mayar wa da Hardo yace gashi a je a nemar masa auren Zainabu in yaso sai ya tafi da ita birnin. Ai kuwa nan da nan dangi suka dauki maganar "Manu zai kwaso mana dangin mayu" Zainabu tana dandali akaje har can su Inna ta da gwoggo Fatima da kawayensu suka yi mata atule, tana zuwa gida ta tarar Inno ta saka yara sunje suna ta jifan gidan su wai mayu ne su sun chinye kurwar Manu. Bakin cikin wannan abu ya saka Yaya Ladi ta hada musu kayansu cikin dare suka bar garin ba tare da kowa ya sani ba. Wannan abu ya tayar da hankalin Baffa na, ya shiga damuwa sosai dan ance har rufe kansa yayi ya daina yiwa kowa magana ya daina cin abinci sai sumbatu da kiran sunan Zainabu, daga nan sai magana ta koma cewar tabbas Zainabu mayya ce dan gashi nan ta kama masa kurwa, akayi ta jike jiken magungunan mayu har dai daga baya ya warke. Sai daya warware sosai ya koma kamar babu abinda yake damunsa sannan ya karbi kudin da Hardo ya bashi ya taho kano neman kudi kamar sauran yan uwansa. Amma maimakon yabi sawun Mamman ya tafi gurin Alhaji Babba shima, sai yaki ya tafi cikin garin kano unguwar Yakasai ya sayi gida madaidaici ya boye sauran kudinsa yana kuma fita neman wani kudin. A hankali sai ya fahimci cewar yana da fasaha ta bangaren kanikanci dan sosai yake jin dadin aiki a karkashin wani bakanike, kuma cikin ikon Allah sai ya yi dace mutumin yana kokarin siyar da garejinsa dan haka Baffa ya dauko ajiyar kudinsa suka yiciki ya siyar masa, nan da nan ya fara wannan sana'a, ya debi yara sunayi shima yana yi da kansa kuma Allah ya saka masa albarka nan take guri ya bunkasa. Ya cigaba da tara yan kudadensa ya hada lefensa yayi komai ba tare da kowa ya sani ba sannan ya koma gida yana neman azo a nema masa aure ya samu mata a kano, nan take Hardo ya aiko aka nemi aure anan bayan layin da gidan sa yake, aka bayar akayi komi sannan matan su Alhaji Babba tare da kanwar Inno da sauran yan'uwa da suka taho daga Kollere suka zo kawo kaya amma suna zuwa sai suka tarar da yaya Ladi a matsayin uwar amarya. Ashe bayan tahowar su sai da Baffa ya yi ciku cikun da ya samu labarin inda suka taho kuma ya biyo su ya sayi gida a kusa da inda suke saboda ya zauna kusa da Zainabu sannan kuma ya turo aka nemar masa aurenta a gurin sabon marikin ta wanda aikatau ne yaya Ladi take yi a wajensa shi kuma ya rike Zainabu kamar ya har yake shirin yi mata aure.
Ai kuwa nan take rigima ta balle, mutanen nan da suka zo daga Kollere suka karewa yaya Ladi tas kamar zasu cinyeta danya, ita dai ta zauna tana ta kukan takaici dan sam Zainabu bata gaya mata gaskiyar waye manemin nata ba dan da ta sani da sam ba zata bari ba balle ayi mata wannan cin mutuncin a gaban jama'a. Babu irin sunan da basu kira yaya Ladi dashi ba, wannan ya saka suma mutanen gidan suka tashi suka tare wa yaya Ladi suka yi wa yanuwanmu korar kare aka watso musu kayansu waje. Wannan ya kara tunzura su, suna zuwa Kollere suka bawa Inno da Hardo labarin abinda manu ya jawo musu a take Hardo ya kirawo Liman yace a daura auren Baffa na da Inna ta wadda duk dangi sun san irin kaunar da take gwadawa manu amma ko kallo bata ishe shi ba duk kuwa da irin baiwar kyawu da Allah yayi mata, dan ko kusa ba za'a haɗa inna da Zainabu ba indai ta gurin kyau ne.
A bangaren Zainabu kuwa ana watsewa daga gurin karbar kayan da ba'ayi ba mai rikonta ya kira yaya Ladi ya tambaye ta ita kuma ta bashi labarin duk abinda ya faru wanda yayi sanadin barin su rugar su, a take yayi mata alkawarin zai samo wa zainabu mijin da manu ba zai taba iya zama kamarsa ba. Haka kuwa akayi sati na zagayowa aka daura auren zainabu aka sakata a mota aka tafi da ita gidan mijinta akan idon Manu.
Wannan kenan....
Tun muna yara labari ya iske mu daga gurin makota na irin wahalar da Inna tasha a hannun Baffa saboda kiyayyar da yake yi mata da kuma bakin cikin raba shi da masoyiyarsa da akayi. Wannan ya saka sana'arsa ma taja baya sosai, yana yin samun kudinsa yaja baya sosai amma sam ba ya taba zuwa gurin Alhaji Babba neman taimako sai dai idan shine yazo gidan yaga halin da suke ciki ya taimaka musu. A haka har shekaru suka ja amma babu haihuwa babu labarin ta, ana cikin haka ne kuma Allah yayi wa Inno rasuwa, wannan yasa Alhaji Babba yaje Kollere ya tattago su Yakumbo Amina da goggo Fatima ya taho dasu gidansa a kano, daga nan kuma duk yayi musu aure anan kanon, a shekarar da Inno ta rasu ne kuma Baffa ya sake sabon aure wanda shi kadai yaje ya nemi abinsa tare da taimakon kanin Hardo da suke dasawa sosai, sai bayan komai ya kankama sannan sauran yanuwa suka sani kuma suka nuna rashin jin dadinsu saboda suna taya Inna ta kishi, amma basu kuma sallama auren ba sai da aka kawo amarya suka bude fuskarta suka ga Zainabu.
Inna ta tayi kukan bakin ciki kamar ranta zai fita, ta hada kayanta tayi yaji zuwa gidan Alhaji Babba shi kuma yazo har gaban Zainabu yace da Baffa "mu yanuwanka kaf babu mu babu wannan matar daka aura, babu mu babu duk wani abinda ya shafe ta" amma Baffa ko a jikinsa. Babban abinda ya kara dagawa yan'uwan Baffa hankali shine dan jaririn da Zainabu tazo dashi a hannunta wanda ko yaye shi bata kai gayi ba. Sunansa Aliyu.
Bayan komai ya lafa zama ya cigaba da gudana cikin rashin jin dadi a gidan mu, Baffa yana iyakacin kokarinsa gurin adalci amma Inna gabaki daya ta burkice, ta riga ta sakawa ranta cewa Baffa yafi son Zainabu a kanta dan haka komai sai take ganin kamar zaluntarta yake yi, ko magana sukayi kasa kasa shida Zainabu sai taga kamar gulmarta suke yi, sannan ga rashin haihuwa, dadin dadawa ga dan da Zainabu tazo dashi wanda Baffa ya dauki son duniya ya dora akansa. A bangaren Zainabu kuma, let me tell you about Zainabu, tunda nake a duniya ban taba ganin mutum mai hakuri irin ta ba, irin mutanen nan ne da ko zaka zuba musu kashi aka ba zasu kula kaba sai dai su karkade maka wanda ya taba jikin ka. Dan zan iya cewa idan da akwai hakkin da Inna take dauke dashi a kanta to hakkin Zainabu ne.
Let me tell you about Aliyu. Zuwansu gidan mu Baffa ya chanza masa suna saboda sunan Hardo ne dashi ya ke ce masa Sadauki, Sadauki tun yana jariri kakkarfa ne na gaske dan karfin sa ne ma ya saka Baffa ya saka masa Sadauki. Baki ne, dan kusan kullum ba'ar da Inna take masa kenan "Baƙin munafiki" ko "baƙi mai bakar zuciya". Yana da godon hanci da nannadadden gashi irin na fulani, bayan wadanda kuma bai dauko komai na Umma (Zainabu) ba.
Shekaru suka sake turawa, akayi haife haife da yawa, musamman gidan Alhaji Babba wanda yayi ta aure aure on his quest for samun yaya maza amma in banda second born dinsa yaya Kabir bai kuma samun namiji ba. Goggo na da yakumbo na ma da akayi musu aure daga baya duk suma duk sun haihu, wannan ya kara daga hankalin Inna. Cikin ikon Allah Sadauki yana shekara shidda a duniya Inna ta samu cikina, amma hatta shi kansa baffa bata bari yasan da cikin ba saboda tana ganin kamar Ummah zata cinye abinda yake cikin nata. Sai da ciki ya fito sannan aka gani, Baffa kamar zai zuba ruwa a kasa ya sha saboda murna, yana murna Ummah tana taya shi.
Baffa ya bani labarin cewa ranar haihuwa ta, shi, Ummah da Sadauki ne suka kai Inna asibiti a motar Baffa. Suka zauna suka jira, Ummah tana ta jerawa Inna addu'ar samun saukin nakuda har Allah ya sauke ta lafiya. A lokacin da aka fito dani a zani aka bawa Baffa shi kansa ba zai misalta irin farin cikin da ya samu kansa a ciki ba, ya karbe ni yana nuna wa Ummah wadda take ta goge hawayen taya Baffa murna. Sadauki yazo ya bude fuskata yana kallona, ya shafa fuska ta yana sannan ya gwada hannunsa a jikin fuskar yana ganin banbancin kalar fatar mu, yayi dariya yace "Baffa wannan babyn kyakykyawa ce" Baffa yace "kanwarka ce sadauki. Sunan ta Haleematus Sadiya" Ummah tace "Allah ya raya mana mai sunan Inno" Sadauki yace "to Baffa mai za'ake ce mata?" Baffa ya shafa kansa yace "matarka ce ai, kai Hardo ita Inno, sai ka zaba mata suna da kanka" Sadauki ya yi shiru yana kallon fuska ta yace "Diyam. Diyam zamu ke ce mata Baffa" Ummah tayi dariya tace "to Allah yasa ta zamo mana maganin kishin ruwa" Baffa shima yana dariya yace "ameen". Ummah ta karbe ni saboda Baffa yaje siyan magungunan da aka rubuta, yana tafiya su goggo Fatima suka zo, da sauri yakumbo ta karbe ni daga hannun Ummah tana tofe ni da adduoi, sannan ta juya gurin Ummah tace "kurwarta kur wallahi. Wannan yarinyar tafi karfinki" daga nan suka juya sunayi wa juna barka tare da yaba kyawuna ba tare da sun lura da Sadauki daya hade rai yana ta zabga musu harara.
[1/9, 10:09 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤ DIYAM ❤
By
Maman Maama
Episode Eleven: Family
Daga asibiti gida suka taho gaba-daya. Suna zuwa Alhaji babba da kawu Mamman suka zo, Kawu Mamman yace "zamu tafi da Amina can gidan Alhaji Babba ta zauna tayi wanka a can" Alhaji babba ya kara da cewa "zata zauna a can sai yarinya tayi kwari, daga nan asamu a basu magungunan mayu da kambun baka saboda rigakafi" Baffa dai bai ce komai ba, Ummah kuma ta sunkuyar da kanta tana share hawayenta dan gudun kar Baffa ya gani ransa ya kara baci.
Daga zuwa wanka sai da nayi wata hudu a duniya kafin mu dawo gida. Inna ta gaya min cewa a cikin watanni hudun nan duk juma'a sai Baffa ya saka Ummah ta shirya ita da Sadauki sun taho dan su ganni amma ko da sau daya ba'a taba barinsu sun wuce ko da gate din gidan ba. Kuma ko sau daya bata taba gaya wa Baffa cewa ba a barinsu su shiga ba. Sai ranar nan ya dawo daga garage dinsa ya samu Sadauki yana ta kuka shi wajen kanwarsa zaije sai Baffa ya tambaye shi "ba jiya kaje ka ganta ba?" Sadauki ya girgiza kai yace "ai ba'a barmu mun shiga ba, kullum in munje koro mu ake yi ace Alhaji Babba yace kar a barmu mu shiga" to jin haka ne fa sai Baffa ya tafi gidan Alhaji Babba ya samu uwargidansa Hajiya Babba yace "wannan idan auren kuke da niyyar rabawa sai ku fada min in aiko mata takardarta, idan kuma kuna son acigaba da auren to lallai a mayar min da iyalina gidana" jin haka yasa Inna babu shiri ta fara harhada mana kayan mu dan tasan halin Baffa.
Yadda tsarin gidan mu yake shine, ta garage ake shigowa daga nan sai dan karamin fili mai bishiyar umbrella da flowers a sides, sai bandaki a gurin. Daga nan zaka shiga karamar kofa zuwa tsakar gida. A tsakar gida kana shiga kofar palon Inna ne a farko, babbab palo ne da dakuna guda biyu suna facing juna. Dakin Baffa kofar sa tana kallon palon Inna, an yi stairs a kofar dakin Baffa da niyyar yin dakuna a saman dakunan sa, amma kuma ba'a samu damar karasawa ba. Dakunan umma kuma suna daga can ciki saboda daga baya aka sayi fili akayi su aka shigo dasu, suma kuma exactly tsarin na Inna ne. Sai kitchen da toilet a tsakar gida.
Ina so ka fahimci wani abu guda daya. Allah ya dorawa Ummah sona kamar yadda take son mahaifina, soyayya ta gaskiya marar algus a ciki. Tun da muka koma gida sai ya zamana koda yaushe ina gurinta, in dai har Inna zata ajiyeni to kuwa Ummah zata daukeni in ina hannun Inna ne dai ba zata iya cewa ta bata ni ba. Wannan yasa sau da yawa Inna ko aiki zatayi sai ta goya ni tace "bazan ajiyeki ba kar waccan mayyar ta dauka". Hausawa su kance mai da wawa, amma wannan baiyi aiki akan Inna ba, ita idonta ya rufe akan kishin Zainabu.
Sadauki har dakin Inna yake biyo ni, Inna ta kore shi amma yaki tafiya in ta hankada shi sai ya zauna a bakin kofa yayi ta kuka shi a bashi Diyam dinsa. Ni kuma tunsanda na fara gane mutane babu wanda nake murnar ganinsa irin Sadauki. Dana fara rarrafe kuwa daga na tashi zan tsallake Inna tana bacci in tafi dakin Ummah ita kuma ta dauke ni ta bani abinci tayi min wanka da kwalliya ta gyara min dogon gashina ta goya ni, Ummah har kaya tasiya min ta ajiye a dakinta saboda in tayi min wanka ta saka min tunda Inna ba zata bata ba. Ummah macece mai tsafta sosai da kwalliya.
Lokacin dana fara magana kalmar dana fara iyawa itace "Sadauki", sadauki ya bani labarin cewa ban ma iya fadi sosai ba dan "sholoki" nake cewa, shi kuma sai ya sakani a gaba yayi da dora min kamar karatu, "ki ce Sadauki" ni kuma sai ince "Sholoki" a haka a haka har na iya, ranar dana fadi sunansa dai dai yaje ya dauko bankinsa da yake taron kudi a kasan gadon Ummah ya fasa ya tafi bakin asibitin Murtala ya sayo min yar tsanar roba ya kawo min a matsayin gift. Na karba ina murna, yace "to wanne suna zaki saka mata?" Nace "Shubeya" (Subay'a) sunan wata jaririya da aka haifa a makotanmu a lokacin. Tun daga ranar kullum ina rike da shubeya ta, hatta bacci tare da ita nake yi har nayi wayo.
Akwai ranar da bazan manta ba duk da kankantata. Ina wasa da Shubeya a tsakar gida Ummah kuma tana wanki Inna tana kitchen tana girki. Wata yarinyar makota ta shigo tace min "Diyam wai babyn waye wannan?" Ta nuna Shubeya, nace "yata ce, yata ce ni da mijina Sadauki". Ai kuwa sai ga Inna da saurinta ta fito daga kitchen tace min "me kika ce Diyam?" Na sake maimaita mata tunda ni a lokacin bansan ma ma'anar kalmar miji ba, nan take inna ta ciro bulala a bishiyar tsakar gidan mu ta daga skirt dina ta ringa tsula min a kafafuwana ina ihu tana cewa "zaki kara cewa Sadauki mijinki?" Ummah ta ajiye wankin hannunta ta rugo da gudu takwace ni daga hannun Inna ta shige dani dakinta ta rufe kofa. Inna ta ringa bugun kofar amma taki budewa sai ma dauka na da tayi ta kaini toilet ta wanke min kafafuna da suka tashi suka yi rudu rudu, ta shafa min vaseline ta kwantar dani akan gadonta tare da Shubeya ta.
A waje kuma bayan Inna ta gaji da bugun kofa sai ta dauki waya ta kira gidan Alhaji Babba cewa ga Ummah nan ta dauke ni ta shige dani daki ta rufe kofa ita bata san me take yi min ba. Nan da nan sai ga gwoggona da nake cewa Aunty Fatima wadda akayi dace taje gidan a lokacin, da Adda Zubaida babbar 'yar Alhaji babba wadda a lokacin take zawarci, da wadansu da suke yammata a lokacin suka zo gidan mu suka yi ta bugun kofar Ummah, ai kuwa tana budewa suka rufe ta da duka Inna kuma ta shige ciki ta dauko ni tana duba lafiya ta, a lokacin Baffa ya shigo rike da hannun Sadauki daya dauko daga makaranta, yana shigowa yaga abinda ya faru ya nemi ba'asi kowa ya bashi side din story dinsa, a take zuciya ta ciyo shi ya rubuta wa Inna takarda saki daya, ya kuma karbe ni daga hannun ta ya mika wa Ummah ni.
Wannan yana daya daga cikin abubuwan da har yau Inna ta kasa mantawa a rayuwar gidan mu. A lokacin sai da Hardo da kansa yazo har kano ya sasanta maganar sannan Baffa ya mayar da ita amma da sharadin kar wanda ya kuma daga hannu ya dakar masa mata. Bayan wannan Inna ta rage tsangwamar Ummah sosai sai dai ba za'a taba kiran zamansu da zaman lafiya ba.
Shekara ta biyar a duniya Inna ta haifi kanwata, Asma'u, tun daga nan kuma shikenan babu wata haihuwar. Sadauki bashi da kokari a makaranta, dan yana daga yan karshe karshe a position a ajinsu, amma kuma Allah ya bashi fasaha a kan kere-ƙere. Wannan yasa kullum daga ya dawo daga school zai shirya yabi Baffa zuwa gareji, kafin wani lokaci Sadauki yasan kan mota sosai dan zai iya kunce inji ya mayar ya hada, duk minor gyaran da aka kawo wa Baffa sadauki ne yake yi kuma ya gyaru sosai. Ina iya tuna lokacin da Baffa yake cewa "Sadauki da ace ni mai kudi ne da kasar waje zan kaika kayi karatu, tunda karatun kasarmu duk theory ne kai kuma kafi gane practical".
Ranar nan ya dawo daga makaranta na tafi da guduna na rungume shi ina masa oyoyo, ya ciro alawar da ya siyo min da kudin taran sa, wadda yasan in dai ya shigo babu ita to sai nayi masa rigima, na karba nace "Nagode Sadauki" ya kamo kunnena yace "daga yau hamma Sadauki suna na" na gyada kai ina murza kunnen da yaja, Ummah ta harare shi tace "sai son girma kamar gwambo, ga kuma mugunta" ni dai na wuce dakin Inna da sauri na kai mata sweet din nace ta bude min. Ta karba tana tambayata "waye ya baki?" Nace "hamma Sadauki ne" ta kamo kunnena da sauri tana daga muryarta yadda Ummah zata ji daga waje tace "hamma wa? A gidan uban wa ya