tayi niyyar kwanciya tabi lafiyar gado tunda babu Islamiyya, wani littafin Hausa ne ta sato a dakinsu Adda Maimunatu, tasan cikin tsofin na Adda Zahra ne kafin bikinta, dan itace mayyar karatu, da yake Hajja bata hanasu, kawai dai wani lokacin zatayi ta fadane in karatun ya hanasu tashi suyi aikin da yake gabansu. Sai dai kusan duk yayyensu maza basa son ganinsu da littafin Hausa, Yaa Khalifa ma yagawa yakeyi, in bakayi wasa ba saiya kwadeka kafin ya kwace littafin, shisa inta dauko saita shige dakinsu ta kwanta ta karanta.
Karatunma saita rasa abinyi takeyi dan ba damunta yayi ba, inta cika kallon takardar sai taji idanuwanta sunayi mata yaji. Duk da haka gara suyi yajin da taje wajen bikin nan, bata da yanda zatayi, haka suka shirya, duk surutun da Khairi ta dingayi bai hanata daukar wani farin hijabi ta zunduma ba, ita da saka hijabi bai dameta ba, cikin wadanda ta ware ne na sallah, sai dogon takalminta. Ko Hajja data ganta saita girgiza kai kawai batare da tace mata komai ba. Mota biyu aka daukesu a ciki har Tudun Wada, taji Hajja na cewa in sunje can sai a daukesu tare da yaran gidan a wuce dasu inda ake kamun bikin. Ita dai Maryam lokaci zuwa lokaci saita tabe baki.
A bangaren Umma Fadime suka yada zango kamar yanda suka saba, har mamakin yanda su Kubra suketa dokin bikin takeyi, zaka rantse wani muhimmancin suke dashi wajen Hajiya Rumanan dama yaran nata. Ita dai ido ma take ta binsu dashi, gara da Adda Aliya ta shigo, itace babbar 'yar Umma Fadime, kuma jininsu ya hadu matuka da Maryam, tayi aure, bata haihu da wuri ba, yarinyarta daya, Huda, duka shekarar yarinyar biyu
"Wai ke nan kikazo kika wani takure"
Tayi dariya har hakoranta suka bayyana
"Tunda naganki dan Allaah taso ki shiryamun Huda, makotana ne suka zo inaso in zuba musu abinci"
Sai ta tashi kuwa, ta cire hijabinta ta ninke, tana bin bayan Adda Aliya, duk wannan dacin ran da takeyi yabi iska, da Khairi ta ganta dariya ta dingayi, Maryam din na mata kama da wadda ba zata rasa iskokai ba, su hau su sauka. Kuma saboda Adda Aliya da ta dauko mata mayafi ta bata sanda za'a tafi wajen kamun, ta ninke hijabin ta saka a jaka ta karba
"Haba ko kefa, kamar ba 'yan mata ba, inace kun shiga ss1 yanzun, ke da nake so nan da shekara biyu ace mun naki bikin zamu sha..."
Maryam ta sunkuyar da kai tana dariya a kunyace
"Kai Adda..."
Adda Aliya ma dariya tayi
"Ko kema karatun zaki tsaya? Yarinya kiyi aurenki, ba gamu ba, auren ya hanamu karatun ne? Allaah dai ya fito muku da mazaje nagari"
Sai ga Maryam ta tafi wajen kamun da tunanin maganganun Aliya fal a ranta. Wai itace zatayi aure? Su duk bikin da akayi a gidansu babu wanda akayi party, harna matan, amman ana shirya Kamu, wannan Abba baya hanawa tunda taron mata ne, ko 'yan uwansu maza basa zuwa wajen. Kuma yana kayatar da ita, sai dai haka kawai taji inda ace za'ayi partyn ma tanaso, ko irin wannan kamun da sukazo, akwai maza da mata a wajen, sannan ita Munira din tasha shigarsu ta gargajiya ta Kanuri, a karo na farko tayiwa Maryam kyau, ga angon daya riko hannunta shima ya hadu, bakine kamarta, dogo sosai, dan duk da takalman da Munira tasa kanta bai karasa kafadarshi ba.
Itama ace haka zasu shigo wajen taro da nata angon, kuma wai saiga tunaninta ya hasko mata Ishaq, zuciyarta tayi wata irin bugawa, musamman data hangeshi da farar shadda kal, ya zaiyi a cikin fararen kaya? Tama taba ganinshi da fararen kaya kuwa? Zata so ta ganshi da fararen kaya, ta tabbata zaiyi kyau.
"Yau sai Munira tayi mun kama da Haris"
Wata da suke zaune a teburi daya ta fada, dan Maryam ta zauna inda Adda Aliya take ne
"Kai haba dai? Aisu suna kama da Baba ne kamar mu, shikuma Haris kamarshi daya da Mami..."
Cewar Adda Aliya, maganganunsu na kutsawa cikin tunanin Maryam, sai ta sake kallon Munira, ta kuma kalli Adda Aliya da take jajur kamar ka taba jini ya fito, dariya ta kusan kwace mata, taya ma za'ayi ace suna kama da juna? Ko kuma ita Munira na kama da Baba, ko dai ba Baban Tudun Wada take nufi ba? Kawai dai tace daga Munirar har sauran 'yan uwan nata, dashi Haris din na kama da Mamin shine abinda zaifi kama hankali.
"Wai baizo ba Haris din?"
Adda Aliya ta girgiza kai
"Ba zai samu damar zuwa ba, yana Italy"
Tunda Mami bata gajiya da fadawa duk wanda zai saurara cewa Haris baya kasar tun da ya tafi, har sun gaji, musamman da aka fara taron nan, zakaji tana
"Dan kiramun lambar Haris, ta Italy din"
Abinma dariya zai baka, in kaga yanda takeyi sai kayi zaton akwai bakon ketare Najeriya a cikinsu, musamman ita Hajiya Rumanan da karatunta ma kacokan a kasar waje tayi, ko dan Haris din ya zamana mutum na farko daya bar kasar da sunan karatu shisa abin yakeyi mata dadi oho. Maryam dai baki ta tabe, in ba dole ba ko maganarsu batason ji, tasan matar ba wani sonsu takeyi ba, koma tace ba son kowa takeyi ba, itama kuma batare da wani dalili ba tun asali batayi mata ba, daga ita har bakaken 'ya'yanta.
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng