi dangantata da dogon suma kamar dai yadda aka ce Idirisu ya yi, ko shakka babu wannan matar bata san aikinta ba.
Tayaya za a ce, daga taɓa tsintsiyar hannu da dokin wuya sai a ce mutum ya mutu? Wannan ma ai ƙaryane da rashin sanin makamar aiki. Ga yarinya sai murmushi take dokawa amma a ce ta mutu! Hakan ba zai yiwu ba, suna kai ta gida zai je ya ƙira Hajiya ya sanar mata da abinda ke faruwa ko za a turo musu mota ya jirasu a Guwal su kaita asibitin Jinjin a dubata da kyau.
***
Cikin tashin hankali ya isa ƙofar gidan Mai Unguwa, lokacin har an yi sallar isha. Yaro ya aika a yi masa ƙiran Mai Unguwa.
Koda ya fito ya sanarmasa cewar ance bai dawo daga masallaci ba, don haka kai tsaye masallacin ya nufa.
Sauri yake rafkawa haɗe da maganganu shi ɗaya tamkar sabon kamun hauka.
"Sarkin fada! Lafiya kake kuwa? Kana tafe kana ta sambatu ko kallon gabanka baka yi."
Mai Unguwa ya faɗa lokacin da ya taho yana haska hanya da tafkekiyar tocilarsa ta ƙarfe tamkar irin na masu gadin nan, sun zo zasu yi karo da juna.
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un! Sannunmu fa!! Sannunmu da haƙuri. Ita kuma sa i ya yi. U'uhumm! Abun gwanin tausai."
Ya faɗa yana goge fuska.
Kallon rashin fahimtar zancen da yake Mai Unguwa ya bisa da shi.
"Ban fahimci zancen nan naka ba Sarkin fada, me kake faɗa ne?"
"U'uhumm! Mun yi rashi babba wallahi. Da an sani aka barta a gida bata je ko ina ba, da duk hakan bata faru ba."
Yanzu kam ransa ya kai maƙura wajen ɓaci, tafiya ya fara yi yana faɗin,
"Shashancin banza da hofi kawai! Yaya zaka tareni a kan hanya ka fara yi mini zance mara kan gado? Badon na yi maka farar sani ba, da sai ince ka fara shaye-shaye irin na 'ya'yan zamanin nan ne."
"Sai haƙuri Ranka shi daɗe! Abin ne da nauyin faɗa."
Ya ɗago kansa da tun ɗazu ke sunkuye zai sake magana, ya ga ba Mai unguwa, bai ma san tafiyarsa ba don lokacin da suka tsaya ya kashe tocilar.
Waigawa ya yi, ya hangosa yana tafiya yana mita. Da sauri ya bi bayansa yana faɗin, a yi haƙuri ranka shi daɗe! Tuba nake, na yi kuskure."
Bai kulasa ba, har suka iso gida, ganin zai shiga ne ya sa shi saurin cewa,
"Ranka shi daɗe! Sai haƙuri, daga wajen haɗarin ɗazun nan nake, al amarin ba kyan gani."
Dakatawa yi yi, ya juyo yana faɗin,
"Shi ne tuntuni ka tsaya kake wani ƙumbiya-ƙumbiya?"
"Ya zama dole ai, sosai na firgita da lamarin. Shi mai tuƙin nasa da sauƙi, doguwar suma ya yi, sai kuma buguwa da raunuka a wasu sassa na jikinsa. Ita kuma yarinyar ta bugu sosai a tsakiyar kayi, har kana hango ƙoƙon kanta, jini kuwa a wajen tamkar kwata (wajen yanka dabbobi), tun daga Tudun mun tsira har muka shigo gari zuwa cikin asibitin nan jini ne ke malala, ga kuma wasu raunuka a jikinta. Mun kai su duka an dubasu, shi yana raye ita kuma an naɗe kan da bandeji sun tafi gida shi ne na nufo nan, don in sanar maka Allah ya yi mata cikawa."
Ya ƙarashe maganar yana share idanun da ba alamar hawaye.
"Ashsha! Ashsha!! Abu bai yi daɗi ba. Wannan hanya tamu, Allah ya kawo mana wanda zai gyaramana shi. Kansila Akilu ya ce zai yi maganar gyaran nan ka ji shi shiru ga masu aikin sa kai ɗin ma kwana biyu sun dakata. Sun sake tone waje sun tafi."
"Ai jiya da yau abin ba kyau, Allah dai ya taƙaita."
"Amun dai, sukuma Allah ya jiƙayinsu."
Har ya juya zai shiga gida, Sarkin fada ya ce,
"Umm! Ranka shi daɗe yarinyar nan ce fa ta rasu."
"Wacce yarinya kenan?"
Ya faɗa yana sake gyara tsayuwarsa.
"Amm! Um!! Ta..."
Katsesa ya yi,
"Wannan inda-indar na mene ne Sarkin fada? Kai tsaye ka faɗama duk kasa gabana sai faɗi yake yi."
Sai da ya ɗan yi jim! Sannan ya ce,
"War wajen Ilu Mai Amalanke ce."
A razane ya ce,
"Wacce kenan?"
" 'Yar tasa ai ɗaya ce, Abulle ce, wacce ake shirin aurama ita nan da kwana huɗu, ta je bankwana ma Baffanta a hanyar..."
"Riƙeni Sarkin fada! Riƙeni, bana gani, zan faɗi."
Shi ne kalmar da ta katse Sarkin fada daga dogon sharhin da yake yi.
_Ummyn Yusrah_
*ABULLE TA MAI UNGUWA*
*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*
_Ummyn Yusrah_
_44_
Gida ya cika maƙil, ba ka jin komai sai hayaniya da ƙarar taunar shinkafa.
Yau wuni aka yi, ana ɗaurawa da saukewa, buhun shikafa mai cin kwano ɗari ya kusa karewa, bai fi saura mudu goma ba.
Wasu ma tun yau suka naɗo tsummokinsu; suka taso ƙeyar 'ya'yansu daga nan har a gama biki.
Suna tsaka da hayaniya ne suka ji ana,
"Hanya, hanya." Ana turo amalanke.
Wasu kuma sai rafka salati suke.
Hankalin wasu matan ya koma kan masu shigowar, wasu kuma kallo ɗaya suka yi, suka kau da kai don ka da hankalinsu ya raja'a wajen su juyo suga daron shinkafa wayam.
Umma Sakina, ƙanwar Inno da ke ta kurɓar miyar ja a bakin murhu ce ta taho hannunta riƙe da ludayi tana tambayar me ke faruwa.
"Ina za a saka ta ne Malam Ilu?"
Mai turo Amalanke ya tambaya,
"Ba ajiyeta za a yi ba, ruwa za a sake watsa mata za ta farfaɗo."
Ilu da ke kiɗime ya faɗa.
"Wai menene a nan ɗin ne kam? Ana tambaya kun yi hiru?"
Umma Sakina ta sake tambaya, bayan ta kurɓe jar miyar dake cikin ludayin ta lashe bakinta.
Kallonta Malam Ilu ya yi ya ce,
"Ina Inno?"
"Tana ɗaka tana sallar ihya i."
"Dama yar..."
"A'a, Malam Ilu!"
Malam Mudi ya dakatar da shi, gefe ya ja shi,
"Malam Ilu kasan taron mata ne, ba a gaggawar faɗa, yanzu sai su cika gida da kururuwa."
"Malam Mudi ba ta mutu ba fa, doguwar suma kawai ta yi, zan ƙira Yaya yanzu ya turo moto mu kaita can asibitin Jinjin a dubata da kyau."
Malam Kallah ya ce,
"Haba Malam Ilu! Rai fa guɗa ɗaya ce a jikin ɗan Adam, ko duk asibitin duniyar nan za ka kai ta ba za ta dawo ba, domin ba wanda ya isa ya ɗagata, tunda ran da ke jikinta ya riga ya fita. Don Allah ka sa ma ranka haƙuri da juriya, idan ka riga ka karaya ita mahaifiyar yarinyar kuma ta yi ya ya? Kasan fa su mata rauni ga..."
"Wayyo Allah mun shiga uku! Yau me zan gani?"
Umma Sakina da ta buɗe gawar Abulle da aka rufe da zani ne, ta haska da fitilar da ta ɗauka a ƙasa ne ta kurma wannan ihun,wanda ya yi sanadin katse maganar da Malam Kallah ke yi ma Ilu.
Cikin sauri suka iso wajen,
"Habba baiwar Allah! Wannan ihu kuma na menene?"
Ba ta basu amsa ba, sai ɗiba ta yi da gudu zuwa ɗakin Inno hannu a ka, tana rusa ihu tana shi ke nan mun mutu mun lalace.
Tana isa ta daka tsalle, ta yi zaman 'yan bori, hannunta da ke kai ta sauƙe ta waresu, ta karkaɗa ta buga a ƙafarta gami da tattaro zaninta zuwa guiwarta, ta sake ɗaga su ta watsa kan cinyarta tana faɗin,
"Shi ke nan Yaya! Ta tafi ta barmu, mun yi rashi, wayyo Allah."
Ta juya ta fyace hanci ta ci gaba da shissheƙar kuka, a daidai lokacin ne matar liman ta sallame sallar da take ta juyo ga Sakina da ke ta zuba maganganu.
"Haba baiwar Allah! Da hankalinki kike ta janyo muku alkaba'i? Ko menene ya faru ai salati ya kamata ki yi kururuwa da ihu ba."
Hanci ta ja, ta share idanunta sannan ta ce,
"Malama ko ke aka yi miki irin wannan mutuwar bazatan sai kin yi kuka, don haka babu ruwanki."
Tana gama faɗi ta ci gaba da kukanta, Inno da tun ɗazu take ta rafka sallah ba iyaka ta yi saurin sallamewa, don tunda ta ga shiru Abulle ba ta dawo ba zuciyarta ke ta wasu muggan saƙe-saƙe.
Ko da ta ji ihun Sakina ba ƙaramin tsorata ta yi ba, sai dai ta san shirme irin nata da maida ƙaramin abu ya zama babba ya sa ba ta kula ta ba, sai da ta ji martanin da ta mayarma matar Liman ne ya sa ta yi saurin sallamewa.
"Kina hauka ne? Malamar kike maida ma irin wannan martanin don ba ki da mutunci."
Inno ta faɗa lokacin da take kallon ƙanwar tata,
"Au! Bayanta ma za ki bi kenan? Sai ki fita kiga me nake yi ma kukan ai."
Ta faɗa tana ƙara sautin kukanta.
Inno ta buɗe baki za ta yi magana, Lami matar Liman ta hanata.
A waje kuwa cire gawar suka yi, aka saka a ɗakin da aka gyara ma mutanen Jinjin, aka janyo ƙofar aka rufe, suka fita da Ilu ana ta tausarsa da basa haƙuri.
Cikin gida kuwa ya kaure da koke-koke da sallallami, don wasu sunga abin da ya faru ta dalilin buɗewar da Sakina ta yi.
Jin hargowar ta yawaita ne, yasa Inno da mutanen da ke ɗakin suka fito don ganin abinda ke faruwa.
_Ummyn Yusrah_
_45_
"Wai me ke faruwa ne?"
Inno ta tambaya cikin fargaba.
Kallo suka bi ta da shi, domin tsoron sanar da ita suke yi, sai nuni da ɗakin kawai suka yi mata.
Jikin ƙofar ta nufa, malama na biye da ita har ta buɗe suka shiga, ƙaramar tocilan da ke hannun malama ta haska musu, ganin abu suka yi rufe a kan tabarma. Sarawar kai da faɗuwar gaba ne ya dirar ma Inno a lokaci guda, sakamakon ganin zanin Abulle da ta yi an rufe abu kamar mutum da shi.
Ba ta iya ƙarasawa wajen ba sanadiyyar ƙafarta da ta kasa ɗaguwa, ga kuma jikinta da ya hau kaɗawa, tamkar wacce ta yi wanka da sassanyar ruwa da sassafe a lokacin damina.
Cikin sanyin jiki malama ta ƙarasa wajen, ta tsugunna. A hankali ta kai hannunta ta yane zanin, ta haska saitin fuskar Abulle.
"Innalillahi wa innalillahir raji'un!" Ita ce kalmar da ta faɗa, cikin sauri ta saki zanin.
Ta taso, juyowa ta yi zuwa ga Inno wacce tunda ta yi ido biyu da Abullenta rufe haka ta san ba ta raye, yatsar hannunta na dama kawai ta ke ta nunawa wajen gawar, bakinta na motsi sai dai ta kasa furta kalma ko guda, har malama ta iso gareta ba ta sani ba, domin jinta, ganinta da komai na ta ya ɗauke, sai nuni kawai da gauraya harshe cikin baki.
"Inno! Lafiya kuwa? Mu je ko?" Ta faɗa a lokacin da ta dafata.
Nannauyar ajiyar zuciya ta saki, sannan ta buɗe baki za ta kwaɗa ihu.
Da sauri malama sanya hannu ta toshe mata baki, tana faɗin,
"Me kike shirin aikatawa? Ihu ma mamaci? Wannan ba ɗabi'a ce ta musulmai ba, addu'a ce kawai soyayya da gatan da za ki yi mata a yanzu ba ihu ko kuka ba. Ki sani wanda ya fimu sonta ya riga ya karɓi abinsa, don haka ki sa ma ranki salama ki yi ta rakata da addu'o'i ki kuma yafe ta, sai ki ga Allah ya kawo miki sauƙin lamarin."
Haka nan ta yi ta tausarta, da ba ta haƙuri. Da taimakon addu'ar da take yi ne ta fara jin sassauci a zuciyarta, ta kuma yi alƙawarin ba za ta bari koda ɗigo ɗaya na hawayenta ya sauƙa ba, da sunan yi ma Abulle kuka.
Haka shi ma Malam Ilu, ya samu salama dalilin tausa da kuma addu'ar da yake yi, ganin haka ya sa duk suka yi haramar gabatar da salloli biyu da ya hau kansu.
Bayan idarwa ne, Ilu ya nufi cikin kasuwa da salularsa don sanar da su Hajiya.
***
Hajiya da ke zaune a falon Alhaji, ta na yi masa bayanin yadda tafiyar ta su za ta kasance gobe ne wayarta ta fara tsuwwa.
Ɗagawa ta yi, cike da mamakin ganin lambar Ilu a daren nan, har wayar ta katse ba ta ɗaga ba. Ƙiran ya sake shigowa, kallon wayar ta tsaya yi, zuciyarta cike da saƙe-saƙen ko lafiya? Kodai Abulle ba ta isa gida ba ne ha...
"Ba ƙiranki a ke yi ba?"
Alhaji ya katse mata tunanin da ta ke yi.
Fuskar wayar ta ɗago ta nuna masa, ganin sunan Ilu yas a ya ɗaga kafaɗa ya mai da kallonsa ga tibi.
Haka nan ta tsinci kanta cikin faɗuwar gaba, ɗagawa ta yi, haɗi da sallama.
Bayan wasu 'yan daƙiƙu, ta miƙe tamkar wacce aka tsikara ma allura.
Cikin rawar murya da tsiyayar hawaye a idanunta ta shiga faɗin,
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un!"
Kalmar da ta ke ta furtawa kenan har ya katse waya.
Ganin yadda hankalinta ya tashi, ga kuma zubar hawayen da take yi ne ya sa Alhaji tambayrta ko lafiya?
Jiki a sanyaye ta zauna kan kujerar tana sharar ƙwalla, ta ce,
"Shi ken an Alhaji! Zainab ta tafi ta barm..."
"Don ta tafi shi ne kike wannan kukan? Ina dai ya ce miki ta isa? Ai shi ke nan."
Ya maida kansa ga kallon da ya ke, kallon mamaki ta yi masa, bai bari ya ji ƙarshen zancenta ba, ya yi gaggawar katseta, ya iya maida ƙaramin abu ya zama babba.
"A hanyarsu ta komawa, suka yi hatsari, mai mashin ɗin yana asibiti, ita kuma Allah ya karɓi abinsa, ya raba gardama a tsakaninmu, da mu da su duk mun huta, kai ma ka huta, ba ka yi niyyar zuwa aurenta ba, ga shi za ka je jana'izarta."
Tunda ta fara maganar ya ke kallon bakinta, kansa ya yi masa nauyi, bai gama fuskantar me take cewa ba.
"Me kike faɗa ne? Ban fahimci ko ɗaya daga cikin abinda kike cewa ba."
Ɗago idanunta da ke ta zubar da hawaye ta yi ta kallesa,
"Baka fahimta ba?"
Kai ya ɗaga mata.
"Zainab ɗin da kake ta fushi akan tafiyarta, har ka ƙi saurarar uzurin mahaifinta Allah ya karɓi abinsa, sun yi hatsari a hanya ta rasu."
Tun kafin ta kai ga ƙarshen maganar, ya sanya hannunsa biyu ya riƙe kansa yana salallami.
_Ummyn Yusrah_
*ABULLE TA MAI UNGUWA*
*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*
_Ummyn Yusrah_
_46_
Girgiza kai kawai yake, yana faɗin,
"Me na aikata ne? Me ya sa ban tsaya na saurari uzurinka ba ƙanina? Har na yi gaggawar yanke hukunci. Komai ya faru ni ne sila kanina, da wani ido zan kalleka a matsayin wanda ya yi sanadin mutuwar 'yarka?"
Ɗago kai ya yi, ya kalli Hajiya da rinannun idanunsa,
"Hajiya! Wallahi ni ne silar mutuwarta, a yau na tsani halina na rashin uzuri da saurin zartar da hukunci, ba tare da jin sahihin zance ba. Da ban yi haka ba, da yanzu tana raye."
Ganin yana neman sakin layi ne, ya sa ta dawo kusa da shi ta zauna. Ta ce,
"Ka yi haƙuri Alhaji, ka saita natsuwarka. Kwananta ne ya ƙare, ko da ba ta tafi ba, dole Allah zai karɓi abinsa tunda kwananta ya riga ya ƙare, ka sa ma ranka cewa, Allah ne ya kaddara ta nan ne ajalinta."
Sosai take ta nusar da shi, sai dai ko kaɗan bai yarda da hakan ba, ya san shi ne sanadin mutuwarta, da bai biye ma zuciyarsa ba, da hakan bai faru ba.
Da taimakon addu'a, ya samu sassauci a zuciyarsa.
Kallon Hajiya ya yi, ya ce,
"Ki duba lambar Tukur direba, ki sanar masa ya zo da asuba mu wuce, ki sanar ma yaran nan su shirya da wuri ka da su ɓata mana lokaci."
"To" kawai ta ce. Ta nufi falon, sai da ta yi ƙoƙarin saita kanta kafin ta shiga, hira suke suna ta ƙyaƙyatawa, jin hirar