x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 6 - ABULLE TA MAI UNGUWA

  • 15001 words
  • 18000 words
  • Out of 44439 words

Category: Love Stories

Views 286

17 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
biki.

Jin buɗe ƙofar yasa Abulle ɗagowa.

"A'a! Ashe ɗiyar tawa ta tashi? Yaya jikin naki?"

"Na jima da tashi, na ji sauƙi. Ina kwana?"

"Lafiya, yaya ƙarfin jikin naki?"

"Da sauƙi." Ta bata amsa a fili.

A zuci kuma ta ce,

'Ina wani ƙarfin jiki, ban sanya ma ciki komai ba.'

"Allah ya ƙara sauƙi."

"Amin."

Har ta juya zata fita, ta juyo ta ce,

"Ki tashi Auntynki ku zo ku ci abinci, ga Babanki ma ki zo ku gaisa, jiya mun je asibiti da shi kina barci."

"To."

Ta bata amsa, ta je har gaban gadon ta miƙa hannu ta bubbuga ƙafafunta.

Idanuwanta ta buɗe, ganin ta tashi yasa ta faɗa mata saƙon Hajiya.

"Na ji ta. Ki je sai na yi wanka."

'Sannu kifi.'

Ta miƙe tabar ɗakin.

Fitowarta ma ba kowa a falon.

Tunani take ina shi mai gidan yake da zata gaisheshi? Ita ba ko ina ta sani a cikin gidan ba.

Kicin ta shiga ta tambayi su Lantana, ita ta fito ta nuna mata wani ƙofa da zai kaita har ɓangaren Alhajin.

Dogon lungune da ya sha sumuntin bature, (Tayis) samɓal ta miƙe ta fara tafiya tana kalle-kalle zuciyarta fal tunanin irin kayan more rayuwa da ke gidan, su kuma suna can cikin karmami.

Ba tayi aune ba, sai ji ta yi santsi ya kwasheta ya timata da kasa, take ta baje a wajen ta yi zaman 'yan biri, sakamakon goge wajen da aka yi bai gama bushewa ba.


_Ummyn Yusrah_

*ABULLE TA MAI UNGUWA*

*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*

     _Ummyn Yusrah_

_21_

Rintse idanunta ta yi, har da ɗan guntun hawaye,ta shiga shashshafa kunkuminta da ta buge a da jikin garu.

Sai da ta ɗau tsawon mintuna goma a zaune kafin ta shiga yin rarrafe zuwa wajen su Hajiyar.

Bata yarda ta miƙe ba, sai da ta isa wani babban ƙofa sannan ta tashi tsaye,

'Aljannar duniya! Gida a cikin gida.'

Shine abunda ta faɗa a zuciyarta lokacin da ta kutsa kai cikin babban falon, sallama ta yi gami da kalle-kalle.

"Shigo mana Zainab."

Hajiya dake zaune kan daya daga cikin kujerun falon ta faɗa bayan ta  amsa sallamar.

A hankali take tafiya don gudun sake afkawa gidan jiya.

Tana jefa ƙafarta kan tattausan kafet ɗin da ke baje tsakiyar kujerun ta yi saurin janyewa, don laushin ya yi yawa, tsore take kada ta kuma jefa kafar ya lume da ita.

Da sauri ta tsugunna a wajen, tana faɗin,

"Ina kwana Baffa!"

"Lafiya lau, ɗiyata ashe ta jirma. Taso a ƙasa ki hau kujera ki zauna."

Yaƙe ta yi, ta ce,

"A'a! Nan ma ya yi."

"Ki saki jikinki, nan ma gidanku ne, maza taso."

Kamar ta kurma ihu haka ta ke ji, gani take kamar lumewa ƙasa za ta yi idan ta sake hawa kan wannan abu mai gashin.

Ƙara matsowa ta yi, ba tare da ta hau kan kafet ɗin ba.

"Ke dai Zainab akwai ƙauyanci! Ace mutum da gidansu ya riƙa abu kamar wani baƙo."

Cewar Hajiya.

Dariya Alhajin ya yi, ya ce,

"Za ta ware ne ai, sai a hankali. Yaya jikin naki?Kin ci abinci dai ko?"

"A'a, yanzu zamu ci."

"To, maza a je a karya, kafin a zo a bani labarin Mai Ludaya."

Da sauri ta miƙe, ta fita.

Tana fitowa ta gurfana ta hau rarrafe.

"Ke! Meye haka?"

Taji tambaya daga sama, ba tare da ta ji tahowar mai tambayar ba, da yake kanta na sunkuye a ƙasa.

Ganin Afreen yasa ta magana.

"Sulewa na yi ɗazu."

Dariya ya saka, ya ce,

"Sai ki riƙa tafiya kina kula." Ya wuce ya barta.

'Ji mugu! Ba ma sannu zai min ba sai wani in kula! Kulo.'

Ta ci gaba da rarrafawa har ta baro wajen, ta iso babban falo.

Tana zuwa ƙofar wajen ta miƙe, ta shiga.

Wajen da suka ci abinci jiya ta wuce ta tarar an ajiye musu komai na karyawa, sai dai ba kowa a wajen.

Daga zamanta zuwa yanzu ta yi tsaki ya fi a ƙirga.

Ga dai kwanukan abinci, amma ba masu cin.

Ga yunwa, ga takaicin rashin zuwan masu gidan.

Ganin ta ɗau lokaci tana jiransu ba su zo ba, yasa ta fara kokuwa da kula. Duk wani dabara da za ta yi don ya buɗu ta yi, amma ya ƙi buɗewa.

Ganin haka yasa ta haƙura ta koma ta cigaba da zaman jira.

A tare suka fito daga gefen Baffan suna kwasar dariya.

Kallonsu Abulle ta yi, take ta ji wani takaici ya ƙara rufeta.

Ji ta yi kamar ta je ta shaƙesu.

Har suka iso wajen suna dariya.

"Ba ki ci abincin ba?"

Afreen ya tambayeta.

Kallon takaici ta yi mishi,

'Banci ba ɗan rainin hankali, da uwar kai kamar Umarun kiyashi.'

A fili kuma ta ce,

"Uhmmm!"

"Me yasa?"

A kufule ta ce,

"Ban iya buɗe kwanukan ba."

Buɗe mata ya yi, ya bata faranti ta ɗibi dankali da ƙwan.

'Ikon Allah! Wannan uwar mai ai sai yasa mutum ya yi lisu.'

Jida tayi yanda zai isheta, ya haɗa mata shayi ya miƙo mata da biredi.

Godiya ta yi mishi.

Ta kalli Lubna da tun zamanta a wajen take danne-dannen waya.

'Albasa dai ba tai halin ruwa ba. A haka dai za a ƙare.'

Ledan burodin ta buɗe ta yagoshi, ta dunƙule ta dauko kofin da ya haɗa mata shayin ta danna a ciki.

Hannu ta sa ta kwaso jiƙaƙƙen burodin, ta hangame baki za ta tura, hakan ya yi daidai da sauƙe kofin shayin da Lubna ta yi daga bakinta.

Kamar ance ɗaga kanki! Sai ko ta yi ido biyu da kwamacalan Abulle.

Furzo da ruwan shayin ta yi, tana faɗin.

"A uzu billahi! Wannan wani irin azanta ne don Allah."

Ta miƙe da shirin barin wajen.

"Sista ba dai kin ƙoshi ba?"

Afreen ya tambayeta.

Juyowa ta yi tana faɗin,

"So kake in yi amai ne? Dubi wani gwale fa da yarinyar nan ke yi."

Ta juya ta bar wajen.

Gallamata harara Abulle ta yi.

'Har da wani korar A'uzun ta, irin ga sheɗaniyar nan. Idan kin ga dama har yauma ta nannaɗe kada ki kuma cin abinci. Har wani Sitta ko sittin ne kai ka ji wajen.'

Ta ci gaba da ba cikinta hakkinshi.


_Ummyn Yusrah_

*ABULLE TA MAI UNGUWA*

*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*


_Ummyn Yusrah_


_22_

Afreen ruwan shayi kawai ya haɗa ya sha da wainar ƙai ya miƙe ya bar wajen.

Kallo ta bishi da shi mai cike da mamaki, har yaushe wannan ɗan ruwan shayin zai ɗauki mutum? Ga abinci nan a wadace ba za su sake su ci ba sai a dangwala a tashi. Shi ya sa ko kaɗan ma ba su da wani ƙiba, wannan kyakykyawar iska aka yi zai iya awon gaba da su.

Juyowa ta yi ta ci gaba da cin abincinta, tana mamakin yawan abincin da aka ajiye ba masu ci.

Wannan kam almubazzaranci ne. Wataƙila don ba su san wahalar noma ba ne shi ya sa suke haka.

Tattaro sauran sayyayyen dankali da ƙwan da ya rage akan farantin ta yi, ta haɗe waje guda ta dunƙule ta kai baki, tana tauna daɗi na shigarta.

Bakinta cike, ta ce,

"U'uhum! Garin daɗi na nesa, wani ya zo Jinjin bai ga moto ba. Su Inno ana can ana gwagwarmaya da ɗumame."

Ta kurɓi ruwan shayin.

Ba ta bar wajen ba, sai da ta tabbatar da cikinta ya gama cika gaba da baya.

Juyi kawai ta ke yi a kujerar falon, tun tana iya zama har ta gaji ta kwanta, gashi kwanciyar ma duk ya isheta.

Wannan wani irin gida ne haka? Ba fita ba aikin komai, duk jikin mutum ya yi ta ciwo. Sai aikin zuba ma kwalba ido kana ganin masu jajayen kunnuwa na ta gwalaɓen magana.

Tsaki ta ja, Lubna da ke zaune kan kujera tana danne-danne a waya ta ɗago ta kalleta ta sake mai da kai ga waya.

Ba tare da ta ɗago ba, ta ce'

"Ke! Ki ɗauko min ruwa a firij."

Waiga-waige ta shiga yi, ba ta ga kowa ba. Kenan ma da ita, ita ce Ke!

Lallai wannan rainin hankalinta ya wuce inda take tsammani.

Juyawa ta yi ta bata baya.

"Wai ba ki ji me na ce ba ne?"

Ta yi tambayar.

Shiru ba amsa.

"Zainab! Wani salon iskanci ne haka? Ina yi miki magana, kin yi banza da ni."

Jin ta ƙira sunanta yasa ta juyowa tana faɗin,

"Ji nayi kin ce ke! A iya sanina Inno da Baffa Zenabe Abu suka raɗamin wanda wasu ke ƙirana da, Abuwa, Abulle. A garin Jinjin kuma Zenabu, kinga ko ai ba lallai in san da ni ki ke yi ba."

Kallon mamaki ta bita da shi. Lallai yarinyar nan bata da kunya.

"Idan ba da ke nake yi ba, da wa nake yi? Za ki tashi ko sai na ɓaɓɓallaki."

Kallon sama da ƙasa ta yi mata, ta ƙare mata kallo tsaf!

'Wai ɓallawa? Allah na tuba ai ko dusa nake ci wuce nan. Yasin damƙa ɗaya na yi miki sai kin gane kurenki. Renon dawa ce ni.'

A fili kuma ta ce,

"Zan karɓo miki da gudu ma."

Ta miƙe ta bar falon.

****

Inna Talle da 'yan uwanta sun yi cigiyar Hamusu har sun fara gajiya ba labarinshi.

Yau kwana biyar kenan da tafiyarshi.

Tun tana kukan fili har ta dawo na zuci.

An shaida mata ya tafi garin Jinjin, lokacin da ta sa a yi mata cigiya a tasha.

Duk wanda ta ji zai je garin Jinjin, saƙonta baya wuce a sanar ma Hamusu ya dawo gida.

Duk wanda ya dawo, ce mata yake bai ganshi ba.

Sosai ta tashi hankalinta, lokaci guda duk ta zabge ta fita hayyacinta.

Ganin halin da take ciki ne, yasa Wani ƙaninta Garbati ya tafi da ita garinsu Ɗan kurma.

Ƙauye ne sosai, ga ƙauyanci har ya fi na Mai Ludaya.

Tafiyar awa goma za ka yi daga Mai Ludaya, zuwa Ɗan kurma.

Su Inno shirye-shirye ake ta yi, ba ji ba gani. Haka ma gidan Mai Unguwa ana ta shirin tarbar sabuwar amarya.

Yayin da galibin 'ya'ya da jikokin Mai Unguwa ke ji kamar su kamashi da ranshi su jefashi cikin tukunya, su gangama mai wuta ya mutu ko su cakuɗa mishi abincinshi da shinkafar ɓera ya mutu kowa ma ya huta.

A fadar Mai Unguwa ma, tawagar ta kasu biyu.

Tawagar da ta fi rinjaye, suna tawagar ƙin auren Abulle da Mai Unguwan, tawagar amincewa kuwa! Ba su fi a ƙirga ba.

***

A hankali take tafiya a kan simintin bature, gudun kaiwa kasa irin na ɗazu, har ta isa ƙofar ɗakin.

Buga ƙofar ta shiga yi.

Daga ciki aka tambaya da waye?

"Nice Abulle."

Tasowa ya yi ya buɗe ƙofar.

"Yaya ne?"

Ya tambayeta.

"Cewa aka yi in karɓo ruwan sha a wajenka."

Kallon rashin fahimta ya yi mata,

"Ruwa a wajena kuma? Duk gidan nan ace ba ruwa sai an aiko ki wajena? Waye a aikoki?"

Taɓe baki ta yi itama, tana tunanin kinibibi irin na waccar mai kama da takardar. Ace duk ruwan gidan ya gagareta sha, a na wajen Afirij!

"Uhmmm! Nima shi nagani. Akwai ruwa a gidan amma wai in karɓo mata a wajenka."

Tsaki ya yi, ya ce

"Wai waye ne?"

"Labano mana?"

"Labano kuma? Waye haka?"

Ya yi tambayar cikin rashin fahimta.

Kallon rashin fahimta itama ta yi mishi.

"Labano ta gidan nan mana. Ko akwai wata ne."

Dariya ne ya kufce mishi, da ya gane ashe Lubna take nufi.


_Ummyn Yusrah_

*ABULLE TA MAI UNGUWA*


*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*


_Ummyn Yusrah_

_Ku yi haƙuri da jina shiru, zazzaɓi ya riƙe ni. Amma sauƙi sosai, masu yi mini addu ar samun sauƙi ina godiya._

_Masu yi min magana ba amsa a private ko cikin group ba amsa ku yi hakuri don Allah, na ɗan yi fama da matsalar network ne._


_Afwan! Sunan garin su Inna Talle Kurmawa ba ɗan kurma ba._

_23_

Dariya yake ta ƙyaƙyatawa, ita kuwa ta gama ƙuluwa, haushi duk ya cikata. Ba abin da ta tsana kamar a tasata gaba ai ta doka dariya ba dalili.

Juyawa ta yi cikin fushi zata tafi, da sauri ya biyota yana ƙiranta.

"Zainab!"

Tsayawa ta yi kafin ta juyo, fuskarta a haɗe.

"Meye?"

"Yi haƙuri! Da fari ban fahimci wa kike nufi ba."
Keɓe baki ta yi, irin kai ka sani ɗin nan.

"Je ki, ki ce mata zan kawo mata kin ji."

Juyawa ta yi ta ci gaba da tafiyarta ba tare da ta bashi amsa ba.

Ganin ta shigo ba ruwa a hannunta yasa ta tambaya.
"Ina ruwan da nace ki ɗauko min?"
"Ya ce in je zai kawo."
Kallon rashin fahimta ta yi mata.
"Shi wa?"
"A firij!"

Tsaki ta ja sannan ta ce,
"Kin taɓa ganin Fridge ya yi ƙafa ne? Ko kuma ya yi baki da har zai ce miki jeki zan kawo?"

Kallonta ta yi, ta ce

"Dama A Firij ɗin kurma ne? Naga kullum yana magan..."

Kafin ta ƙarasa maganar sai gashi ya shigo, yana faɗin.

"Aunty Labano ga ruwan."

"Yauwa, gashi nan ma kin ji yana magana." Cewar Abulle

Yamutsa fuska ta yi,
"Meye kuma wani Labano?"

"Ba ki san Labano ba?"
Ya tambayeta lokacin da ya ke zama kan kujerar.

"Ban sani ba."
"Sabon sunanki ne da Zainab ta raɗa miki yau." Tsaki ta ja cikin jin haushi.
Harara ta galla ma Abulle, tana faɗin,

"Wannan bata da saiti, don iskanci sunan nawa ne zata ƙira da sunan wani ƙasa." Dariya shikam ya sake kwashewa da shi.

"Ke kin cika masifa wallahi, yarinyar da bata iya ba, don ta kuskure ai gyara za a yi mata ba wai a yi mata masifa ba."

"Koma dai meye ku kuka sani. Dallah ni bani ruwana."

Ta faɗa tana faucewa.

'Kya ji da shi dai masifatu, Allah yaso gobe ma zan bar muku gidan ki ci kanki. Cewar Abulle ta juya ta fita.

"Wai gurinka ta je karɓar ruwan ne?"
"Dama ba wajena kika aikota ba?"
"Duk ruwan da ke gidan nan in kasa sha sa sha sai na wajenka? A Fridge fa nace ta ɗauki min."
"To, ai wajen a Firij ɗin ta je karɓo miki."
"Ban gane ba?"
"Suna na ne fa A Firij ɗin wai."

Dariya ta sa, shima ya tayata, kowa yana ƙiran sabon sunan kowa.

Bakin get ta nufa wajen Ɗayyabu mai gadi.

Yana hangota ya wangale baki yana dariya don yasan yau, zai sha labarin Mai Ludaya har ya ƙoshi.

"Abulle! Abulle! Abulle mutan Mai Ludaya. Sai kuma gaki a Jinjin."

Ya faɗa yana tura mata farar kujerar roba.

Bayan ta zauna ya ce,

"Yaya kika ji Jinjin ɗin?"
"Ba daɗi."
Zaro ido ya yi,
"Ba daɗi kuma? Birni ne fa!"

"To, ina daɗi anan don Allah? An jibge mutum waje guda kamar kayan wanki, daga barci sai kafa ma kwalba ido."

Dariya ya yi,
"Wato dai kin fi gane ki yi ta jeka ka dawo ko?"
"Iy mana! Zama waje ɗaya ai haɗari ne."
"Gaskiya kam, musamman ma ga wanda bai saba ba."
"A, to. Ni waje ma nake son leƙawa."
"A yi haka kuwa? Ke da kike baƙuwa idan na barki kika fita ai ba kanta."
"Yasin ba nisan zan ba, yanzu zan dawo."
"To, ai rana ya yi, ki bari zuwa anjima yanzu za a yi sallar azahar ne."
"Dan Allah Baba Ɗayyabu ka bari na leƙa, yanzu zan dawo."

Jin ta girmamashi yasa ya ce,

"To, iyakarki bakin layin nan, yanzu ki dawo."
"Yauware, Na gode."

Ƙaramin ƙofar da ke jikin jet ɗin ya buɗe mata, har waje ya fito ya nuna mata hanyar ƙarshen layin, tana zuwa kuma ta juyo ta dawo.

Godiya ta yi, ta ɗau hanya.

Sunkuyawa ta yi, ta tsinci duwatsu, tana tafe tana ciccilasu sama.

Ta zo wucewa wajen wani masallaci dake jikin wani gida taga wani mai saida gauta, a tsugunne. Har ta wuce sai kuma ta dawo.

"Malam nawa kahin gautar?"

"Hansin da ta dari."

Ta nuna ɗaya tiren da ba mai ita,

"Su kuma wa innan ɗin fa?"

"Duk kuɗinsu ɗaya, mai ita ya zaga makewayi ne, yanzu zai fito amma."

"Ni na naira Ahirin nake so."

Ta kwanto a bakin zaninta.

"To, kawo mana sai in ɗiba miki, da gani ai kema tamu ce daga gida kike."

Dariya ta yi, ta ce

"Kai ma ɗan Mai Ludaya ɗin ne?"

"A'a, a Bugawa nake."

"Taɓ! Ban taɓa ji ba."

"Nima ban taɓa jin naku ba."

Ya faɗa lokacin da yake miƙa mata.

Sai da ta ƙirga, ta ce

"Ƙwara fa huɗu ne?"

"Iy!"

"Taɓ! Can kam sai dai mu je mu tsinko, nan kuma ɗan wannan wai Ahirin hu um!"

Ta faɗa tana tafiya.

Tana barin wajen sai ga Hamusu ya fito daga magewayi.
"Ai kawai mu yi alwala kawai mu yi sallah sai mu wuce."

Cewar Hamusu.

"Kawai ba."

Abokin tafiyar tashi ya bashi amsa.


A yi haƙuri da kura-kuran ciki, ban bibiyaba.

_Ummyn Yusrah_

*ABULLE TA MAI UNGUWA*

*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*

     _Ummyn Yusrah_

_24_

Tana tafe tana cin gautarta har ta isa bakin hanya, sai da ta tsaya ta kalli motoci da babura masu wucewa sannan ta juyo. Ci gaba da wurga duwatsunta sama ta yi tana cafkewa.

Wani gini ta hango da aka fara ba a gama ba aka mai dashi wajen zuba shara. Hango kwalayen sabulai da robobin mai da kwalaben turaruka da ta yi kan bolan yasa ta nufi wajen. Leda ta nema babba ta karkaɗe, Allah ya taimaketa bai yage sosai ba, ta hau tsintar kwalayen sabulu mai hoton mata da robobin mai da kwalaben turaren da basu fashe ba. A ranta tana hango yanda zata jeresu a cikin kwabet ɗinta.

Ta tsinci na tsinta ta bar na bari, ta ɗauko ta nufo hanyar gida.

"Lahhhh! Mai gauta har yanzu kana nan?"
Ta faɗa lokacin da ta zo giftawa wajenshi a ƙofar wani gida.

"Iy, wallahi. Mai gidan nan ne ya ce mu zo mu zubar mai da hyara, ɗan uwana ya shiga ciki zai ɗauko."

"Lahhhh! Aiko zan jirashi ko zan sam wasu kwalayen."

"Yanzu zai fito kuwa."

Suna tsaye sai ga Ɗayyabu da saurinshi.

"Abulle! Zo yanzu Alhaji ya dawo sallah yake tambayar ina kike na ce kin fita sai faɗa yake, me ya sa na barki ki ka fita."

"Allah sarki Baba Ɗayyabu! Yanzu fa zan dawo. So nake a fito da sharar gidan nan sai in ƙara wasu. Kagama wanda na samu a wancan jujin."
Ta faɗa tana ƙoƙarin buɗe ledar shirgin.

"Taho mu tafi, ki zubar da wannan sharar don ba yarda za a yi ki shiga da shi gida ba."

"Abunfa jeren ɗaki ne."

Ta faɗa tana zaro ido.

"Mu je, nan ai su basu amfani da shi. Ana gamawa da shi sai bola."

Ya faɗa lokacin da ya tasa ƙeyarta.

"Hu umm! Nikam ina so, zan ajiye a wajenka, gobe idan zan tafi sai in ɗau abuna. Har Sarai ma zan ɗibar ma wasu itama ta jera a ɗakinta tunda ta kusa aure itama."

"Oh! Mutanenmu akwai son jere. Har yanzu dai ba a barta ba?"

"Tana nan, ku ai nan sai dai ku aje ƙaton kwalba da kujeru muko cika ɗaki ake da jere mai kyau."

"Ci gaba ai aka samu."

Ta taɓe baki

"Amma dai anjima zaka barni na dawo na sake ɗiban wasu ko?"

Zaro ido ya yi,

"Rufamin asiri, so kike Alhaji ya sallame ni a aiki."

"A'a."

"To, ki haƙura da wanda kika samu."

Suna shiga ta ɓoye a cikin wani ɗan lungu da ke gefen ɗakin Ɗayyabu, ta nufi cikin gida.

Duk a falo ta samesu zaune kan kujera.

"A'a! Ɗiyata har kin fara gane gari ne kika fita yawo?"

Alhaji ya faɗa yana miƙo mata hannu.

Zama ta yi a ƙasa can nesa ta ce,

"Gajiya na yi da zaman shine na fita."

"Nan ai ɓata za
End Ads