amma kada ki raina wani. Ki san darajarki, amma kada ki manta da jinin da kika fito daga cikinsa. Akwai mutunci cikin girmamawa, kuma akwai daukaka cikin saukin kai.
Duniya tana iya fada miki ki zama wadda ke sama da kowa, amma zuciyar uwa tana rokonki ki zama wadda ke kusa da kowa. Wannan shine girman da Allah ke so."
" daga karshe bazan gaji da sanar dake cewar zaɓin Allah zaki nema ba, domin zaɓinsa yafi zaɓin kowa, ko kaɗan kada ki bari ya rikita miki tunani, yadda danginsa ke tafi dake kaɗai zai sa ki yanke hukunci a kan yadda yake aibata su a gurinki"
Bata sake cewa komi ba ta miƙe tayi waje.
Kalaman Ammi sunfi tasiri a gareta fiye dana Abu, yadda Ammi ke gaya mata haka Rahma ke gaya mata.
wanne yaƙi ne zai faru idan Abu yasan cewa Ikhalas tana waya da Zaruk?
Www 10 w
shin burinsa zai cika a kanta ko kuma zaiyi rashin nasara?
Wwwwwe
Bilkisu H. Muhd ✍🏻1w²w
[18/08, 4:20 pm] Bilkisu H MUHD: _*GABA DA SO*_
_BY_
*BILKISU H MUHD*
Phone 08031307884
Page 2
*MARUBUCIYAR*
ILLAR SABO
RASHIN RABO
YA YI SAKE
ZAFIN HAWAYE NA
BAKIN KAZAFI
WAYA FI SONTA
GORO DA SANKARA
JINI BIYU
DACEWA
KAUNA CE
BAYAN KUSKURE
MATSALAR KAUNA
TARAIRAYA
DAKE NA DACE
AKWAI BANBANCI
BAKIN KAZAFI
MULKIN MALLAKA
IZZATU
BAYAN KUSKURE
KA AURE NI
KYAUTAR ZUCIYA
*sannan yanzu ta zauna ta kure basirarta gun rubuta muku littafin da bata taba fitar dashi a takadda ba littafine Wanda a online tafara rubutashi , littafin yazo da sabon salo tare da sarkakiya hadi da soyayya mai taba zuciya kowa yaji sunan littafin GABA DA SO zai sojin menene agaba da so daman da akwai abinda yake GABA DA SO,to karanta wannan littafin dan sanin menene ke GABA DA SO.*
makaranta kundai san yadda alkalaminta🖊️yake. Wanda ya santa ya santa Wanda bai santaba yakamata ya gwada karanta books dinta lalle bazata baku kunya ba.
Sannan zaku samu dukkanin littattafai na ta hanyar 👇🏻👇🏻👇🏻
Wattpad:👇🏻
@bilkishmuhd
Arewa Book:👇🏻
bilkisuhmuhd
WHATSAPP GROUP NA BILKISU H. MUHD👇🏻👇🏻
https://chat.whatsapp.com/Fp8jRB4MGGqB1I6J9gc0NE?mode=ac_t
WHATSAPP CHANNEL NA BILKISU H. MUHD👇🏻
https://whatsapp.com/channel/0029VarKaWtBfxnxJ2STpI1o
FACEBOOK GROUP NA BILKISU H. MUHD 👇🏻👇🏻
https://www.facebook.com/groups/1845344956261189/?ref=share&mibextid=NSMWBT
BUSINESS GROUP NA BILKISU H. MUHD 👇🏻👇🏻
https://chat.whatsapp.com/IOFJMOHiTTMJ9cNLRroppc?mode=ac_t
------------------💥
Tunda sanyin safiya ƙofar gidan ke cike a nata faman fita da buhunhunan kayan masarufi kama kan buhunhunan shinkafa, fulawa, katan-katan din taliya da sauran ababen ci, wani abin birgewa shine jama'a sun jeru babu wata hayaniya.
Alhaji Ashir wanda ake yiwa laƙabi da baban sukari da kanshi yake rabon waɗannan kaya duk wanda ya miƙawa zai fara rangaɗo addu'oi har kakan kakansa sai an yiwa addu'a, wani tsoho da aka zo kansa jikin shi na rawa yana sharar ƙwallah ya shiga jero mishi addu'a "ubangiji ya bayyana fatima yasa tana hannun nagari, Allah ya baka haihuwa ubangiji ya rabaka da duniya lfy"
"Ameen, Ameen"
Abin da Alhaji Ashir kawai yake cewa kenan, inda yake jin wani miki na tasowa a can ƙarƙashin zuciyar sa.
*** *** *** ***
Tafe suke su biyu itada ƙawar ta Rahma, gaba ɗayan su sanye suke cikin kayan makaranta sai dai kayan yayi bala'in yiwa Ikhalas kyau kamar ba uniform ba, duk wanda ya kalleta a cikin kayan sai ya sake juyawa saboda yanda kayan ya karɓeta kamar dan ita aka yi, daf da zasu gilma ta gun Ikhalas ta dubi Rahama sannan tace"ban taɓa ganin mutum irin shi ba, idan aka ce dani waye gwanina cewa zanyi baban sukari, ina
ƙaunar bawan Allannan"
Rahama ta dube ta"Kinga ance bai taɓa haihuwa ba yana baƙin cikin ya mutu ya barwa matarshi gado, dan haka yake ɓarnatar da dukiyar sa, saboda abin nasa yayi yawa"
"Mtssss" Ikhlas taja tsaki sannan tace"kawai sai yayi ta rabar da dukiyar sa ba dan Allah ba sai dan mugunta ko? da Allah Rahma kada ki sake faɗin haka in ba haka ba sai a ɗauke ki a matsayin jahila"
daga karshe abin ya nemi ya zame musu rigima hakan ne yasa Ikhlas ta tsuke baki.
-------------------💥
"Bilkisu duba min wani jarababben ne ke ta faman buga mani ƙofa haka kamar wanda naci ban biya ba?"
Bilkisu dake ƙoƙarin fitowa daga toilet ta amsa da " toh"
da sauri ta ƙarasa ta buɗe, wani matashi ta gani da kurar turi ɗauke da buhun shinkafa da buhun fulawa sai ƙaramin buhun suga irin mai cin kwano biyar matashin yace "baban sukari ne yace a kawo nan gidan"
"masha Allah mungode sosai Allah ya saka"
godiyar da yaji tayi yawa ne yasa shi saurin miƙewa ya buɗe dukkan muryarsa "meke faruwa ne a nan?" ya ƙarasa wajan tare da kallon matashin.
"Kai malam wannan kuma daga ina?" Matashin ya gaya masa kamar yadda ya gaya wa Bilkisu, suna ƙoƙarin saukewa Alhaji Ibrahim yace" dakata kai zan saɓa maka muddin ka sauke waɗan nan kayan a gidan nan, an faɗa maka mu mayunwata ne irin ku?, to ku koma kuce dashi lalacewar mu bata kai a kawo mana sadaka ba, ya kaiwa mabuƙata mu kam munfi ƙarfin a bamu, maza ku kwashe tarkacen ku"
Bilkisu kam saboda tsabar mamaki bakin ta ya ƙi rufuwa ga wani nauyi da kunya daya lulluɓeta ji take yi kamar zata haɗiyi zuciya, juyawa tayi ta koma ciki.
......................... 💥
A hanyar dawowar su Ikhlas daga makaranta tun daga nesa suka ga ana nuno su, gaban ta ne ya faɗi ta rasa dalilin nunawar, duk sai taji ta tsargu, har suka iso gun idon matasan na kanta.
Wani ya ɗaga murya yana faɗin" nasan shi sosai fa, da talaka ne futuk sai dai a kawo musu ragowar jagwalgwalon yara suci shi da matarshi, kullum ka gan shi cikin tsumma yake abin tausayi, ban san yadda aka yi ya waye haka ba"
Wata murya taji kamar tasan mai shi yana cewa"wannan ƴar tasa da ita suke takama, gidan da suke ciki ma nata ne, da fa a gidan ƙasa yake haya, ɗakin su ko rufin kirki babu"
Sai hahaha suka sa dariya.
"Ɗan shegiya sai faɗin rai"
da sauri suka ɗaga ƙafa Rahma tace"ikhalas kamar na hango wannan ɗan yayan baban naku a gun kodai da ku suke? ni naga gaba ɗaya mu suke kallo musamman ma ke"
"Su suka sani"
cewar Ikhalas.
....................... 💥
Ammi ce ta bata labarin abin da ya faru a inda itama ta gaya mata maganar da ta jiyo ana yi a waje
" Amman Ammi mai yasa Abu ya ke haka ne baya tsoron bakin mutane, idan baya so sai ya karɓa ko su Baffa hamza sai ya baiwa"
Bilkisu ta sauke ajiyar zuciya," ni na ce ke kanki kin fi kowa sanin halinsa? sai nuna isa gashi bai isa ɗinba"
Ikhalas taji kalamen Ammi sunyi mata tsauri sai ta dingajin babu dadi aganinta bai kamata ta fito da irin wannan maganar agabanta ba kawai ta barshi aranta tunda ita din y'ace.
motsin shigowar da suka ji ne yasa su yin shiru.
---------------------------------------
"Ai in Allah ya yadda sai Ikhlas ta mutu inyaso muga ta ƙarya"
Salisu ya fada.
baffa Hamza ne ya dakatar da shi gun tsinkeshi da wani azababben mari ya dafe kunci yana huci baffa Hamza yace"dan uban ka ƙanwar taka ka ke yiwa fatan mutuwa? ita ɗin mai tayi maka kawai sabida halin ubanta?"
Cikin ƙunci yace"Amman Abba abin nasa ne akwai ban haushi, ya sani mu ba unguwar mu ɗaya da baban sukari ba, yasani mu ba, bamu za'ayi ba, ya san kuma da hakan amman tsabar baƙin hali da son nuna fariya ya....."
"Ba zaka yi mani shiru ba ko? ko kai baka taɓa cin abinci bane?"
" Toh amman Abba ko yanzu babu wanda ya karya a cikin mu"
"Ba zaka yi mani shuru ba ko!!?" gyaɗa kansa yayi, Fuuuu yayi waje yana faman ƙunƙuni.
"An faɗa in Allah ya yadda ƙwaƙwalwar ta sai ta zama ta jakai"
"Abban su Salisu dole fa yaji babu daɗi, kai ban san me yasa baka ganin laifin su ba"
"Banda ke da abun ki Dija kowa fa arziƙin shi yake ci, muma fa mun haifa wataran zamu ci albarkacin yaran mu, baki sani ba ƙila ma a kwai shugaban ƙasa a cikin yaran naki" ya faɗa yana murmushi.
Banza tayi masa ta shige ciki ita bata taɓa ganin marar zuciya irin baban Salisu ba.
........................ 💥
Haj Hauwa ce durƙushe a gaban malam tana faman kuka"yanzu malam babu yadda za'a yi in samu haihuwa?"
Malam ya maida hankali a kan ƙasar da ke gaban sa ya ɗanyi zane zanen sa ya ɗago kai ya dube ta" gaskiya mijin ki ba mai haihuwa bane"
Ta jinjina kai cikin tashin hankali " to malam menene abin yi?" ya ɗanyi shuru yana shafar ƙasar dake gaban sa, sannan ya ɗago yace"kawai dai a sake sabon ta soyayyar yaron ki a zuciyar sa"
"Toh malam kodai a kashe shi?"
Da sauri malamin ya ɗago yana duban ta" ai mutuwa sai lokaci yayi, kuma mu babu kisa a tsarin aikin mu idan lalle sai kisan kike so sai dai ki nemi wani"
Jikin ta ne yayi sanyi duk sai taji ta muzanta " to shikenan a sabunta soyayyar yaron nawa a zuciyarsa in yaso ya zamto sai yadda mukayi da shi" bundle din ƴan dubu dubu ta ajiye masa suka yi sallama.
---------------------------------------
Alhaji Ashir (Baban sikari) shahararren attajiri ne wanda bashi da burin da ya wuce ya farantawa mabuƙata, kullum yana jin cewar an bashi arziƙin ne kawai domin ya taimakawa marasa ƙarfi, har matasa ne dashi waɗan da ya wakilta a kan duk wanda yake cikin unguwar tasu idan bashi da shi a gaya masa, ya sayi motoci irin bus bus ɗin nan dan kai yara makaranta, waɗanda ya ɗauki nauyin karatun su ba zasu lissafu ba, Alhaji Ashir ɗan kwangila ne sannan yana da manyan kantina a kasuwar kwari, ana juya masa kuɗaɗen shi.
Dattijo ne shi ɗan kimanin shekara sittin, yana da mata guda ɗaya, a halin yanzu matarsa ta fari Allah yayi mata rasuwa, sai hauwa wadda i tace ke zaune da shi da yaron ta ƙwaya ɗaya wanda ta haifa a wani gidan wato Nazir, tun yana ɗan shekara goma sha huɗu ta kawo shi gidan, yanzu haka shekarunsa ashirin da takwas, taƙadari ne na gasken gaske, sai dai a gaban baban sukari babu mutumin kirki irin shi, baban sukari ya riƙi Nazir tamkar ɗan cikin sa ƙaton shago ya mallaka masa a kasuwar kwari, sai dai Nazir da haj hauwa basu da buri illa ya danƙa ragamar dukkan harkokin shi a hannun sa, sun bi malamai sun bi bokaye har sun gaji, duk lokacin da baban sukari ke fidda zakka ji suke yi tamkar za suyi hauka, yanzu burin hauwa ta yaya zata sami haihuwa da shi ko dan taci gadon shi, wannan kenan.
Cikin mamaki ta kalli ƙawar tata sannan tace"Lalle haj hauwa yau na tabbatar da baki da hankali, yo idan kika saka aka kashe shi dame zaki ƙaru? ai gwara kisaka ayi masa asirin da zai zamo shi ba'a mace ba, shi ba'a raye ba, yanzu fa da zaran ya mutu waɗanda ma baki taɓa gani ba zasu yunƙura suce ɗan'uwan su ne, kuma dole ne a raba gadon dasu"
Hajiya hauwa ta saki ajiyar zuciya, cikin damuwa tace"haka ne aminiya, yanzu meye abin yi?"
" Abin yi kawai mubi a hankali zamu sami wanda zaiyi mana aiki a kansa, kudi zaki bani naje India kinsan ance sheɗanun bokaye sunfi yawa a can"
Wata uwar shewa suka saka tare da tafawa wannan kenan.
-----------------------------------💥
America
Babban birnin Amurka shine Washington, D.C.
Shi ne cibiyar gwamnati ta Tarayyar Amurka, inda Aso Villa na Amurka wato White House, Majalisa (Capitol Hill), da Kotun Koli (Supreme Court) suke.
Georgetown
Wannan tsohuwar unguwa ce mai tarihi da kudi. Tana cike da gidaje masu tsada, shaguna masu kyau, manyan restaurants, da manyan mutanen kasa. Akwai celebrities da diplomats da manyan ‘yan kasuwa da ke zaune a nan.
The Four Seasons Hotel Washington, D.C.
Yana cikin Georgetown. Wannan hotel din yana da matakin duniya, yana karbar shugabanni, celebrities, da ‘yan kasuwa. Farashin ɗakin dare ɗaya yana iya haura $1000 .
A hotel din wani katon Holl ne wanda ya gama kayatuwa da kayan alatu da wasu irin kujeru na alfarma ga yadda holl din yayi shuru zaka tabbatar da cewar abinda ake tattauna akai yana da matukar mahinmanci.
Wani matashi wanda bazai wuce shekaru ashirin da takwas ba sanye da white shirt da Black jeans yayi aski low cut mai tsafta sanye yake da Rolex agogo a sandar hannunsa da kuma tabarau rayban sai dan karamin zoben gold a yatsan sa takalmin kafarsa
Fendi shoes sai Hermes belt dake daure a kugunshi.
Zaruk kenan yong billions wanda ake ji dashi a wannan zamanin manyan kusoshi ke neman hada hannu dashi ayanzu haka iya da hannun jari a campanunuwa irinsu
Apple Inc. (AAPL)
Kamfani mafi girma a duniya bisa kasuwar daraja (market capitalization).
Yana kera iPhone, iPad, Mac, da sauran kayayyakin zamani.
Saka hannun jari a Apple yana da daraja saboda yana da ƙarfi sosai a kasuwa.
Microsoft (MSFT)
Shahararren kamfani na fasahar zamani.
Yana da software irin su Windows da Microsoft Office, da kuma Azure (cloud computing).
Amazon (AMZN)
Babban kamfani na e-commerce (sayayya ta yanar gizo).
Hakanan yana da Amazon Web Services (AWS) – babban kamfani na girgijen ajiya.
Wanda ke kawo riba sosai.
Nvidia (NVDA)
Kamfani mai ƙera kwakwalwan kwamfuta da ake amfani da su wajen AI, da wasanni (gaming).
Hannun jarinsa ya haɓaka sosai a cikin shekarun baya-bayan nan saboda tasirin AI.
Inda Zaruk ke zaune da wasu irin speakers jere agabansa yana magana kadai zai tabbatar da cewa shidin wani babban kusane da ake ji dashi
Ya dade yana jawabi cikin muryarsa mai ƙarfi da kwarjini, lokacin daya gama jawabin gaba daya aka dauki tafi .
Wadanda suke baki agun kasan cewar yaune ganinsu da shi na farko yayi mutukar birgesu tambaye suke wai waye shi sabida gaba daya shi din bai kaisu haske ba amman fatarshi tafi tasu kwanciya da kyau
gashi da tsayi wanda bai wuce misali ba
siffa mai kyau alamar kulawa da lafiya.
Tafiya da tsayuwa irin ta jarumi
Gaskiya da aminci: baya yaudara, kuma abin dogara ne.
yana da hangen nesa da sanin me yake nema.
yana da Sauƙin kai ba mai girman kai ko wulaƙanci ga mutane ba.
yana da Kiyaye magana da alkawari: idan ya ce zai yi, to sai ya yi.
yana nuna damuwa da jinƙai ga na kusa da shi.
Kyakkyawa ne na gaske . bayan kowa ya gama jawabinsa taro ya watse sai dai shi kasan cewarsa musulmi sai da shi da tsitarin musulmen dake gun sukayi addu,o'insu kafin su watse.
gashi dai ba'a ƙasar musulunci ya taso ba amman yana ibada tamkar yau zai bar duniya, haka kuma mutum ne mai son ibada, abin da zai baka mamakin a kan Zaruk kaf gidan shine kaɗai musulmi, sunyi iya yinsu akan ya koma Christian amman fir yaƙi, kasancewar su a turai kowa na bin ra'ayin sa ne, kafin mahaifinsa John ya mutu ya gargaɗi dangin sa cewar kada wanda ya kuskura ya tilasta shi a barshi a musuluncin sa, dan haka kowa ya sa masa ido, wannan banbancin addinin baisa sun ƙyamace shi ba, suna mutuƙar ƙaunar sa, za kayi mamakin idan kaga Zaruk na yin hausa tamkar ya girma cikin garin Kano, hakan ta samo asali ne ta dalilin gidansu amininsa wanda ya kasance kaf ya kare rayuwarsa a cikin gidansu, kwanciyar bacci ne kawai ke raba su da gidan sai dai yanzu gaba ɗaya sun koma Nigeria, lokacin da uban gidan su ya mutu wato John mahaifin Zaruk a dalilin yadda suka riƙe Zaruk ya sanya John ya mallaka masa dukiya mai tarin yawa har kawo yanzu Alhaji Auwal, Zaruk dinne ya zamo mai gidan sa, arzikin da Zaruk ya gada a wajen John bashi da iyaka, abun birgewar shine baka taɓa sanin waye shi ko a suturar da yake sawa inba sanin ta kansu kayi ba sai ka zaci mai saukin kudi ne sabida rashin hayaniyar kayan wani fannin ya kan saka na matsakaicin kuɗi.
---------------------------------------------
Babban Gida Gini mai hawa da launuka masu natsuwa (fari, grey, da duhu-blue).kewaye da babban haraba
Gidaje Na Cikin Gida (Guest Villas) Domin ma aikata da baki da kuma abokai.
Swimming Pool mai kyan gani da haske da tsakar dare.
Ga Private Garden: Lambu da shuke-shuke masu tsada, kamar orchids da bonsai trees.
Garage na Supercars: Ferrari, Lamborghini, da Mercedes Maybach suna a tsare.
Cikin Gida (Interior)
Babban Falo (Living Room): Mai fadi, design na zamani (minimalist + luxury), da LED lights masu canza launi.
Glass Walls: Ganuwar gilashi da ke nuna lambu ko pool.
Library + Office: Wurin da yake karatu da gudanar da business.
Kitchen na zamani: Inda shi kansa zai iya dafa wani abu idan yana so
Home Cinema: ta kallo fim. Idan ya gayyaci abokai
Fitness Room / Gym: Don ya nuna jikinsa yana aiki, lafiyayye ne.
Balcony mai View: Wurin da zai dinga kallon taurari idan yana jin damuwa tayi masa yawa.
Sanye yake da White Shirt + Dark Jeans
Yana tsaye a gaban gilas din falo yana kallon ruwan sama da tunanin mushinta.
Ikhalas na waya da Zaruk a ɓoye, ta gefe guda kuma tace baban sikari yana birgeta, Iklhas yane😅
Yaya zata kaya tsakanin Baban sikari da kuma matarsa Hajiya hauwa? shin tana yin nasara a kansa domin su samu gadon dukiyar sa?
Tafiyar tamu me tsawo ce kawai ku antayo mu tafi tare💃🏻💃🏻💃🏻
Bilkisu H Muhd✍🏻
[18/08, 4:20 pm] Bilkisu H MUHD: _*GABA DA SO*_
_BY_
*BILKISU H MUHD*
Phone 08031307884
Page 4
*MARUBUCIYAR*
ILLAR SABO
RASHIN RABO
YA YI SAKE
ZAFIN HAWAYE NA
BAKIN KAZAFI
WAYA FI SONTA
GORO DA SANKARA
JINI BIYU
DACEWA
KAUNA CE
BAYAN KUSKURE
MATSALAR KAUNA
TARAIRAYA
DAKE NA DACE
AKWAI BANBANCI
BAKIN KAZAFI
MULKIN MALLAKA
IZZATU
BAYAN KUSKURE
KA AURE NI
KYAUTAR ZUCIYA
*sannan yanzu ta zauna ta kure basirarta gun rubuta muku littafin da bata taba fitar dashi a takadda ba littafine Wanda a online tafara rubutashi , littafin yazo da sabon salo tare da sarkakiya hadi da soyayya mai taba zuciya kowa yaji sunan littafin GABA DA SO zai sojin menene agaba da so daman da akwai abinda yake GABA DA SO,to karanta wannan littafin dan sanin menene ke GABA DA SO.*
makaranta kundai san yadda alkalaminta🖊️yake. Wanda ya santa ya santa Wanda bai santaba yakamata ya gwada karanta books dinta lalle bazata baku kunya ba.
Sannan zaku samu dukkanin littattafai na ta hanyar 👇🏻👇🏻👇🏻
Wattpad:👇🏻
@bilkishmuhd
Arewa Book:👇🏻
bilkisuhmuhd
WHATSAPP GROUP NA BILKISU H. MUHD👇🏻👇🏻
https://chat.whatsapp.com/Fp8jRB4MGGqB1I6J9gc0NE?mode=ac_t
WHATSAPP CHANNEL NA BILKISU H. MUHD👇🏻
https://whatsapp.com/channel/0029VarKaWtBfxnxJ2STpI1o
FACEBOOK GROUP NA BILKISU H. MUHD 👇🏻👇🏻
https://www.facebook.com/groups/1845344956261189/?ref=share&mibextid=NSMWBT