x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 3 - LABULE ASIRIN MAI DAKI free pages

  • 6001 words
  • 9000 words
  • Out of 16315 words

Category: Love Stories

Views 94

25 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
kare saiya zamana sun janyo Barde da Lalaye sun fara wannan muguwar ta'adar. Waje suka gano ma cikin makarantar inda suke zuwa susha kayansu, data kare sai 2Pac ya kwanta ciwon karya, ya dingayi kamar wanda jinnu suka shafa, dole aka mayar dashi gida da permit na kwana uku zuwa sati daya in har bai samu sauki ba.

Kwananshi uku yayo musu kayanta ya dawo musu da ita makaranta, har shayi idan aka basu sai Haris ya faki ido ya marmasa ganyen a ciki, lokacin ne ya samu sunanshi na Ganja, dan ba karamin burge abokanshi yakeyi ba, sunce babban kai yake dashi. Kuma Hajiya Rumana ta kara kankaro masa mutunci data siya masa wata tsadaddiyar waya, haka yayi sneaking dinta zuwa makaranta, aikam ranar ko wani dan sarki ba zai nuna ma Haris jin kai ba. Inda ace Hajiya Rumana ta nutsu ta saka idanuwa akan Haris, data kula da canjin da ya samu, a lokacin kuma data ga duhun da labbanshi sukayi fiye da sauran fatarshi saboda yawan hayakin da yake bankawa cikinshi.

A lokacin yazo hutu, wanda daga shine zasu shiga aji shidda, Alhaji Mustafa ya jima bai saka shi a ido ba, kamar boye masa Haris din yakeyi, sannan Hajiya Rumana ma tana tayashi wannan boyon. Idan da yamma ya dawo gidan sai tace masa Haris na Islamiyya inya tambaya, idan da daddare ne kuma ace ya tafi sallar isha'i, ko kuma ya riga ya kwanta, shi dai bai karyata ba, amman basu taba haduwa da Haris a masallaci ba, duk da unguwar cike take da masallatai, amman ai na kusa shi duk suke zuwa. Sannan yaushe rabon Haris da wata Islamiyya? Ya kan leka dai in ance ya kwanta, har dakinshi, kuma yana samunshi a kwance din, ya dan tsaya sai yayi masa addu'ar shiriya da neman kariya kawai yaja masa kofar.

Sai ya yanke hukunci sai yaga Haris a ranar zai ma fita daga gidan, da yake girkin Hajiya Rumana ne, yayi zamanshi a falo, fushi take tayi masa da baima san dalili ba, yara ne suke yawan hadasu fada, kuma ai ya gaji ya hakura, ya yarda tafi karfinshi akansu, tunda da yace ba zai biyawa su Munira su tafi kasar waje ba, sai tace ita zata biya, nan ne ma ya nuna bata isa ba, sai dai in ya yafe mata su gabaki daya, dole ta hakura, amman yanaji yana gani duk sukayi applying Jami'ar Maiduguri, suka koma wajen danginta, sai dai suzo hutu, a lokacin ma ana maganar auren Munira dinne da wani abokin wasanta na bangaren Hajiya Rumana din, wanda haihuwar kasar Ingila ne, kasancewar mahaifinshi yana aiki acan, akwai 'yan uwan Hajiya Rumana da yawa a kasashen waje. Yaron yanzun haka Likita ne, yana aiki a Birmingham ta kasar Ingila, can dinma zasu tafi, itama sai ta cigaba da karatunta dan ta kusan kammalawa inda take karantar fannin magunguna wato Pharmacy.

Lokacin da Haris ya shigo falon, wando ne dogo a jikinshi, ruwan toka mai cizawa, sai farar t-shirt, sumar da ya dan tara kadan bakikirin da ita, tasha gyara sai daukar ido takeyi, kallo daya Alhaji Mustafa yayi masa yaji gabanshi yayi mummunar faduwa, ya kafe shi da ido bayan sun gaisa yana dorawa da

"Zo nan Haris"

Bai musa ba ya karasa, da yake akan doguwar kujera Alhaji Mustafa yake, shi Haris saiya zauna akan hannun kujerar

"Ya makarantar?"

Ya tsinci kanshi da tambaya

"Alhamdulillah"

Cewar Haris, wata irin rashin natsuwa ce take ta shigar Alhaji Mustafa game da Haris din, bai kawo wani abu guda daya a ranshi ba, ya dai tabbatar akwai wani abu da ba dai-dai ba a tare da yaron nashi, anya kuwa Allaah ba zai kamashi akan sakaci da 'ya'yan Hajiya Rumana ba? Ya kamata ma ace ya gaji ya hakura ya bar mata su? To ta ina ma zai fara yanzun, inda Mukhtar ne ko wani a cikin yaran Fadime da yanzun sun zagaye shi kowa nason bashi labari, amman kalli yanzun yanda kalamai sukayi musu karanci tsakaninshi da Haris, kamar wasu bakin juna.

"Yaushe zaka koma makaranta?"

Haris din ya dan numfasa

"Ranar Monday"

Saiya jinjina kai, kudi yake sakawa Hajiya Rumana na duk wata hidima data danganci yaran, amman yau sai yace

"To ka shirya gobe sai muje muyi siyayyar komawa makarantar ko?"

Cike da mamaki Haris ya kalle shi, saboda abune da bai saba ba,

"Mami ma ta gama saimun komai da nake bukata"

Sukayi shiru na wani lokaci

"Karfe nawa zaku wuce ran Monday din?"

Haris yasan basa wuce karfe goma, direba ne yake kaisu shi da Hajiya Rumana

"Wajen tara da rabi zuwa goma haka muke fita"

Kafin ma Alhaji Mustafa yace wani abu Haris din ya mike

"Ina dan shirya kayana ne Baba, saida safe"

Bai kuma jira amsar shi ba ya wuce abinshi, Alhaji Mustafa yaji wani abu ya takure a cikin kirjinshi, haka ya kwanta da wannan rashin natsuwar, itace kuma ta zame masa wata abokiya a kwanakin har zuwa Monday, da saida su Haris din suka ganshi a shirye tsaf, kallo daya zakayiwa Hajiya Rumana kagane bataji dadin wannan bazata na mijin nata ba. Akan dole akayi tafiyar dashi, har makarantarsu Haris, duk wani report card dinshi da take fada masa wai a makaranta ake ajiyewa sun dai fada mata grade dinshi yasa aka dauko, yaji dan sauki ganin Haris din ya fara kokari, ko a term din da aka fita na bakwai yazo. Ya dai kalli Hajiya Rumana da yaji cewa duk sanda za'a nemeshi yana kasar waje, da alama shugaban makarantar yaji dadin zuwanshi.

Sukayi musayar Lamba, Hajiya Rumana na sakawa a ranta, suna koma gida zata faki idon Alhaji Sa'id ta rufe lambar ta yanda shugaban makarantar ba zai iya kira ba, shikuma ta sauya lamba daya a ciki yanda inya kira ma sai daiya samu wani. Ba zata bari Haris na gab da gama makarantar nan sujawo mata wata fitina da Alhaji Mustafa ba, so takeyi akan Haris ta shawo kanshi ya fitar da yaron kasar waje, a gaban idonta yake maganar watakila Mukhtar na da rabon komawa Madina, tunda su kananun duk sunje Umra, manyan kuma sun hadane harda Hajj, acan zaiyi karatunshi, da tayi magana sai yace mata

"Bafa ni zan kaishi ba, kwakwalwarshi ce zatayi masa sanadi"

Wai ita zai ninke a bai-bai, ta dauki idone ta saka masa, dan ba karamin tashin hankali za'ayi ba ace wani a cikin yaran Fadime ya tsallaka wata kasa da sunan karatu, in har ya nuna mata ba zai fitar da Haris ba, sannan ta riga tayi rantsuwa sai dai yayi abinda zaiyi, amman ko da yardashi ko babu, Haris ba zaiyi karatu a Najeriya ba, haka suka dawo gida. Aikuwa abinda tayi niyya shi tayi data samu ta dauki wayar Alhaji Mustafa.

Sai dai har ranta bataso a kirashi ne akan irin rashin ji da rigimar da Haris yakeyi
Ko a mugun tunani batayi hasashen kiran da za'ayi ma Alhaji Mustafa har akan Haris har ita saiya girgiza...

[24/08, 7:21 am] +234 903 572 3778: #LubnaSufyan ✨
#WomenOfWords
#09035723778 (WhatsApp)

Littafin nan na kudine akan #1k kacal, zaizo a manhajar Telegram ne kawai 20/06/2025 In Shaa Allaah, bayan mun kammala shafukan dandano.

Zaku iya biya ta: 9035723778 Opay, Lubabatu Sufyan.

NAGODE.

*

LABULE...Asirin mai daki

3

Wata tafiya ce mai matukar muhimmanci ta kamashi zuwa jihar Lagos, saboda dole sai yana wajen komai zai tafi dai-dai, da ya sake komawa makarantarsu Haris tunda ya kira lambar da Shugaban makarantar tasu ya bashi sai wata mace ta dauka, haka ya bata hakuri yana rayawa a ranshi cewar an samu kuskure wajen shigar da lambar, wannan rashin natsuwar da yaji tun ranar da yaga Haris ne yake kara girma duk rana, yana darsa masa wata irin fargaba da tafi karfin fassara. Wani abu na fada masa cewar danshi na bukatarshi, yana bukatar yaja shi a jiki ya gano menene matsalarshi.

Satinshi biyu a Lagos kafin ya gama ya dawo Kaduna, sai ya sake shiga wata sabgar bayan ya tambayi Hajiya Rumana ta bashi lambar da take da ita na daya daga cikin Malaman Haris din tace masa babu. Ranar ta kama Lahadi ce, ya kamata ace kuma ya wuni a gida, ko da ba zaiyi bacci ba yana hutawa, sai ya fita wata dubiya, a hanyar dawowa nema kira ya dinga shigowa wayarshi da wata bakuwar lamba, da yake bai cika daga lambar da bai sani ba, amman yanda ake kiran babu kakkautawa yasa shi ya daga hadi dayin sallama.

"Alhaji Mustafa ne?"

Aka tambaya daga dayan bangaren bayan gajeruwar gaisuwa, ya amsa, sannan aka sanar dashi daga makarantarsu Haris ne, haka kawai yaji zuciyarshi ta buga, musamman da aka sanar dashi ana nemansu ne da gaggawa washegari da zata kama Litinin, jiki da murya a sanyaye ya amsa, tunda ance idan yaje din zaiji koma menene, haka kawai daya koma gida, duk da ba dakin Hajiya Rumana yake ba, sai daya sake shiga ya fada mata kiran da akace anayi masa, taji ranta yayi mugun baci, akan me zasu kirashi? Ai kam dole ne zata kora musu kashedi idan taje

"Ba zai wuce kare-karen kudinsu da suka saba bafa, ko kuma kan maganar jarabawar da zasu zana, meye zasu wahalar dakai kai da kake da hidindimu a gabanka, kabarsu kawai goben sai in shirya akaini inji menene"

Ya girgiza mata kai, yanajin ya daina bar mata yaran da hidimarsu, koya ne zai dinga kokarin shiga rayuwarsu da sanin me take ciki

"Zanje din tunda har suka bukaci hakan, banajin akan karamin dalili ne"

Tasan shi, yanayin da yake fuskarshi kuma ya nuna mata babu abinda zata fada da zai sauya masa ra'ayi

"Sai in shirya muje tare"

Wannan ba laifi bane, shisa ya amsata, suka dan kara taba hira kafin ya fice. Baiyi wani baccin kirki ba saboda tunanin daya cunkushe masa, washegari kuwa tun karfe bakwai na safe daga shi har Hajiya Rumana sun gama shiryawa tunda direbanshi ne zai kaisu. Kuma bayaso ace tara na safiya tayi basu karasa ba shisa yayi mata magana ta shirya da wuri, ta fara janshi da hira taga yana amsata dai-dai, sai kawai ta kama danna wayarta ta kyaleshi. Haka suka karasa makarantar kamar wasu bakin juna, a tunanin Hajiya Rumana ba zai wuce Haris yayi fadan daya saba bane, ya kama wani abokin karatun nashi ya jibga. Ko daya wuce aji daya, babu ruwanshi da duk wani yaro na kasa dashi, wannan seniority din da akeyi a makarantar kwana baya cikin lissafin Haris.

Yanda yaran basa shiga hanyarshi haka baya shiga tasu, a aji ma inka cire abokanshi sauran in zasu fita sabgarshi zaiso haka, to fadanshi a tsakanin sa'anninshi ne, sune zai kama ya jibga in wani abin ya hadosu, ya taba jibgar wani Malaminsu dan bautar kasa, ko da yake yace ma ba Malaminshi bane dan Junior section yake koyarwa, shisa baiga dalilin da zaisa ya daga bulala da sunan dukanshi ba, da yake ance matsalar da kudi basa magancewa kalilan ce, dasu Hajiya Rumana ta kashe wannan case din, aka ja masa kunne da suspension din sati biyu kacal. Yau ma ta tabbata Alhaji Mustafa ne zai kwafsa mata, haka suka shiga ofishin shugaban makarantar hancinta a sama, fuskar nan kamar bata taba fara'a ba.

Ko gaisuwar da yayi musu ma, a shaqe ta amsa, tanajin shi yanata koro bayani da wani turancin shi da yake kara shakar da ita, sai ga kunnuwanta sun jiyo mata abinda yake neman sakata fadowa daga kujerar da take zaune

"Ina mai dana sanin fada maka cewa yaranka na daya daga cikin wanda muka kama suna shaye-shaye a cikin makaranta, ansha kawo mana kara, sai dai abune da yake bukatar bincike shisa bamu dauki wani mataki ba mukayi amfani da wasu hanyoyi wajen zurfafa bincike yanda zamu kamasu da laifin..."

Cikin tashin hankali Hajiya Rumana ta katse shi da fadin

"Karya ne, ba dai Haris dina ba, shaye-shaye? Karya ne"

Ai dan shaye-shaye baya boyuwa ko? Ba haka zaka gansu ko a labarai firgai-firgai ba? Duqu-duqu dasu, Haris dinta da zai shigo dakinta ya fita yana bar mata kamshin  turarenshi na Addictive ambergris, Haris din da yake tsaf-tsaf dashi ko da yaushe, sau nawa suna wuni a gidan bata taba ganinshi yana marisa ba? Ko ana nufin har yayi hutu ya gama baya sha saiya koma makaranta?

"Karyane wallahi"

Ta sake fadi, Alhaji Mustafa banda

"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"

Babu abinda yake furtawa cikin zuciyarshi, Shugaban makarantar yayi wani guntun murmushi mai ciwo

"Kuyi hakuri, amman wannan laifine daya taka dokar makaranta, kuma hukuncinshi korane, duk daya kamata mu hadasu da hukuma ne tunda an kamasu da tabar wiwi mai yawan gaske a cikin kayayyakinsu, sannan harda kwayoyi ma, sai dai ba zamuyi hakan ba, zamu tsaya iya korar ne kawai gudun karsu gurbata mana sauran daliban..."

Ya karasa yana tura wata takarda gaban Alhaji Mustafa, sannan ya daga wayarshi yayi kira, sai ga Haris ya shigo cikin ofishin, kayan gidane a jikinshi dan tun jiya da aka tabbatar musu da korace, da safen akace su sauya kaya su cire uniform din makaranta, su dukansu babu wata razana a fuskokinsu, koshi Haris din baiji wani tashin hankali ba tunda dai yasan ai Hajiya Rumana ce zatazo, kuma korarshi daga wannan makarantar ba wani abu bane, da sun fita ya narke mata yace

"Abokaina ne suke sha, muna tare aka kamamu Mami, ke kinsan ba zansha irin abubuwan nan ba"

Zance ya kare, ba zata sake tayar da maganar ba ko a tsakaninsu balle har wani yaji, wata makarantar zata samu ta kaishi, tunda shekararce ma kawai ta rage masa, amman ganin Alhaji Mustafa da yanda ya juyo ya kalleshi sai yaji kamar zuciyarshi ta dunkule waje dayane ta kuma gunguro zuwa tafukan kafarshi da sukayi masa nauyi har yana kasa karasawa ciki, ya tsaya a wajen kawai yana sauke kanshi kasa, duk wani abu da ake fada baya karasawa kunnuwan Haris, bayajin komai banda bugun zuciyarshi da yake amsawa a kowacce gaba ta jikinshi. Yaga mikewar Alhaji Mustafa, ya raba ta gefenshi ya wuce, kafin Hajiya Rumana da itace ma ta rike hannunshi tana janshi suka fita daga ofishin

"Jakunkunan kayana Mami"

Haris ya fadi yanajin yanda harshenshi yake a bushe, direban daya kawosu tasa yazo ya kwashi kayan Haris din ya saka a mota, ita da Alhaji Mustafa suka sake shiga gidan baya, Haris din ya zauna a gaba, data mika hannunta ta riko na Alhaji Mustafa cikin sigar lallashi saboda shirun motar ya fara isarta zarewa yayi kamar ta dora masa garwashin wuta. So take kawai ta gansu a cikin gida, a bangarenta ko nashi su hadu ita da Haris su tabbatar masa da ba zai taba aikata abinda aka fada ba, sai dai in an samu wani akasin. Suna karasawa gidan kuwa shiya fara fita daga motar ya zagaya yana kama hannun Haris da kanshi zuwa nashi bangaren, ta rufa musu baya tana masa magana ganin irin fisgar da yakeyiwa Haris din, ko juyowa baiyi ba.

A tsakiyar falonshi ya tsayar da Haris

"Ka kalleni Haris, ka fadamun gaskiya, an kamaka da wiwi ko ba'a kamaka da ita ba?"

Haris ya kasa dago da idanuwanshi, yasan babu wata shakuwa a tsakaninsu tun tasowarshi, to sau nawa ma suke haduwa da Baban nashi a shekara? Ko lokacin bukukuwan sallah sunfi yin abinsu a Maiduguri wajen dangin Maminsu amman akwai kaunar nan ta 'da da mahaifi, yana kishin shakuwar da take tsakaninshi da Mukhtar, ko da asuba tare suke fita masallaci, inma an taso shi to yanda suke labari sai dai ya koma baya yana binsu kawai, a gaban Alhaji Mustafa, Haris najinshi kamar wata inuwa da sai bayan wani lokaci in ya juya yake tunawa da ita.

"Wai wacce irin tambaya ce wannan? Yama za'ayi ace an kama Haris da irin wannan laifin ka yarda"

Juyawa Alhaji Mustafa yayi yana mata wani kallo da yasa ta rufe bakinta, dan a karo na farko a zamansu ta tsorata da abinda ta gani

"Haris..."

Sai lokacin ya iya dago da kanshi, ya kalli Alhaji Mustafa, ya hadiye wani abu daya tokare masa wuya

"Da gaske ne Baba...kayi..."

Bai karasa ba yaji wata irin iska ta gifta masa da bai taba jin makamanciyarta ba, dan saida ta dauke masa jinshi na wasu dakika, wani irin haske ya gifta masa, yana bude idanuwanshi kuma ya sake jin wata iskar data tabbatar masa da marine, marukane Alhaji Mustafa ya sauke masa guda biyu a jere, yana sake kai masa wani da saida yayi kasa saboda karfinshi

"Shaye-shaye? Haris shaye-shaye? Jinina?"

Tunda yake bai taba tsintar kanshi cikin matsanancin bacin rai irin na yau ba, yara nawa ya dauke a unguwar iyayenshi zuwa rehabilitation centre, ya dauki dawainiyarsu dan ganin rayuwarsu ta inganta sun fita daga muguwar dabi'ar shaye-shaye, ko sau daya bai taba aibatasu ba saboda gudun kar Allaah ya jarabce shi, ko a hanya yaga giccin irinsu zaiyi musu fatan shiriya ne, to me yasa Haris zaiyi masa haka? Ko dan ya sakarwa Hajiya Rumana su? Baisan irin dukan da yakeyiwa Haris din ba, tunda shi mutum ne da bai iya fushi ba tun asali, saida yaga Hajiya Rumana tana tureshi tana kuka, duk da haka bai dawo hayyacinshi ba saida ya sake kaiwa Haris din wani dukan da Hajiya Rumana ta tare ta sameta a gefen fuska

"Ka hadamu kawai ka kashe Mustafa, ai baka da asara tunda kana da wasu yaran maza, in kayi masa lahani ni zaka cutar..."

Take maganar cikin hargowa kamar zata bangajeshi, kallonsu kawai yakeyi wani irin duhu na lullube sashi da yawa na zuciyarshi, neman wani zunubi daya aikata Allaah Ya jarabce shi da wannan lamarin yakeyi, kafin ya fara jero neman yafiya da tsari daga mummunan tunani, yana kallo ta janye Haris din suka fice daga dakin baiko motsa ba, dan hakan ma yafi masa, in yana ganinsu zuciyarshi zata cigaba dayi masa bakine, gara su bashi waje ya samu ya saisaita kanshi. Ita kuwa Hajiya Rumana bangaren Haris ta nufa dashi

"Ka hada iya abinda zaka iya bukata, zamu wuce Maiduguri"

Ya kalleta da idanuwanshi da suka kada, amman babu ko kyallin hawaye a cikinsu duk kuwa irin dukan da yasha, asalima abinda yakeji bashi da fassara sam, kawai dai yana bukatar yaga wani katon nadi na wiwi a hannunshi ne yana busawa, da ita kadai zai raba wannan yanayin ya samu sauki, shisa baiga abinda zai tafi Maiduguri yayi ba a halin yanzun

"Mami..."

Ta katse shi da

"Dan ubanka kayi abinda nace, so kake ka zauna yana ganinka ya illata
End Ads