x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 44 - DIYAM

  • 129001 words
  • 132000 words
  • Out of 175324 words

Category: Love Stories

Views 258

02 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
tashin hankali ya na gaya min wai baki da lafiya, shi yana ganin ma kamar kin mutu dan yaga maigidan ya dauko ki cikin jini ya saka ki a mota ya fita dake. Papa yana office dan haka message kawai na tura masa na dauki kudi da passport na tafi airport. Ban samu jirgi zuwa kano ba sai Abuja. Sai dana shiga Abuja sannan na samu wani zuwa kano ina shiga kano na kira Malam Iliyasu yace min shi bashi da wani labari tunda kuka fita shiru, sai na wuce gidan Alhaji Babba, na shiga har compound din gidan saboda yadda nake jin raina I was beyond caring akan me zai faru in aka ganni. Amma sai na tarar da gidan a hargitse, hankali na ya tashi and I asked wani mai kula da flowers sai yace min ai gobara ce Alhaji yayi duk shagunan sana'arsa sun kone kurmus babu abinda ya tsira dashi. Sai na tambayeshi game da matar Saghir, sai yace haihuwa ce kika yi amma yaran sun mutu, ke kuma an kaiki asibiti amma baisan wanne asibitin ba. Muna cikin magana Inna ta shigo gidan, ta wuce mu ba tare da ta ganni ba kuma na lura hankalinta a tashe yake, ta shiga cikin gidan ta sake fitowa sai na tura wanda muke tare nace yaje ya tambaye ta ya mai jiki? Anan naji sunan asibitin da kike, ana bukatar jini kuma ita ta rasa kowa duk gidan suna gurin Alhaji da yake asibiti shima. Sai na fice ba tare data ganni ba, na je asibitin da kike na nemo dakin da kike na shiga har ciki na ganki. You were sleeping, kamar allurar bacci aka yi miki. Kin kumbura sosai kinyi fari tas. I stayed a dakin for a while ina ganin kamar in na fita bazan dawo in tarar dake da rai ba but i knew dole inyi wani abu sai na tafi nace Inna ce ta turo ni in biya kudi kuma a dauki jini na, akwai wadda a gurin ta tambayeni ko nine mijinki and it pained me to say no. Aka gwada jini na and luckily sai yayi matching da naki"

Na katse shi "wait, wai kai ka bani jini ranar nan a asibiti?" Yayi murmushi "naki fadar kaina ne saboda nasan yadda Inna bata sona zata iya cewa ba za'a karba ba dan kar in shafa miki maita or something like that"

Kullum ina zuwa in duba ki. Na tabbatar kina samun sauki sosai, ranar nan saura kadan Mama ta ganni na buya duk I doubt ko ta ganni ma zata gane ni saboda ni kaina nasan I looked terrible. Ranar nan nazo sai akace min a ranar za'a sallame ki. Sai na tsaya and I saw you sanda kuka fito, ke da Inna da Saghir da wadansu mata. Kuka shiga motar Saghir ke da Inna kuka tafi and I kept following you a kafa sai danja ta tsayar daku har na karaso inda kuke and I did what I shouldn't have done, nayi miki magana"

Da sauri nace "I knew it. Nasan kai na gani amma inna tace wai aljanu ne suka bude min ido". Yayi murmushi. Ban kyauta ba na sani bai kamata inyi wa matar wani magana ba but I did it.

A ranar na koma Abuja daga nan kuma na koma Canada. A cikin jirgin nayi making decision cewa it is time to move on, tunda ke gashi har kin haihu, seven months after the wedding har kin haihu. Dan haka ina zuwa gida na samu Papa nace "am ready to move on yanzu" yace "good. Sai ka tafi makaranta kayi mechanical engineering dinka" sai nace "ina son karatu amma nafi son business, in yaso sai in hada da karatun da business din duka" yace zai saka ni a harkar Mai, but sai nace masa bana son aiki under him, I want something of my own, yadda zan making name for myself ba wai in jingina dashi ba. Na dauka zaiji babu dadi but sai naga yayi murna, yace wannan ya nuna masa how strong I am. Sai yayi signing check ya bani yace in cike kudin da nake ganin zasu ishe ni in kafa kaina. Na rubuta na mika masa sai ya yaga check din yace "wannan kudin da zan bawa wani ne in tazo neman taimako gurina. Ba kudin da zan bawa tilon dana ya kafa business ba. Sai ya sake signing wani ya miko min yace "multiply that by hundred, ka rubuta kaje ka karba. Allah yasa albarka a ciki".

That was the beginning of Abatcha Motors. I chose Kano saboda in samu damar keeping eyes on you. Cikin few months aka gama komai na fara hiring ma'aikata. A lokacin ne Malam iliyasu yake gaya min cewa kuna cikin matsalar kudi dan yaga aba ta fitar da kayan gidan ana siyarwa. So, I talked to someone who talked to someone har aka gayawa Alhaji Babba cewa ga sabon company nan ana daukan ma'aikata and luckily shi kuma Saghir ya dauko takardunsa ya fito neman aiki a lokacin sai aka turo min shi. A gurin interview din dana yi masa ne na tabbatar cewa bai sanni ba. I gave him a job. Amma ba job bane ba dan baya ma cikin list of staff dina. Salary dinsa daban nake bashi and his salary was just like me giving you money. Ina bashi kudin dana san ya isa ya kula dake.

Ina gab da komawa Canada ne sai yazo office dina yana ta complain wai matarsa ce zata haihu kuma doctors sunce ba zata iya haihuwa ba sai dai ayi mata aiki, gashi sunyo masa bill na kudi da yawa. I was scared kar yazo yaki biyan kudin ki zo ki samu matsala so I paid the money. Har na kara masa da kudin ragon suna da sauran hidima, ranar da za'ayi aikin na kwana ina miki addu'ar nasara, I wanted to go and see you but nasan hakan ba dai dai bane ba sai na hakura nace ya kirani in anyi and I asked him ya sakawa yarinyar Subay'a hoping hakan zai faranta miki ranki.

Daga nan na koma school. Carleton University of Canada. Anan nayi karatu tsahon shekaru biyar na fita da matsayin mechanical engineer. A wannan shekarun ne muka yi bonding sosai da yan uwana. My four sisters, Sa'adatu, Yani, Fanna da auta Adama, wadanda Papa ya bani task din koya musu hankali dan zaman kasar turawa ya saka duk sun koma suma kamar turawan. Yanayin shigarsu da yanayin mu'amalar su. I treated them with fire, but sometimes kuma sai inyi musu sanyi muyi ta wasa da dariya. Maman su kuma ta bani goyon baya sosai gurin koya musu hankali dan dama yanayin nasu duk yana damunta itama turancin ne yasa bata iya tsawatar musu.

All those years, nayi iyakacin kokari na dan ganin na cire ki a zuciya ta amma abin ya faskara. Nayi addu'a, nayi azumi nayi sadaka duk da wannan niyar, daga baya sai na saka a raina cewa wannan shine kaddara ta, zan rayu da sanki a zuciyata amma bazan rayu dake ba. Ban dauka cewa babu abinda ya ragu na sonki a zuciyata ba sai dana dawo, ranar da staff dina sukayi surprising dina da party, I saw you there, I tried pretending but then I saw him holding your hand and I couldn't take it, nasan in ban bar gurin ba zan iya rufe shi da duka dan haka na gudu"

Then one day ina dakina na hotel ana ruwan sama, har na fara shirin bacci sai ga wayar Malam Iliyasu yace min mamanki da kanwarki sunzo gidan Saghir ya kore su, ga dare gashi ana ruwa yana jin tsoron kar wani abu ya faru dasu. I left everything na hau mota na taho unguwar ina tafiya ina dubawa, hankalina a tashe ina tsoron kar in zama too late, sai gasu nan kuwa na gansu already har sun fada hannun mugaye. I couldn't imagine me zai faru da Asma'u idan da Allah bai sa Malam Iliyasu ya kirawo ni ba. That was when I decided to sue Alhaji Babba for garejin Baffa da filina. Tunda rashin mutumci suke ji I decided to show them rashin mutunci".

"Wannan shi yayi stating chain of events din da har suka kai ga rufe Saghir"

"Ina so ki fahimci cewa ban rufe Saghir dan in aure ki ba. Yes, I loved you, I love you and I will take your love with me to my grave but da ace zaman lafiya kuke yi da Saghir da babu abinda bazanyi ba dan ganin cewa zamanku ya dore a tare. I would have given everything in dai zakiyi farin ciki. But after na fahimci irin zaman da kuke yi, after what he said a gaba na ba tare dako digon nadama a muryarsa ba, after ke da kanki kin gaya min cewa ba kya son komawa gidansa then I won't let you. Yes, na barwa Saghir kudina intentionally saboda ina so ya dauka, saboda ina son in samu hujjar rufe shi yayi paying for abinda ya aikata. But I didn't force his hands. Shi yayi making decision din dauka da kansa. And that's what took him to prison bani ba".

"Yanzu na dawo gurinki Diyam. Ina neman aurenki bisa yardarki. Yes, nasan shekaru sunja ba lallai ne kina da feelings for me a yanzu ba. Amma ina so ki fada min abinda yake ranki, in kika karbi offer ta ta aure I will surely be the happiest man on earth, in kuma kika ki karba I will be heart broken maybe fiye ma da wancan karon but I will respect your wish. Bazan matsa miki ba ba kuma zan bari a matsa miki ba".

Ina jiran amsar ki.
[3/5, 10:12 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Sixty One: The Decision

Nayi kokarin dago kaina in kalleshi amma na kasa, tun daya fara magana nake hawayen tausayin rayuwata da tasa, wani gurin kuma inyi murmushi ina jin soyayyar sa tana kara ninkuwa a zuciyata. A karshe sai na samu kaina da tambayar kaina. Shin tsakanin ni da Sadauki waye yafi son dan'uwansa?

But can I tell him that? Anya zan iya gaya masa cewa babu abinda ya ragu a zuciyata dangane da soyayyar sa sai ma karuwa da yayi. Sai jin murtarsa nayi a hankali yace "should I start crying? Ko kuma in durkusa a kan guiwa ta?" Na yi murmushi ina karasa goge sauran hawayen ido na, na bude baki sai maganar ta makale, sai kawai nasa hannayena na rufe fuskata. Ya kama dariya yana cewa "you must be kidding me. Yanzu ni in zauna in gama bude miki zuciyata amma ke sai ki rufe fuska? In ba zaki gaya min bama at least let me look at your eyes in karanto amsa ta a can" na girgiza kaina nace "I can't" yace "wait, wai kunya ta kike ji?" Na bude fuskata nasan "mu fulani kunya ce damu" yayi dariya yace "maybe kin manta, nima bafulatani ne" nace "half ba. Mun bar musu kuma" yace "ni ban yarda ba, ko bani da jinin fulani my heart is fulani. Zuciya kuma itace rayuwa" nayi murmushi ina tuna ranar daya fara fada min nice zuciyarsa a Taura. Yace "I still need to hear it. I need to hear you say you love me. In kika fada then I have tukuici for you. Happiness insha Allah, till eternity. Through thick and thin".

Ina sunkuyar da kaina kasa, murmushi a lips dina, ruwan hawaye a idona, nace "kalmar love can't even begin to describe yadda nake jinka a zuciyata. Sometimes ina jin soyayyar ka kamar tayi waya a kirjina Kamar zuciyata ta cika har tana zuba da sonka. Da sonka aka haife ni Sadauki kuma nasan da shi zan koma fa mahalicci na. Bana jin kalmomi zasu iya bayyana soyayya ta gare ka dan duk abinda na fada ji nake yi kamar yayi kadan" sai yayi sauri yace "okay, will you marry me? Please? Sai a nuna min soyayyar a aikace ko zan fi fahimta sosai" sai nayi saurin jan hijab dina na rufe fuskata saboda nauyin maganar sa da naji. Ban san me yasa yanzu nake jin tsananin kunyar Sadauki ba bayan kuma sanda nake karama bana ji kamar haka. Ina jinsa ya sake jawo kujerar sa kusa dani yace "Please say something Diyam. Am dying here".

Hayaniyar su Asma'u ce tasa na bude fuskata amma ban kalli inda yake ba sai na juya inda na jiyo muryoyinsu. Murjanatu tazo da sauri tana cewa "yaya, wallahi naga irin motar da kayi min alkawari as my birthday gift. Please, please yaya ka bar min ita" sai ya dafe kansa da hannu daya yace "zaki saka min ciwon kai Fanna. Please go and make the noice somewhere else" sai na mike tsaye nace "yauwa an kawo abinci, dama yunwa nake ji".

An jera mana abinci iri iri akan shimfidar da akayi mana akan grass carpet din gurin. Muka tafi mu uku muka fara saving kan mu muna ci muna hirarrakin mu amma hankali na tana kansa yana zaune har yanzu a inda muka zauna da waya a hannunsa. Naji shigowar text cikin waya ta sai na duba naga "Please ki ajiye abincin nan kizo mu karasa maganar mu" sai na juya na kalle shi nace "me za'a zubo maka?" Ya bata rai yace "am not hungry".

Anan mukayi sallolin mu, Murjanatu tana ta yi masa nacin mota sai yace ta bari sai birthday din nata. "Ke ba iya motar ma kika yi ba. In na baki me zaki yi da ita?" Tace "koya min zakayi ai" yace "ni bani da lokacin koya miki mota akwai driving schools ki shiga ki koya a can". Sai da magrib ta gabato sannan muka tafi gida. A hanya Asma'u da Murjanatu ne kawai suke ta hirarrakin su amma ni da Sadauki kowa yana hira ne da zuciyarsa. Ni ina rarrashin tawa ne akan ta yarda da hukuncina a kan Sadauki, ina gaya mata cewa hakan shine abinda ya kamata gare ni, gare shi ga Subay'a, ga kuma zuriar dazamu haifa in muna da rabo. But my heart was weeping tana ganin banyi mata adalci ba. Tana gaya min hukuncina ni zaifi affecting ba wai shi wanda nayi wa ba.

Muna zuwa gida yayi packing a kofar gida su Asma'u sukayi masa sallama suka fita, ina hango Subay'a ta fito da gudu sai kuma ta tsaya tana kallonsa sai ta juya ta koma gida. Ya juyo yana kallona, nasan maganar da zaiyi min kuma kirjina bugawa yake da karfi ina tattaro courage din amsa masa, yace "baki bani amsa ta ba Diyam. In kin amince min ina son zanje gurin Kawu Isa" na juyo ina kallonsa, ina tunanin irin smartness ne Sadauki. Gurin Kawu Isa. Yasan a yanzu in ya nemi aurena a gurin Kawu Isa da gudu zai bashi ko dan ya kara bakantawa Alhaji Babba rai tunda har yanzu basu shirya ba. Sai kuma nayi tunanin hakan da Kawu Isa zaiyi shi zai kara rusa yar guntuwar zumuntar da take tsakanin uncles dina guda biyu. Sai nace "ina son aurenka Sadauki. Zan iya cewa shine greatest burina a yanzu. But, ina son muyi shi akan dai dai. Ina son muyi shi ta yadda nan gaba ba zamu zo muna nadama ba" yace "nadama kuma? Akan me zamuyi nadama?" Nace "have you thought about maganar da mukayi ranar nan? Akan forgiveness?" Sai ya dauke kansa gefe yana kallon waje nace "nima da akayi wa laifin nan na yafe musu. And I felt good lokacin da na yafe din ji nayi tamkar na dauke wani abu ne mai nauyi daga zuciyata. Wannan feeling din shi nake yi maka kwadayi. And Subay'a, ƴata ce at the same time ƴar Saghir ce duk yadda bana son Saghir bazan taba cewa ba shine ya haife ta ba. She will come in between us ko da munyi auren ma she will never forget cewa kai ka rufe mata mahaifinta and that may affect me nima a gurinta zata iya tunanin da sani na akayi komai" yace cikin dacin murya "I didn't lock up her father. Shi yayi signing takarda da hannunsa babu wanda ya tilasta masa" nace "but intentionally ka bar masa ai. Kuma kudin ka ne. You can just walk to the court a yanzu kace ka yafe masa a d that will be all" ya girgiza kansa yace "you seem to be forgetting something. Ba kudina ne kadai yake rike da your precious Saghir a prison ba. Ko drygs din ma ni na daka masa a dakin sa?" Naji zafin kalmar 'precious Saghir' din daya fada amma nasan kishi ne yake yi, sai nace "ba kai ka saka masa ba. Abokinsa ne yayi framing dinsa amma yayi framing dinsa ne saboda ya samu damar guduwa da kudinka da Saghir ya dauka, so it circles back to you. Please Sadauki, you have the power, you can set him free. Saghir yayi nadama. I saw it in his eyes sanda naje gurinsa a prison" yace "nadama? Baki san hausawa sunce kowa ya tuba dan yuwa babu lada ba? Ko zaiyi nadama Saghir ba yanzu ba" nace "Sadauki, Saghir fa....." Sai ya daga min hannu yace "stop, Please stop mentioning his name" sai na fahimci wani abu. Duk maganar da nake Sadauki ba jina yake yi ba, kishi ya rufe masa ido gani yake yi kamar saboda ina son Saghir ne nake so ya fito da shi. Ban kuma cewa komai ba sai na dauki purse dina na bude kofa na fita. Ina jin yana kirana amma ban juyo ba duk kuwa da cewa ji nake tamkar tawa zuciyar tafi tashi jin zafin hakan.

Ina shiga na tarar Asma'u da Murjanatu sun saka Inna a gaba suna ta bata labarin guraren da muka je. Sai na wuce su na shiga daki da niyyar rage marata a toilet sai kawai naga Subay'a a kwance a kan gado, na karasa kisa da ita sai naga kuka take yi a hankali hawayenta yana zuba kan katifa. Naji hankalina ya tashi sai na durkusa na jawo ta
End Ads