x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 4 - LABULE ASIRIN MAI DAKI free pages

  • 9001 words
  • 12000 words
  • Out of 16315 words

Category: Love Stories

Views 92

25 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
mun kai a banza?"

Hawayen daya ga sun sake zubo mata saboda yanda ranta yake suya da dukan da Alhaji Mustafa yayiwa Haris sai kace ya kama dan fashi. Ficewa tayi tabar masa dakin. Kaya kala hudu kawai ta dauka, saida ta sake watsa ruwa, sannan ta canza kayanta, tanajin gefen fuskarta ya tashi na dukan da ta tarewa Haris, tayi kwafa zuciyarta na wani irin zafi, bacin ran dukan da yayiwa Haris ya shafe mata komai. Ta riga ta gama tunanin matakin da zata dauka, ai sai yaga Haris dinne zai dakar mata shi.

Shikuwa data bari a daki saiya rasa abinda zai dauka, wayarshi dai tana cikin kayanshi daya dawo dasu daga makaranta, sai kawai ya samu wata karamar jaka ya zuba kayan da basu wuce kala bakwai ba, ya fita yana sa direban Alhaji Mustafa ya bude masa motarshi ya fito masa da kayayyakinshi duka ya kai masa daki, abinda yake bukata a cikin kayan ya dauka, lokacin daya sake fitowa har direban Hajiya Rumana ya juya musu motarta suka shiga, data fada masa Kano zasu je sai subi jirgi ta can, saida ya fita ya sake daukar wasu 'yan abubuwan da zai bukata.

*

Alhaji Jibril shine babba a dakinsu Hajiya Rumana, kuma tun bayan rasuwar iyayensu saiya dauki wannan girman nashi da muhimmanci ta yanda in har zai iya to ko quda ba zai gifta ta gefen kannenshi ba ballantana kuma wani abu na cutarwa, su daman zuri'arsu mutanene da suka gaji arziki na dukiya tun sale-sale saboda tsatsonsu na daga cikin kalilan da suka fara harkar siye da siyar da zinari tun a zamanin baya, 'yan kasuwa ne da 'yan boko da wasu a cikinsu suka rike mukamai, suke kuma rike dashi yanzun a mabanbanta wajaje a cikin gwamnati, wasu ma suna kasashen waje da iyalansu can suke zaune.

A soyayya irin ta Alhaji Jibril da kannenshi, basa laifi, abinda duk suke so shima shi yake so ko da akwai rashin kyautawa a cikin wannan abin, soyayyarsu ta shafe hakan a idanuwanshi, wani irin ahaline da sangarta da wayewa ta samu wajen zama a cikinsu, kuma yawancinsu kaf irin wannan soyayyar da suka tashi a ciki, itace suke kamantawa akan yaransu, ko da yaji abinda ya faru sai yafi ta harzuqa

"Wanne irin duka kuma? Wai har yanzun ba'a daina wannan gidadancin dukan yaran ba, ko da gaske shaye-shayen yakeyi ai janshi za'ayi a jiki a kara nuna masa soyayya aji meye matsalarshi shine zai daina"

Itama dai abinda tayi tunani kenan, sai dai duk wani kira da Alhaji Jibril ya dinga yiwa Alhaji Mustafa bai daga ba, bai biyo bayan kiran ba. Da yake sunsan Haris na ajin karshe ne, sai kawai aka kaishi daya daga cikin makarantun da yaran gidan Alhaji Jibril din sukeyi a matsayin external student, dan jarabawa kawai zaiyi. Shi tuni ma ya sake cikin 'yan uwa anata yawo a gari kamar babu abinda ya faru, musamman da yaji abokanshi ma suna cikin koshin lafiya harma sukayi masa alkawarin saka lokaci su kai masa ziyara har Maidugurin.

A wannan yawon garin ne ya fita shi kadai ya samu abinda jiki da zuciyarshi suke bukata, kuma ba'a hada sati biyu ba ya gane cikin cousins dinshi ma akwai wanda suke busa hayakin, sai kawai suka hade abinsu, nasu idanuwan ma sunfi nashi budewa tunda sun fishi yawo, basa gida Nigeria basa kasashen ketare, bayan bushe-bushen ma harda mata suke hadawa, saiya zamana Hajiya Rumana da hannunta ta raboshi da Kano ta kawoshi inda zai kara lalacewa. Ita kanta saida tayi sati uku a garin Maiduguri, amman ko data huce ta gwada neman Alhaji Mustafa bai daga mata waya ba, bai amsa tarin sakkoninta ba, yanda ta dauki kafarta ta tafi Maiduguri haka ta tattara ta koma Kaduna duk dama 'yan uwanta da yawa basu so hakan ba.

Sai dai ya shayar da ita mamaki, baice mata komai ba, nunawa ma yayi kamar babu abinda ya faru a tsakaninsu, sai itama ta fuske, a gefe daya tanata shiri da Yayanta Modu wanda shi takebi, yana zaune ne a kasar Italy tare da iyalanshi duka, akan yanda za'a fara ma Haris processing samun makaranta a kasar da jarabawarshi ta WAEC ta fito

Wannan shine tsarinta
Kuma shi din ta aikata a lokacin batare da tunanin komai ba

Asalima wani irin sanyi taji ranar da Haris ya sauka kasar Italy, a gefe daya kuma Alhaji Mustafa yayi matukar kokari wajen danne zuciyarshi baice mata komai ba, duk da yasan abinda yake faruwa, yaga Hajiya Rumana ta rantse ta sake rantsewa saita shiga tsakaninshi da danshi kamar ita kadai ta haifeshi, so yake yaga iya gudun ruwanta, shisa ranar da Haris din ya tako yazo da sunan hutu ya birkice mata ta sigar da bata taba gani ba, dan kallo daya yayi musu ita da Haris din da yayi wata irin murjewa saboda hutu da canjin yanayi, sai dai bakinshi yayi duhu fiye da sauran fatarshi, sannan kuma idanuwanshi sunyi wata irin lumshewa da batayi kama data shaye-shaye ba sai ta kara masa wani irin kyau, ya jefesu da tambayar abinda Haris yazo yi masa a gida.

Bata kara shiga tashin hankali ba saida taji ya rantse sai Haris ya koma inda ya fito ba zai kwanar masa a gida ba, itama kuma bai hanata ba, zata iya daukar jaka tabi danta tunda daman ai ta jima da nuna masa ita kadai ta haifeshi, suje kawai ya sallama mata shi

"Nifa kukanki kara batamun rai yakeyi wallahi, uba fa kika sake masa tun kafin in mutu, to meye a ciki? Nayi miki magana? Nace miki wani abu? Bar muku shi nayi yanda kike bukata, shisa ba zai kwanar mun a gida ba wallahi, kuma daga ke harshi babu wanda ya isa yasa inyi azumin kaffara"

Shisa ma ta tsorata matuka, musamman da Haris dinma ya dauki jakarshi duk da hanashin da takeyi

"To zaman me zanyi masa Mami? Kinajin yace ya bar miki ni, duk da daman nidin nakine, to ba sai in bar masa gidanshi ba?"

Kuma bai saurareta ba ya fice tunda ai akace dan gado saiya dara, gadon zuciya yayita a wajen Alhaji Mustafa, jin kai da Izza kuwa daga wajenta ne, tafiyarshi yayi, ta danji sanyine ma daya dauki motarta ya fita da ita, hotel ya kama abinshi. Kuma ko bayan da Alhaji Sa'id din da take tunanin zai shawo mata kanshi yazo sai taga ma kamar ya sake birkicewa ne, dole ya ce mata suyi hakuri su barshi ya dan huce kwana biyu, amman hankalinta a tashe yake, dan yanayine da bata taba ganin mijin nata a ciki ba.

Hukunci ne ta riga ta yanke da take tunanin mafita ne a wajenta da Haris din a wancen lokacin
A yanzun shima Alhaji Mustafa gani yakeyi abinda yayi wata hanya ce da zai nunama Hajiya Rumana kuskuren data yi masa
Kowa ta bangarenshi gani yakeyi ya duba Haris din a yayin yanke hukunci, amman shikuma Haris din fa

Haris ne a tsakiyarsu
Daya na gabanshi
Daya na bayanshi
Amman babu abinda yakeji sai kadaici, kadaici da rashin tsayayye a cikin rayuwarshi
Tangal-tangal yakeyi,
Babu inda yake samun dai-daito sai ya rike wiwi a hannunshi ko yaji mace a tare dashi...
[24/08, 7:21 am] +234 903 572 3778: #LubnaSufyan ✨
#WomenOfWords
#09035723778 (WhatsApp)

Littafin nan na kudine akan #1k kacal, zaizo a manhajar Telegram ne kawai 20/06/2025 In Shaa Allaah, bayan mun kammala shafukan dandano.

Zaku iya biya ta: 9035723778 Opay, Lubabatu Sufyan.

NAGODE.

*

LABULE...Asirin mai daki

4

HARIS

Dakinshi aka bashi a gidan Alhaji Jibril, daki babba sosai tunda hade ma yake da dan karamin falo harda irin kitchenette din nan, duk dakunan yaran gidan haka suke, shi da ko ruwan zafi bai taba dorawa ba a rayuwarshi, haka yayi dariya da yaga kitchenette din. Lokacin daya zabi bangaren Art, yayi hakan ne saboda yasan akwai saukin darasin lissafi a wannan bangaren, baisan ko yana da kokari ko bashi dashi ba tunda ba wani dagewa karatu yakeyi ba. Yasan da yawan matasa, ko yace yara suna da abinda suke so su zama tun kafin su girma, wasu tun suna primary school, shisa da sun shiga ss1 sai su zabi bangare tunda sunsan abinda sukeso su zama, shi dai yasan yana son harkar motoci irin wadda ya taso yaga mahaifinshi yanayi, amman baya sha'awar siye da siyarwa, bayason duk wani abu da zai dinga daukarshi zuwa wasu garuruwa ko wasu kasashe da sunan aiki, yana so in har ya bar garin da yayi settling to ya zamana hutu ya tafi.

Shisa yake so yayi harkar transportation, ya mallaki manyan motoci dama kanana a dinga yi masa aiki dasu, yana kwance a gida yaji alert batare daya fita ko'ina ba. Wannan shine mafarkinshi, sai dai ana karantar harkar transportation a makaranta ne? Har bincike yakanyi idan ya zauna baya komai, bai taba maganar da kowa bane ba, zaiso ace suna irin zaman nan shi da Alhaji Mustafa suyi hira kamar yanda yaga sunayi da Mukhtar, da saiya bashi labarin abinda yake buri, yasan ba zai rasa wasu shawarwari da zai bashi akai ba, ko mutanen da zai hada shi dasu, to gashi a Maiduguri, wata tazara ta kara samuwa a tsakaninsu.

Dakin Salim ya shiga, yaron Alhaji Jibril ne shima, ya zauna akan kujerar dakin saiya hango wata karamar camera, haka kawai ya tashi yaje ya dauka yana juyata a hannunshi, sai yakejin wani abu na shigarshi da bai tabaji ba

"Ta Aise ce fa ta manta zuwan da sukayi"

Salim yace masa, baisan komai game da camera da yanda take aiki ba

"Kana amfani da itane?"

Salim ya girgiza masa kai

"All yours in kana so"

Daukar yayi kuwa ya tafi da ita dakinshi, sai gashi yana bincika yanar gizo yana neman yanda ake amfani da camera din bayan yaga sunanta a jiki, sai gashi ya dauki lokacin da baiyi tunani ba akai, tun azahar har yamma liqis, sallar la'asar ma a daki yayi kayarshi wajen biyar da wani abu. Ya dinga amfani da camera din yana daukar duk wani abu da zai iya a cikin dakin, rabon da wani abu da ba wiwi ba ya sakashi nishadi haka harya manta, ko randa su Salim suka matsa masa ya biyewa wata yarinya bata sakashi nishadi irin wannan ba, wani abune na daban ya cika masa zuciya ya samu waje yayi zaune.

Sai 'yar camera din nan ta zame masa kamar wata abokiya daya jima yana nema, jinta a cikin hannunshi kadai na sama masa natsuwar da baisan yana bukata ba. Lokacin daya gama jarabawarshi yasan abubuwa da yawan gaske da suka danganci daukar hoto saboda binciken da yakeyi akai, kuma a karo na farko ya saka daukar hoton a cikin abinda yake so yayi tare da harkar transportation dinshi. Shisa ko da sukayi waya da Hajiya Rumana tana tambayarshi ko me yake so ya karanta dan ta fara magana da Alhaji Modu a lokacin sai yace

"Photography..."

Yasan shirunta na mamaki ne shisa ya tsinci kanshi da dorawa da

"Akwai abinda nake so inyi Mami, wannan din yana daga ciki, wancen banajin yana bukatar wani karatu mai yawa, banaso in fada miki yanzun"

Abinda yake so shi take so kamar sauran 'yan uwanshi, bayan tayi magana da Alhaji Modu, shima saida ta bashi lambarshi saiya zamana ma dashi suke magana suna shirya yanda komai zai kasance. Saida jarabawarsu ta fito, bashi da wata matsalar komai sannan kuma hankalinshi ya sake rarrabuwa kashi-kashi, shifa daukar hoto ne a ranshi, amman yaga Kawun nashi ya tura masa da wasu courses sama da kala goma wai ya zabi daya. Haka ya zauna ya dinga tunani, kafin ya natsu akan guda daya

"Documentary and photojournalism"

Akwai wani abu da ya tsaya masa a tattare da course din. A lokacin bashi kadai zai tafi makaranta ba, a tsakanin cousins dinshi maza da mata su 8 ne, kuma duk watannin nan daya shafe a Maiduguri, duk shirye-shiryen da akeyi ko sau daya basuyi magana da Alhaji Mustafa ba, baisan sau nawa ya dauki waya ya danna lambarshi yana kasa kira ba, me zaice to? Inya kirashi me zaice masa? Ko kafin ma yayi masa laifi ba waya sukeyi ba, da wahala ma idan yasan cewa ya mallaki wayar balle harya samu lambarshi, shi dai ya jima da haddaceta tun kafin ma Hajiya Rumana ta sai masa waya.

Da lokacin tafiya yayi, mutum biyu zuwa uku zakaga zasuje kasa daya, shi kadaine zai tafi kasar Italy, kuma shi kadaine babu kowa nashi banda Anisa, Munira taje Kano saboda a lokacin ma ana shirye-shiryen bikinta ne, sannan Hajiya Rumana ma tace masa Alhaji Mustafa ya hanata zuwa Maidugurin, sai waya suka dingayi, tana masa alkawarin zata san yanda zatayi taje har Italy din ta dubashi, kasancewar Anisa a wajen bai ragewa Haris nauyin da zuciyarshi tayi na rashin iyayenshi ba, saima inya juya yaga kowa da mahaifinshi, shi da Alhaji Mustafa ba zaizo ba sai ya hana masa Hajiya Rumana zuwa itama, abin yayi masa ciwo na gaske.

Ya dinga fadawa kanshi inya tsallaka ya bar kasar sai dai ita Hajiya Rumanan ta dinga zuwa masa. Duk wasu hotunan kasar Italy daya gani a yanar gizo basu shirya zuciyarshi ba ashe, kasar na da kyau, tunda suka bar airport yake kalle-kalle kamar wani dan kauye, ya dinga jin hannunshi yanayi masa kaikayi da son ace akwai camera a jikinshi da zai dauki hotunan duk wani gini da yayi masa kyau, sai dai 'yar karamar camera din da akace masa ta Aise ce tana cikin jakarshi, kuma jakar na bayan mota. Fushin daya hau jirgi dashi ya nema ya rasa a tsakanin kyawun gine-ginen kasar Italy da kuma yanayin komai da yayi masa kyau.

Tarba mai kyau ya samu wajen matar Alhaji Modu, Binta, amman tun kafin yazo ma yaji ana kiranta da Mamma. Haka aka nuna masa dakinshi inda ya shiga yayi wanka dan ya gaji, ya sake kaya tukunna ya fito, gidan nasu ne yakejin shi shiru, yasan yaran gidan su uku, Khamis da suke kira da Khaam yana India, sai na biyun baima rike sunanshi ba ance a Madina yake karatu, sai Aise itace Auta, baidai san a tsarin Binta da mijinta yara biyu bane ba, Aise kawai sun samu cikinta ne lokacin da basuyi tsammani ba. Bai tsaya wani bata lokaci ba da tace masa abincinshi na dining, inda ta nuna masa ya nufa, yunwa yakeji duk da abinci ba damunshi yayi ba sosai. Amman banda ruwa babu abinda yaci a jirgi, yana zaune ne ma Aise ta fito, a yanda aka fada masa bata wuce shekaru goma sha uku ba, sai dai yarinyar da ta kalle shi tace masa

"Ciao"

Cikin alamar gaisuwa batayi masa kama da 'yar shekara sha uku ba, akwai braces a bakinta, sannan gashinta data kama ta daure da wani ribbon, anyi masa irin kananun twisting din nan ne, kuma ba baki bane ba, kamar ta rina shi ya koma ruwan kasa mai dan duhu, bakace bacan ba, da wani sanyi a tare da ita da yasa Haris kasa dauke idanuwanshi daga kanta harta bace ma ganinshi, yana dai juyo maganarta da yake kokarin fahimta tunda cikin yaren kasar Italy din takeyi, kuma saida ya fara koyonshi online tunda yana cikin abinda ya zame masa dole in har zaiyi karatu a kasar, amman saurin da takeyi wajen maganar yasa kalmomi kadan ya tsinta, haka ta sake dawowa ta wuce shi da robar ruwa a hannunta.

A wannan lokacin, da Haris yake da shekaru goma sha takwas a duniya, Aise ta wuce shi tana tafiya da wani kaso mai girma na zuciyarshi da baisan ya mika mata ba...

Makarantar daya samu, kasa dayane, amman kuma ba cikin gari daya da gidan Alhaji Modu ba, shisa daman harda daki aka biya masa, kwananshi shida a gidan Alhaji Modu kafin yazo dan yayi wata tafiya ne wai, dashi da Binta da Aise da a wannan 'yan kwanakin suka shaku matuka aka tafi rakashi, haka suke ta cakuda hira da Aise din da take gane Hausa kadan-kadan, amman batajin turanci, sannan yaren Kanurin ma kalmomin da take tsinta basu da yawa, shikuma duk yanda ya kara dagewa ya tabbatar dai baya cikin mutanen da suke da kokari, ba karamar wahala yaren Italian din bashi ba, wai danma Aise ta zame masa kamar wani tsani na kara son ya koyi yaren saboda hirarsu ta dinga tsayi.

Saida suka rakashi har dakinshi yanajin shi wani sama-sama, suka kuma gaisa da roommate dinshi mai suna Logan dan dan kasar Amurka ne, Alhaji Modu ya tabbatar Haris din zai iya karasa komai da kanshi, sannan akwai wadatattun kudi a wajenshi tukunna suka tafi, bayan Binta da kanta ta kara masa wasu kudin tana kuma jaddada masa da in yana bukatar wani abin kiransu kawai zaiyi, inma ya kama wani yazo har makarantar ne zasu zo. Suka tafi suna barinshi da kewar Aise da tace ya rike camera dinta bayan ya bata, a cewarta ko yanda shi ya fassara abinda ta fada

"Banaso ka mantani da wuri..."

Yayi dariya, yana fatan ta gane lokacin da yace mata

"Ni da nake kasarku Aise, ko inaso ba zan iya mantawa dake ba"

Zamanshi na shekara daya a kasar Italy wata shekara ce da ta zame masa mafarin abubuwa masu yawan gaske, tana daga cikin shekarun da zaiso ace sune mafarin rayuwarshi gabaki daya saboda yanda tayi masa dadi.

Ya zai manta da Aise?
Ta ina?
Bayan itace mafarin komai, da bata manta camera din nan ba watakila da yanzun yana nan yana bulayi, watakila da baima san me yake da rayuwarshi ba

Kuma a shekarar ya gane samun wiwi a Nigeria yafi wahala akan nan, kusan duk wadanda ya sani a makaranta suna sha, sai dai shan ya bambanta, da yawansu ba irin wanda yakeyi mata sukeyi ba, lokaci zuwa lokaci ne, dan nishadi, sunfi shan giyarsu akan komai, ko Logan bai taba shan wiwi ba, haka ma sigari, bayama shan ko giya, yace masa babanshi mashayi ne na gaske, giya ita ta ruguza gidansu, ta rusa musu farin cikinsu, saboda giyar Mamanshi tabar Babanshi ta kuma kwashe su shida kanwarshi ta tafi dasu, yanzun ma baya magana da Baban nashi.

Duk da giya bata taba burge Haris ba, asalima shi bayan wiwi din bashida ra'ayin karawa da komai, ya dai ji tsoron gwada shan giyar ya kara shigarshi, yaso yayi mamaki da Logan yace yanzun baya magana da Babanshi, sai ya tuna ai shima baya magana da nashi
End Ads