baice mata komi ba, afadace tace "ina zaka kaini? Ba hanyan gidanmu bane nan ba?" Dan kanshi ya sosa yana kallonta kaman yanda take kallonshi murya chan ciki yace "we are going to hotel!" Mummunan gaban Hawwa yayi.
[9/28, 8:18 AM] +234 806 486 0007: YA ALLAH ZAN FARA THIS UPDATE DA ADDU’A! YA ALLAH KAGA YANDA NABADA FREE PAGES NA SAUKE HAKKI, YA ALLAH DUK WANDA YACI HAKKINA YA KARANTAMIN DAIDAI DA HARAFI DAYA A LABARIN NAN YA ALLAH BAN YAFEMAI BAN YAFEMATA BA! HAR ABADA! ALLAH KABIMIN HAKKI NA! YA ALLAH KA SAKAMIN!!
WAYANDA SUKAI SUBSCRIBING THANK YOU! BUT IDAN KUN FITAR KUMA ALLAH YA SAKAMIN BAN YAFEBA!!
HELP ME GROW APPLICATION NAKESO NAYI JARI NAKE TARAWA🥲
EPISODE 4️⃣1️⃣
Wuraren 5 Hawwa ke bude idanunta tana kallon saman dakin komi daya faru nadawo mata, hawaye masu dumi ne sakko daga idanunta, ahankali tafara mosti da idanun dake mata nauyi sosai tana juyowa kanta yayi sauki kaman ba nata ba yanzu tana iya juyawa yadena banging, Ammi ta gani a tsakar dakin kan dadduma ga charbi a hannunta tanaja maida idanunta tayi tarufe she can’t look at Ammi, knocking kofan akayi da sauri Ammi ta tashi tace “shigo” tadaga dadduma tana linkewa daidai Dr yashigo tareda Nurses yazo gaban gadon yana kallon Hawwa data lumshe idanu Ammi tace “Dr har yanzu bata tashi ba nadamu abinci fa”? Murmushi yama Ammi yana duba BP Hawwa dayasan ta tashi yace “maganin hawan jini nasa bacci amman karki damu zata tashi saitai wanka” ijiyan zuciya ya sauke yace “Alhamdulillah BP yasoma sauka” anatse yace “Miss Hawwa open your eyes” ahankali Hawwa tashiga bude idanunta tadan kalli Doctor kadan saikuma ta sauke idanun kasa kawai nauyin kowa takeji, Dr yace “ya ciwon kan? Akwai wani abu dayake miki ciwo yanzu?” Girgizamai kai tayi murya kasa kasa dabaya fita da kyau tace “no” Dr yace “okay that’s great” yakalli Ammi yace “Mama help her to change tadan gyara za’azo a gyara gadon akawo mata abinci kuma, an mata booking massage Yallabai yace bayanta na ciwo, masseuse zasu mata massage din, zatasa hospital clothes bama barin patient namu nasa kayan gida” gyadamai kai Ammi tayi tace “to” Nurses suka ciremata drip din suka fice Ammi taje gaban gadon tana kallon Hawwa da idanunta ke kasa ta kauda kanta gefe dasauri jin Ammi tazo wajen, Ammi dake kallonta tace “Jidda na ya jikin? Babu abinda ke miki ciwo kuma”? Gyadama Ammi kai tayi ahankali batare data kalleta ba tace “eh” cikeda so Ammi tace “tashi muje to kiyi wanka ki chanza” Ammi takai hannunta tadagota tasowa tayi da karfin hali ta sauka daga gadon Ammi tariketa har bayi tabata gadon Ammi tahada mata ruwan wanka, tadawo dakin tabude jakan kaya da Baba da Ramla suka kawo musu jiya taciro brush da zani, saikuma pad datasa Ramla tasa ajakan tadauki daya da wando takoma bayin ta ijiye mata tasake fitowa ta yaye zanin gadon daidai nurse tashigo da wani ta shimfida mata da hospital gown mai kyau na yan gayu sannan tafice saikuma masu abinci suka kawo mata fruits da oat, dasu chips da egg da salad da sausage ga bread saikuma maganin dazata sha a gefe cikin wani glass covered container Ammi sai kallo take komi na masu kudi daban ne.
Kusan 15min tayi abayin Ammi takoma wajen bayin tace “kin gama Hawwa”? Ahankali tace “eh” Ammi tabude tashiga tana kallon yanda taki yadda su hada idanu, maidata gadon tayi tana kallon yanda white and blue flowers hospital gown din yamata kyau ta zaunar da ita tana daga tray na abincin tana ijiye mata tace “yi maza ci kafin sudawo” yatsine fuska tayi batada apatite ko kadan kauda kanta tayi asanyaye tace “Ammi bazan iya ci ba” sosai Ammi ke kallonta saikuma ta matso ta zauna abakin gadon anatse tace “Hawwa” asanyaye Hawwa tace “Naam” batare data kalli Ammi ba, lumshe idanu Ammi tayi tabudesu tace “look at me Hawwa” girgizama Ammi kai tayi dasauri lips nata suka shiga rawa tace “Ammi bazan iya ba” wani iri Ammi taji, hannunta tasa tadauke tray na abincin ta ijiye akan table na dakin sannan ta matso dab da Hawwa ahankali tace “Hawwa look at me” daidai lokacin hawaye yasauko daga idanunta tace “Ammi bazan iya kallonki ba, Ammi banmasan ta yaya zan kalli keda Baba ba” sai takai hannayenta biyu tadaura kan fuskanta tafashe da kuka mai tsuma zuciya she’s hurt, Ni’ima hurt her beyond duk yanda zatayi bayanin tace “wlh, wlh, wlh Ammi ni ba yar iska bace bantaba amfani da kaina ba, Ammi that’s not me, bazan tabama wani fyade ba” hawaye Ammi tashare daga fuskanta Hawwa tabata tausayi sannan takai hannunta takama hannun Hawwa tasauke takai hannunta tajuyo da habanta fuskan Hawwa yajuyo Ammi tanuna kanta tace “Hawwa ni mahaifiyarki ce kina gani aduniyan nan akwai wanda yasan yarsa sama da mahaifiyar ta? I know you Hawwa, nasan tarbiyan da muka miki, I know who you are? Dagani har Babanki babu wanda yama dauki maganar da Ni’ima tayi da mahimmanci, Hawwa yau koda haka kike ko kinfi hakama muna sonki and we will always love you, Hawwa ke y’ata ce inasonki aduk yanda kike aduk yanda kika zama, kinji yarinyana, ki manta da duk wani abu data fada, come here” dasauri ta rungume Ammi tana sake samin wani karfin guiwa iyaye daban suke idan suka nuna they’re with you and they stand with you kafi jinka very strong kankame Ammi tayi tana kuka harwani rera kukan take kaman marainiya tace “Ammi menama Ni’ima? Why all this hate? Sabida ni Ni’ima tazageku ta ma Baba rashin kunya, Ni’ima tamin gori tama Baba gori, Ammi me namata eh”? Tawani ja numfashi tana rera kuka tace “bazan taba auren mijinta ba, Ammi sabida bansami miji ba banda aure shikenan na zama dustbin? Kowa yadauko shiritanshi akaina? Ammi inaso nai aure nahuta maybe only then Ni’ima zata yarda dani I’m not after Baban Yaseer, Ammi babu abinda kemin dadi“ cikin dan fushi kadan Ammi tace “zaki kashe kanki akan Ni’ima ne? Hawwa that girl obviously doesn’t deserve you, abu dayane bazanyi supporting naki ba shine kisamakanki damuwan Ni’ima, Hawwa don’t kill yourself akanta, Ni’ima don’t deserve you Allah use this chance ya nunamiki waye ita, so is time kifita daga rayuwansu both ita da mijinta and move on, toxic people ne dukansu biyun, kiji sauki kidena tunanin komi, I didn’t train you to be weak or to be crying for any girl, Hawwa you are a strong girl wacce guguwan iskan mountain baiyi putting baki down ba saida kikai destination naki, shit happens in this life, friends comes and goes, relationship ends that doesn’t mean bazamu cigaba da rayuwa ba, close chapter Ni’ima and move on learn from your mistakes, no more room for wacce wishes you death, your secrets should be for your stomach idan ba ni ko mahaifin ki ba babu wanda ya isa yaji sirrin ki, move on and be a better person kinji, kihakura da Ni’ima, tace taja miki layi kema kijamata layin kinjini” gyadama Ammi kai tayi ahankali tana kuka har lokacin, Ammi ta matso ta manna mata kiss a goshi sannan tadauki tray na abinci cikin masifa tace “nayi tir da dabi’un Ni’ima ayahya taje zata gani indai duniya ne fadi gareta, Allah zai saka miki” tashiga bata oats tana sha, masu massage sukazo akama bayanta massage dataji kaman an mikar da ita an ciremata duk wani bending da ciwon jiki, no wonder massage keda tsada ashe haka akeji, duk wani tsamin jiki saida suka fitar bacci yayi awon gaba da ita haka nurse’s sukazo suka kara mata fixing drip din tana bacci mai nauyi.
Tun asuba Allah sanya alkhairi akema Baba, kafinma yasamu yabar masallacin was around 8:20 sai farin ciki yake nanma wasu suka sake tsareshi anan waje anamai Allah sanya alheri wani kara son Baba ma akayi a unguwan Baba tsabagen murmushi kumatunsa har ciwo yake sai wajajen 9 yawuce gidansa da sallama ya shiga cikin gidan Maman Ni’ima daya gani a tsakar gidan kan kujera yasa yaci tura ya tsaya, Mama ta washe baki tace “ahhh Malam ka shigo barkanmu da safiya ai tundazu nazo nake jiranka” dan jim Baba yayi saikuma yakaraso ciki yace “Malama Maimuna ya kwana biyu ya yara ince dai kinaji daga garesu”? Murmushi Mama tayi tace “kowa na nan lpy, satin daya gabata ma Usaina ta haihu an samu Abdulwahabu” anatse Baba yace “Masha Allah, Allah ya raya” ya kwalama Ramla kira data fito daga dakin Hawwa tace “gani Baba” Mama yanuna mata yace “kaita ciki bari na zaga nazo” Mama ta mike tabi Ramla ciki tanabin dakin Hawwa dakenan tsaftsaf da kallo shikuma Baba yawuce makewaya.
Fitowa yayi ko kallon Umma dake kitchen baiyiba itama haka yawuce dakin Hawwa inda Mama take, kujera yaja yazauna yakalli Ramla yace “jeki hadamana kari Ramla” gyadamai kai tayi shikuma yakalli Mama kai tsaye yace “ya akayi Maimuna wannan dakike nemana”murmushi sosai tayi tace “na farko dai Malam naji labarin dakebin gari sai shigowa makota suke sunamin Allah sanya alheri diyata Hawwa an daura aurefa shine nake kiran Ni’ima dan abankinta yakamata naji wannan labari amman saiba abakinta nakeji ba, nan fa Ni’ima tafara koro zance aiko saida namata tatas dan har mari na yanka mata, akan namiji zatai kalan haukan nan shine fa na zuro hijabi da sassafen nan nazo nabaka hakurin abinda Ni’ima tayi kuyafe mata Baba bakaga yanda ta damuba dan Allah ayakuri kaga tsakanin harshe da hakori ma ana samun sabani balle kawaye” Baba yace “wannan haka yake” Mama tace “Baba toh dan Allah kuyakuri mune iyayensu karmu zuba musu ido su lalata mana zumunta mu daidaitasu Baba, Ni’ima tayi nadama kwarai kawai shakkan ku take dakuma tana tsoro kar Hawwa taki yafemata amman dazaran kasa baki kowa yasan Hawwa zata hakura Malam”Mama tai shiru tana jiran amsan Baba, dan murmushi Baba yayi yace “Masha Allah naji duk bayanin dakikayi Maimuna” yasakeyin shiru yace “dan yafiya wlh na yafema Ni’ima, ni uba ne akan mene zan riketa azuciya bayan nima yarana zasu iya kuskure da shirme kaman nata, idan zancen yafiya ne nayafema Ni’ima har ranan gobe kiyama” dasauri Mama tace “Alhamdulillah,Alhamdulilah Alhamdulillah, shikenan yaranmu sun shirya” ta washe baki, Baba yayi shiru saikuma yakalli Mama yace “Maimuna dubeni nan, ni ubane kaman yanda kike mahaifiya, hakkine akanmu idan mukaga abinda zai cutar da yaranmu mu kauda abubuwan daga hanya” Baba yayi shiru yana lumshe idanu yana tuna yanda Ni’ima take ikirarin kashe Hawwa yace “idan Hawwa zata yafema Ni’ima bazan taba hanata ba amman idan Hawwa zata dawo da Ni’ima rayuwanta saina hanata!”Faduwa gaban Mama yayi dasauri takalli Baba bakinta tafara rawa, Baba yadan kada kafa yace “wato Maimuna jiya na karanci abubuwa da dama akan idanun Ni’ima, tundaga kissan data dinga ikirari zatama Hawwa, da fatan mutuwa data dinga mata, da yanda dudda mijin natane mai laifi ina shiyabi Hawwa? Shi yake sonta Hawwa bata sonshi amman batai kan mijinta ba kan Hawwa tayi, ga diyata agadon asibiti rai hannun Allah Ni’ima bataji tausayin ta ba karasata takeso tayi” yayi jimm yace “Maimuna ansan mata da kishi amman naga ko kishiyan ka ce take gadon asibiti zakadan tausaya karage wani abun” Dasauri Mama tace “Malam kishi kala kala ne, akwai masu zafin kishi kafahimta” adan zafafe Baba yace “Maimuna fahimtan danayi yasa nike miki bayanin nan, koda yaran nan sun shirya madaman Aliyu na kaunar Hawwa Ni’ima bazata taba kaunar Hawwa ba duk karyace! Ni’ima tariga ta tsani Hawwa! Naga kiyayya a idanunta kibar maganan nan kawai!”.
Mshakur🥰
[9/28, 8:18 AM] +234 806 486 0007: EPISODE 4️⃣2️⃣
Rasa tacewa Mama tayi amman taki giving up ina sai inda karfinta yakare kawancen nan saisun dawo dashi, ijiyan zuciya Mama ta sauke tace “Malam duk naji bayaninka kuma banki ba hujjujinka masu karfi ne, konine naga wacce ke shirin cutar da yarana zan dakatar, amman kuma ka kalli abin ta wannan fuskan mana, ina duk ba Aliyu ne sanadi, dalili, da haddasanan fadan ba? Malam ai komi yakare yanzu, Hawwa tayi aure, babu sauran fada kuma” Baba yayi murmushi irin na manya yace “ke mace ce Maimuna bazaki taba gane yanda zuciyan maza yakeba, idan namiji ya daurama kansa soyayyan wata har abada soyayyan nan baya fita daga ransa, daukeni a misali har gobe ina matukar kaunar marigayiya mahaifiyar Hawwa, shi son gaskiya baya mutuwa, inhar Ni’ima natare da Hawwa dole zata dinga ganin dabi’u wajen mijin nata dazai dinga konamata rai daganan kishi ya motsa afara tunanin illata wani ko kisan kai, maganin kar ayi karma afara naga Ni’ima, Ni’ima taganni, ayayyafe amman adawo tare ban aminta ba, kawai ahakura Aliyu yariga yabata komi, Hawwa takamu da hawan jini hakkinane na kareta gwara ta nisanci mutanen da zasu bata matsala arayuwanta wato Ni’ima da Aliyu dan haka kiyakuri kawai Maimuna, ahakura da kawancen tunda yazo irin gabar nan, zanje nayi kari daganan naje asibiti” yayi maganan yana mikewa bayason zancen bakaramin daurewa yayi yamata maganan hankaliba amman ya tsani Ni’ima da dabi’un datayi, yarinyar ta basa tsoro baitaba sanın haka Ni’ima take ba, tashi Mama tayi dasauri tace “dan Allah Malam ayakuri, Malam kabar yaran nan sudawo tare sunason junansu Malam” dakin Umma Baba yafada Umma ta watsama Mama harara dan basa shiri sabida uwar kawar Hawwa ce rai ba dadi Mama tawuce tabar gidan.
Kari Baba yayi tareda Ramla sannan ta shirya suka fito tare wajajen 11 daidai motar Baban Yaseer na parking Baba ya tsaya turus yace “je gida Ramla natashi tafiya saina kiraki” komawa ciki tayi, Baban Yaseer yafito yazo wajen Baba cikeda mutunci suka gaisa Baba ya zauna kan kujera shikuma ya zauna a tabarma yadan sosa kai yace “Baba zan fara da baka hakuri bisa ga abinda yafaru jiya, Baba kayakuri yawancin maganganun da Ni’ima tayi na tabbatar cewa karya tama Hawwa, kowa yasan hakan ba halin Hawwa bane, Baba dan Allah kayakuri” murmushi Baba yayi yace “bakomi nahakura komi yawuce” ijiyan zuciya yasauke yace “saikuma ahhhhhmmm” yadanyi shiru yana sosa kai Baba yace “ina jinka” kanshi ya sauke kasa yace “Baba inaso kabani daman auren Hawwa! Baba ina matukar son Hawwa, namaka alkawari Baba zan kula da ita nakuma riketa amana Baba, Baba dan Allah dabi’un Niima kada su sa ka ki bani wlh Baba zan kula da Hawwa namaka alkawari babu abinda Ni’ima zata iya mata”
Ijiyan zuciya Babayasauke anatse yace “Aliyu” dagokai Aliyu yayi yakalli Baba yace “Na’am Baba” Baba yayi murmushi yace “Aliyu kai d’a nagari ne da babu iyayen dabazasuyi alfaharin samunka amatsayin d’a ba, Kanada hankali natsuwa da kirki babu wanda bazaiso yahada zumunci dakaiba” yayi shiru chan yace “Allah yana jarabtanmu da abubuwa da dama, wani zubin yana nunamana duk yanda mukakai ga son abu bamu samuba sabida banamu bane” faduwa kawai gaban Aliyu keyi Baba yace “ina sonka Aliyu sosai amman y’ata Hawwa bataka bace, jiya nadaurama Hawwa aure da Ibrahima, Hawwa tariga tazama matar wani!” Faduwa gaban Aliyu yayi dasauri yakalli Bab idanunshi har twitching suke sabida bugawan kirji yama kasa magana Baba ya lumshe idanu yabude, Baba yace “kayakuri Hawwa tayi aure, inaso kaima kaje ka gyara rayuwanku da Ni’ima, ku daidaita kanku, ku shirya ku kula da yaranku, yanzu Hawwa tafita daga tsakiya, babu wani abu dazai kara jawo muku fada, inaso naga ka koma yanda kake d’a da Ni’ima gwanin ban sha’awa, ku manta da komi acigaba da rayuwa anama juna fatan alkhairi kaji Aliyu”baki Aliyu yabude zaiyi magana saiga hawaye mai zafi sun sauko daga idanunshi dasauri yakai hannu ya share yajuyar da kai yana huci zuciyanshi na kuna yanason Hawwa sama da tunanin kanshi, waye Ibrahima? Yaushe Hawwa ta sansa? Ko sanarwan da Baba yayi sanarwa a masallaci ne yasa aka samo Ibrahima? Zafi yaji ranshi namai hawaye suka kara zubowa ya share da sauri still yakasa magana, ba karamin tausayi yabama Baba ba, kana gani kasan Aliyu na son Hawwa sosai, ahankali yace “kayakuri Aliyu, nasan yanda so yake, baya neman shawara idan zai kamaka, amman kayakuri, ka rungumi kaddara, ka gyara aurenku da Ni’ima ka rungumi iyalinka kaji” gyadama Baba kai yayi yakasa motsi Baba yayi shiru yana kallonshi yakai kusan 20min ahaka sannan yatashi muryanahi narawa sosai kaman zai fashe da kuka yace “natafi Baba” Baba ya gyadamai kai duk jikinshi yayi sanyi but this is the right thing, yawuce yatafi Baba shima yayi shiru, saida yaga barinshi unguwan ya kwalama Ramla kira suka tafi abinsu.
Da kyar cikin ikon Allah Baban Yaseer yakai gida gateman dinsu na gaidashi ko iya amsawa baiyiba yawuce yabude flat nasu yashiga yashiga bedroom nasu yazauna yafara fuzar da iska da baki sosai, hawaye masu dumi suka shiga zubomai yasan da Ni’ima duk batai haukan nan ba wlh Baba zai iya bashi Hawwa, yanzu ga shi Baba yaki, yasan rigiman Ni’ima yasa Baba yaji gwara ya aurar da Hawwa ga kowama ko wutan da Ni’ima ta kunna tamutu, iska yakara fuzarwa hawaye masu zafi suka zubomai baitaba sani rana zaizo dazaiji yanajin tsanan Ni’ima ba sai yau jiyayi ya tsaneta completely, bazaima so yaganta ba ko ya kalleta sai iya shaketa, yana ahaka wayanshi yahau ringing share fuskanshi yayi ya daga wayan Ni’ima yagani na kiranshi harta katse wayan bai daukaba tanamai kira na biyar ya daga yakai kunne baiyi magana ba, murya chan kasa tace “Baban Yaseer dama nakira nacemaka kayakuri ne da duk abubuwan dana maka natuba dan Allah let’s forget the past and move on for the sake of yaranmu” Wani kaluluwan abu Baban Yaseer yaji yana tasomai yana zuwa wuya Ni’ima tace “Babyna kaji nasan bazaka iya fushi dani for long ba please kayakuri” kasa rike abun dake wuyan nashi yayi cikin tsantsan tsana yace “bazan taba dawo dake ba, and for yarana ko da ke ko bake zasu rayu, na tsaneki Ni’ima na tsaneki da ko muryanki banso na sake ji, I hate you with everything in me, na tsaneki” yazare wayan ya katse ya jefar yazauna akasa yana dafe kanshi yashiga kurma ihu sosai kaman mahaukaci he’s so heartbroken, gateman yazo yana buga kofansu yana “Alhaji lafiya, Alhaji Alhaji”.