x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 3 - GABA DA SO

  • 6001 words
  • 9000 words
  • Out of 19064 words

Category: Love Stories

Views 98

22 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
NA BILKISU H. MUHD 👇🏻👇🏻
https://chat.whatsapp.com/IOFJMOHiTTMJ9cNLRroppc?mode=ac_t


------------------💥


Haba mommy wannan ta,adin yayi yawa ai bashine ƙaruna ba wanda yafi kowa kudi da a kullim shi bashi da magana sai na ya taimaki jama'a ,wai kinji makudan kudin da yabayar wai wasu malamai zasu tafi can Kan dutse da'awa,amman mu idan mukace muna son kudi sai an tambayi abinda zamuyi dasu kodan ni bashi ya haife niba ai inda ace ni dansa ne komai zai sakar mini shago fa daya ya bani mai naci aciki Mai na bawa mutane na ga jamila na dauke da ciki ni dai gaskiya nagaji kawai ki sama mana mafita"haba Nazir kadinga kasa da murya mana kofa yaushe zai iya shigowa,ni nafison mubishi a sannu mutun ne shi mai wayo idan na nuna ina son abinsa bazai sake gaya mini sirrin shiba kaga yana yawan gaya mini inda kadarorinshi suke idan mukace zamuyi wani yunkuri zamu rasa abubuwa da dama idan muka dan jinkir ta dazaran ya gama gaya mini inda dukkan kadarorinshi suke komeye sai muyi mishi sallama suka jiwo daga harabar gidan " yanake jin murya kamar ta rakiya ta dan leka ta taga aikuwa da gudu ta kwasa kamar wata karamar yarinya suka rungume juna har suna huwaɗuwa haj Hauwa ta ruko hannun rakiya cancan kuryar daki take shirin kaita zasu wuce kawai Nazir ya bisu da kallo babu sannu ballan tana gaisuwa shifa duk wata kawa ta mahaifiyar ta to tazo ne ta yagi rabonta.
   acan cikin daki atsakiyar gado tana zaune dafi'an gabanta kayan ciye-ciye ne kala kala,kai kana kallon rakiya zaka tabbatar da tsohuwar kilakice babu digon kunya a idanunta.
Kaf haj Hauwa ta gama shaida mata abinda ke faruwa da kuma wanda take shirinyi.
"Tabdijan lalle bakima da hankali to duk abinda kika tsara beyiba hajiyata kawai harka zamu bude haj Hauwa ta gyara zama " banfahimta ba " badai baya haihuwa ba to zamu samo mishi yaro awaje dole ki dana bariki bama sai na koya miki ba tunda an taba danawa,kawai sake lale zakiyi ki koma ruwa zabura tayi cike da mamaki" haba rakiya tsofai tsofai dani,kuma fa karki mance ina da saurayin ɗa  bandama ban haihu da wuri ba da yanzu ina da guda uku kafinshi"tsaya tukunnan saratu badai kina jinin al'ada ba" inayi amman wani fannin nakanyi wata biyu zuwa uku kafin nayi" kinga koma kin daina zamu dawo dashi ki samo yaro a manna mishi" a,a rakiya ina ganin wannan hanyar bamai bullewa bace mutuminan yafasan baya haihuwa"to ba yana da sani ba, yasani idan Allah yaga dama zai iya juya lamarinsa ke kodama ya gane dole ya yadda nasani kodan tsira da mutuncinsa, haj Hauwa ta dinga jinjina kai alamar zancen ya shigeta,ammanfa sai kin bude bakin aljihu idan da kuruciya ke za'ake biya idan kuma kin zama iya ke zaki biya,kuma biya mai kyau dazaran komai ya kankama yanzu zaki ga kin zama yarinya,amman kuma sai fa kina hadawa da gyara naga yanzu duk kin sukurkuce kamar bakeba dan yaro bazai baki hadin kai kina tsaminnan ba jibeki kin sanya kaya mai kyau harda su janbaki sai dai gashi sai wani bashi'bashi kikeyi ga tsami nasan awannan hamamin danake ji kin kai sati bakiyi wankaba,"a,a ke Kuma banson cin fuska" kinsanni tin da bana barin abu aciki batare da na amayar ba nasani yadda kike wannan warin na tabbata pant din dake jikinki ba karamin doyi yake ba Kuma--tayi saurin katseta "waike rakiya kin mance wacece ni " yo koma wacece kedai kinsan ba,a bakin komai nake ganinki ba sabida tun muna fita da dan bantai muke tare kinsan ke ba komai bace face matsiya ciya wadda bata da cin yau mune ma muke taimakawa gidan ku da guntattakin abincin da yaran gidan mu sukaci suka rage"haba rakiya wannan cin fuskar yayi yawa,ko kin mance ni mamanku take rikewa nake rakata gun kwaraten ta yawan ma danakeyi ada ai ita ta sanyani a hanya" Kinga to mubar zance haka muyi abinda ke gabanmu haj Hauwa sai cika da batsewa take" haba tawan saki rai mana muyi shawarar yadda zamu ci arziki mubarshi amazaunin sa" hehehe mubarshi fa kika ce ai shi wannan arzikin sai mun cinyeshi tas ko kale bazamu bariba suka kwashe da dariya tare da tafawa" shegiyas ashe har yanzu bakin halin nanan.
------------------------------------
Karfe goma Sha daya da rabi na dare ikhlas ce keta faman Kai komo idanunta a rintse rike da littafi a hannu da alama tana son tabbatar da cewar haddar da take kokarin yi ya zauna mata akanta  sai dai ga mamaki ta wannan karon haddar taki zama innillahi wa'inna ilaihim raju'un wannan shine karo na farko da hakan ta faru da ita wayyo Allah wai meke shirin faruwa da ita ne? ta koma ta zauna gaba daya tunanin zaruk ya hanata sukuni.
   kwance da ammi agado  yadan bude ido ahankali sabida sautin karatun ikhlas da yaji da sauri ya diro daga gado ya kinkimi flast din shayi sai yajishi babu nauyi alamar Babu komi aciki ya ja tsaki.
    Ammi tadan dago Kai.
    "Indai shayi ne na shanye".
"amman dai kinsan ikhlas zata bukata ko"
yafada cike da takaici.
"shikenan sai naki Sha sabida bukatar ikhlas.
Ta koma ta kwanta taja bargo ta rufe kai.
Mikewa yayi ya dauki flast din ya shiga kitchen ya kunna gas ya dora wani tea din baibar gunba sai da shayi ya kammalu ya juye cikin flast sannan ya nufi dakinta.
Ita kam ikhlass tasake mikewa tana zagawa cikin karatu tare da sake rintse i cikin rashin sani ta bangaji abban nata har sai da flast din ya kusa faduwa da sauri ta bude idanunta.
" Sannu Abu bansan ka shigoba.
Yayi murmushi Mai tattare da  kulawa.
" Sannu da himma ikhlas,mamanki ta ce ta kawo miki nescafe din naki ko?
" Eh.
Ya ajiye flast din dake rike a hannunsa
" kifa dinga amfani da nescefe shi zai taimaka miki wajen karatun ki baza kiji bacci ba.
Ta dan jinjina kai alamar to.
" Zanje na wanke uniform Inna gama sai na Sha tea din.
Yayi murmushi .
"Sai dai kijira nefa kuma sukawo wuta kiyi gugan ,na wankesu tun dazu.
Ya juya ya fita ta koma ta zauna agefen gado kaunar Abu na kara ratsa zuciyar ta,duk yadda yake takure ta amman yadda yake nuna mata kulawa tanaji babu Wanda ya kaita sa,an samun uba.
Acan karkashin zuciyar ta tausayawa kanta takeyi da ta yadda ta sake soyayyar wanda bata sani ba ya hudata, ta yadda koda mai abban ta zayyi bata jin zata iya rayuwa batare da shi ba.
Wannan kenan.

Ahankali ta ware idanunta yayin da hasken rana ya dallare mata idanu abu biyu ne ya fado mata makarar yin sallar asuba sai gugan uniform .
"Subhanallahi,
Tayi saurin dirowa daga gado zata fita ta hangi uniform din nata a kan dirowa.
Ta kada Kai cikin murmushi tasan wannan aikin Abu ne,ta fada bathroom tayi wanka tare da dauro alwala ta haukan dadduma tayi sallah bayan ta idar ta zauna ta rasa addu, ar da za tayi kamar yadda Ammi tace a duk lokacin da tayi sallah ta dinga rokawa kanta samun miji na gari, jitakeyi aranta Zaruk din miji ne na gari tsintar kanta tayi da fadin Allah ka sassauta zuciyar Abu ya amince mini zaruk ya zamo abokin rayuwa ta,ta yaya, wani bangare daga cikin zuciyar ta tayi mata wannan tambayar ras taji gabata ya buga da sauri ta kwautar da wannan tunanin muryar Ammi taji tana kwala mata kira da sauri ta mike.
  Alhaji Ibrahim zaune a darning table suna karyawa ikhlas ta fito cikin Shirin makaranta ta durkusa har kasa ta gaidasu ta koma ta zauna agaggwuce ta fara cin abincin  Wanda taci baikai ya kawoba ta sunkuci Jakarta zata fice.
"Abu sai na dawo,ammi natafi.
da sauri Ammi ta dauko raguwar break din nata ta juye mata cikin wata yar karamar roba Mai murfi ta zuge jakar ta  Wanda ke goye abayanta ta zira aciki.
Gudu gudu sauri sauri ikhlas ta fice a gidan.
Alhaji Ibrahim yana kokarin yiwa Ammi magana Handset din Sa ya shiga ruri yayi saurin dauka yadade suna musayar magana daganan ya aje wayar cike da farin ciki.
Tunda ya fara wayar ammi ta kafeshi da ido ta sauke ajiyar zuciya lokacin da ya aje wayar tana kallonsa.
"Yarki fa likafa nata ci gaba,yanzu haka ansanya sunanta agasar da za,ayi acan  abuja  sannan idan har ikhlass tazo koda ta biyar ne  za,a  a fita kasar London kafinma mu je candin sai munje mun sauke farali anyi mana alkawarim zamu sake komawa mu sauke farali lalle lu'ulu'una kyauta ce daga Allah.
"Amman baka ganin idan wannan abin yayi yawa za,a dinga jin tsoron dosanta da sunan aure.
Wani irin zabura yayi.
"Ke kina da hankali kuwa,tabbas na yadda baki San ciwon kanki ba,aini kiga nayiwa lu'ulu'una aure sai naga ta taka kololuwar matsayi a ilimi.
Ammi ta katseshi da fadin
" Kana son kace koda mijii yazo bazatayi aure ba?
"Kinga jinan, wallahi ko dan gidan dangwatai ne ya zo neman aurenta sai na cika burina kan na aurar da ita gareshi in bazai jira ba ya kara gaba,ni nafison ta Sami arziki na kashin kanta ba na mijin ta Wanda ko yaushe zai dingayi mata gori ba ita kadai fa na mallaka sai na baiwa kowa kunya akanta bazata yi irin rayuwar danayi ba muddin ina raye sai ta zama a bar kwatance.
Ammi kawai jinjina Kai takeyi cike da takaici.
"Amman yakamata ka sani tuni ubangiji ya gama tsara mata rayuwar ta.
Kafin ya yi magana ta mike tabar gun dan ta tabbatar ta baro rigima muddin bata dan kwaice daga gun ba.
  Bayan an tashi a makaranta ta dade tsaye tana
Jiran napep duk Wanda ta tsare sai yace ba nan zaiyi ba Iphone dinta ya soma ringing ta dubi fuskar wayar.
"Wayyo Allah Abu ne..
Ta ratsa Kore tare da kafe wayar a kunne.
"Ina kika tsaya kusan awa guda da tashi?.
"Abu mota nake jira har yanzu bansamo ba Amman insha Allah yanzu zan karaso.
"To shikenan sai kin dawo.
Ta maida wayar cikin jaka ta soma tafiya cikin hanzari wani dattijo Mai napep ya hangeta har ya wuce ya fahimci akwai damuwa a tattare da ita ya dawo da baya yayi parking hadi da dan leko da Kai .
"Ina zakije?
Kamar zatayi kuka.
"Sharada.
"Bisimillah,shigo muje.
Tunda ta shiga napep take ta faman sake sake.
"Munzo sharadan.
Tayi firgigita tana kokarin dauko masa kudi dari biyar ta mika masa ta sauka zata tafi.
"Tsaya ki karbi canjinki.
"Kaje kawai .
"Nagode sosai.
Sai da yaja babur din ta gane bai kaiga inda takeson tsayawa ba duk taji ba dadi tabbas yau zatasha tafiyar ƙafa gashi tabashi dukkan kudin ballantana ta sake shiga wani,kwanar mai kwaikwa zuwa masallacin juma,a na sharada akwai tazara yazatayi?
Wata tsohuwa ta hanga rike da uban kullin kaya har rankwafawa ta danyi tafe take dakyar tausayi ya kamata tuni ta mance da tata matsalar.

BILKISU H MUHD,✍️
[18/08, 4:20 pm] Bilkisu H MUHD: _*GABA DA SO*_
    


        _BY_
*BILKISU H MUHD*


Phone 08031307884

Page 3


*MARUBUCIYAR*



ILLAR SABO
RASHIN RABO
YA YI SAKE
ZAFIN HAWAYE NA
BAKIN KAZAFI
WAYA FI SONTA
GORO DA SANKARA
JINI BIYU
DACEWA
KAUNA CE
BAYAN KUSKURE
MATSALAR KAUNA
TARAIRAYA
DAKE NA DACE
AKWAI BANBANCI
BAKIN KAZAFI
MULKIN MALLAKA
IZZATU
BAYAN KUSKURE
KA AURE NI
KYAUTAR ZUCIYA



*sannan yanzu ta zauna ta kure basirarta gun rubuta muku littafin da bata taba fitar dashi a takadda ba littafine Wanda a online tafara rubutashi , littafin yazo da sabon salo tare da sarkakiya hadi da soyayya mai taba zuciya kowa yaji sunan littafin GABA  DA SO  zai sojin menene agaba da so daman da akwai abinda yake GABA DA SO,to karanta wannan littafin dan sanin menene ke GABA DA SO.*
makaranta kundai san yadda alkalaminta🖊️yake.  Wanda ya santa ya santa Wanda bai santaba yakamata ya gwada karanta books dinta lalle bazata baku kunya ba.


Sannan zaku samu dukkanin littattafai na ta hanyar 👇🏻👇🏻👇🏻

Wattpad:👇🏻
@bilkishmuhd

Arewa Book:👇🏻
bilkisuhmuhd

WHATSAPP GROUP NA BILKISU H. MUHD👇🏻👇🏻
https://chat.whatsapp.com/Fp8jRB4MGGqB1I6J9gc0NE?mode=ac_t

WHATSAPP CHANNEL NA BILKISU H. MUHD👇🏻
https://whatsapp.com/channel/0029VarKaWtBfxnxJ2STpI1o

FACEBOOK GROUP NA BILKISU H. MUHD 👇🏻👇🏻
https://www.facebook.com/groups/1845344956261189/?ref=share&mibextid=NSMWBT

BUSINESS GROUP NA BILKISU H. MUHD 👇🏻👇🏻
https://chat.whatsapp.com/IOFJMOHiTTMJ9cNLRroppc?mode=ac_t


------------------💥


Tunda ya rasa mahaifi sa yake ji shi tamkar wanda aka dauke shi daga cikin inuwa aka maida shi tsakiyar kwalleriyar rana, Amman bai san mai yasa ba haduwarsa da Aisha ya sauya komi, itace wacca ruhinsa da zuciyar sa ke mutukar so, tabbas yanzu ya soma jin rayuwa nayi mishi dadi, yanzu yasomajin yana son rayuwa.
Aisha ta zama rayuwar sa farin cikin sa, hakannan ta zama burinsa.    
Sai dai wani fannin ya kan ji tamkar kirjinshi zai fashe idan ya tuna yana soyayya ne da babu yakan tsinci kan shi cikin wani irin tashin hankali, eh babu zai ce mana tun da bashi da tabbaci akanta sai dai yakanji sanyi da rangwame idan ya tuna cewar Allah na karbar addu, ar wanda ya roke shi da izinin Allah koda tana karshen duniya wata ran zai mallake ta kamar yadda yake ji ajikinsa, ya soma sonta da wasa ya maida ta tamkar nishadinsa idan yana jin nishadi yakan kirata kawai musamman idan yana son yin yaran hausa duk da ba Mai son magana bace cikin hikima da dabara yake Mata wayo har ta saki jiki dashi batare da ta sani ba ahakan yayi mutakar sabawa da ita ahankali soyayyarta ta dinga hudashi musamman da ya fahimci tana da kananun shekaru sai yayi amfani da hakan  ya koya mata sonsa yadda bazata iya ba idan babushi sai dai akaf shakuwarsu ya fahimci cewar akwai matsala ita din kuma matsoraciya ce ya kuma fahimci tana mutukar kaunar mahaifinta kuma tana kokarin bin umarninsa dan haka yake fuskantar kalu bale a kaunar su.
Yana zaune a hadadden office dinshi wanda tsananin haduwarsa tamkar fadar wani basaraken ma aikata ake so ya tantance sabobbin da za'a diba a kamfani mutum shida kawai ya iya gani acikin darurruwar muta ne karshen sai wasu ya wakilta rashin daga wayarsa da Aisha batayi ba duk shi ke damunsa yanajin ajikinshi tamkar bashi da lafiya komawa yayi gida.

bayan yakoma gidama yaci gaba da kira nan ma bata dagaba yanzu ne ya kara tabbatar da shakuwar su
ya kasa zaune ya kasa tsaye komi yayi masa baki kallon komi da kowa yake a haka su kansu ma aikatan gidan sun lura da haka, duk da ba mutun ne mai son magana ba gaba daya jisukeyi babu dadi musamman  Jafar da Ayan wadan da ayanzu sune mafi kusanci dashi sabida kasan cewar su musulmai Kuma suma hafcase ne sai dai Ayan balarabane shi Kuma Jafar dan Iran ne amman asalin mahaifiyar su hausawa ne haka kuma Inka gansu hausawa ne sak sai dai hasken fatar da suke dashi shima din ba sosai ba dan Zaruk yafisu haske nesa ba kusaba.
Jafar ne da Ayan suke tattaunawa" kwana biyu kenan bashi da walwala bantaba ganin boss cikin wannan yanayi ba,Ayan yace" to ko Kuma bashi da lfy"kai banace ba ,rabona dai da ganinsa cikin wannan yanayi tin lokacin da aka kama dan uwansa osi,duk cikin harshen turanci suke wadannan maganganun" mai yasa bazamu gwada kiran osi ba?
" wallahi zurfin ciki bayyi ba yau da ace boss zai gaya mini matsalar shi ko ace zan san matsalar zan iya yin komi akai, bashi da magana, amman yanayin sa ya nuna yana cikin matukar damuwa.
" ina kasani boss bazai so haka ba kawai muyi mishi addu, a.

"dai dai da minti daya bana son ganin shi cikin damuwa wallahi boss ya fiye mini komi, bantaba ganin mutum irin saba mai mayar da matsalar wani tashi.

Daga can garden suka hango  yana ta faman danne dannen waya yana kuma kai komo.

Daga inda Jafar yake hangenshi kamar zai saka kuka.

" Ya Allah ka kawo mana mafita.

Zaruk ya koma ya zauna akan wata doguwar kujera irin ta turawa wanda a kayiwa gun rumfa da wata yar'bukka abar sha, awa ya  zube wayoyin nashi akan table cikin yanayin damuwa daya daga cikin wayoyin ya soma ringing da sauri ya dubi wayar bro ya gani rubuce a fiskar wayar ya saki ajiyar zuciya a sanyaye ya dauka hadi da karawa a kunne.

"Assalamu alaikum.

" hi bos yau banji kaba.

" ina cikin koshin lfy.

Jin muryar sa ya tabbatar masa cewar akwai damuwa sai  yaji kamar ya shigo ta cikin wayar dan ya sani in zai kwana yana lallashi  bazai taba jin komi daga bakin saba idan kuwa suna tare kwakkwafin sa zai sanya ya gano komai.

"my boss please, and please kada ka ce dani babu damuwa ina rokon alfarma ka gaya mini inba hakaba na rantse zan toho.
ras gaban Zaruk  ya fadi yasa ni zai aikata, zuwan sa kuma zai haifar da babbar mosifa, zuwan shi zai iya kawo sanadin rasa shi, yana kaunar sa matuka bazai iya jure rasa shiba a duniyar nan yana yi masa kauna irin wanda zai iya yiwa wanda suka fito ciki daya da sauri ya kwarara kansa yasaki rai.
" brother kana jin zan iya samun matsala maina rasa a wannan duniyar, na sani mutuwa dolece nima zan mutu kamar yadda iyayena suka mutu dole zan sawa kaina hak'urin wannan, to amman bacin rashin su bani da wata matsala duk wata daula da hamshakai suke tutiya dashi ina da, sannan ina da dan, uwa wanda yake mutukar kaunata to kagani bani da wata damuwa, kawai dai ka kirani a daidai lokacin da na farka daga bacci
Wata doguwar ajiyar zuciya osi ya saki tare da duba agogon dake daure a tsintsiyar hannun shi.

" bro bacci a irin wannan lokacin?
" mun dan zazzaga camfany shi yasa "Naji dadi, yanzu bani labari,
haka suka cigaba da hirar abinda ya danganci kamfanin sa dake Nigeria. 
---------------------💥
Kwance take tayi ruf da ciki da littafi ajiye agabanta karatu takeyi Amman Tama rasa Mai zata karanta komai ya kunce mata tadaina daga wayar sane don ta gwada ta yadda zata rabu dashi tanajin babu dadi ta yadda take cin amanar Abu  sai dai hakan yasa ta jigata sosai meyasa ta bari hakan tafaru da ita batasan lokacin da sonsa ya hudata hakaba tana kuma ji ajikinta kamar yana cikin damuwa
Ta sauke ajiyar zuciya game da tsurawa handset dinta ido kamar tana sauraron kira ta ture littafin dake gabanta gefe ta mike zaune kanta ne ya dinga Wani irin sarawa bazata iya jurewa ba daukar wayar tayi ta shiga loda number sa ciki kira ta shigayi sai dai har ta katse ba,a daga ba
End Ads