"Eh kinji sarai abinda nace ina son ganawa da mijin na"
Sumi sumi kowa zuciya ba dad'i muka tashi zamu fita mun kai k'ofa mukaji tana cewa "dani kuke zancan, sai kun yabawa aya zak'in ta dan na lahira sai yafi ku jin dad'i, sai kunyi nadamar zuwan ku duniya"
Munji tsoro kowa ya kama gaban shi domin ko Fouraiha ta nuna mamu ita d'in hatsabibiya ce, rai babu dad'i kowa ya shiga gida, kuma zaman jiran tsamanin abinda zata aikatawa, mun sakankance amman duk yanda muke tunanin ta ta wuce haka, dan yanzu ne za'a fara wasan.
(Gaskiya kunga ta kanku, dan yanzu ne Fouraiha zata d'and'anna maku azaba sai kunkai kuna gudu da k'ahuwan ku, na tausaya maku)
*Tofah fans yanzu ne za'a fara wasan ku ciga da bibiya ta domin jin ya zata k'aya*
*Domin gyara ko shawara ku tintub'eni a wannan lambar +22792494512 na gode*ππ
*PRINCESSE CE πΈπ»βπΌπ³πͺ*
24/07/2020 Γ 12:54 - πΈπ»PrincesseπΈπ»: ππππππππππ
*MAK'OTAN ALJANA*
ππππππππππ
_TSARAWA DA RUBUTAWA_
*RAHIMA FALOLA*
_PRINCESSE_
*Marubuciyar*
*SARAKUWA TA*
*GODIYAR SU CE*
_and now_
*MAK'OTAN ALJANA*
Soja "gaskiyar magana kennan, kuma ta nuna mana mungun halin ta"
"To yanzu dai kowa yayi hankali a lura sosai"
Bari mu koma wajan masoya.
Fouraiha tace ma David "ka ajemin kud'in haya zanzo na k'arb'a"
"To sai kinzo ai naki ne"
"Kuma ya kamata a k'ara kud'in haya"
"K'ari kuma? Gaskiya tinda na gina wannan gidan suke cikin ba dad'i idan anyi k'ari"
"Abinda nace shi za'ayi"
"To gimbiya "
"Idan sukaji basu iya zama su kama gaban su a sa wasu sabi"
Fouraiha ta maida David karen ta sai yanda tayi dashi.
Fouraiha ce tsaye tsak'ar gidan sanye da doguwar riga ja, tana hak'a rame tana wasu irin sabatu cikin naji tana cewa duk 'yan gida da abinda ke cikin gidan ya zama nawa malaki na sai yanda nayi da su tana dama wata gumba a cikin wata katuwar tukunya sannan naga ta fito da kwai guda shida ta zo k'ofar gida na ta aza wani sannan ta shata layi da wani jan abu tana magana"Laila daga yau sai yanda nayi daku a cikin gidan nan bazaku zama wani abu ba har abada da keda iyalin ki" sannan ta fasa wani kwai sai dukan abubuwan suka b'ace, sannan ta dawo wajen tukunyar nan ta jefa kwai d'aya saida wani jan hayaki ya fito, sannan ta koma k'ofar d'akin NaΓ―ma yanda tayi a nawa haka tayi ta k'ara da cewa yaran ta sai sun zama manyan b'arayi k'arshe su mutu ga hannu police ('yan sanda), sannan ta koma k'ofar d'akin soja da kai da k'anwar ka rayuwar baza tayi kyau ba kai sai ka zama mai biyan matan banza kud'in ka duk acan zasu k'are, ita kuma Lya'atou karuwan ci et zata sa gaba k'arshe kuyi hatsarin mota ku mutu, ta dawo wajen tukunyar nan koda ta zuba wani abu sai ta b'ace batt, lokacin da take k'okarin juyawa can ta hangi kurwar d'aya daga cikin d'iyan NaΓ―ma yana kalon ta, koda ta juyo sai ya gudu zuwa gidan su daman NaΓ―ma tana k'okarin ta tinda abin nan ya faru take rufe gida ko k'aramar huda bata Bari bale wani abu ya samu damar shiga, can na hangi Fouraiha ta rikid'e ta koma kusu π "ni zan yarda ka gan sirin na kuma n'a kyaleka ka kwana lafiya?" Tana gama rikid'eAwa tabi ta sama cikin lunguna ta shiga gidan NaΓ―ma.
Tana shiga d'akin yaran NaΓ―ma tayi suna barci harda wanda ya gama gulmar lek'enta ta fara cin faratan su ('yan yatsun su) suka fara ihu da neman agaji cikan kwana NaΓ―ma taji kukan d'iyan ta da gudu ta shigo d'akin koda ta kuna wutar d'akin can gefe ta hangi wata katuwar kusanya tana ci fartayen da ta diba n'a d'iyan ta ga hakoran ta zaro zaro sunfi na mutun, da gudu ta tafi kitchen d'auko tab'arya domin bugawa wannan kunsanya amman lokacin da zata buga mata kawai sai ta rikid'e ta koma mutun katuwa da jar riga har k'asa, ai ko yaran suna ganin haka sai ihuuu can sai ita Fouraiha ta bude bakin ta Wani hayaki ya fito duk sai suka zuba sai barci, har ita NaΓ―ma wannan d'an barci wai tayi mafarkin wai wata tsohuwa ta d'aure ta sannan tazo ta mata kashi a fuska bayan haka wacan matar mai doguwar riga taje neman wuka domin a yanka ita NaΓ―ma ai da gudu Allah ya bata wani karfi ta kubce tana ta gudu sai ga wannan matar da tsohuwa suna biyan ta a bayan ta gaji iyakar gajiya sai ta fad'in tana kuka tana cewa "ku kashe ni bazan iya tsira ba shikenan" sai wacan matar mai wuka a tazo zata caka mata sai wufff ta farka tana zufa sai gasu kwance itada yaran sanan tace "Kai mafarki akwai firgitar wa wallahi"
Ta cicib'i yaran ta suka koma d'akin ta duk ta rungume kayan ta sai ta fad'a tunani tana kalon sili (plafon) sai ga wani jini yana rubutu da kanshi *BA ZAKI TSIRA BA SAI NA KASHE KI, MUTUWA ZAKIYI....* Ai NaΓ―ma da ta ari na kare yanran ma baya ta barsu suna ihu da neman agaji sai gasu a kofar gida na........
*(Wai na gaji wallahi kaina ciwo,domin jin ya da zata kaya ku ci gaba da bina)*
_sai naga comment da yakai 50 ko hiya da haka zan cigaba da typing ko n'a mayar dashi na kud'i tinda baku son comment_
*Shawara a tintub'eni a wannan lambar +22792494512 n'a godeπππ*
Sai ga NaΓ―ma a k'ofar gida na ta bubugamin k'ofa da k'arfi, "Laila dan Allah ki bud'e k'ofar nan wayo Allah mun shiga uku" cikin barci naji ihu NaΓ―ma na tashi zaune tareda mai gida na mu bud'e k'ofar sai gata tsaye duk a firgice a tsorace tana kuka ga majina a hanci, nake tambayar ta ko lafiya yaran kuma Mike faruwa ne wai???
"Kashe mu zata yi yara na ta ilatamin su" ta fashe da matsananci kuka taban tausayi wallahi.
Muka d'unguma da miji na zuwa gidan ta domin dubo mi ya samu yaran nata, abinda na gani yafi k'arfin tinani na, yaran kwance sun kasa tashi kafafuwan su duk jini babu farce ko d'aya wani kuma harda dindinge abin babu kyai gani sai kuka nake tunanin nayi idan nice aka yiwa yara na haka ko yazan yi? Gaskiya wannan matar ta cika maras imani, mu d'auke su mun kaisu gidan mu da taimakon oga na muka musu bandeji kafin safe mu kaisu asibiti, wannan daren ban runtsa ba ina zaune ina jinya su kar wani abu ya same su hata yara na ma, wajajen biyar da asuba na shiga douche (batroom) don inyi wanka da alwala ina wanke fuska ta na daga kaina don kalon madubi ai abinda ya ban tsoro saida nayi fitsari a wando (maganin masu kalon madubi cikin dare kennanπ) wani mutun tsaye ya rufe fuskar shi da wata jar hula ga wuka a hanun shi ya saita wuya, ai da gudu na baro batroom na fito ina haki, "miye kuma?" oga ke tambaya ta wani mutum na gani a kewaye nake sanar da shi, "babu kowa a gidan nan fah kinsani sai mak'ociyar mu da yaran ta, "wallahi ba wasa nake ba",ina karkarwa ina kuka duk na firgice "to muje mu gani" muka d'unguma zuwa makewaya muna shiga kuma ba kowa muka duba bayan k'ofa babu, yace "kin gaji ne wallahi muje ki kwanta zan kula da ke matata" mun juya don fita daga batroom kennan muka ji madubi makewaya ya fashe, kafin mu tantance abinda ke faruwa sai mukaji iska mai karfi ta bud'e tagar batroom d'in, muna cikin wannan hali kuma mugaji k'ofar falon tana "crac crac " kamar anason bud'eta da k'arfin tsiya muka ruho muna zuwa ta bud'e wannan mutumin da nagani a madubi tsaye da wuka a hanun shi ba shiri muka bud'e baki sai ihuuuuuuuuu har mai gida na sai mutum ya b'ace b'at.... Gidan nan muna ganin azaba gaskiyar Fouraiha da tace na lahira sai yafi mu jin dad'i.
Oga na kamar wani zarare, yana sambatu. Allah dai ya kyauta.
Mai gida na yayi fushi matuka don cewa yayi idan yak'i take so a Shiga ro bismillah wannan cin zalin yayi yawa, "Allah ya kaimu safe lafiya sai na nuna mata ..."yayi kyaici .
A b'angare na nayi nayi in nuna mashi illar abinda yake son aikatawa amman yaki saurare na dan ina guje mashi nadama marar anfani, fad'an da yafi k'arfin ka maida shi wasa.
Nayi tagumi ina tunani "Fouraiha, Fouraiha mi muka aikata maki mai muni haka ?mi mukayi da zaki cutar da mu?miyasa ????
Domin jin amso shin wannan tambayoyin kuci gaba da bibiya ta.
Na kusa mayar dashi na kud'i tinda abun haka ne.π
(Wasu sun fara k'orafin akan wai mi yasa basa adou'a to ai sai idan adini ya zauna wa mutum zaman bariki fah,hummm baku iyacin albasa sautu ba,bamu fara komai ba cikin labari yanzu ne zamu fara shi tinda mijin Laila ya fusata)
(An b'atamin rai shiyasa kuka jini shuru sai na huce yanzu ma kad'an nayi sai monday insha Allah,kuma wasu na k'orafin bana maida comment to wallahi sai idan ban lura da shi ba, masu bina prvt sune shaida ina amsa masu idan sukace suna son book daga farko zan tura idan akwai wanda yamin magana ban gani ba to yayi hankuri jiki da jini, aiko ne yamin yawa ga office ga gida ga typing har biyu yazan yi a ringa uziri)
Bayan wannan abun da ya faru miji na yayi fushi mai tsanani bar yana cewa "wannan k'aramar yarinya ta adabe mu haka ta zama mana anoba, to ba zata sab'u ba wai bindiga a ruwa, gwara ayita ta k'are kowa ya huta"
Laila tace "Allah ya huci zuciyar ka mai gida, amma nidai a tunanin na abi abun a sannu"
Bayan safiya tayi nake tambayar NaΓ―ma "wai mi ya faru daren jiya ne ?"
Kuka take ba na wasa ba dan gaskiya na lalashe nace ta sanar dani abinda ya faru.
Tana gayamin tana kuka, bayan ta gama d'anta shima yake gaya mana abinda ya gani kuma yaji.
Miji na yayi mamaki abinda yaron ya fad'a saΓ― yace "abin fa muna tunanin k'arami ne ashe ya girmi tunanin mu"
Nace "mai gida kayi shuru bana son kana d'aukar abin da zafi haka mu fito mata ta bayan fage kawai, tinda ta zama wata kamar bok'anya ko matsafiya to sai a nemo irin su a had'a ta dasu suyi mana maganin ta"
Miji na "bari naje akwai wani mai duba da na sani nazo dashi muga abinda zaiyi"
NaΓ―ma "kuje ku kawo duk wanda kuke so mman nidai bazan k'ara kwana a gidan nan ba tafiya ta kawai zanyi na huta da anoba"
Laila "tafiya zaki yi haka, bayan kudin haya d'Γ kika biya na watan nin? Kuma bai kamata ki sare haka ba wannan yakin ya kamata muyi shi tare"
NaΓ―mai "bana wasa da rayuwar yara na, da tawa rayuwar kawai a sabar tani"
Laila tace "naji kedai ki jira mai gida ya zo dan Allah"
"Kinsan fa ni harakar masu duba kaje adubo maka bala'i,bani cikin shi"
"Kin cika taurin kai wallahi"
"Naji kuje ou dawo ina jira"
Mai gida yaje tahowa da mai duba, ita kuma taje kai yara asibiti, ni kuma na shiga gyairan gida.
Mai gida na ya isko layi koda aka zo kanshi yana shiga mai kai ga isa wajen malamin duba ba yaji yana cewa "kai kuma lafiyar ka, na ganka matace amma kuma ya akayi kake tafiya (ma'ana kana raye)?"
"Ni kuma matace?ban gane mi kake nufi ba?"
"Eh na ganka ka mutu to miya fito da kai alhalin kana gawa?"
"Nifa ba matace bane ya kai malam"
"To muje ka kaini wajen kwancin ka na gani"
"To muje"
"Jira na shirya, dan bansan abinda zan taras ba"
Malam ya shiga ya shirya ya fito, harda wata jarka ta ruwa, sun kawo k'ofar gida, suka tsaya malam yace "anan kake kwana?"
"Yace anan muke muna da yawa" yace "to ai nan mak'abar ta ne kuke kwance ciki, kuma duk an tsunbance shi, dole sai an kori wanan abun da aka kewaye ku dashi"
"Mun shiga uku Haka ta mayar damu kennan?"
Malamin duba "kazo min da duk mutanen da ke zaune a gidan nan yanzu" mai gidan na yace muzo ga malamin nan yazo, duk mun fito muna tsaye gaban shi, yana rike da wata k'araurawa szi fitar da hayaki take, yace mu tsugun na gaban shi babu gardama muka tsugunne, "yanzu zan kare ki daga mungu abun da aka maku" ya fara wasu sabatu koda ya gama yace "yanzu babu abinda zai tinkare ku ya cutar da ku, duk na kore shi" ya fito da wani farin gari da ruwan a jarka duk ya had'e su guri daya, ya Shiga cikin gidan duk wani lungu da sak'o na gidan saida ya zuba, sai kuma wajen gidan, d'aya gama yace "yanzu babu abinda zai same ku ku amshi wannan ruwa idan zaku wanka ku zuba k'ad'an cikin ruwan wanka, sannan cikin d'akunan ku ma ku ku zuzuba a ko wane lungu kafin ku kwanta, duk abinda ke cutar da ku bazai samu damar k'ara cutar daku ba,bale ya tunkare ku"
(Shin mun ware da wannan anoba ta Fouraiha koko yanzu muka fara wasan?)
Wajajen 23h (sha d'ayan dare) duk gidan sit kaje ji dan babu mai son yayi wani motsi, masu cika dare an dena anji tsoro, Fouraiha na hango tana sauya halita zata fara sana'ar tata n'a bamu tsoro, mu duka harda yara na d'aki na muka koma duk mun kudun dune, can sai muka ji wata irin muyar tana kuka tana neman agaji ataima keta, can kuma sai shuru, mai gida yace "bari na lek'a na gani wake ihu?"
"Wallahi babu inda zaka"
"Ki bari na dibo wake kuka"
"Babu mai motsawa daga nan Allah"
Can kuma mukaji shiru kamar anyi ruwa an d'auke. Sanun sanun tsoro ya fara tasiri a zuciyoyin mu ai sai muka ji iska n'a k'ad'awa ta fenΓͺtre (windo) ga wata inuwar mutum tsaye yana kalon mu ta tagar d'akin, can kuma ta inuwar ta gusa tana ta yawo tana buga k'ofar ta kasa shigowa ga sayu tafiya anaji, can kuma abin ya koma saman ruhin d'akin wannan karon ba tafiyar mutum d'aya bace mutane diyawa ne can sai wani cikin su ya fad'o ji kake "timm"
Can sai kuma tafiya ta tsaya sai aka koma k'ofar d'akin ana bubuga wa da k'arfi, mai gida na yace bari yace ya duba kafin nayi wani yunk'urin har ya fita a d'akin, daga dakin nace kar ya bud'e ya tambaya tukun nan, "wane ne" shuru babu amsa sai kawai ya juyo yana zama kennan kuma aka koma buga k'ofar wannan k'aron kamar za'a b'ale k'ofar, nace "kar ka koma ita ce fah" "kwantar da hankalin babu inda zani" kusan minti goma sai muka ji shuru, sai kuma ihu Lya'atou k'anwar Soja tana neman agaji "dan Allah ki bud'e min k'ofar zan mutu" mai gida yace "kina ji fah tana neman agaji haka zaki barta azaluma ta kashe ta" "ba ita bace n'a sani k'ar kaje"kafin nayi magana tuni har ya kai k'ofar d'akin, ya d'ebi ruwan da malamin ya bamu, koda ya bud'e k'ofar ya isko ta kwance shame shame, nidai ina daga fenΓͺtre (windo) ina kalon Lya kwanace a galabai ce, sai kuma muakji bud'ewar k'ofa koda muka juya gidan soja ne tare da k'anwar shi tsaye ai sai oga ya zabura kafin yayi wani yunk'urin wannan k'anwar Soja da ke kwance ta banza ta b'ace, nayi ihu kiran shi ya shigo koda yayi taku biyu sai ga wannan mutumin mai hula na jiya ya baiyana gaban shi ya d'aga hanun ya kwad'a mashi mashi har uku, sai ga mai gida na kwance, gaskiya bazan iya barin shi cikin wannan halin ba haka na jashi cikin d'aki yana wani iri da idanun shi kamar mai ciwan farfad'iya fa kunfa a bakin shi, ni kuma shekarun mu dashi bayada wannan ciwo, kuka nake kamar raina zai fita.
Lya'atou k'anwar Soja duk wannan abun gaban ta ya faru safiya nayi tace ina wallahi bazata k'ara kwana a gidan nan ba ta tatara kayan ta, ta shiga don yin wanka sai gashi babu ruwa a cikin gidan sai da ta fito makewaya waje can ta samu ruwa,sai kawai tace mari tayi wanka da ta koma kuma abun yawa zaiyi, dayake batroom d'in babu nisa