ya zauna, Salman ya maida kofan yarufe yakoma gaba yashiga ya zauna driver shima na shiga mopol dinshi ma haka, anatse yace “hospital” Dasauri driver yace “yes sir” yatada motan suka fita yana kallon hanya chan yace “music” waka aka samai yafarabi yanadan shaking kai yadaga wayanshi yayi selfie yasa a instagram story nashi hankalinshi kwance.
*
Kansu Ni’ima tayi da plastic chair data dauka dasauri Baban Yaseer yajuya yana sauke Hawwa agadon yajuyo yasa hannu da zafi zai karbe kujeran ta zame tai gefenshi zata rafkama Hawwa dake kallon Ni’ima completely heart broken Baban Yaseer yabude hannuwanshi ya tsaya agaban Hawwa, Ni’ima tace “kama rungumeta idan zakayi amman saina halakata, saina halakata wlh, Allah ya kasheki ya dauki ranki sai inga wazakaso Aliyu? Inaso naga ko zaka bita kabari kuyi soyayya, ba sumbatar juna kukeso kuyi ba kuka ganni kuka wayance? Ka tashi agabana” hannu daya Baban Yaseer yasa ya fizge kujeran daga hannunta yana kokarin ijiye chair a gefe tabi gefenshi zatayi kan Hawwa taji an riketa gam juyowa tayi daidai Ammi na dauketa da mari jikake tasss! Hawwa ta zabura tana kokarin mikewa ganin yanda Ammi ta zubamata mari but takasa tashi, Ni’ima ta dafe kuncinta tana kallon Ammi da jan idanu, Ammi tace “kika kara maganan banza anan saina sake daukeki da wani marin shashasha” Ammi takalli Baban Yaseer dake tsaye yana kare Hawwa cikeda fushi tace “tashi agaban yarinya na bar wajen nan, tashi nace!” ba musu yatashi ahankali yakoma wajen kofa ya tsaya ranshi in yayi dubu yabaci sabida abinda Ni’ima keyi, Ni’ima takalli Ammi idanunta jajir har lokacin kallon Ammi take tace “kika mareni Ammi? Ko uwata bata taba bari naba saike”?Ammi na kallonta jin maganganun datake rai abace tace “saisa ni nake tayata bawa diyarta tarbiya, kika karamin gara gara anan saina sake daukeki dawani marin, you’re very, very and very stupid Ni’ima hauka kikeso kiyi sabida namiji? Eh?” Shigowa Baba yayi zuwa wajen ya tsaya kusada Ammi babu alamun wasa akan fuskanshi yace “meke faruwa Zainab”? Ni’ima Ammi ta nuna tace “Malam Ni’ima tana daya daga cikin dalilan dayasa Hawwa kenan wajen” azuciye Ni’ima tace “menayi? Nakira yarku na yanke alaka da ita, naja mata layi, bansonta arayuwana dayake mayya ce, bakar mayya mara zuciya ce ita wacce tai kwantai haka ta dinga bina tanajan gwuiwowinta akasa tana rirrikeni tana kuka tana karna rabuda ita, nikuma na tattake hannuwan banzan nawuce nayi tafitata” sosai Baban Yaseer ke kallonta hakama Baba da Ammi yanda take magana kaman ba Ni’ima ba, can a sweet person turn monster over night? Sabida namiji? Ni’ima tace “mijina nawane kadai wlh, ba best friend ba ko kanwata ce saina jamata layi wlh, kugayama yarku tafita daga harkan mijina” nuna Baban Yaseer Ammi tayi tace “ga mijin naki nan ai shiya kawo kanshi nan, dau abinki kubar nan” cikeda rashin kunya tace “eh zan dauki abuna amman saina gama, yar iskan yarku kokarin sumbatan mijina take, mara kamun kai da natsuwa, Hawwa zata iyama maza fyade sabida tsabar bukat……” tsawa Ammi daka mata tace “Ni’ima!” Rai abace sosai tace “nasan waye Y’ata! Jedai ki bincike mijin naki, munsan kalan tarbiyan da muka bata” ganin Ni’ima zatai magana tabi Ammi da chachan baki yasa Baba yakalli Baban Yaseer strictly yace “Aliyu dauki matarka kutafi, mungode Allah saka da alkhairi” cikeda tsantsan rashin kunya Ni’ima tace “ba dole kace ka gode ba anci kudin mijina an koshi, yazo yabiya kudin asibiti da kudin magani, mayu kawai kwadayayyu masu neman kai da yars……” fizgota Baban Yaseer yayi yajuyo da ita tai facing nashi ganin abin nata yazama hauka yadaga hannu zai kwasa mata mari Baba yace “kul!”
Washegari Sunday around 11 tafito su Hamza na samata komi a booth, Baffa yace “Hawwa ayi tuki ahankali kinjini” murmushi tayi tace “toh Baffa na” Ammi tace “Allah kiyaye hanya, dan Allah banda gudu” Gyadamata kai Hawwa tayi su Ramla suka rungumeta tamusu sallama tafito, text tama Ni’ima tace “gani nashiga hanya zan dawo office gobe”.
Karfe biyu dawani abu anadai neman karfe uku Hawwa ta shigo Abuja hanyan hospital din su Ni’ima tawuce direct ta shiga tai parking ta kashe motan, wayanta tadauka tafito abayane ajikinta baki tawuce ciki office din Ni’ima tawuce tareda knocking tana budewa wata nurse ce aciki tana ganin Hawwa tai murmushi tace “wajen Ni’ima kikezo? Bakuyi wayaba ai batanan yau is her off” amutunce Hawwa tace “okay okay nagode” tajuyo tafito motanta tashiga tafita daga hospital din wlh she’s so worried rabon datai magana da Ni’ima tun Friday wani irin fushi Ni’ima keyi da ita haka, hanyar gidansu Ni’ima tayi har zuwa layinsu mai kyau, gaban gidansu ta tsaya tai horn maidaidaicin gidane mai kyau ga babban bakin gate nasu, lekowa mai gadin yayi Hawwa tadanmai murmushi tana jiran taga yabude gate saitaga yabude karamin gate da fara’a kan fuskanshi yace “Hajiya barka da yamma” gyadamai kai tayi tace “ya kuke” yace “Alhamdulillah” saikuma ya tsaya sakaka yana kallonta Hawwa tace “budemin gate ko basanan ne”? Bazai taba iya maimaita abinda Ni’ima tacemai ma hakan yasa dasauri yace “eh basanan tun safe suka fita” danjimm Hawwa tayi kaman daga sama sukaji muryan Yasmeen ta tsandala ihu tana kuka wayyo kafanta dasauri maigadin yakalli gate saikuma yajuyo yasauke kanshi kasa, Hawwa dake juyo muryan yaran tace “kace basanan ba muryan Mims naji na kuka ba” dan sosa kai yayi da hannu kanshi na kasa yakasa kallonta yace “ahhhmm Madam tacemini duk randa nakara barinki kika shiga gidan abakin aikina kiyakuri Hajiya” dasauri da kunya yajuya ya shiga gidan tareda maida gate din yarufe Hawwa tai shiru tana wajen she don’t even know wat to think, her mind just went blank wlh takai minti ashirin awajen kafin tadan fuzar da iska taja motan tabar wajen.
[9/23, 8:52 PM] M Shakur: 💫GARGADAN SO💫
✍🏻M SHAKUR
EPISODE 3️⃣7️⃣
Kusan 5min Khaleel da Baba sukai ahaka sannan yadaga kanshi daga kafadan Baba yakalli Baba yace “kahuta? Kadena damuwa”? Gyadamai kai Baba yayi yace “nahuta Ibrahima” sauka Khaleel yayi yadauki crutches din yabashi Baba ya karba suka fito tare, Ammi bata wajen hanyar dakin sukayi Khaleel yaci tura dagadan nesa Baba yajuyo yakalleshi yace “bazaka shiga ba” dan sosakai yayi saikuma ya dauke kai ahankali yace “uhmmm kunyan nakeji” dariya Baba yayi irin na manya dinnan jin maganan dayayi yace “kunya? Wai kunyan Ammi”? Dasauri Khaleel yajuya yana gyadamai kai yace “bye Baba sai munzo anjima” kafin Baba yayi magana har yayi kofa su Salman dake wajen suka budemai kofa yafice suka bishi Baba yace “jama’a wannan yaro akwai shiga rai, Ya Allah inama Hawwa na kwadayinsa sosai, Allah inhar alkhairi ne auren nan kasa ya tabbata yau” yayi maganan a yana shiga cikin dakin da murmushi kan fuskanshi yayi inda Hawwa take dake bacci anmata allurai da dama, Ammi na zaune ta buga tagumi ganninshi yasa Ammi takalleshi da damuwa akan fuskanta, Baba yajuyo yaja kujeran plastic chair ya zauna cikeda farin ciki yace “kidena damuwa Zainabu kiyi addu’a inhar Ibrahima rabon Hawwa ne kuma mijinta ne yau za’a daura mata aure” dasauri Ammi ta kalleshi tace “waye kuma Ibrahima Malam”? Labarin Khaleel yashiga bata all abubuwan daya sani, tai shiru Allah yasani yanda taga Khaleel yayi da Baba taji ya burgeta, banda haka Ni’ima said some disturbing about Hawwa, ita mace ce, sannan ita uwace, ko yara irin su Ramla sunsan sha’awa yanzu, Hawwa ba yarinya bace, babu bawa da baida sha’awa, tanaso Hawwa tai aure ta sami natsuwa da kwanciyan hankali, ba maza Hawwa kebi ba, bata iskanci so dole ne a irin shekarunta taji yana bukatan namiji, tabbas Hawwa na bukatan natsuwa, abun yamata, 50/50 Ammi keji azuciyanta, one side na zuciyanta ya goyi bayan auren sabida abubuwan da Ni’ima tafada especially bukatun Hawwa kafin yarsu tafada halaka, kota kauce hanya amata auren, zuciya ba kashi bane tsokace duk yanda takai da karfin imani shedan zai iyacin galaba akanta wata rana idan takasa hadiye sha’awar, another bangaren zuciyanta kuma zaiso ayi bincike akan koma waye Ibrahiman but idan aka tsaya bincike kafin agama yaron yagudu ko yace yafasa fa? Cus abinda ke faruwa kenan dazaran sunzo su gudu, yagudu yaushe Hawwa zata kara samin wani yafito ga Ni’ima ta tasata agaba? Sotake tai aure tai nisa da anguwan ta huta da bakin cikin Niima, she kind of reason with Baba sabida yanda samari ke guduwa gwara su kama Khaleel dinnan as earlier as possible, zata taya Hawwa addu’a Allah ya albarkaci auren ya kauda fitina su sami fahimtan juna, amman dai tai auren Hawwa na bukutan natsuwa kafin tafada wani hali, ganin tai shiru tana tunani yasa Baba yace “kin yarda Zainab? Dan banso mukara fada yanzu komi yawuce, ni da kene iyayen Hawwa, banda mu batada kowa, ada nai kuskure dana dinga bala’i dake, gayamin abinda ke ranki dan hukuncin nan tare zamu yankewa yarmu” murmushi Ammi tayi jin yanda Baba ya girmamata yabata matsayi yakuma karramata, anatse tace “na yarda Malam, nakuma aminta idan Alkhairi ne Allah yasa su dawo adaura idan ba alkhairi bane kuma Allah ya musanya mana yabata miji da gaggawa” Baba yace “Ameen Ameen” yana murmushi suka cigaba da hira, abinci aka kawo musu akace an riga an biya kudin abincin duk sukaci Ammi takira Ramla tace kartai girki, tabama Baba wayan Hawwa tace “Malam kira wajen aikinta ka sanar dasu tayi hatsari” Baba yace “nemomin number kaman DIG naji tana kiran Ogan nata duba kiciromin number” Ammi ta karba tana ciromai.
WAIWAYE BAYA KADAN..!
Ana fitar dasu waje har parking space aka kaisu aka tsaitsaya akansu kaman barayi, Salman yace “you have 10secs to leave this hospital else we hand you over to police and press charges against the both of you, we have cctv camera in every corner of this hospital starting from patient room” kallonta Baban Yaseer yayi yanda take kallonshi tana haki, ranshi ya baci iya baci da abinda tamai, baitaba sannin this is who Ni’ima is ba sai yau, cikin kakkausan murya yace “daganan kiwuce gidanku, namiki iyaka da gidana zankira mai gadi na shaidamai kada ki shiga gidan nan, kije na sakeki saki daya!” Faduwa gabanta yayi sosai zatai magana kawai yabude motan yashiga yawuce tabishi da kallo kirjinta na bugawa, Salman yadaka mata tsawa. “Madam leave our hospital!” Jikinta har rawa yake ta wuce ta shiga tata motar ta kunna tabar asibitin.
School nasu Yaseer yawuce direct ranshi na suya ya daukosu yace zasu danyi tafiya na 2week, sukaje gida yahada kayansu tundaga kansu Ipad yasasu a mota kawai sukai Kano gidan iyayenshi sukaje yakaima mahaifiyarshi yaran sunata murna yace suyi kwana biyu yasayo musu komi washe gari yabar Kano da sassafe danso yake yaje yaga Baba he made up his mind zai auri Hawwa yanzu, he wants to make her his wife.
****
[9/23, 8:52 PM] M Shakur: 💫GARGADAN SO💫
✍🏻M SHAKUR
EPISODE 3️⃣6️⃣
Chak Baban Yaseer ya tsaya sabida yanda Baba yahanashi, Baba na kallonsu yace “ba’a dukan mata barta da halinta kutafi kawai, Ni’ima karki damu babu ko biyar na mijinki a asibitin nan, kutafi Aliyu” kunya ne yakama Baban Yaseer kaman kasa ya tsage yashiga ciki, yajata da karfi yace “let’s go” tutturjewa take tana kallon Hawwa dake zaune abakin gadon gwanin ban tausayi tana goge hawaye dake zubomata da sun kasa daina zubowa, Ni’ima can’t even describe yanda takejin tsanan Hawwa kawai so take ta mutu atleast idan ta mutu zata huta, Baban Yaseer zai natsu, ina jitayi bazata iyaba a haukace ta fizge hannunta kaman mai ciwon hauka ta taho tace “Wlh wlh saina kasheki banga dalilin da mijina zaifi sonki akaina ba, yana kirana dakikiya sabida ke ba, he’s telling me kinfini komi” kawai Ni’ima tai kan Hawwa da sauri Ammi ta zauna tana kama Hawwa zuwa jikinta dake sheshekan kuka ahankali dabai fita irin hurtful cry dinnan dayake fita daga soul naka, azuciye Baba ya tare Hawwa da Ammi yakama karfenshi daya a hammata gamgam yazare daya yarike a hannu yadaga sama, daidai Baban Yaseer na kamata tana ihu da karfin gaske, Baba yace “Idan ban miki karatun Alam nashara da karfen nen ba ba sunana Baba ba, hauka kikeyi ne? Nace hauka kikeyi ne? Ni’ima kin haukace ne? Kinmanta kawarki dakuke zuwa wajena nabaku kwandala kwandala na siyan alawa? Ni’ima Hawwa fa dakike fushi dani idan na bata mata rai? Sabida miji Ni’ima kikema kawarki fatan mutuwa? Ina amintan? Ina kauna da soyayya ina? Ina zumunta? Duniyan nan duka duka guda nawa take? Dudda ina nemawa y’ata miji har ina bada sanarwa a masallaci mesa bantaba mata kwadayin mijinki ba? Kin taba tunanin maisa ban ma Aliyu tayin Hawwa ba? Sabida nasan ayanda y’ata ke sonki bazata taba so ta auri mijinki ba! Nima bazan taba kaunar ku lalata zumuntan ku ba! Ni’ima haukacewa kikeso kiyi ne? Kunfi shekaru ishirin kuna tare meyayi zafi haka? Auren Aliyun tayine menene haka? Bakida lafiya a kwakwalwanki ne”? Tana kallon Baba tana fizge fizge da Baban Yaseer tace “eh hauka nakeyi Baban Hawwa! Akan Aliyu zan iyafin hakama haukacewa, yarka ta kiyayi mijina kawai kagaya mata, ta kiyayeshi!” kallon Aliyu Baba yayi yace “Aliyu dudda bansan ko Ni’ima ko wacece wannan ba amman dauketa kubar wajen nan kar raina yabaci” daidai lokacin some Doctors da Nurses da security na shigowa dakin, senior consultant dinsu yace “what is going on here? This is hospital not arena, why are you all traumatizing my patients? Everyone outside” Fizge hannunta Ni’ima tayi kaman mahaukaciya tana kallonsu tace “sakan mini hannu” takalli likitocin tace “patient dinku tai kwantai batai aure ba, ubanta gabaki daya yagaji da ita har tallanta yake gida gida lungu lungu, shine yanzu suke kokarin a manna ma mijina ita” Dr yakalli Baban Yaseer dake faman riketa yace “Sir I know you are a Muslim and bazaka so nasa security maza su dauki matarka ba, nabaka 30secs idan baka dauketa kun fitaba zansa maza su fitar da ita this is hospital not wrestling arena, munada patients dayawa dakuke tayarma da hankali, we can sue her for this, please kindly take her out” Aliyu da kunyan dubiya yasa jikinshi ma yayi sanyi yakai hannu zai dauketa ta fizge tareda tureshi takalli Hawwa dake kallonta idanunta sunyi jajur sabida kuka tanuna kanta tace “mijina zakibi Hawwa? Mijina? Wlh wlh saidai ki mutu ko nida ke mu mutu tare daki auremin miji” tana maganan tai wajen gadon Dr yama security guys magana sukai kan Ni’ima suna tareta suka rirrike mata hannuwa Ni’ima tafara ihu na boo 👻 mutum tace “jama’a azo aga husband snatcher, wacce bakin halinta yasa for almost 30yrs babu wanda ya aureta, ubanta ma yagaji da ita neman kai yake da ita, infact yar iska ce, amfani take da kanta da daddare sannan take iya bacci, nitake kira ina bata maganin rage sha’awa kullu yaumin, aure takeso idanu rufe, da ace tanada mashinshini da tuni tabi maza sabida yanda takeda bakin jaraba, Hawwa harija ce duk dare saitai kukan neman namiji” wani irin nishi Hawwa tafara jin yanda Ni’ima ke tona mata asiri da karya da gaskiya zuciyanta yafara bugawa da karfi security sukai waje da Ni’ima, Ammi na ihu ganin yanda Hawwa keyi “Dr something is wrong with Hawwa na Innalillahi” akai kan Hawwa ana sa Baba da Ammi su fita waje.
A reception Ni’ima tacigaba da ihu mutane na taruwa patients na fitowa daga daki suna lekowa aga meke faruwa, kaman ba ita ake jaba tana nuna Baba da Ammi dasuka fito suna kallonta tace “wazai taimakama tsohon nan ya auri yarsa datai kwantai ba miji? Bai bama yarsa tarbiya ba sabida ciyar dashi datake yasa maza ke tsoron aurenta, itace komi nashi babu abinda yake tsinanawa sai gulman yan anguwansu, kunsan yarsa har gayu takeci tasa janbaki kowani zai ganta yace yanaso amman shiru babu machinchini” “get this mad woman out of this hospital!” Sukaji muryan Khaleel dayasa kowa yajuyo har Ni’ima da Baban Yaseer daidai Khaleelna saukowa daga staircase, tundazu yana asibitin nan but yana office dinshi asama, karasowa yayi yana tafiya daidai kaman sarki ya tsaya daidai gaban Baban Yaseer dake kallonsa batare daya kalle kowa na wajenba sai Baban Yaseer din yace “take this mad woman and this photo husband of hers out of my hospital and duk randa nakara ganin any of them in my hospital I will fire tundaga gate workers to workers na reception din nan!” Yayi tsawan da saida wajen ya dauka, kawai Baban Yaseer yaga exra security na zuwa aka rikemai hannaye both side kaman baraw idanunshi cikin na Khaleel dake kallonshi irin kallon sworn enemies dinnan kawai aka jashi har sukakai wajen kofa kallon Khaleel Baban Yaseer yake sannan aka fitar dashi da matar tasa….
Suna fita Baba kawai yaji jiri na dibansa yayi baya zai fadi dawani irin sauri Khaleel yazo wajen yatareshi ahankali yace “Baba!” Kallonsa Baba yayi ahankali, ganin hawaye na tsatsowa a idanun Baba yasa da sauri yakama hannun Baba yasa akan kafadanshi ya karbi crutches nasa daya yamikama Salman sannan yawuce da Baba yana dinginshi zuwa wani office dake wajen Ammi tabisu da kallo tana mamakin waye mutumin nan?.
Zaunar da Baba Khaleel yayi kan gadon dakin Salman yashigo yabashi crutches din ya karba ya ijiye yawuce yafita sannan yadawo wajen Baba stethoscope dake office din yadauka ya makala a kunne sannan yadauki abun auna BP yazo wajen gadon yadan kalli Baba in very cute and dan shagwaba voice yace “Baba don’t pay attention to whatever she says” yashiga auna BP Baba duk Baba yana kallonshi, chan ya saurari pulse nashi da heartbeat sannan ya ciccire komi yace “jininka yahau kadan a little sleep da magani will help zansa akawo ma” yajuya zai fita ahankali Baba yace “Ibrahima!”Juyowa Khaleel yayi ahankali babu wanda yataba kiran sunanshi ahaka sai Baba, tsayawa Khaleel yayi gaban gadon gently Baba yace “kaima likita ne”? Ahankali Khaleel ya gyadamai kai yace “eh” gyadamai kai Baba yayi saikuma ahankali yakai hannayenshi dake rawa rawa yakama duka hannayen Khaleel yarike Khaleel ya kalli yanda yarikemai hannu yayi shiru, baki Baba yabude ahankali zaiyi magana saiya fashe da kuka irin na manya dinnan, Khaleel yayi shiru yana kallonshi sai