Hajiya Inna ta rasu, kusan tafi kowa jin mutuwar 'yar tsohuwar a gidansu, ta jima tana kuka, har saida kowa ya dinga mamakinta. Kuma kusan Maryam zatace a wannan lokacin ne mutuwar ta bude mata ido, tasa ta fara fahimtar rayuwar gabaki daya dama abinda ta kunsa. Dan a lokacin ana gab da bikin Adda Maimunatu ne, tunda ita taki karatun, dakyar tayi diploma, tunda ta hadu da Yasir dashi sojane, ta rufe idonta, sonshi takeyi har bata iya boyewa a gaban kowa, haka Maryam zata dinga lekensu idan yazo zance, labarin Hajiya Inna na fado mata.
Wani labari da yaki barinta har yau, lokacin tana aji daya a sakandire Hajiya Innar ta basu shi, amman ko yau ta rufe idanuwanta tar muryar Hajiyar ke dawo mata
"Ai mu da Allaah Yayiwa tsahon rai muna ganin abinda ya ishemu, mu lokacinmu ai sai kayi sa'a ne ma za'a fada maka anyi maka miji, koni nan bansan kalar Alhaji ba sai bayan an daura mana aure, saboda yanda iyayenmu suka san cewa sun isa damu, ba zamu koyi numfashi mai karfi ba balle muyi musu kan hukuncin da suka yanke mana"
Da yake maganar ta zauna mata, duk da karancin shekarunta haka ta dinga juya zancen duk lokacin da zataji an saka rana ko kuma anyi aure, tana kara hankali tana mamakin yanda za'a daura maka aure da mutumin da baka taba gani ba
Ta ina zaku fara zaman?
Ya zakuyi a haduwar farko?
Me zakace masa?
Shi ma kuma fa?
Idan ita akayiwa irin auren nan ya zatayi
To wai idanma aka daura sai ta ganshi baki kato irin mazan da basa burgeta sai yaya kenan?
Dan ita duk a cikin abubuwan data dinga tunani, mafi muninsu shine ace namijin ya kasance baki, haka kawai bakaken maza basa burgeta, watakila dan mazan farko-farko da ta farajin sun kwanta mata a rai farare ne, fararen ma indiyawa, tunda gidansu mayun kallon indian films dinne harma da series. Duk sanda zata ga manyan matan gidan na zance in taga saurayin baki saita tabe baki, inta ganshi fari kuwa ta dinga fara'a kenan kamar wajenta akazo. Shisa a yau da ta hangi Adda Maimunatu da Yasir sai take jin inda ace yafi haka haske da anyi namiji mai kyau, da Addanta ta more miji, to wanda ya auri fari ai shiya more, ko wajen hotunan biki saima sunfi haskawa.
Ace dai farine kamar Hamma Ishaq din Baba Murtala, murmushi ya kwacewa Maryama, duka shekara daya da wani abu kenan da Ishaq din ya samu gurbin karatu a Zaria, taji ance Injiniya zai zama, da yake ba zata tuna fuskarshi ba sosai, Khairi dai bata cika hasken fata ba, kusan ita Maryam dinma ta fita haske, sai gashi ya biyo 'yan gidan da suke ABU din suma sunzo hutun karshen mako, Ishaq farine har wani dorawa-dorawa yakeyi, da gashin kanshi kamar ya kara tirawa, dogone amman bashi da jiki, 'yan gidansu sunce wai Khairi tafishi kyau, duk gidan Baba Murtala ma babu wanda aka tarawa muni irin Ishaq, saboda shi guntun hanci gare shi, sai wasu jajayen labba shi ba bature ba. Haka ta dinga kallonsu kamar basu san abinda sukeyi ba.
Ta ina za'a hada Khairi da Hamma Ishaq? Anya a wankan farko na jarirantaka an wanke musu idanuwansu da kyau kuwa? To ai a idanuwan Maryam duk wanda yazo a fari, musamman namiji, to cikin kaso dari na kyau dai ya tafi da tis'in, sauran goman kuwa ai ba wani abu bane ba, ballantana shifa ga gayu, ga kamshi, ga labbanshi irin na indiyawan da take gani a fina-finai. A zuwanshi na karshe gidansu, wajen satar kallonshi duk ana zaune a falo, ta dibo kunun aya, tayi tuntube tana shekawa Adnan shi a saman kai, ya kuwa kai mata wani duka da Ishaq ya tare mata yana fadin
"Ya za'ayi ka kaiwa mace irin wannan dukan Adnan? Ai sai kaji mata ciwo"
Shikuma Adnan din yaja tsaki yana mikewa, baiko ce musu komai ba
"Dawo nan kinji kanwata..."
Ta kalle shi, yanda ya ajiye kalmar kanwata din na zauna mata a wasu sassa na jikinta, shine abinda ya kashe mata jiki ya hanata mayarwa da Adnan maganar da tasan babu abinda zata janyo mata a wajenshi sai duka, a wannan ranar inda ace Maryam tasan cikakkiyar ma'anar kalmar da bature yake kira da "crush" da tace abinda ya faru da ita kenan akan Ishaq
Ya samu wani waje da yafi ko'ina laushi a zuciyarta yayi zaune batare dama ya sani ba...
[24/08, 7:21 am] +234 903 572 3778: #LubnaSufyan ✨
#WomenOfWords
#09035723778 (WhatsApp)
Littafin nan na kudine akan #1k kacal, zaizo a manhajar Telegram ne kawai 20/06/2025 In Shaa Allaah, bayan mun kammala shafukan dandano.
Yau Alhaji Sa'id yaje makarantar yaran ne ya biya musu kudi, wannan aikine da mazan gidan sukaso sauke masa tunda jimawa, amman yaki, har yau duk wani PTA da za'ayi, in ba uzuri na rashin lafiya ba da kanshi yake zuwa musu makaranta. Haka yakan ware wasu ranaku ya dauke su da safe ya sauke kowa a tashi motar, ko kuma yayi musu bazata ta hanyar zuwa ya daukosu, wani abu da baya gajiya da jin dadin yi, ko dan irin farin cikin da yake gani a fuskokin yaran nashi. Kowane da nagari baya bukatar dalilin da zaiso iyayenshi, da ace ana da bukatar wannan dalilin, Alhaji Sa'id zai kasance cikin iyayen da ba zasu taba gajiyawa ba.
Tun yana makarantar yake ganin kiran Hajiya Rumana, yasan ba zai wuce kara ta kawo masa ba, a lokutta da dama har mamakinta yakeyi, yasan inda zata iya rabashi da Alhaji Mustafa, data jima da yin hakan, sannan kuma bashi da wata daraja da kima a idanuwanta, ko yaranta in dai zasu hadu haka suke gaishe dashi kamar an cusa musu tsumma a baki, da yake sunyi gadon dagawa da jin kai irin nata. Amman kuma duk randa Alhaji Mustafa ya murde mata, bata da wanda zata kira sai shi. Saida ya gama abinda yakeyi, niyyarshi ma saiya koma gida ya karya, amman yanda ta dinga jera masa kira bayan kira ya tabbatar matsalar babba ce, shisa ya daga, aikuwa kuka takeyi kamar anyi mutuwa, har saida gabanshi ya fadi, bai ma fahimci abinda take fada ba, ya daiji Haris ya kuma ji Mustafa, sai yace mata gashi nan zuwa gidan.
Ya kuwa karya mota yana nufar hanyar Tudun Wada, da yake akwai 'yar tafiya, makarantar yaran na wajen Rabah Road. Yana isa, baima shigar da motarshi ciki ba, ya dai juyata yanda in yazo tafiya ba sai yayi hakan ba, kanshi tsaye bayan ya shiga gidan ya wuce bangaren Alhaji Mustafa, ya kwankwasa da sallama a bakinshi, da kanshi ya taso ya bude masa kofar yana dariya
"Yanzun nake zancenka a raina fa"
Cewar Alhaji Mustafa, sukayi musabaha, suna kara gaisawa kamar wadanda sukayi shekaru basu hadu da juna ba, kallo daya zakayi musu ka fuskanci irin shakuwar da take tsakaninsu
"Yanzun dinma kararka aka kawomun"
Alhaji Mustafa yaja tsaki mai karfi
"Karma ka fara shiga maganar nan Sa'idu, na riga na rantse saiya koma inda ya fito, in taga ba zata zauna ba itama zata iya tattara nata kayan ta bishi"
Ya karashe maganar yana haki saboda yanda ranshi ya kara baci lokaci daya
"Azumi uku dai, ai bansanka da raki ba"
Hararashi Alhaji Mustafa yayi
"Bafa wasa nakeyi ba..."
Ido ya dauka ya sakawa Hajiya Rumanan, daman jiranta yakeyi daga ita har Haris din. Tun lokacin da ya aureta ya fara gane halinta na jin kai da nuna isa, sannan da ace shi din namiji ne mai sanyi, ba karamin raini zatayi masa ba. Halinshi na kin daukar da yawa daga dabi'unta yasa ta dinga kokarin sauke kadan daga ciki, musamman akan danginshi da take ganin basu kai su rabesu ba. Duk da haka in sunzo din ba dadinta sukeji ba, akace shimfidar fuska ma wani abune, to harsu tafi in ba magana takeyi ba, babu wanda zaiga hakoranta.
'Yan uwanshi basu fara jin dadin kawo masa ziyara ba sai bayan daya kara aure, sai kuma ta tsiro da wani abu na kai masa korafi cewa yanzun duk wani nashi ya juya mata baya, basa ma sauka bangarenta saboda ya auro tasu, kuma suna ganin ita bata haihu ba, wani zubin ma kuka take sakashi a gaba ta dingayi, ai sunzo gidan taga sunayi mata dariya akan rashin haihuwarta, bai huta da wannan fitinar ba sai da ta samu cikin Munira, sai kuma bayan ta haihu ya zamana hankalinta kacokan ya koma kan yarinyar, kamar shi dinma bata da wani lokacinshi saina yarinyar, da yake yana samun duk wani abu da yake bukata a tare da Fadime sai bai wani damu ba.
Gwarne tayi tsakanin Munira da Anisa, duka shekara daya da wata hudu ne tsakaninsu, har a danginta saida aka nuna a dauke mata Munirar sai taji da rainon Anisa, in yaso idan tayi kwari sai a dawo da ita, tace bata bukata duk zata iya hadasu tayi rainonsu. Sun fara samun matsala da ita ne akan yaran, lokacin Munira na da shekara biyar, ta dauki kofin shayin data gama sha tana bugawa a jikin TV, yana zaune sai yayi mata tsawa, yanda Hajiya Rumana ta karaso ta dauke yarinyar da ta fashe da kuka, idan wani ya hango daga nesa zaiyi zaton makami ne a hannun Alhaji Mustafa
Kallon mamaki kawai ya dinga binta dashi a lokacin saboda yama rasa abinda zaice mata, a hankali kuma saiya kula da itafa akan yaran nan harshi bai isa ba, baisan abinda ya kamata dasu ba sai ita, kowanne irin hukuncine akansu in dai ba ita ta yanke ba to baiyi ba. Cikin danginta ma kafarta kafarsu, haka gidan iyayenshi, in dai ba tare da itaba, to yaran basa zuwa, yaran Fadime ma da yake tsoranta sukeji basa shiga bangarenta sam, saiya zamana tashin hankalin da Alhaji Mustafa ya dingayi akan ganin yaran sun shaku ya tashi a banza, shi dai ba wuni yakeyi dasu ba, wani zubinma sai yafi satika biyu baya garin. Sannan akan yaran Hajiya Rumana dai duk wata tufka da zaiyi yana barin gidan zatabi ta warware.
Da ta haifi Haris kuma sai abin ya kara ninkuwa, saboda soyayyar da take nunawa yaron ya wuce yanda za'a misalta. Haka aka cigaba da rayuwar, ya rasa yanda zaiyi da ita akan yaran, ga abin yana damunshi sosai, ko yanda su Munira suke mu'amala da danginshi a darare kadai ya isa abin takaici a wajenshi. A hankali kuma ya yarda Hajiya Rumana na daga cikin kaddararshi ne da babu yanda zaiyi da ita, abinda ya faru gaban idonshi dai zai tsawatar, shisa babu ma wata shakuwa a tsakaninshi da yaran, da yawan lokutta in suka gaishe dashi duk sai su bar falon, musamman Haris da yafisu sangarta, sai rashin jituwarsu yafi yawa da Alhaji Mustafa, tunda su Munira in fada yayi musu zasuyi shiru, harma su bashi hakuri.
Amman Haris sai yayi magana, sai yayi kokarin yin bayani ko dai ya fadi wani abin, duk zafin Alhaji Mustafa akan Haris ya fara dukan yaranshi, sukayi wata rigima da Hajiya Rumana har tayi yaji ta kwashi yaran ta tafi Maiduguri, rigima akayi sosai, tunda danginta sun goya mata bayane a fadan, dakyar Alhaji Sa'id yayi ruwa yayi tsaki ya shawo kan aminin nashi sannan aka samu dai-daito. Da yake a lokacin ma Haris din ya kammala primary dinshi, sai kawai ta nuna masa wata makarantar kwana ta kudi take so Haris din ya tafi, makaranta ce mai tsadar gaske da take a garin Kano. Da yaki amincewa dan yana ganin alamar kangara a tare da Haris din.
Yana gudun idan yayi nisa da idanuwanshi abin zai iya fin haka, da taga alamar kamar yana neman yaki amincewa, ya tafi Abuja, ya dawo ya samu Haris baya gidan, taje da kanta tayi masa duk wani abu daya kamata ta kuma biya kudin. Suka sake wani rikicin kamar zai saketa, nan ma dai Alhaji Sa'id ta samu, ya lallaba mata shi, sai dai har kasan ranshi bayason wannan makarantar kwanan da aka kai Haris, tunda ga 'yan uwanshi nan a Kaduna suke karatunsu, Mukhtar da Haris din ya ba shekara biyu, alamu sun nuna ma lokaci daya zai hada da gama primary din da kuma haddar Al-Qur'ani.
Kuma yawan misalin da Alhaji Mustafa yake yiwa Haris da Mukhtar idan yanayi masa fada ko yayi laifine abinda yasa Haris din baya kaunar ya bude ido yaga Mukhtar, saiya zamana in zai hadu dashi sau goma saiya kwade shi sau goma, ko da kuwa Alhaji Mustafa zai karyashi ne, Mukhtar dinma daya hangoshi yake neman maboya, babu jituwa ko kadan a tsakaninsu. Mukhtar bai samu salama ba sai bayan tafiyar Haris makarantar kwanan nan. Kuma duk wani tsoro da Alhaji Mustafa yake dashi akan nisan Haris shine yake faruwa acan makarantar.
Tun satin da aka kaishi, maganar da Hausawa sukayi na sai hali yazo daya ake abota ta tabbata akan Haris, da yake aji dayane su dukansu sababbin dalibai ne, lokacin ake kokarin fahimtar juna. A satin ya hadu da, Idris, Sulaiman da Yakub, kuma sai aka hadasy daki daya, haka suka samu sukayi musayar gadaje da wasu a cikin dakin yanda suka koma makotaka da juna. Basu hada wata a makarantar ba duk wani Malami daya kwana ya tashi saida ya sansu, shugaban makaranta ya haddace fuskokinsu, suka kafa tarihin kasancewa 'yan aji daya da suka gagari seniors dinsu. Idan wani laifin suka aikata, makaranta bata da contact din kowa saina Hajiya Rumana, idan ma aka nemi ganin mahaifinshi sai tace baya kasar.
Ita kuma ba fada take iya yiwa Haris din ba, duka yaran bakar fatarta suka biyo, gara Munira ita kai tsaye ba zaka kirata da baka ba, sannan fuskarta sak irin ta Alhaji Mustafa ce, hakama Anisa duk da bakinta dashi take kama, Haris ne duk yanda ake cewa ba'a gane kamannin jariri, a asibiti ma Nurses suka fara maganar yanda yake kama da ita. Hasken fatar da jarirai sukanyi Haris baiyi ba, da duhunshi ta haifoshi, kunnuwanshi bakikirin, aikuwa kafin ma ayi arba'in yayi baki, irin wannan duhun fatar Hajiya Rumana daya hadu da hutu yasa take wani irin kyalli, da yake tana da cikar gashin gira, sannan gashin kanta ma duk da bamai tsayi bane sosai a cike yake, ya kwanta luf har gaban goshinta, haka gashin idanuwanta ma, tana da irin kyawun da idan wasu manyan fashion houses din zasu ganta zasu kafa mata nacin zame musu model.
Wannan kalar fatar Haris ya biyo, cikar gashin da kuma kyan daga kallon farko. Yanda idanuwanta suke haka nashi suke, kamar da ruwa a cikinsu, in yayi dariya zaka ga ta isa har cikinsu, haka idan ranshi ya baci zaka ga kyallin bacin ran nan a cikin idanuwanshi, yana da irin idanuwan nan na kalilan mutane, idanuwa masu tonon asiri, wanda zasu haska maka har kasan zuciyarshi inka natsu a cikinsu. Shisa ko yayi kokarin kama bakinshi sai su fada maka duk wata kalma da bai furta ba. Wani irin so Hajiya Rumana takeyi masa da ita kanta bata san iyakarshi ba. Sone daya makantar da ita daga ganin laifukanshi, a wajenta kome Haris zaiyi kuruciya ce, zai bari idan yayi hankali. A wannan bigiren ya kammala ajinshi uku, ya kuma shiga aji daya inda ya zabi bangaren Art, tunda bason karatun yakeyi ba, yama fara kokartawa ne tun wani zagi da aka hadu akayi musu a staff room.
Wata Malama ta kirasu da
"Dakikai"
Kalmar nan tayi masa ciwo matuka, da yayiwa su Sulaiman magana kan ya kamata su fara maida hankali sai abin ya basu dariya, shi dai ya kyalesu ne tunda ba'a dole, ya dai fara canzawa ta bangaren karatun, shisa ya zabi Art din, a tunaninshi zaifi mishi sauki tunda akwai saukin lissafi a duka subjects din. Wannan shekarar itace tazo musu da sauyi daga shi har abokanshi, Idris duk yafisu girma, suna kiranshi da Barde, sai Yakub da soyayyar da yakeyiwa wani sanannen mawaki 2Pac yasa lakabinshi ya koma haka. Sulaiman daman ana kiranshi Lalaye ne tun suna aji daya. A lokacin Haris ne bashi da wani sunan banza.
Lokacin da suka dawo hutun first term na aji hudu a Sakandiri ne suka ga canji mai yawa tare da 2Pac, da yake su mahaifiyarsu bata tare da Babansu, tun suna primary suka rabu, gallazawar da mahaifinsu ya kula suna fuskanta ne ma yasa duk ya daukesu yana rarrabasu a makarantun kwana, sai dai babban wanshi da aka tura kasar Amurka, haka ya dawo ya zama rikakken dan shaye-shaye, yanzun haka wannan komawa hutun da 2Pac yayi ma an kai yayan Rehab saboda kwakwalwarshi ta fara samun matsala. Wani abu da iyayen 2Pac da ma abokanshi basu sani ba tun yana aji daya ya fara sha, daga maganin tari, saiya koma sato kwayoyin daya ke gani wajen yayan nashi, kuma sai kowa yayi bacci yake dauko daya ya rabata wajen gida takwas, saiya totse kashi daya yake iya samun bacci.
Kamar yanda dabi'ar masu shaye-shaye take, suna girma abin yana gaba, saiya zamana a hankali yake kara dosage din, wannan hutun daya koma kuma ya hadu da wasu abokan da suka girmi kanshi sai suka koya masa shan wiwi, da yake Baban 2Pac na tunanin zai cike musu gurbin rashinshi da na mahaifiyarsu hadi da gallazawar matarshi sai yake sakar musu kudi sosai da sosai, harma baisan abinda zaiyi da kudadenshi ba lokutta da dama, sai yanzun daya fara amfani dasu yana siyan wiwi. Itace yayi sneaking dinta da yawa, da yake abokan sun koya masa yanda ake boyonta, kasan takalman makarantarshi. Sai dare ya raba in ya nada saiya boye da lighter dinshi ya tafi bandakin makaranta ya zuqa.
Haris shiya fara kamashi, da farko ya tsorata, har saida sukayi fada da 2Pac din, amman abu na kuruciya, sai yanda 2Pac din yake nada wiwin ya kuma kunnata yana zuqa ya fara burge Haris, harya gwada shima, ranar farko kara daya ya zuqe bayan tarin daya dingayi a zuka wajen biyar kamar zai shide amman yaki hakura, sai dai maimakon cajin da yake ta kwadaita masa, sai yaji kamar kawai wani abune yake dan yawo a kanshi, bai bugu yanda ya kamata ace yayi ba. Kafin term ya