x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 4 - GABA DA SO

  • 9001 words
  • 12000 words
  • Out of 19064 words

Category: Love Stories

Views 101

22 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
sai da ta maimaita Hakan kusan sau uku babu alamar za,a daga tilas ta hakura ta koma kasa kan tayis ta kwanta tana jan wasu ayoyi azuciyar ta ko taji sanyi tana karatun tana kissima kammanninshi .
Bata sanshiba Amman tanajin ajikinta zata soshi ko ya yake da wannan tunane tunanen bacci yayi awon gaba da ita ,bacci Mai tattare da mafarkai iri'iri.
Washe gari wunin ranar haka tayishi cikin rashin kuzari zo kaga tashin hankali gun Alhaji Ibrahim gaba daya ya wuni yanayi mata hayaki da rubutu wai kila ana son taba mata tauraron tane wani turare daya gumbuda mata sai da ta kusan barin duniya dan tsabar tarin wahala bai iya fita ko kofar gida ba cike yake fal da zullumi ita kuwa Allah, Allah ta dingayi ya fice ta sake kiran sa ko zai daga kiran haka ne yasa ta kwarara jikinta hadda debo su wanki tanayi .
A sitting room tana jiyo su yana magana da Ammi.
" Mai nace dake ,so ake a tabata yanzu dataji hayaki bagashi ta mike ba.
Ammi kawai binshi takeyi da kallon ta kaici ita kuwa can cikin zuciyarta tana tausayin Abu tana Kuma tausayawa kanta aranar ko masallachi baije ba agida yayi sallolinsa.
Tun karfe tara ta tattara ta koma dakinta.
Karfe dayan Handset dinta ta hanga yana fidda haske alamar kira ya shigo, kamar yadda ta saba ko yaushe wayar tata a silent yake  koda yar uwa mace  Abu beyadda ta kira taba wai kada su juyar mata da tunani Rahman ce kadai ya amince suyi mu'amala da ita sabida tare suka taso sannan gidan su yan bokone sannan ko yaushe intazo zai ga karatu suke yi.
Abinda besani ba ita din ce ke kokarin rusa masa ginin daya dade yana ginawa.
Har wayar ta katse wani kiran ya sake shigowa bata iya daukaba tunanin Abu takeyi da kwalla taf idanunta.
Ya zabi ya hana kan shi komi ya gyara ta duk wani abun daya danganci kayan gayu sutura mai tsada turarurruka maya mayen gashi  kafin ta zama haka har dako yashayi sukanyi kwanaki basu dora tukunya ba muddin zai biya mata bukatar makarantar boko
Yakanyi alfahari kansa ya fasu a duk lokacin da ya kalleta baya son kowa ya rabeta musamman ma da baiwar da Allah yayi mata ya bayyana kwakwalwar ta tamkar bata mutane ba duk abinda kwakwalwarta ta gani sai ta dauka tamkar wanda ake bude mata kwakwalwarta ajuye mata

Yana mutukar kaunar ta fiye da yadda yake kaunar kansa haka ne yasa ya saka mata tsaro sosai tare da takunkumi ya kuma takure ta, yana sakar mata fuska sosai amman idan aka zo batun karatu baya sassauta mata yana jin duk wanda ya rabeta yana sa rai da cutar da ita zai yi dan haka koda wadanda suke jini daya bai yadda su rabe taba.
Wayar na sake cigaba da ringin akaro na biyar da sauri ta mike tayi tattaki zuwa bakin kofa kamar yadda ta saba a duk sa'adda zatayi waya ta kulle tare da murda key ta koma ta rufe windows duk sabida wai kada iska ya debi maganar ta ya kai waje ta komo ta zauna ta janyo bargo ta rufa bayan ta dauki waya
"Ishahh
Ta yadda ya furta sai da yasanya ta saki wani dogon ajiyar zuciya.,bazai nuna mata ya damu da rashin daga wayarsa da batayi ba, tasanshi ba lalle yayi mata maganar  ba mutunne shi mara son dawo da magana baya idan abu ya wuce bai fiya maimai tashi ba.

'' bakiyi bacci ba?
Jinjina kai kawai tayi tamkar tana gabansa.
"Ina son ki hadani da Abu
gaba daya idanunta sukayo waje jikinta ya hau rawa jitake yi ma kamar ya gama gaya Masa  cewar suna soyayya har ta soma tunani hukuncin da zai yanke mata ya katse mata tunani.
''ina rokonki da ki amince, ina ji ajikina kece wacca Allah ya zaba mini, tunkan nasanki kike zuwan mini amafarki bansan kiba amman nasan muryarki, ki amince mini nayi alkawari, baza kiyi dana sani ba.
"ba yanzuba ina jin tsoro papa zai dauki mataki a kaina baya son na kula kowa kumama dan baka ganni bane nifa karama ce ban....

" kullum haka kike cewa amman ai dolene ya aurar dake ko tunda kina ganin lokacin baiyi ba ,kawai kiyi mini alkawari baki da mijin da ya wuce ni ni kuma in Zaki kai shekaru dari nayi alkawari zan jiraki- - -

"Kayi hakuri.
Akufule yace

" Nacinye shi...
" Shiwa
Ta tambaya.
Hakurin mana
Batasan sa adda ta dinga dariya ba har yanajin sautin dariyar cikin wayar sa.

"Wallahi, idan zan rasa ki, zan haukace. Ban san yadda zan iya cigaba da numfashi ba,
Ina sonki baby ina mutukar sonki Kada ki barni. Kada ki gushe daga zuciyata. Kada ki sa ni rayuwa ba ke ba. Zai fi sauki a cire zuciyata gaba ɗaya.

Yagama kashe mata zuciya wani irin sonsa ne ke tasowa daga can cikin ranta.
" Bansan kiba ban taba ganin kiba kawai sonki  Allah ya halitta min bansan mai hakan ke nufiba naji kawai ina tsananin sonki haka nayi Alkawari tsakanina da Ubangiji bazan taba aure ba muddin kina raye duk kuma yadda zaki boye mini nayi alkawari sai na zakuloki domin Allah ya halicce kine dominni haka nake ji ajikina sai kin zamo tawa,tawa ni, ni kadai.
Takasa ce masa komai tasani duk yadda yakeji tanajin fiye da hakan

"Allah ya hada fuskokin mu ,shine kawai Mai wahala agare ni duk Wani tsaro na Abu zan iya ji dashi nasan yadda zan bi dashi.
Hmmmm kawai tace yayinda ya shiga yi mata hirar da dole ta saki jiki dashi sosai  hirar tasa mai tattare da bugun ciki yana son sanin a inda take sai dai duk yadda hirar ta kaiga yi mata dadi bata sake ta sanar dashi a Wani state take a Nigeria ba hakan ya tabbatar masa da cewar tabbas tana da mutukar wayo Kuma tana bin dokokin abbanta Hakan na Kara daga darajarta a idanunsa.
" ina zuwa.
Tace dashi yauma bata jira maizai ceba ta katse wayar.
Zubewa tayi agodo ta shiga rusa kuka kukan da takejin shine kadai zai sanyaya mata rai.

To mutane na ya abin yake ne ,ga  Ikhlass na ganin cewar duk yadda Zaruk ke sonta bai kamo kafar taba ankya kuwa, kunfasan shi so makahone inda ace abinda take ikirari hakane ai da bata boye masa halinda zuciyar ta ke ciki ba,amman dai muje zuwa

Bilkisu H MUHD -----✍🏻
[18/08, 4:20 pm] Bilkisu H MUHD: _*GABA DA SO*_
    


        _BY_
*BILKISU H MUHD*


Phone 08031307884

Page 5


*MARUBUCIYAR*



ILLAR SABO
RASHIN RABO
YA YI SAKE
ZAFIN HAWAYE NA
BAKIN KAZAFI
WAYA FI SONTA
GORO DA SANKARA
JINI BIYU
DACEWA
KAUNA CE
BAYAN KUSKURE
MATSALAR KAUNA
TARAIRAYA
DAKE NA DACE
AKWAI BANBANCI
BAKIN KAZAFI
MULKIN MALLAKA
IZZATU
BAYAN KUSKURE
KA AURE NI
KYAUTAR ZUCIYA



*sannan yanzu ta zauna ta kure basirarta gun rubuta muku littafin da bata taba fitar dashi a takadda ba littafine Wanda a online tafara rubutashi , littafin yazo da sabon salo tare da sarkakiya hadi da soyayya mai taba zuciya kowa yaji sunan littafin GABA  DA SO  zai sojin menene agaba da so daman da akwai abinda yake GABA DA SO,to karanta wannan littafin dan sanin menene ke GABA DA SO.*
makaranta kundai san yadda alkalaminta🖊️yake.  Wanda ya santa ya santa Wanda bai santaba yakamata ya gwada karanta books dinta lalle bazata baku kunya ba.


Sannan zaku samu dukkanin littattafai na ta hanyar 👇🏻👇🏻👇🏻

Wattpad:👇🏻
@bilkishmuhd

Arewa Book:👇🏻
bilkisuhmuhd

WHATSAPP GROUP NA BILKISU H. MUHD👇🏻👇🏻
https://chat.whatsapp.com/Fp8jRB4MGGqB1I6J9gc0NE?mode=ac_t

WHATSAPP CHANNEL NA BILKISU H. MUHD👇🏻
https://whatsapp.com/channel/0029VarKaWtBfxnxJ2STpI1o

FACEBOOK GROUP NA BILKISU H. MUHD 👇🏻👇🏻
https://www.facebook.com/groups/1845344956261189/?ref=share&mibextid=NSMWBT

BUSINESS GROUP NA BILKISU H. MUHD 👇🏻👇🏻
https://chat.whatsapp.com/IOFJMOHiTTMJ9cNLRroppc?mode=ac_t


------------------💥


ta tunkari tsohuwar. da sauri ta karbe kayan hannunta
"Sannu kaka,Ina zakije?
"Yauwa jikata yar albarka,zanje gida ne,
"Amman Ina ne gidan,wacca unguwa?
"badawa nake,can zani.
"bara natsarar miki abun hawa ya kai ki ko.
"da kin barni sannu a hankali zan iya karasawa,kune yaran yanzu bakwa jurewa tafita.
wannan kalmarce ta sanya ta karewa tsohuwar kallo babu alamar wahala atare da ita asalima atamfar dake jikinta ta supar holland ce babba takalmin kafarta da gyalen da ta cukyikuyeshi a wuya su kadai kayan kudine abin kallo wanda ba jikin kowaba ta jinjina kai kawai kila rikici ne kawai ta tsufa
"a,a kaka badawa fa ba nan bace,kibari kawai.
Kan kaka ta sake magana tini  ta tsayar da napep.
" badawa zaka kaita dan Allah ka tabbatar da ka ajiye ta a kofar gidansu kaji.
"naji Amman abani dubu daya.
" Haba malam kana ganin dai tsohuwa ce ka rage mata.
" Shikenan naji kawo dari Tara, wallahi dagashi babu ragi.
Ikhlas ta juya ta kalli tsohuwar.
"Kaka kinji abinda yace.
" shiyasa nace aƙafa zani,kuma kinganni nan ko naira biyar ban fito da itaba ki kyaleni kurum.
Ai bata gama rufe baki ba mai adaidaita ya kama gabansa,ita dai batajin zata iya barin tsohuwa agun ga hadari na faman ganga mowa
Haka tasake tsare wani wai tana tunanin za,a dubi tsufanta akaita fir kowa yaki wata dabarace ta fado mata Iphone  dinta ta da karamar wayar ta dauko daga cikin jaka ta nufi Mai siyar da man dake gaf da inda suke tsaye ta riga ta tabbatar da nan ne gun zamansa har gidan su tasani makocin su Kawar Rahama ce dan haka batayi shakkar dosar saba
"Malam ni yar nan unguwar ce dan Allah ga wayata kabani aron dubu biyu zan kawo maka kudin anjima sai kabani wayar tawa.
"Tab lallema yarinyar nan ance da ke ni soko ne kawai dan kin maidani shashasha ki kawo mini wayar sata kice na baki dubu biyu lalle kinci Kai, ki bar gunnan ko na kira yansanda nace dasu ga barauniyar waya nan.
ta koma gefe ta tsaya cikin tunanin mafita

Faisal wanda tauraron shi ke haskawa mutum ne mai ji da kansa ga izza tamkar wani basarake kai daganinsa zaka fahimci irin mutane nan ne "yan takife marasa tsoro kwayar idon sa kadai zaka kalla ka tabbatar bashi da kunya ba kuma shi da tsoro baya shakkar taka kowa kuma bashi da kunyar firta magana a lokacin da ya so duk girmanka zai iya yagaka a ɗabi'unsa kaf babu abin birgewa kamar kyautar sa yana da kyauta na ban mamaki haka kuma shi din yana da mutukar kyau, kyakkyawa ne na gasken gaske sai dai shi  wankan tarwada ne wato chocolate colour
tunda ta fara wannan hada hadan yake kallonta birgeshi takeyi ayadda take actin dinta kyakkyawar ce ita ga kananan shekaru babu abinda yafi Jan hankalinsa da ita irin dimple dinta Wanda ko magana takeyi lobawa yake ga dan karamin zagayayyen bakin ta wanda da gani zayyi dadin kiss take ya shiga ayyana gashinan sun kebe da ita.
Shifa Faisal idan yaga mace ko asuturce take zai kalle ta ne a tsirara, ya kware sosai gun iskanci koda matar aure ce ta kawo kanta indai mai kyauce zai amshi gayyatar ta in kuma budurwa ce muddin tana mu,amala da maza barkatai to zai yaga ta ya kyamaceta shifa tsabar kwarewar sa yana ganin mace mai bin maza zai ramfota,duk da tantirancin sa Amman ya tsani mace mara kamun kai.
dirowa yayi daga kan motar ya nufeta.
" Ko zan iya taimaka miki,?
Yafada yana watso mata wani mayen kallo.
Kallo daya tayi masa tayi saurin kawas da kai sabida yadda taga yana wani ƙare mata kallo.
" atakyace tayi masa bayani.
Ya kunshe wata dariyar mugunta aciki.
"zan baki sama da dubu daya kibata har tasami dan canji amman da sharadi.
Tadago da idanu luuu tana kallonsa
" Zan baki duk abinda kike bukata sabida naga kina son taimako,ki bani lambar wayar ki.
bata iya ha'inci ba ba kuma tayin karya sai dai a yanzu zata iyayin duka biyun domin taimakon tsohuwar nan.
Batasan sa adda ta shiga lissafo masa wasu lambobin karya ba.
Tunda ta fara karanto mishi ya dora idanunshi akan kirjinta ko kiftawa baya yi tsabar kwarewa babu yadda za'ayi ta iya fahimtar yadda ya ke kallon nata jiyakeyi kamar zai ruƙumƙumeta. cikin dashasshiyar muryar ta mai fusgar duk wani mai sauraro tace
" kudin sunyi yewa.
Ta danyi mishi nuni da tsohuwar dake dan nesa dasu.

" ita ce nake son biyawa kudin mota, nasan dubu daya zai isheta inya so sai ka bata dubu biyu tarike canji a hannunta
yana kare mata wani mayen kallo.

"oh no, Ai kyautar manya zaki yi ta yadda zata ji dadi kawai bata dubu biyar sai Allah ya hada mu cikin ladan.
da sauri ta kada kai.
" nagode, amman kabata dubu biyu.

" ke fa, bakya bukatar komi?

" hakan ma na gode.

Ya mika mata dubu biyu ta karɓa ta yi masa godiya hadi da saurin barin gun.
Wata doguwar ajiyar zuciya ya sauke cike da tsananin bukata
zai bar gun ya hangi iphone a aƙsa ƙasa ta lulluɓeta ya ɗan durkusa ya dauka fuskar wayar yaga hoton ta  zai bita ya bata wani tunani ya zo mishi komawa yayi cikin motar sa.
-----------------------------------------
Alhaji Ibrahim na ta Kai komo yakasa samun nutsuwa lokaci lokaci yakan Kai duba ga agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa ammi tafito daga kitchen
"Haba Alhaji ikhlas fa ba yarinkya bace ballantana ta bata tana kuma da kamun kanta balle kace tatafi gantali Ina tunanin wani muhinmin abunne ya tsayar da ita.
"Kinsani kinsan yadda nake da tarin makiya da Y'an bakin ciki zasu iya yin komi akanta zasu iya lalata mata rayuwa zasu iya yi mata asiri zasu-
Cike da takaici ta katseshi.
" haba Alhaji yakamata ka sani koda duk duniya zasu taru akanta don su cutar da ita muddin Allah bai amintaba babu abinda zai sameta.
Yaja tsaki.
Mtss.
"Kinga rufamin baki,bazaki taba gane waba,waima shin kin bata rubutun tsarin jikinta jiya tasha,ko,ko dai yauma kin mance?
Yakafe ta da ido.
"nikam na sha,afa da zaka yadda da shawarata kawai ka mikawa Allah lamuran yarinyar nan,inko ka cika yin shishshigi sai ya barka da iyawar ka.
Tini idanunsa suka juye zuwa jajaye.
"Nace da ke,ke na barwa lamarinta ko Yaya wallahi idan baki fita daga idanuna ba zan saba miki
Sumsum ta bar masa gu cikin faɗin Allah ya kyauta.
Atsorace ta shigo gidan tana tafe kamar wacca kwai yafashewa aciki tuni yayi kanta da bugu da gudu ammi tafito daga daki ta shiga tsakaninsu.
Yana huci.
" Ki matsa yau sai ta gaya mini gidan ubanda ta tsaya,Inba haka ba sai na lahira yafita jin daɗi.
Cikin kuka ta zayya ne musu abinda ya faru
Cikin daga murya.
"Ashe baki ajiye wannan banzan halayyar takiba,idan kikayi wasa da wannan raunannan zuciyar taki za,a dinga cutar dake, ke dai da abin da ya Kai na tausayi da Wanda bai kaiba duka tausayi yake baki.
"Abu matar tsohuwa ce shiyasa na taimaketa----
"dallacan yi min shuru,ita din na tabbatar tana da jikoki da dangi,kina son kice kin fisu damuwa da ita ne,ko kuwa kin fisu tausayinta.
"Kayi hakuri bazan sake ba.
Kofin dake kusa dashi ya dauka ya cillo mata ji kake kum a goshinta ta dafe gun cikin  tsananin azaba.
Yaci gaba da banbamin fada.
"Aisu jikokin nata ko "yayan nata sunsan tsohuwa ce suka bari tafita,sabida sunga zata iya ne,kuma daga yau Ina son ki cire wannan shegen tausayin daga zuciyarki in ba hakaba zamuyi ta samun matsala da ke,ke inma takaice miki muddin kika cigaba da tafi da zuciyarki ahaka bazan yafe mikiba,tashi kiban guri.

Ammi zaune akan tabarma,yayin da ikhlas ke zaune akan kujera ɗan tsuguno tana wanke wanke gaba daya tunanin inda ta yadda wayar ta take kafin ta fito daga daki ta duba jakar ta bataji wayar ta aciki ba.
Ammi ta numfasa." ba,a biyayya ga sabawa umarnin ubangiji ko da kuwa umarnin iyaye ne.
Ikhlas tadan dakatar da wanke,wanken tana kallon Ammi.
" Ina nufin kada ki Soma hawa layin da Abu ke son ɗoraki dan shi tausayi yanki ne na imani,kada ki fasa taimakawa Wanda ke buƙatar taimako muddin kina da yadda zakiyi,
Wasu hawaye suka silalo kan kuncin ta sani Abu ba zai taba daga mata kafaba tabbas akwa kura.
Ammi ta kafe ta da ido tana nazarinta  ta sani akwa abinda ke damun ta.
"Ikhlas ai anwuce gurin ya kamata a ce kin kwantar da hankalinki indai ba kuma akwai wata matsalar ba.
Kokarin ɓoye damuwarta tayi.
"Ammi naji tsoro naga ran Abu ya baci sosai,
Ƙokarin kwantar mata da hankali take.
"Kada mu biye mashi shi wani irin baudadden mutum ne.


  A dakin ta gaba daya tagama zazzage ko ina tare da juye dukkan kayan dake cikin jakar har yanzu gani take zata iya ganin wayar  ko ina na dakinta ta hautsina babu alamar wayar ta.

Zama tayi dirshan a kasa kuka take yi sosai komi nata na cikin wayar yanzu mai zata cewa Abu
Rahama ce ta shigo dakin baki bude take duban aminiyar tata wadda ta koma tamkar wata taɓaɓɓiya.
"ke ikhalas lafiya kuwa, mai kike nema haka?
Cikin muryar tashin hankali.
"wayata na duba ko'ina bangani ba.
Azabure tace "kina nufin iphone? Ikhlass ta jinjina kai.
' tab babbar magana, ke kin tabbatar da kin shigo da ita cikin gidannan?
Shiru ikhalas tayi tana tunani.
" ina tunanin agun da na saka wannan tsohuwa a mota na yadda wayar.

" wacce tsohuwa kuma.

Labari tabawa Rahama yadda komi ya faru.

"Ai kinji garin neman gira kin rasa ido, tasowa zaki yi mubi hanya.

" to amman mai zancewa Ammi?

" zan roketa cewa zanyi zaki rakani gidan kitso.
-----------------------------------------
Tamgamemen gida ne wanda kana gani ka san ma mallakin gidan yaci ya tada kai gidan na dauke da wasu mahaukatan get guda uku kafin ma ka nutsa cikin gidan gaba daya intaluck ne tun daga get din farko har kawo na karshe inda zai sadaka da cikin gidan akwai bangaren ma aikatan gidan sai bangaren karen sa wanda ya ke kira da champion yana ji da karen mutuka  kamar yadda shima karen ke ji dashi,  sai can gaba shine shashin masu gida
Zakuyi mamaki idan nace duk girman gidannan tsohuwa ce aciki sai ɗan ji kanta da kuma masuyi musu hidima girki shara, wanki da guga sai masu bawa furannin gidan ruwa.
Setting room ne Wanda yagama gajiya da kayan alatu ga wani sassanyar kamshi dake faman tashi hoton  faisal ne kato window size tare da wani handsome kyakkyawa fari kwal kamar balarabe sai wani hoton wanda handsome dinne kadai ajiki yana faman murmushi sanye da kayan mu irin ta Hausawa an Rubuta Ahmad a jikin hoton da manyan baki sai wani hoton nashi wanda yake sanye da wando 3cotter da riga mai yankakken hannu yana amsa waya da alama baimasan an dauka
End Ads