An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
[18/08, 4:20 pm] Bilkisu H MUHD: _*GABA DA SO*_
_BY_
*BILKISU H MUHD*
Phone 08031307884
Page 1
*MARUBUCIYAR*
ILLAR SABO
RASHIN RABO
YA YI SAKE
ZAFIN HAWAYE NA
BAKIN KAZAFI
WAYA FI SONTA
GORO DA SANKARA
JINI BIYU
DACEWA
KAUNA CE
BAYAN KUSKURE
MATSALAR KAUNA
TARAIRAYA
DAKE NA DACE
AKWAI BANBANCI
BAKIN KAZAFI
MULKIN MALLAKA
IZZATU
BAYAN KUSKURE
KA AURE NI
KYAUTAR ZUCIYA
*sannan yanzu ta zauna ta kure basirarta gun rubuta muku littafin da bata taba fitar dashi a takadda ba littafine Wanda a online tafara rubutashi , littafin yazo da sabon salo tare da sarkakiya hadi da soyayya mai taba zuciya kowa yaji sunan littafin GABA DA SO zai sojin menene agaba da so daman da akwai abinda yake GABA DA SO,to karanta wannan littafin dan sanin menene ke GABA DA SO.*
makaranta kundai san yadda alkalaminta🖊️yake. Wanda ya santa ya santa Wanda bai santaba yakamata ya gwada karanta books dinta lalle bazata baku kunya ba.
Sannan zaku samu dukkanin littattafai na ta hanyar 👇🏻👇🏻👇🏻
Wattpad:👇🏻
@bilkishmuhd
Arewa Book:👇🏻
bilkisuhmuhd
WHATSAPP GROUP NA BILKISU H. MUHD👇🏻👇🏻
https://chat.whatsapp.com/Fp8jRB4MGGqB1I6J9gc0NE?mode=ac_t
WHATSAPP CHANNEL NA BILKISU H. MUHD👇🏻
https://whatsapp.com/channel/0029VarKaWtBfxnxJ2STpI1o
FACEBOOK GROUP NA BILKISU H. MUHD 👇🏻👇🏻
https://www.facebook.com/groups/1845344956261189/?ref=share&mibextid=NSMWBT
BUSINESS GROUP NA BILKISU H. MUHD 👇🏻👇🏻
https://chat.whatsapp.com/IOFJMOHiTTMJ9cNLRroppc?mode=ac_t
------------------💥
Ɗakine madaidaici babu wasu tarkace a ciki,daga ɗan ƙaramin gado medium size sai set ɗin akwatuna masu ɗan karan kyau sai ɗaukar ido suke da alamu basu ji jikiba, daga can gefe guda wani tebur ne mai ɗan girma da tulun wasu manya-manyan littattafai akai, daga jikin bangon ɗakin katon hoton tane wanda suka ɗauka da gwamna da mahaifinta ALHAJI IBRAHIM sun sanyata a tsakiya, kusa da hoton agogon bangone wanda akayi mishi ado da ruwan gwal.
Kwance take akan ɗan madedecin gadonta tayi ruf da ciki da littafi agabanta tana karantawa, yanayin yanda tayi kwanciyar hakan ne yabawa bajajjen Hips dinta damar buɗewa wanda a shekarun ta goma sha takwas tsaf zaka rantse ƙugun babbar mace ne, sanye take da riga mara nauyi iya gwiwa mai dauke da hannun shimi, rigar tabada kyakykyawan haɗin kai wajan bayyana farar fatarta, iPhone dinta ta hanga yana fidda haske alamun kira yashigo, dam! taji gabanta ya buga, cikin sauri ta mike ta nufi ƙofa ta kulle tare da murɗa key ta koma ta rufe window ta saki labule ta koma gado ta ɗauki wayar ta janyo lallausar bargonta ta rufa dashi sannan ta ɗauki kiran tareda sanya wayar a kunne.
''Assalamu Alaikum" taji ya faɗa cikin tattausar muryar da ako yaushe bata gajiya da jinshi.
"Ameen" ta amsa cikin muryar raɗa a takaice, duk da cikin yanayin raɗa tayi maganar hakan bai hana zazzaqar muryarta bayyanaba, cikin nutsuwa taci gaba da fadin "maiyasa ka kirani yanzu?, kamance nace da kai ABU baya fita da wannan lokacin,? dan Allah kada ka sake, inajin tsoro, inajin tsoro idan ya gane kasheni zaiyi..... "
"Oh God, tom shikenan ayi mini afuwa mancewa nayi". shuru sukayi zuwa wani lokaci sannan ya numfasa yace"Baby kina kan layi?"
shiru tayi, batare da tace komai ba.
" ko kinajin tsoron magana ne?"
Duk da tana cikin blanket saida tadan leƙo da kanta waje tasake kallon dakin zuciyar ta cikeda tsoron mahaifin nata, duk da cewa ta kulle koi'na, sannan tamaida kanta cikin blanket din ta sassauta murya tace"eh haka ne, dan Allah kayi hakuri muyi magana anjima, ka kirani adaidai lokacin da kake kirana"
Motsin tahowa taji da sauri ta katse wayar ta koma da sauri ta murɗa key ta buɗe ƙofar sabida gudun zargi ta komo da gudu ta kwanta tanajin lokacin da Abu ya turo ƙofar ya shigo ya dade tsaye akanta zuciyar ta sai bugawa takeyi da karfi tamkar zata faso ƙirjinta tanajin tsoro kada ZARUK ya sake kira, fuskarta ta hada wani uban gumi wanda yasa lallausar sumar kanta kwanciya akan goshinta, maimakon ya fita sai ya koma ya zauna a gefen gadon, mufici ya dauka yanayi mata firfita.
"Oh Allah" tace azuciyar ta, dole ta dan motsa a hankali ta bude manyan idanuwanta sukayi ido biyu dashi, wani tausayinshi ya kamata, bata taɓa
ganin ubanda keson ɗansa kamar Abu ba, anya kuwa tayi wa Abu adalci da take aikata abinda a kullum yake gargadinta da aikatashi?.
ya katse mata tunani yayi tareda fadin" lu'u lu'u na harkinyi bacci haka da wuri?" murmushi tasaki wanda yayi nasarar loɓawar kumatunta duka biyun, mikewa tayi ta zauna "Abu kainane naji yanayi mini ciwo amman yanzu natashi bara na ɗanyi karatu"
yayi murmushi cike da tsananin soyayya irinta ɗa da uba, cikin kulawa yace" tom shikenan bara na kawo miki shayin kisha ko"
"Abu kabarshi kawai cikina ya cika"
"A'a kin mance shiyake taimaka miki gun karatu?" bai jira ta sake magana ba yayi waje.
Cikin zafin nama ta ɗauki wayar ta switching dinshi baki ɗaya.
-------------------💥
Rantsatstsiyar motar daya gani tsaye a ƙofar gidan sa ƙirar Range rover ne yasa sai da gaban sa yayi wata irin bugawa, to amman kuma mai ya kawo su gunshi?.
sanin cewar baici bashin kowa bane ya bashi ƙwarin gwiwar ƙarasawa gareshi. Kafin ma ya ƙarasa bakin motar wani haɗaɗɗen Alhajin birni ya ɓallo murfin motar yafuto, nan take gaba ɗaya wajan ya gwaure da wani irin ƙamshi kai da ganin mutumin zaka tabbatar da acikin masu kuɗin ma shiɗin yaci ya tada kai.
Cikin takun isa da ƙasaita irinna masu dashi ya nufo Alhaji Ibrahim fuska a sake tare da miƙa masa hannu, sai da Alhaji Ibrahim ya danyi jim kafin ya miƙa nasa hannun.
Cikin fara'ah baƙon yace" ya kamata mushiga daga cikin mota ko kuma mu ɗan keɓe dan naga kamar muna a kan hanya ne"
"Haba malam ya daga ganinka zakace mu shiga motarka,? ai kagaya mini abinda ke tafe da kai tukunnan, nufar kama danayi ba ƙaramin shahada nayiba domin zai iya yuwuwa zuwa kayi dan ka cutar damu nida ɗiyata".
Murmushi Alhajin yayi kawai sannan yace" Kada ka damu bazan cutar da kaiba alkhairi ne ke tafe dani, yanzu tunda baka amince da shiga motata ba ka saukeni a inda yayi maka"
"Yauwa yanzu naji magana, jirani na fito" ya faɗi hakan tareda shiga gida, bakon na binshi da kallo shi dariya ma yake bashi yaga alamar kwata-kwata bashi da yadda, amman yasan zai saki jiki in har yaji abinda ke tafe dashi.
Hango shi yayi tafe da kujeru guda biyu irin ta roba.
Bayan sun zauna baƙon ya kalli Alhaji Ibrahim yace" Idan bazaka mance ba Alhaji haruna wanda akeyiwa laƙabi da mass gyaɗi-gyaɗi hardashi a halartar taron da aka yi na daliban da suka wakilci ƙasa da ƙasa a can Abuja inda ƴarka IKHLAS ta lashe gasar har kusan zan'iya cewa a wannan karon shi yabaku kujerun makka kafin hon zubairu balannaji ya fara baku"
Abu Ya jinjina kansa alamun gamsuwa, saide acan ƙasan zuciyar sa gaba daya ya gama ƙosawa, yana son jin mai ke tafe da shi. hakane yasa shi katse shi cikin rashin iya maganar sa kamar yadda kowa ya sani babu ruwan sa da kai waye yakan furta duk abinda ya zo bakin shi.
" da Allah malam ka gaya mini abinda ke tafe da kai ni na gaji kana wahalar dani ina da abin yi" furucinsa yayiwa baƙon zafi, amman babu yadda ya iya, shiyasa ko kaɗan bayason mu'amala da talaka.
" ok ai yanzu zantafi, kamar yadda nayi maka bayani shi mass yaya nane kuma....."
"Ashsha ai kaji irin ta, ni bana son wannan kewaye-kewayen, ba sai ka faɗi dangantaka ba kawai gaya mini mai ya kawo ka?"
Tofa Alhaji nazifi ya fara harzuƙa, sai dai ya shiga lallashin zuciyar sa gudun samun matsala.
" to na fahimta, ɗan sa ne yaga Ikhlas yana so abinda ya kawo ni kenan"
wata iriyar zabura Alhaji Ibrahim yayi tamkar wanda aka aikowa da sakon mutuwa.
" yarinya ta ko secondiri bata gamaba kuma koda ta gama sai tayi karatu mai zurfin-zurfi sai ta kai ƙololuwa kamar inda na tsara"
"Ikon Allah"
Alhaji nazifi yafurta a zuciyar sa, nan kuma Allah ya kawomu, tabbas bahaushe yayi gaskiya da yace ɗan kuka mai jawa uwarsa jifa, jibifa ko sacondry bai iya faɗi ba amma shi yake cin irin wannan buri.
" ranka ya daɗe na fahimce ka wato ƴarka karatu zata yi sosai ko?
"Yis fadi ka ƙara"
Alhaji nazifi ya ƙara danne dariyar dake son kwace masa, Allah sarki yana son yin turanci sai dai bakin ya kasa.
" muma gidan mu gidan ƴan bokone kamar yadda kake ɗin nan ɗan boko, da ikon Allah zamu cika maka dukkan burinka a kanta, kawai ka amince da mu.
" kamar yaya?" cewar Alhaji Ibrahim.
" Ina nufin zatayi karatu a gidan mu, inma likita ta karanta zamu gina mata asibiti nata na kanta muna da tarin dukiyar da bazai taba karewa ba zamu....."
"Kaga Malam dakata Dan Allah!!, kada ka batawa kanka lokaci, yarinyata zata samu duk abinda take sone akan kanta bata dalilin mijin taba, ninasan wahalar da nasha Kuɗi ba asiri bane! Kuɗi ruwa ne — yau yana nan, gobe ya zube. Ina son 'yata ta dogara da kai, ba ta zauna tana jiran sadakar aure daga dansa ba. Na raini Ikhalas da gumi, da addu'a, da halacci. Ba zan miƙa ta hannun kuɗi ba!dan haka bana son taci arzikin mijin ta ballantana yayi mata gori, idan har son ta yake da gaske, yana iya jiran wannan lokacin"
Yana faɗin haka ya mike tsaye alamar ya gama magana, hakane yasa shi ma Alhaji nazifi ya mike ya soma tattaki zai nufi mota.
Alhaji Ibrahim yabi bayan Alhaji Nazifi da kallo sannan cikin daga murya yace"wallahi ko da ɗan Ƙaruna ne zai zo sai na cika burina, kowa daga yaga ɗiyata ta sami daukaka sai yace zai lallaba ya raɓeta duk sai nayi maganinku, dan kuna ganinku da kuɗi, to ina sa rai duka nan gaba sai kundawo ƙarƙashin ta tun yanzuma ga ishara kun fara gani"
Alhaji Nazifi ya juyo ya kalle shi tareda faɗin" shikenan babu damuwa hakan yayi kyau"
Ya shige motar sa ya figa da ƙarfi.
Da gudu ta miƙe jiki na rawa sabida yadda ya buɗe dukkan muryarsa cikin ƙwala mata kira sai da ta kume da ƙyaure.
Ta yo waje da sauri jikin ta har rawa yake, a setting room ta ganshi tsaye yana faman kai komo zaman ma ta ga gareshi, tana kokarin tsugunawa cikin masifa ya juyo ya kalleta.
" kigaya mini wanene zubairu ballannaji? wani shaiɗanin ɗan nasa kika turo ya zo neman auren ki!!?"
ya kalli ƙofar daki tareda daga murya yace"ke! kina ina?"
Ammi ta fito daga ɗaki a sukwane, babbar mace mai cikar kamala da kuma haiba a fuska.
kallonta yayi yace"maza ɗauko mini wayar ta a ɗakin nata"
ya faɗi hakan yana mata nuni da ikhalas wadda tayi tsamo-tsamo kamar anjiƙa ɓera.
Jinjina kai kawai Ammi tayi ta nufi hanyar ɗakin.
kallonsa ya maido kan Ikhalas yace"zaki buɗe baki kifaɗamin gaskiya ko sai nayi miki illah?"
A nitse ta soma magana.
" Allah shine shaidata Abu ban taɓa jin irin wannan sunan ba"
Adaidai lokacin Ammi tadawo, ta rissina tareda mika mishi wayar.
Wayar ya kunna ya shiga bincike lungu da sako na ciki.
Gaban Ikhalas ne ya fara faɗuwa, tarasa gane a ina take, jinta take ita ba'a sama ba, kuma ba'a ƙasa ba, tsoron ta ɗaya kada a samu akasi ZARUK ya kirata adede wannan lokacin, ƙirjinta kamar zai fashe saboda tsoro.
"karɓi wayar"
ta ji yana cewa.
Tayi wani firgigit da sauri tasa hannu ta karɓa.
yana huci kamar wanda yayi dambe ya kalleta.
"kada ki kuskura na kamaki kina mu'amala da wani namiji, kibari idan lokaci yayi da kaina zanyi miki zaɓin mutumin da ya dace dake, muddin kika tsaya kika dage zamu sami irin mijin da yayi mana, yanzu karatu zakiyi, yanzu kika soma sa ƙafa ba kiyi komai bama a karatu, nasarorin da kike ta samu ya tabbatar mana da cewar keta dabance, ke zaɓaɓɓiya ce cikin al'umma, Ubangiji ya nuna mana hakan, dan haka dole ne muyi amfani da damarmu, ada anayi mini gorin ɗa, ban haihuba, haka kuma da Allah ya tashi bani haihuwa sai ya soma da bani mace a lokacin dangina da abokai suka dinga zinɗena, lokaci ɗaya sai ubangiji yayi musu ishara da baiwarki, Ikhlass sai na nunawa mutane cewar mace zata yi fiye da abinda na miji zaiyi, idan mace na iya zama shugabar ƙasa to a ƙasarnan a kanki za'a fara"
Ya dubeta tare da dafa kafaɗarta, ya cigaba da magana cikin cizon leɓe kamar wani mai cin alwashi.
" wahalar da nasha sai na fanshe, nima sai anzo ana kwatance dani in taka duk wanda naga dama, bazan yi alfahari dan kin auri wani shahararre ba zanyi alfahari ne kawai idan ke kika zama wata"
Ammi tana tsaye tana kallonsa, mamaki ya gama kashe ta a tsaye, kallonsa take kamar wani taɓaɓɓe.
Ajiyar zuciya ta sauke tare da faɗin "Allah ya tabbatar mana da alkhairi"
Ƙuro mata ido yayi yana son fahimtar wani abu.
Cikin halin ko'in kula yace" gashi nan yana kan tabbatar wa tunda mun fara cin arzikin ta tunkan taje ko ina, ji nakeyi da yawon haya muke yi bani da komai ba wani wanda ke ganinmu da mutunci, yanzu fa munsami jari mun sauke farari, saiki duba ki gani nan gaba ya zamu dawo"
Ya dawo da kallonsa ga Ikhlas.
"Maza jeki, Allah ya haska rayuwar ki"
Tunda ta komo daki komai ya kunce mata, kanta taji ya sara tsabar ciwo, hakan yasa cikin sauri ta cire ribon ɗin dake kanta tasaki lallausan dogon gashin ta ya bazu a kan doron bayan ta ko za taji sauƙin ciwon kan, hannun ta tasa akan goshin ta tare da lumshe ido, idan abban ta yana wasu maganganun takan ga tamkar yana da matsala a ƙwaƙwalwarsa, a kullum yana yin wasu abubuwa tamkar bai yadda da Allah ba, ya mance cewar a kwai mutuwa zai iya dauke ta ko Kuma ya dauke shi gashi gaba ɗaya, yaƙi kyautata ma'amala tsakanin shi da dangin shi, bashi da burin da ya wuce ya dasa tsanan su a zuciyar ta, shi kam mai suka yi masa haka har yake cin alwashi a kansu? ko kaɗan baya son su raɓeta, duk kuwa da cewar duk lokacin da ta shiga cikin su kamar zasu cinye ta, ƙauna suke nuna mata muraran...
Shigowar Ammi ya katse mata tunani, zama tayi a bakin gado tana fuskantar ta.
"Yar gata, matso ki zauna kusa da ni. Kafin duniya ta koya miki wacece ke, ki bari na fada miki.
Na haife ki da bege, na raina ki da addu’a. Allah ya azurtaki da baiwa da basira, kuma na gode masa. Amma ki sani, baiwa ba hujja bace ta raina wasu. Girma na gaskiya ba yana cikin jin kai bane, yana cikin saukin kai.
Na lura da yadda mahaifinki ke kokarin nuna miki cewa ke daban ce – wato ‘gifted’. Hakika, Allah ya baki abin da ya bambanta ki, amma kada ki bari hakan ya zamar miki abin daukaka har ki fara ganin kanki fiye da sauran mutane.
Wanda ke sonki da gaskiya zai koya miki kauna, ba kyama ba.
Zai kara miki tausayi, ba tsana ba. Zai kara miki son zumunci, ba yanke shi ba. Amma idan yana koya miki cewa dangi basa da amfani, ko cewa ke kin fi kowa – to yana cire miki darajar zuciyar da zata tsira da mutunci.
Ki saurare ni da zuciyarki, ba kunnuwanki kadai ba. Mutum mai kirki ba ya nuna hasken shi da gurbata wasu ba. Idan haskenki na gaskiya ne, zai haskaka kowa a kusa da ke, ba ya kona su.