x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 5 - LABULE ASIRIN MAI DAKI free pages

  • 12001 words
  • 15000 words
  • Out of 16315 words

Category: Love Stories

Views 93

25 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
Baban, ko kuma haka zaice nashi Baban baya magana dashi baisani ba, bambancin dai ba wani mai yawa bane, kawai dai yaga Logan bai damu da rashin nashi Baban a rayuwarshi ba, shikuma ya damu, ya damu sosai, har yanajin wani fili da rashin Alhaji Mustafa ya bar masa, filin da ko tarin tarkacen kayan daukar hotunanshi bai maye masa gurbinshi ba balle kuma wiwi, ko azo maganar matan daya rasa dalilinsu na like masa da binshi duk inda zaiyi. Tun zuwanshi yaga yanda mata suke sonshi, basa kuma gajiya da fada masa yana da kyau, musamman idanuwanshi.

Idanuwan ya sani, tunda shima ai yana ganin kyawunsu, amman fuskarshi koshi din gabaki daya baya tunanin yana da wani abu da zasu dinga binshi har haka. Bawai sonsu bane bayayi, mata sunyi masa, sosai, tun a Maiduguri ya gano wannan bangaren nashi, ya kuma tabbatar da abinda yasa akace mata sune abokan rayuwa, akwai wani abu mai laushi da yake so a tare dasu, ko rauni zai kirashi bai sani ba, ko hannun mace ya rike a cikin nashi saiya dinga kallon bambancinsu yatsunsu, yanda na matan yake kasancewa sirara, da wani laushi na musamman yana masa kyau, shisa baya taba gajiya da rikewa, balle nan din da suke ba jikinsu muhimmanci, ansa farata da suka sha kwalliya, duk da bayason ya gansu dogayen nan, ya fison ganinsu gajeru.

Ko da akayi musu hutun lokacin yayi shekara daya harda wani abu, ya mayi kwana biyar a gidan Alhaji Modu, da Hajiya Rumana tayi masa tayin komawa gida yayi hutun saiya tsinci kanshi da amsa gayyatarta, yana so yaje yaga Alhaji Mustafa, suyi magana, saboda yana so ya dinga kiranshi a waya suna gaisawa ko da ba kullum ba. Sai gashi duk wani doki da yakeyi yabi iska lokacin da Alhaji Mustafa ya kare masa kallo daga shi har Hajiya Rumana ya furta kalmomin da yakejin zafinsu a kowanne sassa na jikinshi har yanzun

"Me yakeyi mun a daki? Me yakeyi mun cikin gida?"

Da tayi kokarin magana ma saiya kara da

"Ya koma inda ya fito Rumana, kema in kinaso zaki iya tattara kayanki kibishi, amman wallahi ba zai kwananmu a gida ba!"

Shi daya dauko kafafuwanshi tun daga Italy kawai saboda ya zauna a kusa da Alhaji Mustafa ko da gaisuwar da suka sabace suyi, shaf ya manta a wajenshi bashi da wani uban, Alhaji Mustafa ne kawai, kowa zai gwada, komin kokarinshi ba zai maye masa wannan gurbin ba, amman a wajen Alhaji Mustafa shi din wani dane cikin yaran daya haifa, dan da ko dashi ko babu shi zaiyi rayuwarshi hankali kwance, tunda ai daman idan namiji ne babba ya jima da gane shi din bakomai bane in dai Mukhtar yana nan, kamar dama can Alhaji Mustafa na neman maraba dashine yanzun kuma ya samu. Shisa hankali kwance yace wai ya barwa Hajiya Rumana shi, kamar wani abu marar muhimmancin da za'a iya kyautarshi hankali kwance.

Saboda Hajiya Rumana ne kawai bai nemi tikitin komawa inda ya fito ba, shisa ya kama hotel ya zauna abinshi. Kuma 2Pac na gari, daman sunyi waya, sai yazo suka shiga gari yawo abinsu. Kwananshi bakwai a hotel din nan, yana raba bacin ranshi da wiwi da mata. Baima san ana can ana rikici a gidansu da Alhaji Mustafa ba, dan saida Alhaji Sa'id da kanshi ya taka har gidan iyayen Alhaji Mustafa da mahaifinshi ya jima da rasuwa, ya samu 'yar tsohuwar nan ya fada mata abinda yake faruwa ganin aminin nashi ya botsare. Da shi da Hajiya Rumanan ta kira ta hadasu tayi musu nasiha sosai ta kuma ce masa in dai ta isa dashi tana so ya bar Haris ya janye kalamanshi, yama hakura da maganar gabaki daya tunda dai yaro ya fara karatu, kuma Hajiya Rumanan tace ta gane kuskuren da tayi harta bashi hakuri.

Da gaske ranshi ya baci irin wanda bai taba ba game da Hajiya Rumana, amman ai karya yakeyi yace baya kewar danshi, baya son ace yana cikin rayuwarshi. Daga gidan nasu ya tambayi Hajiya Rumana inda Haris yake ta fada masa, text tayiwa Haris tana sanar dashi cewar Alhaji Mustafa zaizo daukarshi, dan kawai jikinta ne ya dinga bata zai iya kasancewa Haris din na tare da wasu abokai da ba zaiso ace Alhaji Mustafa ya ganshi dasu ba. Aikuwa bama abokai bane ba, macece, macen daya sallama yana mika mata kudaden da baisan adadinsu ba tunda so yake ta tattara tayi gaba batare data ishe shi da wasu tambayoyi ba, a gurguje ya harhada jakarshi daya baje kamar ya samu dakin gidansu, ya shiga ya sake watsa ruwa, yayi brush, saida ya kusan karar da kwalaben turare biyu a jikinshi, har tari ya dingayi.

Sai yaba kanshi dariya, to me yake boyewa ne? Warin wiwin? Ko kuma kamshin matan da yake tunanin ya like masa? Me yasa yake boyewar? Alhaji Mustafa ne fa, daya nuna baya bukatarshi kwanaki kadan da suka wuce, amman yanzun daga ance zaizo ya daukeshi ya rikice, zuciyarshi har wani bugawa takeyi, kamar abinda yake ta jira kenan. Tare da Alhaji Mustafa suka koma, shi ya karbar masa jakarshi ya saka a bayan mota, sai direban daya kawo Alhaji ya dauki motar Haris din

"Da ka kawo mukullin na tuka Baba"

Haris ya furta a dan darare, Alhaji Mustafa ya kalle shi

"Ni Haris? Zan baka mukulli ka tukani salon ka janyowa matana takabar da basu shirya ba"

Sai yayi dariya, shima Alhajin dariyar yayi, suka shiga motar ya jasu zuwa gida, a hanya ne Alhajin yace masa

"Me kake karantawa?"

Haris yaji zuciyarshi ta matse a kirjinshi, shekara daya amman Alhaji Mustafa baima san abinda yakeyi a Italy ba, so yake ya bashi hakuri, sai dai bayar da hakurin ya zama wani abu da bai saba ba, baima san ta inda zai fara ba, muryarshi a hankali ta fito lokacin da yace masa

"Documentary and photojournalism"

Alhaji Mustafa yayi shiru yana juya ma'anar course din cikin kanshi, jin yayi shiru yasa Haris cigaba da magana

"Ni hoto kawai nake so in dauka, amman dana fara karatun kuma inaso inyi abubuwa da yawa, inaso duk hoton da zan dauka ya zamana yana isar da wani sako ne, irin hotunan da tarihi ba zai manta dasu ba, watakila idan nayi sa'a har dani din"

Yanajin shi, duk wata kalma da ta fito daga bakin Haris, Alhaji Mustafa yaji ta, a karo na farko yau danshi ya bude baki yana bashi labarin wani sashi na rayuwarshi, sai kuma ya zamana yana kokawa da fahimtarshi akan wannan sashin

"Wanne irin hotuna ne wannan Haris?"

Haris ya dan daga kafadunshi

"Nima bangama sani ba har yanzun, idan nazo nace maka inaso in zama war photographer zaka barni?"

Zuciyar Alhaji Mustafa ta buga daya hango danshi da ba soja ba, tsaye a filin yaki da camera a hannu, amman saiya tsinci kanshi da fadin

"Zanyi maka addu'a, Allaah Ya tsareka ya baka sa'a a duk inda zaka shiga akan kuma duk abinda zakayi"

Haris ya lumshe idanuwanshi, ya budesu wani sanyi da bashida alaka da AC din cikin motar na ratsa shi

"Ina kuma so inyi harkar transportation..."

Alhaji Mustafa ya sauke wani numfashi

"Wannan dinma yafi kwantamun, na kasa hangoka a filin yaki da camera a hannu Haris"

Dariya Haris din yayi mai sauti

"Allaah dama bindiga ce da sauki"

Haka suka dinga hira har Haris baiso suka karasa gida ba, da suka fita daga motar suka jera zuwa ciki saiya dinga jin inama ace Mukhtar zai leko, yau ya ganshi shine ya jero da Alhaji Mustafa suna hira

Ranar ta zama mafari
Ta kuma budewa Haris wata kofa da yake tunanin bashi da hanyar samun mukullinta a tare da mahaifinshi...



[24/08, 7:21 am] +234 903 572 3778: #LubnaSufyan ✨
#WomenOfWords
#09035723778 (WhatsApp)

Littafin nan na kudine akan #1k kacal, zaizo a manhajar Telegram ne kawai 20/06/2025 In Shaa Allaah, bayan mun kammala shafukan dandano.

Zaku iya biya ta: 9035723778 Opay, Lubabatu Sufyan.

NAGODE.

*

LABULE...Asirin mai daki

(Shafin karshe na dandano)

5

MARYAM

Ba wani haske na azo a gani Maryam take dashi ba, mutane da yawa ma in suka kalleta kai tsaye ba zasu kirata da fara ba, tana da kalar fatar da yawancin duka yaran gidan Alhaji Sa'id suke da ita. Sai dai babu siririya kamarta, rashin jikin natane yasa ake ganin kamar wani tsayi take dashi, sannan ita din ma'abociyar son dogayen takalma ce, suma suna taimakawa wajen kara mata tsayin da bata dashi. Yau dai duk wanda yasanta kallo daya zaiyi mata ya gane tana cikin bacin rai, haka inka matsa kusa da ita, rashin haskenta ba zai hanaka ganin shatin yatsun Hajja akan kumatunta na haggu ba.

Hijabinta a hannu ta dawo dashi yau daga makaranta saboda an yagashi tun daga wuya har kasa, uniform dinta da rigar ruwan madara, wandon kuma ruwan kasa, biji-biji kamar wadda tayi hakar rijiya, dambe ne kwasa a makaranta, tana da kawaye, ko tace 'yan ajinsu da suke shishige mata, ita bata cika shiga shirgin kowa bane saboda bata da hakuri, yau dinma wata 'yar aji biyar ce ta bangajeta da gangan, tayi magana ta zageta, ita kuma ta wanka mata mari, daman suna jin haushinta tunda tayi fada da kanwar yarinyar, da suke aji daya, shine su biyu sukayi mata taron dangi, a garin rabon fadan nema aka yaga mata hijabi. Dukan da akayi musu a makaranta na hukunci bai wani dadarata da kasa ba, inda sabo wannan ba komai bane ba.

Hajja ce da bata tsaya tambayarta abinda ya faru ba ta hauta da zagi yayi mata ciwo, kuma dan tace

"Ko gobe suka kara shiga shirgina sai sunji a jikinsu"

Shine ta mareta, danma wai Khairi tana wajen tanata bawa Hajjan hakuri kamar harshenta zai tsinke, haka sauran 'yan gidan da suke nan suka janye Maryam din suna kara tausar Hajja, mai hakuri bai iya bacin rai ba, ga Maryam da kafiya, shisa in takai Hajjon bango ba karamin duka takeyi mata ba, fadan saiya nemi komawa kan 'yan gidan, wanda duk yayi mata magana a zafafe take mayarwa, duk suka tattara suka fita harkarta, ta samu waje can kan kujera mai zaman mutum daya ta takure jikinta, abincin daren da suketa hada-hadar shiga kicin suna zubowa ana dawowa falon kamar yanda aka saba ita bata tashi ba

"Maryam in zubo mana?"

Khairi ta tambayeta

"Banaci"

Ta fadi can kasan makoshi, AbdulKarim da yake jinsu, yake kuma ganin yanda Khairi din ta kasa sukuni tun shigowarshi yaja karamin tsaki

"Ki wuce ki zubo abincinki kizo ki zauna kici kafin in kwadeki kema da kayan takaici, tun dazun kike binta tana shareki, ba saiki kyaleta ba da shegiyar zuciyarta ta banza da wofi"

Murguda baki Maryam tayi, shigowar Alhaji Sa'id ta hanata maganar da ta bude bakinta zata fada, anata yi masa sannu da zuwa yana amsawa, itama can kasan makoshi tayi masa sannun, yayi dariya yana zama tare da fadin

"Waya taba mun Auta ne yau?"

Akasa dariya, lokacin kuma Hajja data fito da babban farantin data hado masa abincinshi ta karaso, Abdulkarim harya tayata ta hanyar janyo teburin da aka saba dora masa abincinshi akai ya ajiye, ita kuma ta dora farantin

"Halan ke kika tabamun Auta yau"

Tayi murmushi, Alhaji Sa'id ya sake cewa

"Taho nan kinji Mairama, zo muci abinci tare, kina zaune duk zasu nemoki allura ai"

Maryam din ta saki fuska tana murmushi

"Waye zatayiwa allura? Wai Abba ka yarda yarinyar nan na da hakurin zama Nurse?"

Asiya tayi maganar da mamaki

"Ita ai ba Nurse take so ba, midwife tace...ko Mairama?"

Da sauri ta daga kanta tana murmushi, ta kuma baro kujerar da take zaune ta koma kasa gefen kafafuwan Alhaji Sa'id

"Midwife? Tafdin..."

Sagir yace yana kashewa da dariya hadi da dorawa da

"Irinsu ne masu marin mai nakuda"

Aikuwa akasa dariya

"Abba kana jinsu ko?"

Shima dariyar yakeyi

"Kyalesu, shima Sagir din kina zaune zai kiraki kizo ki taimakawa matarshi, zaki rama"

Wannan maganar da Alhaji Sa'id tayi saita rufe bakin Sagir din da yaji kunya, tare dashi Maryama taci abinci sunata hira kamar ba ita bace take ta fushi, a cikin hirar ne da dabara yayi mata nasiha kan muhimmancin hakuri da kuma rage fada

"Bakomai akayi maka zakace saika maida martani ba..."

Tayi shiru tana amsawa da

"In Shaa Allaah Abba"

Kamar da gaske taji maganganun, bayan duk wanda yake falon yasan ta bayan kunnenta nasihar take shiga in dai Maryama ce. Washegari kuwa da sanyi-sanyi take shirinta, kunun gyada akayi musu da fanke, an kuma yi kosai ga wadanda fanken bai damesu ba, ita duka biyun tanaso, dan in akayi fanke har diba takeyi ta tafi dashi, amman yau ko surutun da take damun kowa dashi batayi, tunda taga yanda garin yayi bakikirin alamun hadari taji komai ya fice mata daga rai

"Season din mutuniyar fa ya kama, yanzun bakin kowa zai huta"

Tanajin Asiya, bata da lokacinta, tunda har daki ta samu Hajja tace mata tana zazzabi, ko zata samu dalilin da zata fasa zuwa makaranta, sai tace mata

"Allaah Ya saukaka, saiki nemi paracetamol kisha, ki jefa wani a jakar makarantarki ki tafi dashi"

Ita Hajjan abin mamaki yake bata, tana tunanin tun Maryam na da shekaru biyu a duniya duk lokacin da za'a fara ruwan sama taji kararshi zata firgice ta saka ihu, har saida akayi zaton ko akwai shafar jinni a lamarin nata, haka aka dinga kawowa Hajjan hayakai da rubutu iri-iri, musamman dangin Alhaji Sa'id da suke neman fada a wajenta, harda garukan magani, ta karba da godiya, rubutun tasa aje a juye cikin kasa, magungunan kuma ta watsar. Tana girma suna gane kara tabbatar da babu wani Jinnu da suka shafeta, ruwan saman ne kawai take tsoro, koma ace duk wani ruwa da Maryam take ganin ba zata iya controlling ba. Da hankalinta sau daya ta taba zuwa saloon, shima haka ta kullo kan da kumfar da komai ta dawo gida ta karasa wankewa. Dan suna kwara mata ruwan farko taji tana neman shidewa saboda yanda ta firgita.

Ruwa ko a cikin fina-finai za'a nuno teku sai taji hankalinta ya tashi, tsoro ya shigeta, su basa tsoron su fada su mutu? Khairi ta taba ce mata

"Ruwan teku, su kogi da sauran ruwa daban fa Maryam, shi ruwan sama in ba Allaah Ya kawo annobar ambaliya ba ina kika tabajin wani ya nutse a cikinshi?"

Saita harari Khairin

"Idan kuma na santsi ya kwasheni na fadi, na buga kai, ruwan ya dinga sauka akaina ina shaqewa harna mutu fa?"

Dariya Khairi tayi ba 'yar kadan ba ranar

"Nifa gabaki daya na rasa me yasa bakwa tsoron ruwan sama"

Cikin dariyar Khairi tace

"Ke dai zance na rasa dalilin da zaisa ruwan sama ya dinga baki tsoro"

Ta jinjina kai

"Ai dalilin tsoronshi ya ninka rashin dalilin, ko kin manta tazarar tafiyar shekara nawa Mu'allim yace tana tsakanin sama da kasa ne? To ace tun daga can ruwan yake saukowa harmu samu, shi kadai ba abin aji tsoro bane ba? A karajin tsoron Allaah, balle kuma ace ruwan ya taho da iska, tsawa da cida, idan ina tsaye a fili akayi tsawar ta fado kaina na soye kuma fa? Ko ke kukan kwana daya zakiyi, a ranar ma kina iya cin amanata in dai za'a kawo shinkafa da miya, tsaf zaki share hawayenki ki saka plate a gaba"

Dariyar dai Khairi ta cigaba dayi, abubuwan da Maryam take tsoro a duniya, tasan ba masu yawa bane ba, in aka daga yatsun hannu ma za'a iya kirgasu, sai dai tsoron da take yiwa ruwan sama har tausayi take bata, saboda in akace damuna tayi to kusan ko da yaushe idanuwan Maryam din cike suke da firgici mai yawa, inda Khairi na da iko to zatace a dinga kyaleta tanayin zamanta a gida kamar ranaku irin na yau da duk wata alama ta nuna cewar ruwan sama za'a sheka, in dai zaka zauna da Maryam na yini daya a lokacin damuna saika fuskancin tsoron nan a tare da ita, ko fada bata cika yi ba, bata dama kuzari ne ko kadan.

In akace ruwan dare akeyi ko baccin kirki bata iyawa, farkawa goma Khairi zatayi zasu hada ido tunda kunna fitilar dakin takeyi ta koma can karshen gadonta ta takure kamar wadda take tsammanin shigowar 'yan fashi. Yanzun ma haka ta saka uniform kamar an zare mata lakka, tana ta kallon kowa ne zuciyarta batayi mata dadi. Adnan ne zai kaisu makaranta, saiga Alhaji Sa'id yama rigashi fitowa yace shi zai kaisu

"Abba ni zazzabi nakeyi"

Maryam ta fada kamar mai shirin yin kuka, daman hannunta a cikin na Khairi suka fito

"Zazzabi dai, ko na ruwan sama?"

Khairi ta danne dariyarta, idanuwan Maryam suka ciko da kwalla

"Babu abinda zai faru kinji, baki ga nine zan kaiku makarantar ba yau..."

Ita dai inda za'a barta zatayi zamanta a gidane

"Abba kaine zaka kaisu makarantar bayan duk gamu nan?"

Muryarshi ta fara isa kunnuwanta, wani dumi ya lullube ilahirin jikinta kamar an rufa mata bargo, ta tsinci kanta da sake dumtsa hannun Khairi da take rike dashi kafin ta daga kai a hankali, bakar rigace mai laushi a jikinshi data kara haska farar fatarshi

"Ai duk na hutar daku Ishaq, yau ni zan kaisu"

Murmushi ya danyi, ko tace labbanshi ne kawai suka motsa, kuma sai ya zabi ya saka idanuwanshi cikin nata

"Ina kwana"

Ta furta akan labbanta dan ko sauti ya fito ita bataji shi cikin kunnuwanta ba, sai ya kara fadada murmushin shi har hakoranshi na bayyana

"A dawo lafiya"

Yayi mata maganar irin yanda tayi masa, a karo na farko sai taji yau inda ruwan sama zai balle, kuma ace daga ita saishine a filin tsakar gidan nan, in dai har zai tsaya yanayi mata murmushi haka to zata tsaya a kasan ruwan nan tare dashi. Haka ta shiga mota, shikuma yana tsaye a tsakar gidan har sai dai motarsu ta fice, yana barin Maryam da tunanin ko yaushe yazo gidan? Ita dai harta kwanta jiya bata ganshi ba, a gefe daya kuma tana fatan Allaah Yasa harta dawo makaranta bai tafi ba, dan haka kawai tana so ta kara ganinshi.

*

Tasan ana biki gidan Alhaji Mustafa, bikin Munira,a bakin Hajja ma ta fara ji, kafin ta dinga ganin katikan bikin na watangaririya har a falon gidan, alamun an badasu da yawa, harda irin gate pass din nan na dinner din da za'ayi da kuma na wajen kamu. Da ta gani saita tabe baki, a ranta tana raya

"Waye zaije bikin wannan bakar yarinyar mai bakar zuciya"

Ai taga kokarin Hajja da take ta faman zarya tun ranar laraba, har wani anko akayi musu, yau ranta baya mata dadi tunda akace za'aje wajen bikin dasu, ita da
End Ads