ba, tabbas ko waye wannan,namusammanne agun Faisal .
[18/08, 4:20 pm] Bilkisu H MUHD: _*GABA DA SO*_
_BY_
*BILKISU H MUHD*
Phone 08031307884
Page 7
*MARUBUCIYAR*
ILLAR SABO
RASHIN RABO
YA YI SAKE
ZAFIN HAWAYE NA
BAKIN KAZAFI
WAYA FI SONTA
GORO DA SANKARA
JINI BIYU
DACEWA
KAUNA CE
BAYAN KUSKURE
MATSALAR KAUNA
TARAIRAYA
DAKE NA DACE
AKWAI BANBANCI
BAKIN KAZAFI
MULKIN MALLAKA
IZZATU
BAYAN KUSKURE
KA AURE NI
KYAUTAR ZUCIYA
*sannan yanzu ta zauna ta kure basirarta gun rubuta muku littafin da bata taba fitar dashi a takadda ba littafine Wanda a online tafara rubutashi , littafin yazo da sabon salo tare da sarkakiya hadi da soyayya mai taba zuciya kowa yaji sunan littafin GABA DA SO zai sojin menene agaba da so daman da akwai abinda yake GABA DA SO,to karanta wannan littafin dan sanin menene ke GABA DA SO.*
makaranta kundai san yadda alkalaminta🖊️yake. Wanda ya santa ya santa Wanda bai santaba yakamata ya gwada karanta books dinta lalle bazata baku kunya ba.
Sannan zaku samu dukkanin littattafai na ta hanyar 👇🏻👇🏻👇🏻
Wattpad:👇🏻
@bilkishmuhd
Arewa Book:👇🏻
bilkisuhmuhd
WHATSAPP GROUP NA BILKISU H. MUHD👇🏻👇🏻
https://chat.whatsapp.com/Fp8jRB4MGGqB1I6J9gc0NE?mode=ac_t
WHATSAPP CHANNEL NA BILKISU H. MUHD👇🏻
https://whatsapp.com/channel/0029VarKaWtBfxnxJ2STpI1o
FACEBOOK GROUP NA BILKISU H. MUHD 👇🏻👇🏻
https://www.facebook.com/groups/1845344956261189/?ref=share&mibextid=NSMWBT
BUSINESS GROUP NA BILKISU H. MUHD 👇🏻👇🏻
https://chat.whatsapp.com/IOFJMOHiTTMJ9cNLRroppc?mode=ac_t
------------------💥
Fada doctor yakeyi sosai kamar zai rufe iyayen da duka .
Duk inda wannan Mara imanin yake yakamata ayi Shari,a dashi,kin kuma dauki hakkin yarinkya wadda bataji ba bata gani ba asali ma babu alamar cewar tataba sanin wani inda hakan ta faru baza,ta Sami wannan matsalar ba gashinan ya lallata muku rayuwar yarinkya inhar ba,a dace ba da yuwuwar ta hadu da ciwon yoyon fitsari.
Cike da kulawa likita ya mayar da kallon sa ga zainab wadda saboda tsabar wahala ta kode tayi wani irin rama.
",ya sunanki? Ya tambaya gaba daya idanun su duka a kanta,
Tashiga hauhawa kamar mai jin tsoro.
"Kugaya mini ina ne nan aina nake,mai nakeyi anan?ina tambaya kunyi mun shuru kowa na kallona kamar ba mutum ba.
Kakarta ta toshe baki da hijabi tana kuka shi ko malam idanunshi sunyi jawar yanajin abinda yafi kuka zuciyarshi na faman tafarfasa.
Likitan ya maida kai kasa yana cigaba da rubuce rubucensa.tsahon mintina biyar ya dago .
"Yanzu kafin muyi komai zamu fara baku gado sannan za a yi mata taimakon gaggawa kafin komai ya biyo baya
"sannu zainab.
Kawai binshi tayi da ido daga bisani tayi murmushi mai hade da kuka.
Bayanin likita ya gama gigita su da dubun danasani musamman ma kakar ta.
Zainab ta dubi kakar ta wadda ke faman kuka ta dauko hannu tana shafa fuskar kakar.
" kema fyade yayi miki, yaji miki ciwo sannu kaka, mugune, Amman Ina sonsa.
Dukkan wadanda ke dakin kallon kallo suka koma yi.
" likita mai ke shirin faruwa?
"cikin kunan rai ya dubesu.
" tsahon wani lokaci takai cikin wannan sumbatun.
Sai ga kwalla wani na bin wani a fuskar baban zainab
"ka tambayi babarmu ita ta hana kowa zuwa inda take a wani daki ta ajiye ta kusa da bandaki ko fitila babu, abincima ba, a bata sai ta kama babu mai shiga gunta kawaicina ya hana na bibiyeta gashi na cutar da ita.
babarmu kuwa kuka take yi sosai idanunta duk sun tattasa ita kuwa zainab daga ta kalli wancan sai ta kalli wannan sai tayi murmushi wani lokacin tayi kuka bara na barku anan Wanda zamu Dora nan gaba.
--------------------------------------
Rakiya kina ganin wannan yaron zai saurare ni kuwa jibeshi fa tamkar shiyayi kansa, kai banajin zai Soni, "aikinji ki , kina abu kamar karamar yarinya waya gaya miki batun so akeyi, in batun so ake daman mai zaiyi dake mtss, magana ce kawai na kisaki data masu karfi dan wannan sai kin dire mishi sama da milyan guda ,dan haka idan yayi miki sai kiyi bayani ta sauke wani ajiyar zuciya " rakiya wannan ya cancanta,wannan dan shilan Aiko Nazir dina be kaiba , rakiya atura mishi milyan biyu banason murabu ina son mu kulla alaka mai karfi,ina sonsa" ke Kam dadina dake kenan ,in kika kuskura kikayi mishi zancen soyayya zaki kwabawa garin ki ruwa kawai kedai kibi abinda na gaya miki.
-----------------------------------------
Ya caba kwalliya har ya gaji ya fito sai kamshi yake
Akan darduma ya ga kaka tana jan carbi ya kalleta yana murmushi ya matsa daf da ita ya ɗan rankwafa.
"Kakata zan fita a nema min sa, a zan je gun mutuniyar.
bata iya magana ba sabida addu, a take yi cikin daga hannu ya kama hanya zai fita daidai lokacin ta shafa
" da izinin Allah daga kanta zaka ga darasu, daga kanta zaka kiyayi duniya sai ta wahalar da kai kuma har a bada tafi karfin ka, ko a zaman aure bazaka taba samun taba
Ta sake daga hannu.
" Allah na rokeka akan wannan baiwa taka ka nuna mishi iya karsa idan ka tsara cewar matar sace ka juya lamarin kada ya taba samu ta ka kuma azabtar dashi da soyayyar ta mai zafi kila hakan ya zamo sanadin shiriyar sa ta---
" haba kaka!! Irin wannan mugun jafa,i haka kamar ba jinin kiba.
" wallahi kaima sai kayi kuka kamar yadda kasa iyayen yara kuka ko jikakeyi bansan abinda kake shukawa ba, wallahi kar nake kallon ka da idanuna biyu.
tafice tabarshi tana nemawa ikhalas tsari ga fadawa tarkon azzalumi irinsa.
Rahama ce tayi kudin mota suka koma sunyi iya duban su basu ga wayar ba
suka dau hanya suna dubawa nanma shuru dole babu alamar wayar komawa suka yi gida ajigace Allah ya taimaka Abu bai dawo ba.
Sallama suka yi da Rahama ta koma gida ita kuma ta koma dakin ta cike da tunanin abinda zata gayawa Abu.
Har karfe dayan dare bata iya rintsawa ba ta mike ta shiga bathroom ta dauro Alwala ta fito ta shinfida darduma ta dauko alkur'ani mai girma ta shinfida ta hau ta fara jero sallar nafila sai da taji kafafunta na neman gagararta tsayawa sannan tayi sallama ta janyo Alkur'ani ta soma tilawa. Karamar wayar ta ta hanga yana haske alamar kiranta ake da sauri ta mike cikin goge kwallar fuskar ta ta ratsa kore Assalamualaikum ya ce kafin ta amsa ya fara magana,kada ki boye mini gaya mini maike damunki tayi murmushi yayin da kuka ke neman kwace mata" maiyasa kace haka?" Baby nayi mafarki mara dadi yau akanki tin daga lokacin na kasa samun nutsuwa ta danyi dum cikin kokarin daidaita kanta" babu komai kaji," please baby kada ki juya mini baya in kikayi haka zan haukace Ina mutukar sonki Ina sonki dayawa dan Allah kibani magani yau," magani wanna iri," ina son ganinki yau Ina son hotonki hakanne zai rage mini radadin danakeji , "Zuciyata ta samu natsuwa tun daga lokacin da kika shigo rayuwata."
"Ki ce min 'Ina sonka' sau ɗaya, zan rayu da wannan jin daɗin har abada."shuru yayi yana son ji daga gareta,bata da niyar magana" baby zaki toro min picture ɗin yanzu?
" kayi hakuri idan ka ganni bazaka soni ba " saboda me?"bani da kyau ni mummuna ce duk abinda yake mai kyau ajikin mace bani da---stop it,I say stop ya isheni haka ni nace kibani hotonki Ina sonki aduk yadda kike dan haka ki bar wannan shirmen" tsintar kanta tayi da fadin bani dashi,"ok to yayi kyau nagode duf ya katse wayar
Wani irin son sa taji yana kara ruruwa acikin zuciyar ta, tanajin tausayin shi kwanciya tayi akan darduma yazatayi ne tayaya zata iya cireshi arayuwar ta.
Abu ne ya turo kofa daidai lokacin ta maida hankalinta kan alkur,anin dake gabanta .
" ashe idon ki biyu
" nakasa bacci.
"ki dauko littafi ki dan taba karatu, karatu yafi zama da irin wannan lokacin.
Wani kallon shakku ta koma yi masa, ta fahimci Abu ya dauki karatunta da muhinmanci fiye da ibadar ta in banda haka Alkur'ni fa yagani ajiye a inda take fa bata ce komi ba banda binshi da ido da tayi tana son sanar dashi batan wayar ta amman takaici ya hana ta magana.
Ya kamata mu waiwaya baya dan jin wanene Mahaifin Ikhlas wato Alhaji Ibrahim.
Tuna baya
Bai taba shiga aji dan koyon karatun boko ba,na muhammadiyya ma ba sosai yayi ba,in da ya lakanta hakan da rashinjin da ya shuka,
alokacin baya shine bin kucakan matan lungu shine tare hanya yana dumbularwa "yan mata kirji shine tsokana shine gantali idan yafita tun safe baidawowa sai zai kwanta bacci yau iyayensa bazasu taba cewa sun moreshi koda ta hanyar tayasu aikin gida ba, sai d'aga murya akan tasu ko cewa sukayi mikon ruwa insha sai da kunkuni da buga kafa yake zuwa wani sa'inma ko kallonsu bayayi wadannan halayya nasa su suka saka iyayen suka sallamashi Hakan bai sa ya nutsu yagane cewa gajiya sukayi suka barshi da halinsa ba ko kadan befito daga dangin da suke da abin hannu ba kaf dinsu babu Wanda za,a nuna ace yana da dan abin hannu duk Wanda ka duba acikinsu beki a tallafa masa ba dangin bawani yawa ne dasu ba har kawo lokacin da yarasa iyayen nasa bai sauya halayya ba tabbas hausawa na cewa idon iyaye mashine bai tashi gane kuren saba sai da ya rasa iyayensa anan ya gane cewar duk wani daga masa kafa da akeyi sabida mahaifansa ne
yayyensa wa anda suke uba daya ma burus sukayi dashi haka ne yasa yatashi tamkar wani shashasha kowa kyamarsa yake bashida wani suturar kirki na sakawa idan kaga yaci abinci to dako yaje yayo a kasuwa sannan ya Sami kudin da zaici abinci
yana dan shekara ashirin da bakwai yaɗan soma mallakar hankalinsa inda wani bawan Allah Mai suna malam isa ya jashi jikinsa ,malam isa kayan gwari yake saidawa idan aka siya Ibrahim ne ke kaiwa masu siye cikin mota sannan a sallameshi.
[18/08, 4:20 pm] Bilkisu H MUHD: _*GABA DA SO*_
_BY_
*BILKISU H MUHD*
Phone 08031307884
Page 6
*MARUBUCIYAR*
ILLAR SABO
RASHIN RABO
YA YI SAKE
ZAFIN HAWAYE NA
BAKIN KAZAFI
WAYA FI SONTA
GORO DA SANKARA
JINI BIYU
DACEWA
KAUNA CE
BAYAN KUSKURE
MATSALAR KAUNA
TARAIRAYA
DAKE NA DACE
AKWAI BANBANCI
BAKIN KAZAFI
MULKIN MALLAKA
IZZATU
BAYAN KUSKURE
KA AURE NI
KYAUTAR ZUCIYA
*sannan yanzu ta zauna ta kure basirarta gun rubuta muku littafin da bata taba fitar dashi a takadda ba littafine Wanda a online tafara rubutashi , littafin yazo da sabon salo tare da sarkakiya hadi da soyayya mai taba zuciya kowa yaji sunan littafin GABA DA SO zai sojin menene agaba da so daman da akwai abinda yake GABA DA SO,to karanta wannan littafin dan sanin menene ke GABA DA SO.*
makaranta kundai san yadda alkalaminta🖊️yake. Wanda ya santa ya santa Wanda bai santaba yakamata ya gwada karanta books dinta lalle bazata baku kunya ba.
Sannan zaku samu dukkanin littattafai na ta hanyar 👇🏻👇🏻👇🏻
Wattpad:👇🏻
@bilkishmuhd
Arewa Book:👇🏻
bilkisuhmuhd
WHATSAPP GROUP NA BILKISU H. MUHD👇🏻👇🏻
https://chat.whatsapp.com/Fp8jRB4MGGqB1I6J9gc0NE?mode=ac_t
WHATSAPP CHANNEL NA BILKISU H. MUHD👇🏻
https://whatsapp.com/channel/0029VarKaWtBfxnxJ2STpI1o
FACEBOOK GROUP NA BILKISU H. MUHD 👇🏻👇🏻
https://www.facebook.com/groups/1845344956261189/?ref=share&mibextid=NSMWBT
BUSINESS GROUP NA BILKISU H. MUHD 👇🏻👇🏻
https://chat.whatsapp.com/IOFJMOHiTTMJ9cNLRroppc?mode=ac_t
------------------💥
Faisal kwance akan wata doguwar kujera sanye da gajeren wando sai singlet kan kafet lemone ajiye sassanya kofin har wani raba yake daya daga cikin wayarsa ta dauki ruri ya kalli wayar ya basar har ta katse wani kiran ya sake shigowa yaja tsaki in bai daga kirannan ba bazata bari ya hutaba
Ya ratsa kore ya kafa a kunne.
"Hy, hot milk where are you?
Muryar wata mata ta tambaya
" Ina jin ki, kifadi abinda kike son fadi ko in katse wayar.
Daga daya bangaren tace
"oh my god, what wrong?
"please malama bana son damu, nace kidaina kira, kawai ki turo test.
" kayi hakuri ranka ya dade, daman ina son ganin kane, gaba daya na kasa samun nutsuwa.
"ke mahaukaciya, agurina yanzu kingama bandaro, nagaji da tuwo ina son sauyi,
Ta soma magana cikin damuwa.
" kada kayi mini haka, yanzu haka na kama mana daki.
"kinga inkin amince akwai wannan kanwar taki yar lukutannan ita kawai nake muradi, kiyi mata waya sai ta canjeki.
Wata uwar ashar ta danna ya katse wayar.
Ko ajikinsa ya gyara zamansa ya mika hannu ya janyo wata drowa wata yar karamar roba ya dauko ya bude wasu irin kwayoyi ne a ciki ya dauki guda shida ya watsa a baki ya kora da ruwa ya koma ya kwanta lamo tuni ya mance inda kansa yake.
Bayan wasu awanni ya dawo hayyacinsa ya tashi ya shiga bathroom ya ware shaya a kansa ya dade ruwan na zuba akan nasa a hankali wani nutsuwa ya fara saukar masa sannan ya dauki soso da sabulu ya cuɗa jiki bayan ya gama ya dauraye jiki ya dauki tawul ya tsane jiki ya janyo daya tawul din ya daura.
Handset din ikhalas ne rike a hannunsa ya na faman shige da fice a ciki yayi murmushi abubuwan ta gwanin burgewa itace mace ta farko da ta soma birgeshi tana da kyau ta gama hada komi ga hotunanta da familyn ta da malaman makarantar su daya bangaren kuma hutunan tane data dauka lokacin saukar ta ya tsayar da idanunsa akan wani hoto data dauka babu hijabi sai dan siririn bakin mayafi data yane kanta dashi wasu daddeku daga cikin kwayoyin gashinta sun rufu akan fuskarta wasu abubuwa yaketa aiyanawa aransa,.
Gaskiya yarinyar nan mai kyauce acan karkashin zuciyarsa ya dinga jin tanayi mishi wani irin kwar jini ya Kai yatsa yana zagaye saitin bakinta dashi tamkar tana gabansa wani irin azababban Sha,awarta ya dinga fusgarsa idan bai idar da nufinsa akantaba zai iya haukacewa.
Tadade tsaye akansa bazata taba mance wannan kyakkyawar fuskar ba tsaf ta fahimci "yar aljanna ce,sunan da talakaba ma ikhalas kenan tun lokacin da ta Kira ɗanta da surukar ta awaya tana basu labarin irin jahadin datayi akanta da suka tambayi sunan ta tarasa Mai zatace sai cewa tayi yar aljanna ita din haka take komi kankantar alheri kambamashi takeyi takasa mance fuskar ikhlas, tana jin ta a ranta ta rasa mai yasa
To amman mai ya hada lalataccen jikan nata da wannan salihar.
"mai sunan baba aina kasan wannan yar karamar yarinyar?
Yayi murmushi.
" kaka, kema kin yaba kenan, ko?
Ya fada yana kallon ta.
"nace aina kasan ta, ka bani amsa ba.
" kakahh, manene naki na daga hankali nifa namiji ne, namiji wanda yasan abu mai kyau,dan haka na yaba.
"Allah bazai baka ikon cutar da itaba,mutumin banza.
Tana huci tana komi taciga da banbami.
"Wallahi wannan tafi karfinka albarka na tattare da ita dan haka kayi ahankali in ba hakaba sai ka tafka dana sani.
Ya dinga kyalkyala dariya.
" Haba yar tsohuwa ni akwai matar da zata fi karfina a wannan duniyar tun daga larabawa indiyawa ballantana bakar fata yar mutsiyata,ai kawai Kisha kuruminki Ina tabbatar Miki da kyar ne in baza a kawo miki ɗan da zaki goyaba.
Yana magana yana dariyar ƙeta.
Carbin dake rike a hannun ta, ta daddage ta tsula masa tsakanin ta da Allah ta kai mishi dukan ya gantsare sabida ta shige shi har tsakar kansa.
"ah kajimu da tsohuwa da Carbin zaki dakeni, sabida kawai ina son kawo miki tattaba kunne.
Ta tsorata sosai kaf halinsa babu Wanda bata saniba Inya kwallafa rai akan mace duk ustazan cinta sai ya lalata ta yasan salo salo na yaudara idan yana narkar da kudi sai ka dauka injin kudi ne dashi yake bugawa mace daya ce ta gagareshi awannan duniyar itace zainab
Ya hadu da ita Kamar yadda ya hadu da ikhalas , zainab yarinyace "yar kimanin shekara ashirin da daya nitsattsiya ce yar malamai tana da kyau daidai nata haduwarsu da ita ya gama haukacewa kota halin kaka yana son kasan cewa da ita amman ko kallo bai ishetaba duk hanyar da yabi taki bari ta ce masa koda sannu haka ne yasa yadinga bin sahunta har ya yi bincike akanta yagama sanin komi akanta sai dai ya lura cewa iyayenta irin iyayennan ne masu gudun duniya hakane yasa ya sauya taku inda yaje ga mahaifinta ya nuna cewar yanason auren zainab abashi dama su dan fahimci juna,wannan dalilin ne yasa zainab ta fara tsayawa dashi da ike shidin maye ne ko ince shidin na da banne yasan duk yadda zayyi ya mallaki zuciyar mace komi tsaurin ta iya kalamensa sun taka rawar gani gun mallakar zuciyar ta kallo daya yayi mata ta kamu da wani mugun sonsa sai dai hakan bai sa ta saki jiki da shi ba sabida wani mugun kunkyace da ita ko ido bata bari su hada dole ya boye maitarsa ya kudurce a ransa dole ya biya bukatarsa koda sama da kasa zasu hade.
Kafin mahaifinta yabashi dama da kansa ya tura mutane neman aurenta ya kuma ce a cikin wata daya yakeson agama komi,mahaifanta sun nuna sai dai asaka wata shida don sugama kintsawa,take ya nuna cewar baya bukatar komi shi yagama komi yana da komi duk da haka sunki amincewa haka yasa ya dinga bin danginsu har aka shawo kan mahaifinta ya amince zo kaga inda yadinga yi musu barin kudi akwatuna kawai sat hudu aka kawo basu sallama ba sai da sukaga gidan da za,a kaita da kayan dakin daya zuba Mata, duk anyi wannan sha, ani batare da sanin kowa nasa ba.
Awata dayan aka gama biki ankai zainab gidan ta kowa ya watse inda yashigo tana zaune a kan sallaya ta kudundune Kai kuka takeyi sosai hannu ya Kai ya dagata cak ya zaunar da ita ajikinsa ya fara aiwatar da abinda ta kasa ganewa ganin yana neman zakewa yasa ta fara magana cikin raunannaniyar murya.
"Jinakeyi sai munyi sallah ko.
Cikin wata shakekkiyar murya.
Jinakeyi sai da na biya sadaki na kuma cika duk wasu sharadai ko cewa akayi idan bamuyi sallah ba aure mu ya haramta? daman shi mutunne wanda bai iya rarrashi ba,jin maganar tasa tayi banbarakwai
ahankali ta kada Kai hadi da tsuke baki akan gado ya direta yana kokarin sauke alkawarinsa duk yadda tayi ihu tayi kuka baisa ya sauraraba yadda yayi Mata Babu kyawun gani bai kyaletaba sai dai yaga bata iya motsin arziki ya Suri pillow ya koma sitingroom .
koda asuba tayi da kyar ta mike tana tafiya cikin rintse ido da cije lebe ga wasu zafafan hawaye na faman bin kuncinta wani irin zazzabine ya rufeta jitakeyi kamar mutuwa zatayi wanka tayi kamar yadda musulunci ya tanadar Mana azaune tayi sallah akan dardumar bacci ya kara dauketa .
bugun kofa ne ya tasheta batayi yunkurin tashiba tana tunanin Faisal zaije ya bude Amman sai