Malam, idan rabon shi ce fa?"
"Bama rabon shi ba ne."
"U um fa Malam! Kasan fa rabo ajali ne, ba mu san me Allah ke nufi kan hakan ba. Idan dai ita Abullen tana so ai shikennan."
Jinjina kai ya yi, kafin ya ce, "Kuma fa kin kashen jiki, kince Allah a lamarin dole in saduda tunda ita ɗin ma bata da wani tsayayye."
"Ke Abulle! Mai Unguwa ne ya turo Sarkin fada cewar yana son aurenki, me kika ce?"
Sai yanzu ta gane kan wa suke zancen su, domin da duk a baibai take fuskantar zancen nasu.
'Wai yau ni Mai Unguwa ke son aure? Lallai ina da sa a.'
Zancen zuciyarta kenan, kafin ta sake dulmuya wata duniyar tunanin.
Hangota ta yi a gidan Mai Unguwa, an dire mata wani ƙaton kwanon kaya shaƙe da dafaffiyar shinkafa 'yar gwamnati mai santsi da miyar ja, ga kuma ƙatuwar kaza a kai, gefe kuma ga babban kwanon sha cike da sassanyar ruwan ranar ƙasa.
Sake kallon ƙeta ta yi ma hinkahwar a karo na ba adadi, tana kuma tuna irin cin walaƙancin da za ta yi mishi.
Sake ware ɗaurin zaninta ta yi don yayi sako-sako gudun kada cikin nata ya yi saurin cika, ta kalmashe ƙafafunta waje guda, ta zura hannunta ciki ta gauraya gefe guda, ta ciko hannunta ta kai shi zuwa bakinta.
"Kingani ko Inno! Na gaya miki yarinyar nan ba son auren nan za ta yi ba, gashi ko amsa bata bamu ba."
Maganar da mahaifinta ya yi, shi ya hanata jin ɗanɗanon hinkahwar da ta shaƙe hannunta da shi, maganar ce kuma ta yi silar dawo da ita daga duniyar tunanin da ta afka.
Ta ji takaicin rashin ɗanɗana girkin, sai dai duk ranar da Allah ya kai damo ga harawa ba ƙaramin ɓarna za ta tafka ba, cin huce haushi za ta yi mishi.
Murmushi ta yi, wanda sautinshi ya fito, "Kin gani ko Inno? Kuka fa ta ke yi, gara a janye maganar nan idan yaso a jira har ta samu gwani."
Cewar Malam Ilu.
Salallami Inno ta sanya tare da tafa hannayenta, ta iza ɗaya a haɓarta ɗayan kuma ta ɗago fitilar dake ajiye ta haska fuskar Abullen da shi.
Kallo suka bita da shi, fuskokinsu fal mamaki.
Madadin suga hawaye ya wanke fuskarta, murmushi ne ke ta bayyana a fuskarta, idanunta kuma a rufe.
"Ke Abulle! Lafiyar ki kuwa?"
Inno ta tambayeta.
Da sauri ta buɗe idon ta sunkuyar da kai alamar kunya ganin yadda iyayen nata suka tsatstsareta da ido.
A guje ta bar wajen ta nufi ɗakin kwananta, zuciyarta cike da farin cikin nesa ta kusan zuwa kusa.
"Shikennan ai Malam, abu ya zo gidan sauƙi, alamu sun nuna ta yi na am da zancen. Sai ka yi maza ka sanar da su kai ma ka sami lafiya."
"Ai kamar yanzu ma kuwa ba sai an kai gobe ba."
"Sai kuma mu toshe kunnuwanmu, don za mu sha surutu gurin jama ar garin nan."
"Yo Inno! Idan sun yi ma ai za su bari, da yardar yarinya ai aka yi, ba dole aka yi mata ba."
"Haka ne kam."
Ya miƙe yana faɗin, "Barin je in sanar ma Sarkin fadan."
"To, a dawo lafiya."
Tunda aka sanar ma Sarkin fada bai yi wata-wata ba, a daren ya isar ma Mai Unguwa.
Washegari Mai Unguwa ya turo wakilanshi neman auren Abulle, da sadakinta dubu ɗari. Take aka sallama musu aka kuma sanya musu mako biyu mai zuwa aure.
Kafin kyaftu da Bismillah, zance ya karaɗe illahirin unguwar su Abulle, ya karaɗe garin mai ludaya da ƙauyukan dake maƙwaftaka da su.
Tsegumi ne kawai ke yawo ta ko ina, ga uwar Indo ma ta ɗaga hankali a gidan Mai Unguwa.
"Kai dai ba ka taɓa rabo da abun kunya, ka rasa wacce za ka aura sai ɗiyar cikinka. Allah wadai wallahi, girma dai ya faɗi."
Cewar Tabawa.
Kallo Mai Unguwa ya bita da shi, kafin ya ce "Abun kunya? Ai mu gaba muka bashi ba baya ba, in dai ta nan hanyar ne. Yaya ina ƙoƙarin raya sunnar Ma aiki Rasulullahi, kuma ki ke neman jifata da wasu kalaman da basu dace ba?"
Harara ta zabga mishi,
"Wani raya sunnar? Ka rasa lokacin da zaka rayar sai da duk furfura ta gama baibaye ka, mutuwa yau ko gobe, amma ka ke wani ƙiran raya sunna."
"Kai Tabawa! Ni da ke ba wanda ya san gawan fari, har yau ba za ki rage kishi ba. Yarinyar nan dai naga ƙarama ce, ba ruwanta, bata san komai ba. Don Allah ki sassauta kishin nan naki a kanta, kinga Lami kam ko a jikinta, bata wani nuna damuwar ta ba."
Gyara zama ta yi ta ce, "Lami daban Tabawa daban. Yo ita dama ɗaga hankalin me za ta yi? Taga jiya taga yau, abu tun zamanin ƙuruciya kuke tare, tun auren saurayi da budurwa, ta riga ta ci lokacinta ai, tunda ko ni nan ma ta haifeni few da aniya, balle kuma wata can wai ita Abuwa. Har ka ke wani ƙirinta da yarinya, ƙarshen yarinta inga Inno ta sanya majanyi ta goyata a baya, ta kuma ɗauki bulumboti ta liƙa mata a baki sai in yarda."
Ganin da gaske take, zancen nata ba na ƙare ba, yasa ya miƙe yana gyara zaman rawaninshi ya saiti hanyar fita yana faɗin,
"Ni dai na faɗa miki, ki sa ma ranki salama ki yi fatan a zauna lafiya kawai don kin san bani son fitina a gidana." Yana kaiwa nan yasa kai ya fice.
Tana huci tana faɗin,
"Za ma ka dawo ne ka samen, da rawani kamar an naɗa gammo."
Yana fita Indo ta faɗo ɗakin kamar wacce aka hankaɗo.
Gallamata harara Tabawa ta yi tana faɗin, "Ba ki iya tafiya a hankali ba ko? Kin wani faɗomin ɗaki kamar wacce kare ya biyo."
"Yi haƙuri Tabawa! Mutane ne suka ishen a gari, wai me yasa za a bar Baba ya auri waccar yarinyar? Wasu sunce don yana mai unguwa ne ya sa zai yi musu fin ƙarfi, wasu suce sayen ta yi yi, wasu ma cewa suke wa..."
Tsawa ta daka mata, "Koma me suka ce, ba ke kike jajiɓo ta ba? Inda ba ki talla mishi ita ba ina zai ganta? Na ji kuma ance saurayinta da suka daɗe tare ya yi ƙaura ya dawo wajenki, kinga da ta tashi huce haushin ta sai ta huce kan mahaifinki. Kinga nan da kwanaki goma ta zama kihiyar uwarki kenan. Sai ki shirya tarbar sabuwar uwa."
Ranta ɓace ta ce, "Allah ya satura! Ko rabin-rabin uwata ba ta kai ba, na san kuma kwaɗayin hinkahwa ne zai kawo ta Yasin za ta ga walaƙanci."
Masifa ta rufeta da shi har bakin da ya gama rinewa da goro yana fidda kumfa, inda ana bada aron baki, da ba abun da zai hana Tabawa ta yo aro yau.
Haushin kaza kenan.
Ummyn Yusrah
[9/22, 3:52 PM] Ummyn Yusrah🧕🏻: *ABULLE TA MAI UNGUWA*
*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*
*(HWA)*
_UMMYN YUSRAH_
_A ƙara haƙuri dai._
_10_
"Yi maza ki je gidan Goshi ta baki daddawar nan, kafin ki dawo na gama daka kukar sai a haɗa musu waje guda ki tafi, kinga rana na tafiya, kada dare ya riskeku, ga hanyar ba kyau ne da ita ba." Cewar Inno da take ta tiƙar busheshshen ganyen kukan da ta zuba a turmi, babban burin ta ta mai dashi gari.
"To Inno!"
Ta fice daga gidan ta nufi gidan Goshi mai Daddawa.
"Abulle! Abulle!! Abulle!!!"
Tun daga nesa yake ta ƙwala mata ƙira, sosai ta jishi ta ƙi juyawa Ganin ƙiran nashi ba na ƙare ba ne, yasa ta juyo a fusace tana hararar shi.
"Wai lafiya kake yi min irin wannan ƙira kamar wani tsohon makaho ko wacce ta sace maka ɗan taure?"
Ƙarasowa ya yi yana dariya ya ce,
"Yo Abulle don na ƙwala miƙi ƙira haka ai ba laifi ba ne, tun ranar nake so mu haɗu mu tattauna amma kin ƙi kulani."
Kallonshi take mai haɗe da harara,
"Kam me zan saurareka? Cemaka aka yi ina da lokacinka? Ka dai san ni ba sa arka ba ce ko?"
Cike da mamaki ya hangame baki kamar wani gaɓo yana kallonta kafin ya ce,
"Nine fa"
Ta yatsina fuska tana faɗin"Kaine wa?"
"Hamusu rabun ran Abulle."
Ya ƙarashe maganar cikin yanayin shauƙin so, har yana wani jijjiga jiki irin na jin daɗin nan.
"Hamusun Indo dai! Ai ni yanzu na wuci saninka."
"Ni ɗin?"
"Kai ɗin fa."
Ta juya ta fara tafiya, ko mai ta tuno sai kuma ta juyo ta yi mishi kallon sama da ƙasa.
"A je a bi wani sarkin, ba da ni ba, auren talaka."
Ta juya ta yi gaba.
"Dakata! Kada ki yi ƙoƙarin jifana da duwatsu, ina mai shawartarki da ki adanasu ki gina gida da su domin nasan duk daren daɗewa zai yi miki amfani. Sannan kada ki yi kuskuren ƙonani da wuta domin da shi muke kunna fitilun da ke haskaka duk wani gida da ke faɗin kyauyen nan. Duk ranar da ki ka kuskura ki ka yi wannan gangancin ina mai tabbatar miki da cewar za ki dawwama cikin duhu."
Yana kaiwa nan ya juya cikin ɓacin rai,
"Matsalar ka ce wannan kuma, mayaudari kawai."
Ta ja dogon tsaki ta wuce aikanta.
"Kinsan da tafiya a gabanki amma ki ka sami waje ki ka zauna ko Abulle?"
"Inno da na same ta a gida ai ba zan zauna ba, hegiyar yawo ne da Goshin nan kamar wacce ta ci ƙafar kare."
"Ni tafi ki je ki shirya, shegen iyayin tsiya, kin san hanyar Mai Rangwangwan ba kyau ne da shi ba. Idan ku ka yi dare ku kuka sani, don ma mai babur ɗin ɗan garin ne da ya sauƙeki gida zai wuce da sai dai ki zauna sai gobe kuma."
"Inno to a bari mana gobon na tafi."
"Ungo nan."
Ta watso mata yatsun hannunta biyar.
"An ƙi a barwa goben. Dududu bikin saura kwana goma ne, idan kin je gidan Kawun naku Talle ki ka dawo Jinjin za mu tafi can gidan Kawun ku na burni, nan ma ki kwana biyu ki zo ki bi gidajen dangi na kurkusa suma ki musu sallama."
Murna ne ya rufeta da ta ji batun tafiya Jinjin, itama za ta je burni ta ga yadda yake.
Ruwa ta dauka a bokiti ta je ta watsa, tana fitowa ta sa kaya, yau ba batun kwalliya, kayanta kulle a cikin ɗankwali, sai wani ƙaramin buhu da aka sa mata dankalin hausa, kuka da daddawa.
Sallama ta yi ma Inno, bayan ta gargaɗeta ta kuma ja mata kunnen ta kula ta kuma dawo akan lokaci.
Muntari ya ɗaukar mata buhun kukan, suka nufi tasha wajen mai mashin ɗin da aka jima da yi mishi magana.
Tana isa ba ɓata lokaci ya suri Abulle da wata mata suka ɗau hanya.
Gam Abulle ta riƙe ƙarfen jikin mashin ɗin, domin idan ba haka ba a yadda suke cafke a kan hanyar nan za a iya tsintota a ƙasa idan aka daka wani tsallen.
Taimakon ta ɗaya a tsakiya take, ba don haka ba, abun ba dama ne.
_Ummyn Yusrah_
*ABULLE TA MAI UNGUWA*
*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*
_Ummyn Yusrah_
_11_
Kwananta biyu a Mai Rangwangwan ta dawo, cike da ɗoki da murnar zuwa birni. Har gida ta je ta sanar ma Sarai itama za ta birni gidan Baffanta Jafaru don haka gara a daina yi musu yanga, don ba a fi su tsumma ba, balle a baɗa musu ƙwarƙwata.
Kwananta ɗaya a Mai ludaya washe gari suka ɗau haramar barin gari zuwa babban birnin Jinjin.
Tsarabar 'yan Maraya daban da ta ƙauye, domin su ba daddawa ba kuka.
Kabeji ce da kayan miya, sai kuma manyan kaji guda biyu.
"Inno! Su mutanen Jinjin ɗin ba su cin kuka da daddawa ne? Naga nasu tsarabar daban da ta Mai Rangwangwan."
Abulle ta tambayi Inno, ganin yadda aka bambanta tsarabarsu
"Ke, tuwon girma ai miyarsa nama. Su can me za su yi da wani kuka da daddawa? Tuwon ma ai sai su shafe mako huɗu ma ko fiye da hakan ba su yi shi ba."
Cikin mamaki da sakin baki ta ce,
"To Inno me suke ci kuma?"
"Ohho! Idan mun je kya gani."
Tsuke bakinta ta yi har suka tattari shirginsu suka ɗau wanya.
Kalle-kalle kam Abulle ta yi shi, mussaman ma da suka fara shigowa cikin birnin, ga kwalta shimfiɗe kamar tabarma, ƙarafunan wutar layi a tsaye kan hanya, jere reras kamar an dasa bishiyoyi.
"Ikon Allah! Kayan burni daban da na ƙauye."
Abulle ta faɗa a bayyane.
Kallo wasu daga cikin mutanen cikin motan suka bita da shi, don daga dukkan alamu ita ɗin sabon shiga ce a zuwa Maraya.
Amai ko ta yi shi yafi sau biyar, tun tana wanke jikinta da shi har aka bata tallafin leda.
Har cikin tasha aka sauƙesu, anan ne fa taga tarin jama a, sai kaiwa da komowa a ke yi, kowa na sabgar gabanshi. Abulle kam banda kallo ba abun da ta sa a gaba.
Idan Inno ta yi gaba, sai ta sake dawowa baya ta jawo hannun Abulle idan ta ga wani abun. Wani lokacin ma tuntuɓe take yi ko ta yi karo da wani abun tsabar kallo. Haka dai har suka tsare adaidaita zuwa unguwar su Baffa Jafarun.
Nan ma dai mamakin ne cike da Abulle ganin mashin mai ƙafa uku, ga kuma gidaje harda masu hawa-hawa.
Wani akan wani.
'Ikon Allah! Na zaune bai ga gari ba.'
Zancen da Abulle ta yi a zuciyarta kenan.
Tafiya dai-tafiya dai, har suka iso inda za su, suka biya mai adaidaita, ya ƙara wuta.
Buga get ɗin ƙofar gidan suka yi, da sauri mai gadin ya zo ya buɗe musu ƙofar. Ganin Inno da ya yi ne yasa shi wangale baki yana faɗin,
"Maraba lale da mutanen Mai ludaya. Yau kune a garin namu?"
"Maraba dai Ɗayyabu! Gamu kamar an jefomu."
"Sannunku, ku shiga mana."
Ya faɗa yana ɗaukar wasu daga cikin kayan da suka zo da shi ya yi gaba.
"Inno kin san shi ne?"
"Farin sani ma kuwa, a Mai ludaya yake shima, ɗan gidan Malam Datta mai katako."
"Au! Na ɗauka ai tsabar zuwan da kike ne ya sanki."
"Yo ni yaushe ma nake zuwa? Rabon da garin nan tun ina goyon Muntari da muka zo yi ma Baffanku barka da dawowa daga Makka."
Haka suka ƙarasa har cikin gidan Inno na yi mata bayani, ita kam inda za a shaƙeta ma ba ta san ɓaɓatun da Inno take yi ba, don gaba ɗaya hankalinta ya tafi ga kallon tsari da haɗuwar da gidan ya yi.
Zuciyarta ke yi mata tambayar,
'Wai dama suna da dangi masu kuɗi kuma 'yan burni shine ba su taɓa zuwa ba?'
Ita dai a saninta da wayonta sau biyu ma ta taɓa ganin Baffan nata a ƙauyensu, sai dai Babanta ya zo ko kuma ya yi musu aike daga nan.
Suna ƙoƙarin shiga falon, Ɗayyabu kuma na fitowa. Ya ce,
"Inno wannan kamar Abuwa?"
"Ita ce."
"Ikon Allah! Girma dai ba wuya, ta girma abunta."
Ya faɗa yana riƙe haɓa.
"Girma kam ai ba wuya Ɗayyabu, musamman ma na 'ya mace. Yanzu ma sallamar Baffanni take zata gidan aure."
"Ikon Allah! Ashe dai zamu Mai ludaya kwanan nan."
Ya wuce yane 'yan zantuttuka, su kuma suka shiga.
Sanyi da ƙamhi ne ya ziyarci sassan jikinsu da hancinsu.
Abu guda ne ya faɗo ma Abulle, tunowa da ta yi da ɗakin Inno mai tsamin ƙuli.
_Ummyn Yusrah_
*ABULLE TA MAI UNGUWA*
*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*
_Ummyn Yusrah_
_12_
Tunowa da tayi da ɗakin Inno mai ɗankaren tsamin ƙuli da wasu tarkace.
Da sallama suka ƙarasa cikin falon, Hajiya da yaranta biyu suna zaune kan kujera suna kallo.
Da fara a Hajiya Sabuwa ke yi musu Maraba da zuwa, a ƙasa ƙaramar kafet ɗin da aka ɗaura kan tayis ɗin falon suka zube. Inno na amsa maraban da take yi musu yayin da imanin Abulle ya gama tafiya ga kallon kayan alantun da ke falon.
'Yan gaishe-gaishe suka yi, nan Hajiya Sabuwa ta shiga tambayar jama ar gida.
Dungurin Abulle ta yi tana faɗin,
"Kekam mene ne haka? Saki iya gaisuwa ba ne?"
A firgice ta dawo hayyacinta, tana faɗin,
"Ina kwana?"
"Ita kika gani ma, ai ga manyan masu hankalin da suka fita ma basu iya gaisuwar ba balle kuma ita."
Kallon su Inno suka yi suna mai daɗin,
"Sannunku da zuwa. Kun zo lafiya?"
Daga nan basu kuma ɗorawa ba, suka cigaba da abun da suke yi. Don su a zatonsu irin baƙi masu zuwa neman aikin nanne ne suka zo.
"Ke Lubna! Tafi ki kawo ma baƙi ruwa, Kai kuma Afreen ka ɗauko musu lemo."
Kowa ya tafi ɗauko abun da aka aike shi.
'Lubina! Ji wani suna kamar na makarai don Allah, ga wani ma wai a firij. Idan kana raye a duniya dai kaga abu.'
Zancen zucin Abulle.
"Inno ina fatan dai anan za a bar min ɗiyata ta kwana biyu ko?"
Hajiya Sabuwa ta tambaya.
"Hajiya ai itace silar zuwan tawa ma, nan zan barta ta kwana biyu, ni yau zan koma. Bikinta ya zo saura mako guda tazo yi muku sallama."
"Amma ko kin kyauta wallahi, dama ba ta taɓa zuwa nan ba."
"Hajiya, kuma ai ba zuwan kuke yi ba, ko yaran nan ma ku ɗan riƙa kai su suga dangi abun ya gagara, tayaya za su yi zumunci a tsakansu?"
"Wallahi ni kaina ina son su je, sai dai makaranta ba su da lokaci, ga kuma halin Alhaji bayaso su matsa ko ina."
"Makaranta ko ai ba zai hana su zumunci ba, naga ai suna ɗan samun hutu, ko mako guda suka je suka yi ai za su ga danginsu. Alhaji kam kada a yi mishi sharri, don kin san halin mazan namu idan ba ke mace kin sasu a hanya ba ba yadda za a yi su ce miki jeki, ke mace ke ya kamata ki riƙa yi masa nuni da hakan tunda ki ga shi ba mazauni ba ne."
"Haka ne kam wallahi, don idan ka biye tasu zumuncin ma ba za a yi shi ba."
"A to, gara dai a riƙa ƙoƙartawa. Kada wataran a haɗu a hanya ba a san juna ba."
Dariya suka sa.
"Inno ai ba za a yi haka ba ma, ga biki ya zo, sati za muyi a Mai ludaya da yaddar Allah."
"Allah ya yaddar mana."
"Amin dan na biyur Rahmanti."
Ruwan gora mai sanyi aka kawo musu da kofi, ga kuma lemon kwalba, guda biyu mai ja da baƙi.
"Ke Lubna zo ki zuba musu mana kin ja kin zauna, wannan ƙanwarki ce Zainab 'yar gidan Baffanku Ilu da mahaifiyarta."
Hajiya ta ke gabatar ma yaran nata da su Abuwa.
Kallo yarinyar ta bisu da shi, tana mai taɓe baki, na ganin yadda suke a jigace kuma wai ace danginsu, danginma na kut da kut!