x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 10 - ABULLE TA MAI UNGUWA

  • 27001 words
  • 30000 words
  • Out of 44439 words

Category: Love Stories

Views 292

17 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
yana faɗin,
"Wannan waje ba kyau ko kaɗan. Allah ya jiƙansu, ai sai mu je, idan an kai su na dawo in yi ƙiran. Ban ji labarin mutuwar ba, sai yanzu."

Ya faɗa lokacin da suka rankaya cikin gari.

***
Tunda ya dawo daga sallar asuba yake ƙawance, tubka da warwara kawai yake, ga kuma wani irin yanayi da yake ji a jinkisa wanda ya kasa gane na mene ne? ga rana har ta hudo. Haka nan ya miƙe jiki ba ƙwari, ya ɗauraye ƙafafuwansa ya mulkesu da mai ya ɗau tiren gautarsa ya rufo ƙofar ɗakin nasu, ya nufi kasuwa gurin da suke sari. Zuciyarsa cike da tunanin Innarsa ko awani hali take.

***

Cikin wayo da dabara, ta yi ta tambayar Ɗayyabu tashan da ake shiga motar zuwa Mai ludaya, ba tare da ya kawo komai a ransa ba ya sanar da ita, har ma da abubuwan da bata tambayesa ba. Suna zaune Daddy ya zo wuce wajen aiki, Afreen ma ya fita.

Ganin haka yasa ta miƙe ta nufi cikin gidan. Ba kowa a falon, da sauri ta nufi ɗakin da take ta ɗauko jakar kayanta. Tana shirin fita daga ɗakin Lubna ta leƙo.

Kallon sama da ƙasa ta yi mata, a razane ta yar da jakar. (Abinka da mara gaskiya.)

"Ki zo inji Hajiya."
Ta faɗa ta juya

Haushi da baƙin ciki ne ya dirar mata lokaci guda. Naushin jakar tayi da ƙafarta ta yi waje.

****

Ya kai kusan minti ishirin a wajen yana kai komo a wajen, neman zaren da zai sadasa da Baffa, shiru ba labari. Ƙarshe dai sai da ya hau kan bishiya ya ɗaga wayar sama na ɗan lokaci kafin abinda yake nema ya samu. Magana ya shiga yi tamkar wanda ya tara bataliya guda, yake da burin kowa ya ji abinda yake faɗa.

Fuskarsa kawai zaka kalla ka tabbatar da cewar saƙon da yake son isarwa bai sami karɓu ba.

Bai kai ga ƙare maganar ba, daga can aka datse wayar, haka ya sauƙo ya nufi gida jiki ba ƙwari tare da tunanin yanda zai tunƙari Mai Unguwa da zancen da kuma yanda mutanen gari za su tasasu a gaba.

Turus! ya ja ya tsaya lokacin da ya iso ƙofar gida, take fuskarsa ta bayyanar da alamar mamaki.

****
Hajiya dake zaune a falo tana ta rarrashin Abulle da ta cire damuwa ta kuma saki jikinta wayar ta da ke jefenta akan kujera ya fara ruri, dagawa tayi, ganin sunan Alhaji yasa ta yin murmushi, ta latsa koren madanni ta kara a kunnenta.

"To, gani zuwa."

Amsar da ta bayar kenan ta miƙe, tana tunanin me kuma ya dawo da Alhaji gida a wannan lokacin, ƙarfe sha ɗaya na safe.

Miƙewa tayi, tana faɗin,

"Bari je Daddynku ne ya dawo, zan zo yau a bani labarin garin Mai Ludaya da Mai Unguwa."

Tana wucewa Abulle ta bi bayanta da harara, don duk maganar da take yi ba fahimta take ba. Yare ɗaya ne kawai a yanzu zata iya ganewa shi ne 'Shirya ki tafi gida.' ga dukkan alama kuma basu shirya hakan ba.

'Ki gudu kawai ba tare da kin tsaya ɗaukar jaka ba.'

Tana kai nan ta miƙe ta nufi hanyar waje, cikin sa a kuwa taga ba Ɗayyabu mai gadi a wajen.

A wankali ta buɗe ƙaramar ƙofar da ke jikin get ɗin ta fita.

Tana fita kuwa ta sa gudu iya ƙarfinta.

***

A tsaye ta sameshi a falon, rai ɓace.

"Alhaji! Lafiya kuwa?"

Ta tambayesa lokacin da ta ƙarasa shigowa.

Juyowa ya yi ya kalleta.

"Ina yarinyar nan?"

"Wacce? Lubna?"

"Zainab!"

"Au! Yanzu na barota a falo."

"Ta shirya, yanzu Tukur zai zo ya maida ita, ya je shan mai ne."

Ido ta zaro, ta ce

"Lafiya Alhaji?"

"Ke dai ki yi abinda nace kawai."


_Kun makaro, sai dai ku tura jakar kayan abulle._


_Ummyn Yusrah🧚🏼‍♀_

*ABULLE TA MAI UNGUWA*

*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*

_Ummyn Yusrah_

_37_

"Don Allah Alhaji me ke faruwa ne? Ka sanar da ni mana."

Ta faɗa tana kallon fuskarsa,

Zama ya yi, yana girgiza kai cikin takaici, sannan ya zauna.

"Da na ɗauka ina da iko da 'ya'yan Ilu a matsayinsa na ɗan uwana, sai dai yau ya gwadamin akasin hakan."

"Alhaji ban fahimta ba fa! Don Allah ka sanar da ni, me ke faruwa."

"Wai har ni Ilu zai ƙira ya ce in turo yarinyar nan gida?"

Zama ta yi, tare da jan numfashi. A tunaninta ma wani gagarumin al'amari ne, sai dai sanin halin mijin nata na mai da ƙaramin abu ya zama babba ya sa ta ce,

"Alhaji! Wannan ai ba abun tashin hankali da ɓacin rai ba ne, shi ya sa na ce tun farko a sanar da su zaman nata."

Wani irin kallo ya watso mata mai cike da jin haushi,

"Wannan ne ba abin tashin hankali ba? Ina yi mishi bayanin zata zauna a nan ta yi karatu, yana faɗamin an riga an sa mata rana, idan aka fasa hakan zai iya shafar kima da mutunci na gidanmu, sabida rashin wayewa irin na mutanenmu. Ki je ki sallameta, ko ɗaurin auren ma ba zan je ba. 'yarsa ce ya yi duk yadda ya so da ita."

Ido ta zaro,

"A dai yi haƙuri abi komai a hankali. Ya kamata ka karɓi uzurinsa, idan ya so, sai ka je can ɗin ka yi masa bayani yadda zai fahimta, idan ya so, sai a sami shi Mai Unguwar ya janye batun auren, inaga hakan zai fi."

"Ba inda za ni."

Ya faɗa yana ciro waya a aljihu, danne-danne ya yi, kafin ya kara a kunne.

"Kan ina?"
Abinda ya faɗa kenan, ya ɗan tsaya jim! Kafin ya sake magana.

"Ka dawo kawai an fasa zancen karatun, yanzu Tukur zai kai ta gida."
Ya katse wayar, ya sa hannu a aljihu ya ciro kuɗi.

"Ga dubu goma nan ki bata, idan zaku tafi sai in baku kuɗin da za a yi hidima da shi."

"Amma Alhaji sai naga kamar ka yi saurin yanke hukunci, da dai an je can ɗin an yi musu bayani in..."

Dakatar da ita ya yi,
"Bana son wani dogon zance, kema idan kinga ba ki da ra ayin zuwa sai ki zauna."

Miƙewa tayi, ta bar falon gaba ɗaya, don ta san yanzu sai ya dawo kanta.

Sam bata ji daɗin yadda ya yi saurin yanke hukunci ba.

Ɗaki ta nufa, manyan kwalaye ta ciro guda uku, ɗaya setin kula mai huɗu, ɗaya kuma, setin kofuna da jug ɗayan kuma setin tukwane.

Tana cikin jeresu a cikin wani buhu ne, Afreen ya shigo, hankali a tashe.

"Mommy wai da gaske Zainab tafiya zata yi?"

Ɗagowa ta yi, fuskarta da alamar rashin jin daɗin tafiyar nata, ta ce

"Hummm! Haka Daddynku ya ce."

"Mommy to me ya sa?"

"Ka sanshi ai, da maida ƙaramin abu ya zama babba. Yanzu haka ya yi ma maganar Babanku rashin fahimta ne, ya hau dokin zuciya."

Zama ya yi a bakin gado,

"Daddy Ho! Me Baban ya ce ne Mommy?"

Nan ta labarta masa yadda aka yi.
Matsowa ya yi kusa da ita, ya riƙo hannunta yana faɗin,

"Mommy don Allah ki roƙe sa ya barta, idan ta koma tsohon nan zasu aura mata, kinga kuma da ƙuruciyarta za a cutar da ita. Don Allah Mommy!"

Ya ƙarasa maganar tamkar mai shirin yin kuka.

"Afreen! Da da yadda zan yi in hana da na yi, sai dai babu, Alhaji ya riga a tirje, sai dai mu yi haƙuri. Idan yaso ko gobe ne sai mu shirya mu tafi, daga can mu rokesu ko Allah zai sa su yarda."

"Allah yasa."

****

Manyan buhunan biyu aka sauƙe da kwandon kayan miyu, tumatur biyu, tattasai biyu, attaruhu ɗaya, da ƙaramin buhun albasa, da jarkar manja a ƙofar gidan Ilu.

Ana gama sauƙewa, sarkin fadar Mai Unguwa ya biya masu amalanken kuɗinsu suka juya. Ilu da ya yi mutuwan tsaye don mamaki ne yasa ya yi saurin ƙarasawa wajen, ganin Sarkin fadan na neman ɗan aika zuwa cikin gidan.

Yana isowa, Sarkin fada ya fara,
"Ranka shi daɗe! Kaga uban Abu, sirikin babban mutum. Kaga zuriya masu rabo da babbar sa a! Mai Unguwa aiko ni, ya ce ga shinkafa a yi ta dafa ma jama'ar garin Mai Ludaya da maƙwaftanta kowa ya shaida, bikin da ba a taɓa yin irinsa ba, ba kuma za a taɓa yi ba."

Gaba ɗaya Ilu ya rasa bakin magana, domin bai san me zai ce ba a yanzun. Yana buƙatar kaɗaicewa don samun damar tunanon mafita.

Yaƙe ya yi, wanda ya fi kuka ciwo.

Hannu ya sa a aljihu ya ciro naira dubi, gudan ɗari biyar, sai gudan ɗari biyu, sai gudan ɗari, sauran duk gudan goma ne da ishirin, sai hamsin.

"Gashi ka zo yau ban fita ba balle in ba da na goro, ga wannan ba yawa, a yi haƙuri. Tukwuici na musamman na zuwa da izinin Allah."

Karɓa ya yi ya jujjuya su alamar sun yi kaɗan, kafin ya cusa magoginsa a baki ya goge haƙorarsa ya furzar da tukar kafin ya ce,

"To, ai shi ke nan, tunda dai mai yawar na hanya, ai ba damuwa. Idan an shiga a gaida gimbiyar."

"Zata ji."

Cikin zaƙuwa ya amsa masa, don ya zaƙu ya tafi.

Yana tafiya ya nemo majiya karfi suka tayashi kwansar kaya.

Kafin ka ce me, zance ya zaga gari, irin kayan abincin da Mai Unguwa ya tura gidansu Abulle.

_Ummyn Yusrah_

[11/22, 9:13 PM] Ummyn Yusrah🧚🏼‍♀: *ABULLE TA MAI UNGUWA*

*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*

_Ummyn Yusrah_

_An sami kuskuren lamba a shafin da ya gabata. 36 ne aka sa 37._

_37_

Fitowa ta yi daga maɓoyarta, wanda ta ɓoye lokacin da ta hango motar Afreen ya shigo layin. Waige-waige ta shiga yi, daga bisani ta juya ta cigaba da zuba sauri tamkar mai shirin tashi sama.

Wani nannauyar ajiyar zuciya ta yi, lokacin da ta iso bakin titi. Kallon yadda ababen hawa ke kai kawo kawai take yi, ta rasa ta ina zata fara tsaran abun hawa, ga jikinta dake ta kaɗawa tamkar mazari

****
Mommy! Yanzu ina take?"
Kallonsa ta yi,
"Tana falo ai, can na barta."
"Shigowata banganta ba, wataƙila ko don ban kula bane. Barin dubata."
Ya miƙe ya fita.

Kai tsaye falon ya nufa, bai ganta ba, ya nufi ɗaki, bata ciki, sai jakarta da ke ajiye a tsakar ɗakin.

Tunaninsa ne ya bashi, tana banɗaki, me yiwa ta na wanka ne. Hakan ya sanya ya koma ɗakin Mommyn suka ci gaba da tattaunawa yanda zasu yi don ganin an fasa auren Abullen idan sun je goben.

***
Duk kayan da aka shigo da shi, ɗaki ɗaya aka tarasu.

Cikin sanyin jiki Ilu ke yin komai.
Ganin mutane sun fara taruwa a gidan ne, ya buƙaci da su keɓe a ɗakinsa da Inno don jin yadda suka yi.

"Malam me ya faru ne? Duk naga jikinka ya yi sanyi. Ba dai wani abin ne ya sami mutanen Jinjin ɗin ba?"

Inno ta tambayesa lokacin da ta shigo ɗakin ta ganshi zaune ya taƙure, fuskarsa kuma na bayyanar da alamar damuwa.

"Bari kawai! Yaya ya ce Abulle ba za ta dawo ba, yanzu haka makaranta zai sa ta."

"Malam! Auren fa?"

"Na yi masa maganar, sai dai ya ƙi ya saurareni, ya kuma karɓi uzurina."

Ƙirjinta ta buga da hannayenta duka biyun tana mai kallon sa.

"Yaya kam,  nema yake ya ja mana  abun magana a gari."

"Na ma rasa ta cewa nikam."

"Yanzu Malam meye abun yi?"

Cikin yanayin damuwa ya ce,
" Ni kaina ban san ta ina zan fara ba. Ga kuma kaya da Mai Unguwa ya turo da shi, a yi amfani da shi wajen shagalin buki. Ban san ta ina zan fara sanar da shi zancen Yaya ba! Ban san da wani ido zan kalli jama'ar garin nan ba. Ta dalili hakan duk wani kima da daraja ta zuri'armu zai iya shafa."

Don numfashi ta ja,

"To, Malam! Ko dai komawa za ka yi ne ka gwada ƙiran ita Hajiyar ta lallaɓa Yayan ya barta ta dawo?"

Miƙewa ya yi, yana zura takalmarsa a ƙafa, yana faɗin,

"Haka ma za a yi, barin je yanzu. Ku cigaba da shirye-shirye kada ki nuna wani alama da mutane za su gane akwai matsala."

"To, a dawo lafiya. Allah yasa a dace."
"Amun."
Yamsa ya fita, itama ta koma suka ci gaba da aikinsu.

***

Ko kaɗan baya jin daɗin tallar yau, badon kuɗin mota da yake son tarawa a yau gobe ya wuce gida ba, da ba  abinda zai sa ya fito.

A haka yake yake bin tituna, idan ya ga lungu ya shiga, sai dai cikin da sauƙi.

Gidan Alhajin da ya zubar ma shara ne ya faɗomasa. Cikin azama ya ɗau hanyar Unguwar zuciyarsa cike da fatan samun nasara.

****

"Ina Zainab ɗin?"

Mommy ta tambayi Afreen lokacin da ta fito, ta gansa zaune a falo.

"Ban sameta a falo ba, na leƙa ɗakinta bata ciki, ina tunanin wanka ta shiga."

Ya bata amsa

"Wani irin wanka ne haka har yanzu? Alhaji ya fara magana, ta shirya kafin Tukur ya maida shi wajen aiki ya zo ya kaita, ya dawo."

Ta yi maganar tana tafiya ɗakin don ganin irin wankar da Zainab ke yi, wanda ya hanata fitowa har yanzu.

Shima ɗakin Lubna ya nufa, kwance ya sameta, tana daddana waya.

Bayan ya shiga ne, ya zauna kan kujerar.

"Yau dai mutumiyarki zata tafi ki huta."
Ya faɗa yana dariya,

Ɗagowa ta yi, tana yi masa kallon rashin fahimta.

"Wace mutumiyata kuma?"
"Zainab!"

"Tafiya kuma? Daddy ai ya ce zata yi karatu anan ko? Ba ɗazu ka fita duba makarantar da za a sata ba?"

Ta jero masa tambayoyin, kallonta ya yi, ya ce,

"Kinsan Daddy ai! Abu kaɗan ke harzuƙasa."

"Me aka yi to?"

Nan ya faɗamata abinda Mommy ta faɗamasa.

Karo na farko kenan da ta ji batason tafiyar Abulle, zata je ta roƙi Daddy ko zai yi haƙuri, ya je ya ba Mai Unguwa haƙuri ya haƙura da auren zuwa wani lokaci.

_Ummyn Yusrah_
[11/22, 9:14 PM] Ummyn Yusrah🧚🏼‍♀: *ABULLE TA MAI UNGUWA*

*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*

_Ummyn Yusrah_

_38_

"Ina kuma zaki je, kin barni a zaune?"

Ya tambayeta, lokacin da yaga ta ɗau hanyar fita daga ɗakin ba tare da ta yi masa magana ba.

"Zan sami Daddy ne."
Abinda ta ce kenan, ta yi gaba ba tare da ta jira taji me zai ce ba.

Keɓe baki ya yi, ya ɗage kafaɗunsa  fili ya ce,
"A dawo lafiya. Shalelen Daddy."

Yana shirin miƙewa ne Mommy ta shigo,

"Zainab fa bata ɗaki, na duba banɗaki ma bata nan."

Cikin mamaki ya ce,
"Bata ciki kuma? Ni dana ga bata ɗakin na yi zaton banɗaki ta shiga."

"Bata nan kam, zo ka duba ko tana kicin. Barin sanar ma Daddynku tana shiryawa."

Ta juya, shima ya fice zuwa kicin.

***
Yana tsaye, ya kara waya a kunnensa, yana sarma Tukur da ya ƙirasa yana sanar masa ya iso, ne ta shigo.

Sauƙe wayar ya yi, ya kalleta
"Mamana yaya aka yi?"
Ƙarasawa kusa da shi ta yi, ta riƙo hannayensa duk biyun, ta ce

"Daddy! Don Allah kada ka bar Zainab ta..."

Cire hannunsa ɗaya ya yi daga nata, ya ɗaga mata alamar ta dakata yasa ta katse zanceta ba tare da ta kai aya ba.

"Idan dai kan wannan zancen kika zo, to na riga na rufe shafinsa. Idan kuma da makasudin zuwan naki, ki sanar da ni, zan koma wajen aiki ne."

Girgiza kan da ta yi, ya yi daidai da gangarowar hawaye daga idanunta.

"Kuka kuma Mamana? Indai zaki bita maza ki shirya ku tafi, idan an yi bikin sai ku dawo."

Yana kaiwa nan ya yi waje, don baiso ta matsamasa ya santa da naci.

Cikin sanyi jiki ta bar falon zuwa wajen su Mommy da ke ta neman Abulle.

Duk wani saƙo da lungu na gidan sun bincika ba ita ba dalilinta. Har Ɗayyabu suka tambaya ko ta fita, ya sanar da su bata fita ba, ɗazu dai sun jima da ita anan daga bisani ta tashi ta koma ciki.

Abu wasa-wasa, sai gashi yana neman zamewa gaske.

Suna tsaye cirko-cirko tamkar zakarun da suka ƙoshi suna neman abokan gwabzawa ne a harabar gidan, cikin tashin hankali, ƙira ya shigo wayar Mommy.

Sunan da ta gani ne, yasa gabanta ya yi mummunar bugawa.

Sau biyu tana tsinkewa taƙi ɗagawa, tunaninta idan ta ɗaga ya tambayeta 'yarsa ta ce masa me?

Bata shirya wannan amsar ba a yanzu, domin batasan wani irin ruɗani zasu shiga ba, domin a yanzu ma tasan cikinta suke, tunda har taga ƙanin mijin nata ya ƙirata.

****

Ya yi tsaki ya fi a ƙirga. Gashi dai wayar na ƙara, amma anƙi ɗagawa, tunaninsa kada dai itama Hajiyar irin amsar Yayan nashi take son sanar da shi. Tunda ga alama ya nuna, ya ƙirata ta ƙi ɗagawa.

Saƙowa ya yi, daga kan bishiyar, ya zube a ƙasa, ya jingina da jikin itacen bishiyar.

Zuciyarsa ce ke rayamasa, anya ba zai gudu ya bar garin ba? Ya gudu ya je ina? Ita Innon kuma yaya zata yi idan ta ji labarin ya gudu. Gaskiya bai yi mata adalci ba, a ce babu shi babu Abulle, amma kuma fa yana tunanin irin badaƙalar da za a kwasa a garin, gara kawai ya gudu, idan ƙura ta lafa ya dawo. Idan yaso Inna za ji da su.

Yana gama tunanin ne ya miƙe, ya ƙara cusa ƙafarsa cikin ƙwaftarsa tamkar mai shirin zuwa kiwon shanu."

Ya yanki jeji, ya hau tafiya.

*****
"Garbati! Ina fatan ka tura Salele ya tafi duba ɗan nan? Duk hankali na yana garesa."

Inna Talle ta tambaya, lokacin da ta dogaro sandarta ta fito daga cikin ɗakin da aka yi mata masauƙi.

"A'a! Yaya, keda ba ki da lafiya kuma sai fi fito? Da dai kin zauna waje ɗaya ne, kinga jikin naki duk ba ƙwari"

Dalu da ta taho da sauri ta riƙe Innar ce take magana.

" Indai ba Hamusu na gani a gabana ba ai zama bai ganni ba. Gara kawai in fita in nemo ɗana da kaina, tunda naga ku baku damu da batar nasa ba. Da ɗanku ne ya bata, cikinku ba mai zama a gidan nan."

"Yaya ki yi haƙuri, ana iya bakin ƙoƙari wajen nemosa, za a gansa nan bada daɗewa ba."

"Zaki sake ni, ko sai na dokeki da sandar nan? Kuna nan zaune ku ci ku sha hankali ƙwance ne zaki ce ana ƙoƙari? Ina shi mijin naku? Kai Garbati! Ka zo ka maidani Mai Ludaya kokuwa?"

"Ki yi haƙuri, ya tafi kai Salele can Mai Ludayan, daga can zai wuce Jinjin ɗin."

"Au! Sun tafi?"

"Eh, sun tafi."
"To ai shi ke nan, yanzu kam zan ɗan sami nutsuwa. Allah yasa a dace."

"Amin Yaya, mu je ki kwanta."

"Ke ni barni! Kwanciya kamar wata ruwa. Barni a waje sha iska."

"To, mu je ga tabarma can sai..."

"Wannan ai iskanci ne! Hatsin ne aka bar yara suke wasa da shi?"

Garbati ya fara sababi lokacin da ya shigo gidan.

Da sauri Delu ta fara bubbuga hannunta a baki, alamar ya yi shiru.

Ai kamar ta ƙara tunzurasa

"Lallai Delu baki da mutunci! Ina magana kina yi min nuni da in yi shiru? Wato ga sakarai ko?"

Ya nufota kamar zai kai mata duka.

"Wa nake ji kamar Muryar Garbati?"

Da sauri Delu ta ce,
End Ads