zama hammanki? Babu hadin danga da garafuni kar in kara jin kince masa hamma" na saka kuka saboda zafin da kunnen yake min nace "na daina Inna" ta sake ni na fita da gudu gurin Ummah ina share hawaye na, ta dauke ni ta dora akan cinyarta ta bude min alawar tana rarrashina. Daga ranar ban kuma cewa Sadauki hamma ba shima kuma bai kuma cewa in gaya masa ba
Shekarar da aka saka ni primary Sadauki ya shiga secondary, dan haka a lokacin Baffa ya siya masa keke yake zuwa akai. Ni kuma Baffa ne da kansa yake kaini a motarsa tunda makarantar mu babu nisa kafin ya fita amma ranar nan sai na saka rigima nace ni a keken Sadauki zan ke tafiya, nan take Sadauki yace "Baffa ka barta, kaga hanya daya ne sai in ajiyeta in an taso kuma in biya in dauke ta" Inna tace "kaji mugunta, salon kake kayar da ita a hanya kullum? In banda mugunta ga motar ubanta sai ace ta hau keke? To ba zata hau din ba" na makale kafafa ina kakalo hawaye, Baffa ya tsaya yana kallon Inna saboda yaji zafin maganar ta amma saboda muna gurin sai kawai yace "bishi ku tafi, Allah ya kiyaye hanya" Ummah tace "ka bi a hankali, kar kaje kana wannan rawar kan naka ka jefa ta a kwata" ni kuwa sai tsalle da murna, ya dora ni a gaban sa ya saka na rike kan keken sannan ya taka keken muka tafi. Muna barin layin mu na saki kan keken na fara kokarin mikewa tsaye, ya rike ni da hannu daya yace "ki zauna Diyam, zaki fadi fa" na ture hannunsa "ka tsaya kaga abinda zamuyi, irin na titanic, nice rose kaine jack" na mike na bubbude hannayena, ai kuwa kafin yayi managa na zame zan fadi, garin rikeni shima ya biyo ni sai gamu a kasa a kan kwalta, guiwowina duk sun daddauje goshina ma haka. Na dage kuwa tun karfina na ringa zunduma ihu, yayi rarrashin duniyar nan naki inyi shiru, haka ya dauko ni da hannu daya ya jawo keken da daya hannun muka taho gida.
A bakin gate muka tarar da Baffa yana shirin fita. Yana ganin mu ya taho da saurin sa ya karbe ni a hannun Sadauki ya dora ni a saman mota yana duba ciwon da naji. Tun kafin Sadauki ya bada labarin abin da ya faru sai ga Inna ta jiyo kuka na ta fito da sauri tana cewa "ai dama sai da na fada, yaron nan babu komai a zuciyarsa sai zallah mugunta, gashi nan yaje ya jefar min da yarinyar ya cuce ni" Baffa ya juya kanta shima da nasa fadan sukayi tayi, basu san sanda Ummah ta fito ta dauke ni ta wankemin ciwon da naji ba ta chanza min kaya sai ji sukayi tace "baban Diyam ko zaka kaita chemist a duba ciwon sosai?" Baffa ya juyo yana kallonta yace "Allah yayi miki albarka Zainab" tayi murmushi tace "ameen, Nagode". Sannan ta cewa Sadauki "kaima sai ka bisu a duba hannunka" sai a lokacin duk muka lura cewa shima yaji ciwo a hannunsa yana ta jini, yayi saurin nuna jarumta ta hanyar cewa "babu komai" amma Baffa ya tilasta masa sai da ya bimu.
Na jima da wannan tabon a goshina, duk wanda ya tambaye ni sai ince "Sadauki ne ya kayar dani a keke".
"Diyam, ba zaki cigaba da cin abincin nan ba sai nazo ko?" Na daga kai ina kallon Inna da take zazzare min ido cike da barazana. Na debi shinkafa a chokali na kai bakina ina taunata da kyar saboda koshin da cikina yayi ji nake kamar zanyi amai. Na shawabe fuska "Inna wallahi na koshi, nasha tea, naci bread, naci kwai, bazan iya cin shinkafa ba kuma amai zanyi" tace "kiyi aman, sai ki zo ki cigaba da ci" na kalli kofa da sauri saboda motsin mutum dana gani, ta gefen labule na hango Sadauki sanye da uniform dinsa, muna hada ido yayi min alamar in taho da hannunsa, na ture abincin na sunkuci jakata zan fita Inna ta fizgoni ta dangwarar akan kujera tace "in kika fita daga dakin nan sai na yanke kafafuwanki" ta harari kofa tace "bakin munafuki, babu inda zakuje tare" ta kara dangwara min kwanon shinkafa a cinyata.
Muryar Baffa na jiyo a tsakar gida "kai kai kai, Sadauki wai baku tafi ba har yanzu? Ai kun makara, ina Diyam din?" Nayi saurin ajiye kwanon amma hararar da Inna ta jeho min yasa na dauka na cigaba da rikewa. Baffa ya leko yace "ke Diyam, ki fito ku tafi mana kin makarar dashi zaki sa a dake shi" Inna tayi charaf tace "ya tafi kawai kar a hukunta shi a makarantar su. Diyam bata gama karyawa ba" na ajiye kwanon nace "na gama Baffa, tun dazu na gama Inna ce ta hanani fitowa" na zagaya ta gefenta na fice daga dakin da sauri na rungume sadauki shi kuma ya dauke ni ya dora akan kekensa muka tafi.
Haka mukayi ta fama kullum ba fashi, kullum sai inna tayi ƙoƙarin hanani bin Sadauki ni kuma sai na nace na bishi. Shi zai kaini har class dinmu yaga na shiga sannan ya tafi tasa makarantar. A lokacin dana kara girma kuma sai ya daina dorani a keken sai dai mu tafi a kafa yana jan kekensa a hannu har sai ya kaini sannan shi kuma ya hau ya tafi tasa. Haka islamiyya ma tare za muje, in asma'u ta biyo ni sai in korata ince tabi yaran makotanmu. Sadauki shine yayana, shine abokina, shine kawata, shine abokin shawarata, duk da cewa a lokacin akwai yarinta sosai dan haka duk shawarar ta shirme ce, shima kuma tunda ba wani girmata yayi sosai ba haka zai bani amsar shiririta.
Duk kawayena, na boko dana islamiyya sun san Sadauki, wadda bata sanshi a fuska ba kuwa to tabbas tasan sunansa saboda da wahala in muna hira in iya hada sentence guda ba tare da sunan sadauki ya fito a ciki ba. Duk kuwa sanda wani a ajin mu ko ajin gaba damu yaci zalina ko na tsokani wani ya dake ni to tabbas sai jikinsa ya gaya masa in ya shiga hannun Sadauki, wannan yasa ake shayin tabani ko a yaran unguwa sai dai in na tsokani yaro yayi hakuri dan dole dan sun san cewa sadauki ƙashi daya ne dashi.
Bashi da surutu sam, he is a good listener rather than a talker, ko a gida in dai kaji yana hira to dani ne, ko da Baffa, amma ko Ummah basu cika zama suyi doguwar hira ba. Yana da zuciya da fada in an taba shi ko an taba ni, amma ni din ko daga min murya baya iyayi balle yayi min fada. Kuma duk zuciyar Sadauki, bai taba daga kai ya kalli Inna in tana gayawa Ummah magana ba, sai dai ka gani a fuskarsa cewa ransa ya baci amma ba zai mayar mata ba. Yana da kazar kazar sosai kuma baya zama guri daya, in har baya makaranta to yana gareji in kuma baya can to yana gida yana aiyuka, zai share gidan mu tas ya gyara wa Baffa dakinsa ya wanke masa mota. Watarana nace masa "Sadauki kai baka gajiya ne? Ka kwanta ka huta mana" Sai yace "wa kika taba gani yayi achieving wani abu a kwance? In kana son wani abu you have to work hard to earn it".
Ranar nan, a lokacin ina primary 5, ina da shekaru goma da yan watanni sadauki kuma yana sha shida. Anti Hafsa, wadda muke kira da Mama tazo gidan mu, suna ta hira da Inna ni kuma ina kwance sun dauka bacci nake yi naji Mama tace "ni Addah kullum sai inga kamar kara ramewa kike yi, har yanzu kin ƙi ki kwantar da hankalinki kiyi ƙiba kema" Inna tace "hmmm Hafsa ina hankalina zai kwanta ne bayan wannan mayyar ta sakani a gaba, ita da wannan baƙin dan nata sun hana zuciyata hutawa sam" Mama tayi dariya tana riƙe baki tace "kai Addah, daga ni har ke fa mun sani cewa bafa mayyar bace da gaske, muna sane muke takewa kawai dan mu bata mata rai amma da mayyar ce da ba tini ta cinye ki ba ko ta cinye yayanki? musamman tunda ita bata haihu anan gidan ba?" Inna tace "to ai yanzu gashi danta ya chinye kurwar Diyam ko? kamar yadda ita kuma ta chinye ta baban Diyam, na rasa yadda zanyi da yarinyar nan, nayi fadan nayi nasihar nayi dukan amma abun ya faskara, gashi da shegen naci kamar jinin mayu, bana son mu'amalar yarinyar nan da yaron nan wallahi kullum gani nake kamar zai cutar da ita, kullum in suna tare sai inyi ta fargaba" Mama ta sake dariya tace "bafa mayen bane kin sani kuma. Yara ne, ki barsu suyi wasansu mana, ki kwantar da hankalinki kiyi tayi mata addu'a" Inna tace "idan ba maye bane ta bangaren uwarsa waye yasan waye shi ta bangaren ubansa? Ni fa tunda matar nan tazo gidan nan da yaron nan ban taba jin ko da sau daya ta ambaci mahaifinsa ko wani dangin mahaifinsa ba, ban taba ganin an kaishi dangin ubansa hutu ba. Ni ba dan makota sun tabbatar mun an daura mata aure anan bayan layi ba da sai ince anya ba shege bane ba? To ko ma dai ba shegen bane ba akwai wani mummunan abun da suke boyewa a game da mahaifinsa. Shi kuma babansu ko na tambayeshi cewa yake ina ruwana? Wai ai Allah ma ya hana mutum ya shiga abinda babu ruwansa" Mama tace "to yanzu menene abin yi?" Inna tace "yanzu ni dai so nake ki tambayi baban Diyam tunda wannan satin zasuyi hutu dan Allah ya baki ita da Asma'u duk ki tafi dasu gurin ki suyi hutunsu a can kona samu zuciya ta ta huta kafin su dawo". Mama tace "au yanzu akan agolan kike so ki raba yara da gidan ubansu? To Allah ya sa ya bani din dan kinsan halin mijin naki ba wanda yake gane kansa sai zainabu abu, Allah yasa ma kar yace sai dai in hada har sadaukin in tafi dasu tare" ta fada tana tsokanar Inna, Inna tace "Allah ya kiyaye. Allah ya tsari gatari da saran shuka. Insha Allah ko kofar gidanki ba zai sani ba ballantana ya ga ciki". Ni dai ina kwance ina jinsu, amma sai naji duk raina ya baci saboda babu abinda na tsana irin a kaini wani gidan, saboda bana so a raba ni da Sadauki.
Bayan ta tafi da daddare ina dakin Ummah muna cin abinci a plate daya dani da ita da sadauki. Tana ta loda min nama a gabana wai inci inyi girma in kamo Sadauki. Shi kuma yana ta min dariyar yadda na dage bil hakki nake cin abinci wai kamo shi zanyi duk kuwa da cewa a lokacin ya kusan yin biyu na a girma tunda ni bani da garun jiki shi kuma girma ne dashi. Nace da Ummah "Ummah menene agola?" Tayi shiru tana kallona bata ce komai ba, na cigaba "Inna naji ita da Mama suna cewa wai Sadauki agola ne, sannan kuma maye ne" Inna ta ajiye chokalin hannunta, Sadauki ya kamo hannuna yace "Diyam, agola shine yaron da aka haifa sai iyayensa suka rabu sai uwarsa tayi wani auren ta tafi dashi, mijinta kuma ya rike shi kamar dansa. Kamar ni kenan yadda Baffa ya rike ni amma ba shine ya haife ni ba" nace "to kuma da gaske kai maye ne?" yayi dariya yace "sosai ma kuwa. Yanzu ma sai in cinye ki" ya fada yana yi min chakulkuli ni kuma ina kyalkyala dariya nace "wayyo na tuba kar ka chinye ni" hararar da Ummah ta zabga masa ne yasa ya sakeni muna cigaba da dariyar mu sannan Ummah ta kalle ni seriously tace "Diyam, idan kinji innar ki tana hira da wani, ko cikin yan uwanku ko baffanku, ki daina zuwa kina gaya min kinji? Nima kuma in kinji ina magana da wani kar kije ki gaya mata. Babu kyau kinji?" Na gyada kaina. Asma'u ta leko tace "addah ki zo inji Inna" Ummah ta yafito ta tace "zo Ma'u kici abinci" Asma'u ta makale kafada, Ummah ta dauko cinyar kaza tace "zo ki karba" a hankali Asma'u ta shigo ta tsaya daga nesa ta miko hannun. Ummah tayi charaf ta kamata ta dora akan cinyarta, tun Asma'u tana zillewa har sai gata dumu dumu tana lomar abinci. Muna cikin yi mata dariya nida Sadauki Inna ta shigo da saurinta, ta damki kunnena ta damki na Asma'u, a tare muka saki kara a haka ta fige mu har daki taja kofar ta ta saka sakata.
[1/11, 10:44 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Thirteen: My Saviour
Ranar da mukayi hutu a ranar Mama ta aiko babban danta yaya Mukhtar wanda kusan sa'an Sadauki ne yazo tare da drivern su ya dauke mu. Lokacin Sadauki bayanan sun tafi gidan yaya Ladi shida Ummah, haka na shirya raina duk babu dadi ga yaya Mukhtar yana tayi min jaraba wai in yi sauri ina bata masa lokaci ni kuma Allah Allah nake su Sadauki su dawo kafin mu tafi dan muyi sallama amma ina, haka ya tasa keyar mu yana ta rankwashi na muka shiga mota ina ta waigen ta inda Sadauki zai billo amma har muka sha kwana babu shi babu alamar sa.
Tun daga nan fa shikenan na turbune fuska kamar an aiko min da mutuwa. Da muka je gidan ma da kyar na gaishe da Mama, ta harare ni tace "ke kuma me akayi miki kike wannan bacin ran?" Nan take hawaye ya fara zubo min, na saka bayan hannu na ina gogewa nace "ni gidan mu zan koma" yaya Mukhtar ya dungure min kai yace "yi mana shiru anan, shagwababbiya kawai" ai kuwa nan take na bare baki "wayyo Allah na wayyo Sadauki" Mama ta tafa hannu tana salati "wayyo Sadauki? Dama abinda duk Adda take fada gaskiya ne? To zaki ci ubanki ne ke da sadaukin, babu inda zaki je muna nan dake a gidan nan".
Mama yayanta biyar, yaya Mukhtar ne babba sai yaya Abdullahi sannan Rumaisa wadda take sa'a ta kuma a lokacin kusan itace best friend dina bayan Sadauki sannan Muhsina sai Rufaida yar auta kuma sa'ar Asma'u.
Tunda muka je gidan, ga dai kayan wasa nan iri iri saboda babansu mai budi ne amma ni sam basa gabana, sai in ringa tunanin ina ma tare da Sadauki muka zo, nasan da zai so video game din su Abdullahi. Mama tayi fadan har ta gaji ta rabu dani tace "shegen taurin kai irin na uba" ni dai nayi tagumi ina kallonta. Da Rumaisa kadai muke dan yin hira, shima kuma duk kusan hirar sa ce dan ita din ma mutuniyarsa ce saboda ni, duk sanda taje gidan mu yana yi mata wasa sosai. Ranar nan muna backyard,su yaya Mukhtar suna ball mu kuma muna kallon su. Nayi tagumi sam hankali na baya tare dasu ban sani ba ashe hawaye ne suke bin kumatu na, kawai sai jin saukar ball nayi a goshina, na hantsila na fada bayan bench din da muke zaune, nan take sai ga jini yana zuba daga hancina. Rumaisa ta zagayo tana yi min sannu, na mike ina kallon yaya Mukhtar da yake yi min dariyar mugunta alamar shine ya buga min ball din yace "yanzu sai kiyi kukan mai dalili ai" murya can kasa nace "Allah ya isa na kuma sai na gayawa Sadauki" ai kuwa a guje ya bini har bayan Mama, ta rike shi tana tambayar abinda ya hada mu ga hancina da jini, ni dai ban tsaya bin ta kansu ba na shige daki na rufe kofa.
A daddafe mukayi sati biyu, a ranar da muka cika sati biyu kuwa sai ga Baffa ya sako Sadauki a gaban mota sunzo daukar mu. Ina fita maimakon in tafi gurin Baffa sai na wuce shi na tafi gurin sadauki. Mama ta fito ta gaishe da Baffa tana mita "hutun nasu fa bai kare ba, ni ai ba'a gaya min yau za'azo daukar su ba gashi ko dinkunan su ba'a karbo a gurin tailor ba" Baffa ya daga Asma'u da tazo gurinsa da gudu yace "in an gama dinkin a aika musu dashi gida".
Tun a mota na fara zayyanawa Sadauki duk irin cin zalin da yaya Mukhtar yayi min, tun daga dungemin kan da yayi har zuwa doka min ball da yayi a ka. Baice komai ba sai ya mulmula min goshin kamar yanzu akayi dukan. Bamu kuma tayar da maganar ba ni har na manta ma sai kawai rannan Mama ta aiko yaya Mukhtar ya kawo mana dunkunan da tayi mana ni da Asma'u. Sai da muka gama gwaggadawa muna ta murna ya fito Inna ta biyo bayansa tana bashi sakon godiya zuwa ga Mama, bai yi aune ba sai jin saukar ball yayi a goshinsa, ya hantsila ya fadi a gaban Inna jini yana bin hancinsa. Muka daga kai cike da mamaki sai ga Sadauki yana saukowa daga stairs din saman dakin Baffa, ya tsaya a gaban Mukhtar yace "gobe ma in Diyam ta kara zuwa gidan ku ka sake buga mata ball aka".
Inna tayi kukan kura ta riko shi, amma sai nayi sauri na rike hannunta har ya samu ya zame ya fice da gudu, ai kuwa sai tayo kaina, na ruga sai dakin Baffa na rufe kofa ina leken ta taga. Tayi ta banbamin fada tana debe wa Sadauki albarka "bakin mugu mai bakar zuciya. Allah ya isan sa, idan ya dake ta ina ruwanka? Dan uwanta ne, kai kuma fa? Marar asali" tayi tayi dai babu wanda ya kula ta, ta tashi Mukhtar ta bashi ruwa ya wanke fuskarsa amma sai ya kasa fita wai tsoro yake kar Sadauki ya kuma kamashi a waje. Haka ya koma daki har sai da na fito nace "kayi tafiyarka, babu abinda zaiyi maka ai ya ramamin". Kuma haka