x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 50 - DIYAM

  • 147001 words
  • 150000 words
  • Out of 175324 words

Category: Love Stories

Views 267

02 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
wancan auren" a can kasan makogwaron sa yace "more of what?" Tace "everything" yace "like?" Tace "caring" yace "and?" Tace "tunda nace everything ai ina nufin everything ko? Sai na lissafa maka?" Yayi dariya yace "so nake ki fada da bakin ki, yadda in lokacin yayi zan tuna miki cewa ke nema da kanki" ta bata rai tace "abinda kake nufi fa ni ba shi nake nufi ba, we are not talking about the same thing" yace "zaki sha kwana ko? To gaya min ni abinda nake nufi" tace "ni ban san me kake nufi ba fa" yace "to in baki sani ba ya akayi kika san ba abu daya muke nufi ni da ke ba?" Tayi rolling eyes dinta tace "good night Aliyu" yace "ashe tsoro na kike ji tunda zaki gudu, ki tsaya mana" tace "ba tsoro nake ji ba bacci nake ji, ina da school gobe" yace "hmmm okay, Allah ya tashe mu lafiya, but I will still demand to know that 'everything' da kika fada, ko ba gobe ba ko watarana I will get the words out of you".

Suna gama wayar Sadauki ya ajiye phone din yana kallonta, sai kuma yayi murmushi sannan ya lumshe idonsa ya kwantar da kansa a bayan kujerar office dinsa yana dan jujjuya wa a hankali. Sai kuma ya mike zaune sosai ya jawo system dinsa yana duba calendar, yasan ranar dasu Diyam zasu fara exams ya kuma san ranar da zasu gama sannan yasan ranar da zasu koma school, sai ya duba dates din da suke tsakanin hutunsu da komawar su school yana neman weekend mai perfect date for their wedding, sai idonsa ya sauka akan date din, his birthday. Ya dafe kansa yana fadada murmushin sa. He is going to have a perfect birthday gift for his 30th birthday.

Mama ta kira shi kamar yadda tace zatayi, ta kuma maimaita masa abinda already Diyam ta gaya masa sai ta tambaye shi shima akan date, sai ya maimaita mata abinda Diyam tace mata "duk sanda aka saka dai-dai ne Mama" ta tabe baki tace "ai shikenan, idan manyan sunzo ayi magana dasu".

Washegari ya hau jirgi daga kano zuwa Maiduguri ya samu Alhaji Babagana wanda yake kani ne a gurin Papa kuma shine dai wanda shekaru goma da suka wuce yazo ya nema masa auren Diyam aka hana shi. Yanzu ma shi zai sake dawowa tare da Alhaji Bukar su karasa abinda suka fara. Nan take shi kuma ya kira Papa ya gaya masa sannan ya bashi izinin ya dauki sauran yan'uwa suje su hadu da Alhaji Bukar suyi duk abinda ya dace. Sai da suka gama wayar sannan Sadauki ya gaya masa date din da ya keso a saka. Sai shi kuma ya tambaye shi "kana ganin ba za'a samu matsala ba? Kar azo ayi irin ta wancan karon" Sadauki yace "babu matsala in sha Allah, tunda wannan karon ai sune da kansu suka nemi azo din".

Daga Maiduguri sai yayi branching a Yobe yaje damagun gurin yaya ladi wadda take zaune a gidan cousin dinta da Sadauki ya gyara musu shi tas ya zuba musu kayayyakin more rayuwa kuma ya daukar musu yan aikin da zasu ke kula dasu. Bayan sun gaisa ta gama loda masa tuwo da fura sai ya sanar mata da duk abinda ake ciki, yana maganar yana murmushi. Sai ta rike baki tace "Diyam din dai Aliyu?" Ya dago kai yana kallon ta yace "Diyam din dai. Ko kina kishi ne?" Ta tabe baki tace "ni dai daka hakura da Diyam din nan da nafi jin dadi, kazo ga yammata nan birjik ka zaba ka darje in ma hudu kake so a tsakanin yau da gobe sai a samo maka su amma kai ka nace sai yarinyar da yan'uwanta suka wulakanta ka, suka wulakanta mahaifiyar ka, suka wulakanta ni kakarka?" Ya daga kafada yace "ita nake so, ita ma kuma tana sona kuma in anyi auren da ita zan zauna bada yan'uwanta ba" Hajiya Dije, cousin din Yaya Ladi tace "amma duk da haka Aliyu, ko bayan anyi auren ne ya kamata ka samu budurwa ka kara da ita" sai ya mike tsaye yana daukan hularsa a hannu fuskarsa da murmushi yace "kar ku damu, bayan anyi auren da sayi daya zan dawo nan sai in aure ku duk ku biyun a rana daya" yaya ladi ta tabe baki dan tasan shirishitar da maganar yake yi, tace "to ai shikenan, uwarka ma haka nayi ta fama har sai dana hakura" ya durkusa a gabanta yace "kisa mana albarka kawai ke dai. Kiyi mana fatan alheri" ta dafa kansa tace "Allah ya sanya alkhairi a ciki, Allah ya baku zaman lafiya ya kuma kade duk wata fitina da zata taso sannan ya baku zuri'a mai albarka" yayi kyakykyawan murmushi yace "yanzu kika yi magana. Karki manta, ke ce uwargida ran gida a gurina, ita kuma amarya ta sannan kuma zuciyata".

A gidan Baffa aka sauki bakin da suka zo daga Maiduguri, aka bude musu part din Baffa inda Inna ta zauna da, Mama tazo da yammatan ta suka hadu suka shirya musu abinci mai rai da lafiya wanda duk da kasancewar su masu hannu da shuni amma sun tabbatar cewa an karrama su. Sannan Alhaji Babba yazo, Kawu Isa ma yazo sannan abban su Rumaisa shima yazo suka zauna suna ta hira ta wasan fulani da barebari suna ta dariya kamar sun saba. Sai a lokacin ne su Alhaji Babba suka san asalin waye mahaifin Sadauki, jin hakan ba karamin girgiza su yayi ba, ba kuma karamin nadama ya saka musu ba. Lallai rashin sani yafi dare duhu, wanne irin gorin arziki ne basu yi wa Sadauki ba? Wanne irin wulakanci ne basu yi masa ba shida mahaifiyar sa?

Sai da suka nutsa sannan Alhaji Bukar ya gabatar musu da dalilin zuwan su cewa suna nemawa dansu Aliyu Umar Abatcha auren yarsu Halima Usman Kollere, sai Kawu Isa ya gyara masa yace "dan mu dai. Sadauki ai dan mu ne kamar yadda Halima take yar mu. Ku kawai zuwa kuka yi dan ku tunatar damu akan abinda ya kamata muyi tuntuni amma kuma son zuciya da kuma rabo ya hanamu aikatawa sai yanzu da Allah ya sake dawo mana da damar" Alhaji Babba yace "mun bawa Aliyu auren Halima. Duk sanda kuka shirya sai ku dawo a saka rana" Alhaji Babagana ya jawo yar jakar daya shigo da ita ya ajiye a gaban Alhaji Babba yace "a shirye muka zo. Kuma munzo da ranar mu amincewar ku kawai muke nema" sai ya fadi ranar da Sadauki ya gaya masa, yace "lokacin yarinyar tana hutu" babu musu kowa ya amince da hakan, sannan suka sake gaisawa yanzu kuma a matsayin surukai. Sai kuma Alhaji Babba ya roki gafarar su a bisa abinda yayi musu wancan zuwan. Su kuma suka yafe cikin sigar tsokana dan mayar da abin wasa.

Bayan tafiyar bakin ne aka kirawo Inna da Mama da suke cikin gida suka zo akayi musu bayanin abinda ya faru da kuma ranar da aka tsayar. Alhaji Babba ya mikawa Mama jakar da aka bashi yace "ga abinda suka kawo" Mama ta bude sai ta dago kai tana girgiza wa tace "wannan kudin sunyi yawa, albarkar aure ake bukata ai bawai yawan kudi ba" Kawu Isa yace "nima dai naso ince haka, amma sai naga tunda bani suka mikawa ba gwara inyi shiru" Inna tace "ai duk daya ne babu bambanci, suma kuma nasan sun mika masa ne saboda shine Babba" Abban Rumaisa ya kalli Alhaji Babba yaga yadda yayi da fuskar abin tausayi kamar wanda yayi laifi sai yace "tunda an riga an karba ai ina ganin shikenan. Albarka kuma sai muyi ta saka musu ita mu kuma tayi musu addu'a shikenan". Sai Kawu Isa ya tashi yayi musu sallama tare da fatan alkhairi sannan ya tafi.

Ana isar da sako gurin Sadauki ya turawa Diyam message

"save the date. 25th August"
[3/20, 10:04 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: DIYAM
By
Maman Maama
Episode Sixty Nine: Mrs Abatcha
Assalamu alaikum
Naga votes dinku, kuma kamar yadda nayi tsammani kusan 99% sun goyi bayan a fito da Saghir. Inda aka samu rabuwar kai shine akan lokacin da za'a fito dashi, kafin biki ko bayan biki. I followed the majority kamar yadda nayi alkawari amma na rubuta in such a way that suma minority din zasu samu satisfaction.
Thank you.
We are almost done insha Allah.
Ta lumshe idonta tare da jingina kanta da jikin kujerar da take zaune akai tana murmushi mai sauti wanda yafi kama da dariya. Murjanatu da take zaune kusa da ita tana cin abinci ta dakata da abinda takeyi tana kallon Diyam sai ta bude ido tace "what? Menene ya faru kike dariya ke kadai?" Diyam ta daina dariyar da take yi amma bata ce komai ba sai Murjanatu ta warce wayar daga hannunta ta karanta message din nan take ta mike tana tsalle tana kiran Judith, Judith tana fitowa tayi mata bayanin cewa auren Diyam za'ayi sai itama ta kama murna suna rawa a tsakiyar palon, Diyam tana zaune tana kallon su a ranta tana jin kamar ta tashi suyi rawar tare amma sai ta hana kanta.
Sai da suka gama tsallen murnar su sannan Murjanatu ta zauna tana haki ta jawo phone dinta, Diyam ta bude ido tace "hey, me zakiyi?" Murjanatu tace "su Adama zan gaya wa" Diyam tace "ai za'a gaya musu a can, ki barsu kawai saji a can" Murjanatu tace "yanzu su Adaman ma kunyarsu kike ji? To Papa zan gayawa ma, in ce masa gaki nan kin saka waya a gaba kina ta dariya kin kasa rufe baki kina murna zaki auri dansa" nan da nan Diyam ta mike ta murde hannun Murjanatu ta karbe wayarta ta tafi daki tana cewa "nayi seizing phone dinki, bazan baki ba sai anyi hutu".
Tana shiga dakin Murjanatu ta dauki tata phone din ta kira Sa'adatu wadda a lokacin suna tare da Falmata sai suka kira Adama da taje school a lokacin suka hada conference call sannan Murjanatu ta basu labarin abinda yake faruwa. Duk sunyi murna sosai musamman da yake wannan shine biki na farko da za'ayi a gidan su. Sa'adatu tace "oh su yaya Aliyu za'ayi aure, I wonder ta yaya suke magana da Diyam din da wannan turbunanniyar fuskar tasa" Murjanatu tayi dariya tace "wallahi in kunga dariyar da yakeyi mata ko, zaku dauka chanja shi akayi gaba ki dayan sa" sun jima suna hirarrakin su sannan suka lissafa kwanakin da ya rage kafin bikin sai kuma suka fara tsare-tsaren events din da zasu shirya. Sai da suka gama Murjanatu tace "Allah yasa ya yarda, zamu iya gama shirya komai yace shi ba za'a yi wa matarsa kwalliya a shiga da ita cikin mutane ba, kishi ne dashi kamar me".
Sai da suka gama Murjanatu ta dauki wayar ta kai wa Diyam har daki ta mika mata tace "thank you for letting me use your phone" sai ta ajiye ta fita da sauri tana dariya. Diyam ta dauki phone din ta duba numbers din da Murjanatu ta kira, sai tayi murmushi tana mamakin zumunci irin na wadannan mutanen, sam basa nunawa Aliyu yan ubanci ko dan akwai wayewa sosai a tare da su?
Daga gida ma Mama ta kira Diyam ta yi mata bayanin duk halin da ake ciki, sai kuma ta umarce ta data kira Rumaisa suyi shirye shiryen abinda zasu yi kafin tazo gidan.
Sanda sukayi waya da Sadauki kuma sai yace mata "guess what? Na sayi fili zan yi gini" tayi dariya tana rike baki yace "au, dariya ma na baki ko?" Tace "I tot zaka sayi gida ne kawai, ko kuma ma ka riga ka siya" yace "hmmm, nima na dauka zan siya gidan ne, but then an opportunity presents itself to me, na saka a nemo min gida sai dillalin ya gaya min akwai wani fili ma in ina so, sai na bincika na gano ashe fili na ne, filin mune Diyam da Baffa ya siya mana zamu gina gidan mu, all these years ba'a gina shiba har sai daya dawo hannun mu. And now I hired wani construction company da aka bani labarin sa a Abuja 'Moon Construction Company' sunce zasu gama komai within a month. Ina ganin ai yayi ko? Tunda muna da kusan watanni biyu nan gaba"
Diyam taji dadi a ranta tana jinjina hikima irin ta ubangiji. Tace "yayi sosai ma" yace "zasu turo min samples na building plans dinsu, sai mu zaba ni dake sannan sai su fara" sun jima suna hirarrakin su sannan suka yi sallama suka ajiye wayar. Sai ya cigaba da zama hannunsa rike da phone din yana kallon hotonsu shi da ita da yake kan screen din wayar, a Oxford suka dauka sanda yaje, selfie ne yayi musu suna tsaye a gaban motarta shi yana murmushi ita kuma ta turo baki tana hararar sa. Yayi murmushi saboda ya manta me yayi mata a lokacin take hararar sa kuma yasan itama kanta in da zai tambayeta ta manta. Ya saka babban dan yatsansa a hankali ya shafa fuskarta a jikin hoton sai kuma yayi sliding din hoton sama ya nemo number din one of his lawyers ya kira "barrister akwai maganar da nake so zamu yi Please, lets meet in my office in an jima. Okay, thank you".
Diyam har ta fara sabawa da rashin Bassam a school, duk da dai kullum in ta kalli empty kujerar kusa da ita sai taji babu dadi. Sai a lokacin tayi nadamar rashin exchange din numbers da basu yi ba at least da yanzu ta kira shi tasan halin da yake ciki. And then one day, suna gab da fara exams din su sai gashi ya shigo ana tsakiyar lecture. Yayi ignoring lecturer din da yake masa kallon yazo late yana distracting din class sai ya wuce empty seat din kusa da ita ya zauna ya juyo yayi mata murmushi sannan suka mayar da hankalinsu kan lecture din da ake yi. Sai da aka gama lecturer din ya fita sannan Diyam tace masa "welcome back prince Sadiq" ya juyo yana kallon ta da mamaki dan shi dai ba zai iya tuna sanda ya gaya mata daga inda yake ba, yace "Prince? Yaushe na gaya miki haka?" Tace "ba ka gaya min ba, Aliyu told me" yace "shi din ya akayi ya sani?" Tace "okay, ba direct ya gaya min ba, kace ka taba ganinsa a gurin daurin auren yayanka a abuja last year, shi kuma yace daurin auren da yaje abuja last year na jikan sarkin Abuja ne, so, in yayanka ya kasance jikan sarki to kuwa kaima jikan sarkin ne, ko ba haka ne ba?" Ya dauke kai yace "an baki A1 a fannin bincike" tayi dariya tace "tell me everything. Dame da me ya faru? I hope komai ya warware yanzu and you are back to your old self again"
Yace "well, bayan mun rabu naje gurin aunty Hafsat but she refused to see me. Nayi iyakacin kokari na amma abin yaci tura but sai na ci sa'a uncle Zayed ya dawo, dama yayi tafiya ne lokacin da muka samu sabani dan haka bai ma san abinda ya faru ba, I explained everything to him kuma na dauki laifina sai ya saka ni a gaba muka tafi Nigeria tare" ya danyi dariya yace "ba karamin taimako na Allah yayi ba da muka je tare dashi, da maybe in Daddy ya fara jibgata sai na kwanta a asibiti" Diyam tayi dariya tace "anya kuwa bakayi girma da duka ba?" Yace "not to my Daddy, ba ruwansa da girma na wallahi dukan tsiya zaiyi min Mami kuma ba zata hana shi ba. But Allah ya taimake ni Uncle Zayed ya shiga maganar, and my grandparents too, sai komai yazo da sauki musamman tunda na karbi laifina kuma na bada hakuri. And now Ya Ameen ne ya dawo dani tare da wife dinsa Humairah itama zata fara karatu. She is an artist, yana so ne ta samu qualifications din kawai" suka yi shiru Diyam tana tunanin ina ma dai itama nata family din zasu zama irin haka in É—a yayi wa wani family member laifi sai iyayensa su danne son da suke yi masa su hukunta shi har ya zamanto su ake bawa hakuri ma.
Bassam ya cigaba da cewa "Mommy, my grandma, tace wai in zabi budurwa a cikin cousins dina in place of khausar, but nace mata ta barsu duk na gode, saboda duk wadda na zaba din za'a iya forcing dinta dan a faranta min and I don't want to end up like Saghir dinki, in zauna da matar da bata so na, so I decided zan jira, rayuwar ai yanzu ta fara ko? Zan jira har Allah ya hada ni soulmate dina da zata soni kamar yadda kike son Aliyun ki" ya karashe da sigar tsokana. Ita kuma tayi murmushi tace "ka lallaba ni in baka kanwata" yace "wacce kanwar?" tace "Murjanatu" ya daga hannu yace "no, no, no. Thank you so much but no. Wannan yarinyar samarinta sun kai cikin container".
Suna tare har aka tashi. A lokacin ne ta bashi labarin itama cigaban da aka samu a nata bangaren, ya taya ta murna sosai da sosai sannan shima ya tambaye ta game da shirye-shiryen da take yi. Ta daga kafada tace "ba fa abinda zanyi ni, ina naga friends din ma da zan shiryawa event. Nasan dai Inna zata yi taron yan uwa da abokan arziki and that will be all" Bassam yayi shiru yana kallon ta sannan yace "kinsan wani abu? Matar yayana dana gaya miki mun taho tare zata fara school itama, zan hada ki da ita ina tunanin you two will like each other. Zaku iya zama friends" Diyam tace "no, ni bana son friendship da yayan masu kudi" yayi murmushi yace "babanta ba mai kudi bane ba, mai rufin asiri ne. Kuma bafulatana ce irin ki" tace "in babanta ba mai kudi bane ba ai mijinta mai kudi ne" Bassam yace "that makes the two of you" sai ta sunkuyar da kanta tana murmushi, the mare thought of Sadauki as her husband yana saka ta murmusawa.
Suna rabuwa da Bassam ta kira Sadauki
End Ads