x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 1 - LABULE ASIRIN MAI DAKI free pages

  • 1 words
  • 3000 words
  • Out of 16315 words

Category: Love Stories

Views 82

25 Aug 2025
Start ads
After Image Ads

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


[24/08, 7:21 am] +234 903 572 3778: 1

"Wacece Maryam Sa'id?"

Tana aji uku ne taci karo da wannan tambayar a cikin slam book da ake ta zagayawa dashi tsakanin 'yan ajin, haka suka dinga kallon juna ita da littafin nan,  saboda ita dai tun asali ba gwanar bada labari bace ba, ko film ne ta kalla in kace ta baka labarin abinda ya faru saita rasa ta inda zata fara, akwai lokacin da suke kallon wani indian series mai suna "saloni ka safar", haka suke binshi kafa da kafa, in babu wuta za'a kunna generator, kamar wanda akayiwa asiri. Wani episode mai zafi akayi, duk basa nan sun tafi wajen sunan matar Khalifa da ita ba'aje da itaba saboda tana karambau, haka suka zagayeta suna jiran tayi musu bayani, data fara kamo tsakiya tana jonawa da farko, haka Shukra taja tsaki

"Wallahi da gangan ma mukayi asarar lokacinmu muna tambayarki Maryam, ke an taba kulla abin kirki dake daman? In dai labaranki mutum zai jira ya hadu da takaici"

Kuma tasan da gaske ne, tunda a ranar ta rasa ta inda zata fara amsa wannan tambayar, to wacece ita ta wacce fuska? Halaye? Tarihi? Halaye dai ai ba masu yawa bane ba, ba kuma boyayyu bane, tunda kowa za'a tambaya tashin farko zaice ita din mafadaciya ce ta kwatance, dan ko a lokacin da take primary ba'a cacar baki da ita, kafin ka numfasa ta sauke maka mari in yaso a kacame da dambe, wanda yafi wani karfi ya kwaci kanshi, tunda har wanda suka wuceta aji saida suka kiyayeta, haka ake cewa yanda take lange-lange kamar za'a iya kaita kasa, kashi dayane da ita. Haka 'yan gidansu in suka fadi wannan zasu kara da wani hali nata guda daya, kishi, tsananin kishin da har Hajjarsu take roka mata sauki akanshi.

Dan kishine irin wanda bata kaunar taga wani ya rabi ko da 'yan uwantane, dan akansu nema Hajjar ta fara gane kishin da Maryam take dashi har takan ce

"Allaah Ya rabaki da wannan kishin Maryam, 'yan uwanki ma kenan, inaga mijinki?"

Kawayen Khairi kuwa da take ganin suna kusan sa'anni da ita sun sha wahala a wajenta, musamman na cikin unguwarsu, balle kuma a makaranta, baka isa a fito break ta ganku kuna cin abinci da ita ba, saita turmusaka cikin kasa, gashi ko taron dangi akayi mata sai anyi da gaske ake iya kaita kasa, shisa duk suka hakura da kawancen da Khairi, idan Hajja ta daketa kan abinda tayi kuwa saita je ta rama akansu, tunda halinta na uku taurin kaine, inta kafe ko kasheta za'ayi ba zata daina abinda takeyi ba, shisa ma Alhajinsu ya hana dukanta saiya kama dole

"Kar yarinyar nan ta kangare muku, yara irinsu ja ajiki, soyayya da fahimta suke so ba kyara ba, ku fahimci abinda bataso din, idan abune da zai iya cutar da ita a gaba sai ayi kokarin fahimtar da ita a hankali..."

Hakan kuwa aka cigaba da tafiya, amman kuma ai tana ganin yanda take kara girma tsoron halayen nata na cika idanuwan Hajja, amman kuma ai kamar kowa ba zata rasa halaye nagari bako? Kuma tana da yakinin sune suka rinjayi wanda suke hadata fada da kowa na gidan suka sakata shiga ransu sosai, wani abu da take alfahari dashi a ko ina, tunda yanzun zuciyar Maryam babu kowa a cikinta banda iyaye da 'yan uwa. Ita kawaye basu dameta ba, kawai 'yan uwanta su hadu su sota fiye da kowa, ko da wani zai rabesu tofa kar su damu dashi yanda suka damu da ita, kai gabaki dayama su din kar wani ya nuna yana sonsu fiye da ita, shine matsalarta.

To duk ya zata takaita wannan tunda a hakama kadan ne a cikin halayenta ta sakasu a wannan slum book din da aka bata shafuka biyu kacal a ciki, idan kuma asali ake nufi ta ina zata fara? Ai asalinta ba zai cika batare da iyayenta ba, tushensu shine nata, babu ta inda zata bada tarihinta bata hada dasu a ciki ba. Alhaji Sa'id shine mahaifinta, kuma dan asalin kauyen Matazu ne ta jihar Katsina, su tara mahaifiyarsu ta haifa, amman su biyu suka rayu, dan tanayin wabi ne, sauran yaran duk rasuwa sukeyi kafin ayi suna, har a lokacin abinka da kauye akace watakila ta zagi mayya ne da take ganiyar kuruciya, shine take bibiyarta, wasu kuma suce ko asiri ne, kowa da abinda yake fada. Sa'id ne ya fara tsayawa, bayanshi ta kara guda biyu sannan Murtala, dagashi kuma sai haihuwar ta tsaya mata.

Masu karamin karfine matuka, tunda gonar gado ce mahaifinsu da gabaki daya danginshi ake nomawa, a ciki ake duk wata hidima ta yau da kullum, annobar amai da gudawa da ta shiga garin a wata shekara, ana tsananin zafi, itace tayi ajalin mahaifinsu Sa'idu, inda mahaifiyarsu tabi shi kwanaki sha biyu tsakani, sai rikonsu ya koma hannun Kanin mahaifinsu Ya'u, shikuma duk karamin karfinshi mata hudune dashi, yara maza duk wanda yakai shekara biyar sai a watsa shi almajiranci, dan haka aka hada da Sa'idu da yake da shekara bakwai lokacin, da kuma Murtala da bai karasa cika hudu ba tunda shi kanshi Ya'u yasan cikin matanshi babu wadda zata dauki wahalar Murtalan.

Da aka tashi kuma duk kukan da suka dingayi sai aka rarrabasu, shi Sa'idu akayi Zaria dashi, Murtala kuma garin Kano. Da yake Sa'id irin yaran nan ne masu shiga rai, yana da wani sanyi a tare dashi idan ka kalle shi, baiyi wahalar abokai da suke fita yawon bara tare ba, bai kuma rufa wata uku ba ya zamana ko shi kadai ma saiya fita yawonshi, tunda sunyi sa'a Malamin nasu nagari ne, banda karatu baya sakasu irin aikace-aikacen gona da wasu Malaman sukeyi. A irin yawon ne yaje wani gida a cikin unguwar samaru yawon bara, da aka bashi abinci, yaga shinkafa da miya harda salak, rabon da yaci abinci ya koshi irin ranar tun iyayenshi na da rai, yana gamawa saiya rabe kasan wata bishiya da take kofar gidan ya kwanta.

Bacci ya kwashe shi, wani bacci da ya zame masa silar alkhairai masu tarin yawa, dan a wannan kwanciyar da yayi ne maigidan ya dawo ya same shi, kuma kankantarshi saita bashi tausayi matuka, ya shiga gidan nashi dashi, ya cewa matarshi kullum zai dinga zuwa ana bashi abinci, batayi musu ba ta amsa. Safe, rana, dare haka Sa'id yake zuwa karbar abinci, ya taba zuwa ya samu ganyayyaki duk sun zubo a harabar gidan yace ta bashi tsintsiya ya share, da taki tunda almajirin da yake zuwa yanayi mata wannan aikin a lokacin Babba ne, zazzabi yake fama dashi kwana biyu.

Sai dai nacin da Sa'id ya saka saita bashi, tayi mamakin ganin ya share gidan kwal, sai gashi yana dan yi mata kananun aikace-aikace, sai aiken da ba'a rasa ba, a hakan kuma yayi sabo da dan gidan Mustafa, har iyayen saida suka dinga mamaki, tunda Mustafa kowa yasan kamar dage yake wajen fada, shisa duk ya kore abokan harna cikin unguwa, amman a ranakun da babu islamiyya, alhamis da juma'a har sautin dariyarshi zaka dinga jiyowa suna labari da Sa'id, akace mai da wawa, sannan su Alhaji Usman mutanen kirkine kwarai, irin kirkin da baya wahalar samu a zamaninsu, kirkin nan na maida dan wani naka, sai son inganta rayuwar Sa'id ta shiga rayukansu, da kanshi ya taka har makarantarsu Sa'id sukayi magana da Malaminshi, ya dauke shi ya sakashi a makarantar boko.

Wannan shine mafarin samun ingantacciyar rayuwa. Sa'id, amman duk da haka yasan iyakarshi, yanda duk suke janshi a jiki yana kama kanshi na sanin fa har abada shidin almajirin gidansu ne, ya samu karatu har matakin NCE inda baisha wahalar samun aikin koyarwa ba a lokacin, sai dai ya samu aikin ne a garin Kaduna, shikuma Mustafa da yake yana da wata irin kwanya, kuma gurbin karatu a Ahmadu Bello ya samu, sai gashi ya samu scholarship zuwa kasar Ingila inda ya dora karatunshi, yayi dabarar yin duk wani aiki da ya samu yana adana kudadenshi, yana da burika masu yawan gaske, babban burinshi shine zama hamshakin mai kudi.

Lokacin daya dawo har Sa'id yayi aure, ya auri Asma'u da kannenta dalibai ne a makarantar da yake koyarwa, a lokacin ita tana makarantar kwana ne aji uku, kuma sun taka har Matazu domin tabbatar da gaskiyar asalin Sa'id kafin su bashi aurenta. Haka dan uwanshi Murtala bayan gwagwarmaya daya sha, tunda shi karancin shekaru yasa kamar ba zai rayu ba a almajirancin da aka kaishi, ya fada harkar garuwa, ya samu nasibi a cikinta, dan da wannan sana'ar yayi aure, yana kama haya anan cikin kwaryar Kano, kafin daga baya ya bude gidan ruwan shi, inda ake dandazon dibar ruwa duk rana.

Yanzun haka yaranshi biyar ne da matarshi Furaira data saka yaran suna kiranta da Mummy, dan kuwa macece da batayi ilimin boko ba, na addinin ma an samu na bautawa Ubangiji, amman tana matukar son harkar gayu, kullum gidanta tsaf zaka ganshi, haka ma yaranta guda biyar ne kacal, tunda taji labarin tsarin iyali ta karbe shi da hannu bibbiyu, so takeyi su samu ingantacciyar rayuwa irin wadda ta gani a tare da yaran Alhaji Sa'id lokacin da takai musu ziyara a garin Kaduna. Suyi ilimi na boko dana addini. Sunayensu ma itace take shigewa 'yan gayu tana adana duk sunan da yayi mata dadi, Asaad ta farayi, sannan Aminatu da taci sunan mahaifiyarta suna ce mata Minal, Ishaq, Hibba, sai Autarta da Murtala ya sakawa sunan mahaifiyarshi Zainab suke ce mata Khairi. Wannan sune iyalan Murtala kanin Alhaji Sa'id.

A filin jirgi Mustafa ya hadu da Rumana da babban wanta, da kuma matarshi, tun daga kallon farko yaji cewar yaga abokiyar rayuwa, Kanuri ce, yar Maiduguri, baka kyakkyawa ta gaske. Duk da yaji dar saboda fuskantar da yayi na cewa 'yar masu kudi ce, haka dai yayi jarumtar karbar katin dan uwanta da yagansu tare. Kuma da yake akace matar mutum kabarinshi, bai samu wata matsala ba, saiga Bafullatanin usuli ya taka har Maiduguri neman aure,dan Mustafa farine kal, ko sumar kanshi ka kalla zaka san cewa bafulatani ne, iyayenshi tsatsonsu fulanin Yola ne. Anyi shagali dai-dai da zamanin, tunda bayan aiki daya samu a shekarar da aka bude gidan man NNPC, wato 1977, duk da baya fatan aiki a karkashin kowa, suka tare a garin Abuja.

Ya fara binciken yanda zai kafa business dinshi na siyar da motoci da tun asali shine plan din da yake dashi. Da taimakon Allaah da kuma tsantsar naci irin na Mustafa ya kafa AU motors, inda daga baya ma ya ajiye aikin nashi da kudi suka fara zauna masa, kuma ya tattara ya baro garin Abuja ya dawo Kaduna ya kara kafa wani branch din na AU motors, yanzun haka yana da branches uku ne, Abuja, Kaduna, Kano, sai dai na Kadunan ma duk yafisu karfi. Jinkirin haihuwa suka samu shi da Rumana, wani abu daya saka iyayenshi matsa masa karin aure ganin irin dukiyar da yake ta tarawa babu magaji a fadarsu.

'Yar uwarshi ya aura Fadime, bayan tarin rikicin da suka sha da Rumana, dan macece ita mai izza da ji da kai, sannan tana matukar kaunarshi. A shekarar Fadime ta samu ciki, kuma saida tayi yara uku sannan Allaah Ya bawa Rumana ciki itama. A yanzun haka, Rumana na da suke kira Mami, na da yara uku ne, Munira, Anisa, sai Haris. Inda Fadime (Umma) take da guda bakwai, Aliya, Halima, Kubra, Shatu, Mukhtar, sai Ibrahim.

Kuma Maryama da duk 'yan uwanta sunsan amintar da take tsakanin babansu Sa'id da kuma Mustafa, dan karin karfin arzikin Sa'id din kowa yasan sanadin Mustafa ne daya kara fadawa harkar noma, sai kuma ya zamana Sa'id din shine yake kula masa da wannan bangaren, in ba haka ba, da basu taso cikin rufin asirin da suke dashi ba, dan aikin koyarwar da yakeyi ba wani kudi bane da za'ace za'ayi hidimar yau da gobe a ciki har a adana wani abu. Dan rufin asirin da Sa'id din ya samu a lokacin, ya kuma karasa ginin daya daukeshi shekaru takwas yanayi, sai 'yan uwan da suka watsar dashi a baya suka dawo sunaji dashi, ciki kuwa harda Murtala da Sa'id din shine yake bibiyarshi sosai da zumuncin nasu ya jima da watsewa. Saima da akaji ya tafi aikin Hajji, bayan dawowarshi kuma Asma'u da suke kira da Hajja tun asali saboda Hajiyayye ake ce mata a gidansu da yake an haifeta ranar arfa, su sai suka takaita shi zuwa Hajja, sai dangi sukace dawa Allaah Ya hadasu ya dinga biya musu bukatu in ba Alhaji Sa'id ba.

Su bakwai Asma'u ta haifa, Ahmad, Khalifa, AbdulKarim, Zahra, Yazid, Asiya sai auta Maryam. Amman tun tasowarsu kullum gidansu cikin jama'a yake, yaran dangi da sukazo hutu daga Matazu, wasu kuma na wajen Baba Murtala da sukazo daga Kano. A cikinsu kuwa wasu ma nan suka kwaso kayansu suka dawo da zama, su bakwai sai suka samu karin mutum biyar, Maimunatu, Sagir, Adnan, Saifullahi, da kuma Khairiyya da 'yar gidan Baba Murtala ce, kuma shekara daya da rabi ta bawa Maryam. Hajja duk ta hadasu ta rike kamar daga cikinta suka fito, tun tana samun matsala da wasu a cikinsu har suka warware suka saki jiki suna mata rikon uwa kamar yanda takeyi musu na 'ya'ya.

A irin amincin da yake tsakanin Alhaji Sa'id da kuma Alhaji Mustafa da Zahra ce ta makala masa Baban Tudun Wada, saboda acan unguwar yayi katafaren gidanshi a garin Kaduna, sunan saiya bishi. Ya kamata ace matansu ma suna wannan amincin, amman babu, saboda Hajiya Rumana bata bada wannan damar ba, musamman da taji labarin wanene Alhaji Sa'id a bakin 'Yan gidansu Alhaji Mustafa, a raine take kallonshi, saboda har a zuciyarta ta kasa aminta dashi a matsayin aminin mijinta bayan yaronshi ya kamata ace ya zama. A karkashin shifa yake ci yana sha. Ita kuwa a irin izzarta me zaija mata kawance da matarshi.

Shisa itama Hajjan ta kama kanta, duk kirki da hakurinta tana da gudun wulakanci, sannan daga ita har mijinta dabi'ar cusa kai ba halayyarsu bace ba, yanda duk Alhaji Mustafa yaso ya juya Hajiya Rumana akan sha'anin gidan aminin nashi dole ya gaji ya kyaleta, garama Fadime ita duk wata hidima da zata taso a gidan Alhaji Sa'id da ita ake wuni anayi har a kammala, duk da Hajja ta girmeta saita zame mata kamar wata Yayaa da bata da ita a kusa tunda duk yan uwanta suna can Yola. Wannan zumunci nasu yayiwa Hajiya Rumana tsaye a wuya yana kara saka mata tsanar duk wani abu daya danganci Alhaji Sa'id da ahalinshi.

A lokacin bata hango wata alaka zata shiga tsakaninta da iyalan Alhaji Sa'id data wuce tunaninta ba.

In su Maryam sunje gidan Alhaji Mustafa, in zasu karaci buga bangaren Hajiya Rumana dansu gaisheta, ba zata taba bude musu kofa ba, daga bayama sai suka daina zuwa, suyi zamansu bangaren Fadime, har su gama abinda ya kaisu a mayar dasu gida. Wannan shine tarihin da Maryama zatace nata, tunda ya hada duk wani abu kama daga asalinta, da kuma duk wasu mutane masu muhimmanci da suke da alaka ta kusa data nesa da ita. Maryam taso ace ta samu Kakanninta, tunda a halin yanzun Malam Ya'u kawun mahaifinta ya jima da rasuwa, sai matarshi Hajiya Inna, kuma sosai Maryam takejin dadin zama a wajenta duk idan sukaje Matazu, saboda labaran da take basu masu abin dariya da ban al'ajabi.

Tana aji uku na a makarnatar Sakandire
End Ads