x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 2 - MAKOTAN ALJANA

  • 3001 words
  • 6000 words
  • Out of 17284 words

Category: Horror Stories

Views 192

17 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
kifin ya tashi yazo ya d'ora kanshi saman gaz, wutar gaz ta kunan kanta, kashiyar juya kifin ta fito daga cinin ma'ajin ta tana motsa kifin da kanta"


"Ya salam!!!"

"Allah mama Fido saida nayi fitsari a wando vatare da nasan abinda ke faruwa ba, Can naga kifin yana kwashe kanshi cikin kwano da koshiya sai gaz ya kashe kanshi, kwanon yana yawo a sararin samaniya, wutar kitchen ta mutu komai ya tsaya,saiga kwanan ya fito yazo har a falo bisa table, sai ga télé (telenbijin) ta kuna kanta, télécommande (remote na chanza tashoshi wlh bansan lokacin da na fito ba ta fenêtre (taga)sai k'ofar gidan ki"


"Kennan k'ofar gidan ku rufe take?"

"Eh a rufe take"

"To muje mu duba"


Mun tafi tareda mai gida na, lale k'ofar rufe take mun bud'e mun shiga amman komai a mazaunin shi yake hata kitchen komai daidai, saida da aka tab'a gaz anji shi da zafi....

Muka ce mata to ba komai tace ina ira wallahi bazata kwana gidan ita d'aya ba, dole muka ce ta biyomu mu kwanta tare.....



*Washe gari....*








*Comment*
_and_
*Share*




_Domin gyara ko shawara ku tintub'i wannan number +22792494512 na gode_😇😇








*PRINCESSE CE*✍🏼✍🏼👸🏻
24/07/2020 à 12:52 - 👸🏻Princesse👸🏻: 😈😈😈😈😈😈😈😈😈😈




*MAK'OTAN ALJANA*





😈😈😈😈😈😈😈😈😈😈




_TSARAWA DA RUBUTAWA_
*RAHIMA FALALA*
_PRINCESSE_





*Marubuciyar*
*SARAKUWA TA*
*GODIYAR SU CE*
_and now_
*MAK'OTAN ALJANA*






*Ina ganin comment d'inku na gode sosai Allah yabar k'auna*




🇳🇪 *TAURARIN NIGER*🇳🇪
(Tsintsiya mad'aurin d'aya)✍🏼✍🏼



2️⃣0️⃣↪️3️⃣0️⃣



*Washe gari*

Tinda safe Soja ya tadamu daga barci yana bubuga k'ofa taki budewa ko ina take yana zage zage dan bashi hankuri ko kad'an.


Ni na fito nace yayi hankuri ai gata nan wajen mu ta kwana.


"Tana ina?"

Lya ta fito daga cikin gida na duk a tsorace take dan tasan shi ba yada Wasa idan ya hau kad'an yake jira ya maketa.


"Kam uban can miye haka ? Daga gidan iban wa kike da wannan shigar?"

"Yi hankuri zo muje zamu zan sanar da kai abinda ya faru"

Mun shiga gidan su duk na gaya mashi itama ta maimaita mashi abubuwan da suka faru da ita daren jiya.

Mi zaiyi inba dariya ba kamar an aiko shi, "kar ki cemin da wannan shekaru naki kina irin wannan tunanin na yara, gaskiya kin bada ni"


"Wallahi grand frère (yaya) ni ba yarinya bace nasan abinda nake gayama ka ka yarda dani"


"Eh na yarda da ke, wuce ki chanza kaya jikin ki kar kuma nasake gani kina hana mutane barci"

"To grand frère....."

Bai bari ta k'arasawa ba, "ya isa wuce kije".


Soja yana girgiza kai ana cewa Lya ta girma mai irin wannna tinanin, dan shi bai ma yarda da irin wannna sirkulen ba bale wani aljani .....yana kalon mu a matsayin wasu tab'ab'i.
Ni kaina da Bata faru dani ba bazan yarda ba.
Haka muka ci gaba da rayuwa cikin tsoro da fargaba.

*Bayan sati d'aya*

Ousama Soja yayi dare a bakin k'ofa dan har David ya riga shi kwanta wa, idan yana so yayi waya da budurwa shi dake kasar waje haka yake zaman shi k'ofar gida, sabida lokutan mu ba d'aya, to haka ta kasance dashi a ranar, ya fara Waya kenan "masoyiya gani ina kalon sararin samaniya ga taurari nan gwanin kyau Amman basu kaiki kyau ba" Ousama mayaudari ne ga duk macen da shiga hanun shi, to wannan ranar dai abun bai je mashi yanda ya kamata ba.

Suna cikin waya sai tana tsinkewa réseau (network)na yankewa.
"Allô allô....(Hello hello) sai kiran ya yanke yana k'okarin maida kiran wata irin guguwa ta taso ta turnike shi,yana cikin kare fuskar shi guguwar ta tsaya koda ya bud'e idonanun shi ya hanko wata mace tana tunkaro shi cikin doguwar riga bak'a.

"Wake nan?wake nan?"

Cikin duhun dare bazai iya tantance wacece ba, haka ya cigaba da magana "ki tsaya anan wacece?"


Mace ta tsaya nesa dashi, koda ya ga haka sai yayi anfani da wayar shi ya kuna hitilar ya haska.........







(Wa zai gani?domin sanin yanda zata kaya ku cigaba da bibiya ta)


*Kuyimin uzuri wallahi ciwan kai na wuni dashi, ina barar adou'oinku*🤲🏻🤲🏻🤲🏻🤲🏻









*Comment*
_and_
*Share*






_Domin gyara ko shawara ku tintub'eni a wannan lambar +22792494512😇😇 na gode_









*PRINCESSE CE*👸🏻✍🏼
24/07/2020 à 12:53 - 👸🏻Princesse👸🏻: 😈😈😈😈😈😈😈😈😈😈




*MAK'OTAN ALJANA*





😈😈😈😈😈😈😈😈😈😈




_TSARAWA DA RUBUTAWA_
*RAHIMA FALOLA*
_PRINCESSE_





*Marubuciyar*
*SARAKUWA TA*
*GODIYAR SU CE*
_and now_
*MAK'OTAN ALJANA*






🇳🇪 *TAURARIN NIGER*🇳🇪
(Tsintsiya mad'aurin d'aya)✍🏼✍🏼



3️⃣0️⃣↪️4️⃣0️⃣



Koda ya haska baiga kowa ba kawai sai yace barci yake ji,ya kamata yaje ya huta,ya shigo gida kenan baikai ga kawowa k'ofar gidan shi ba ya hangi macen d'azu tana kisanto shi, "ya akayi tazo har nan?" Cikin zuciya yake magana, wannan karon baiyi magana ba daya aza k'afa d'aya itama ta aza ai sai ya ari na kare sai gudu sai cikin gidan shi ya rufe k'ofa da gudu sai cikin dakin ya rufe duk ya jik'e da zufa ga tsoro duk ya mamaye shi, yana sauke lumfashi can ya juya kalonshi ga fenêtre (taga) halau ita ce bakin taga ba shi sai salon, ya iske Lya na karatu.

*Grand frère (yaya) lafiya ?"

"Ina lafiya,wata mata can waje cikin doguwar riga bak'a"


"Bari mu gani"

"Kar kisaki ki fita kindaiji abinda na gatamiki"

"Toh"

Can sia ya sake kai duban shi ga taga baiga komai ba, sai ya sauke wani gwauran lunfashi suka ci gaba da hira sama sama.
Can sai suka ji cikin kitchen kwandon kashiyai ya fad'i duk sun zube, "kina jin abin nake ji kuwa?"

Lya ido duk sun cika da hawaye tace "yaya gaji ko sun fara wayo Allah !!!"
Sai ga wutar salon(falo) ta d'auke yayi yayi ta kunu taki kunnuwa, can kuma kitchen abubuwan sai k'aruwa suke, banci koshiyai yanzu ga assiette (tagaran)na cin abin ci ake fasawa, abu yaki k'arewa,can dai ya samu k'arfin gwiwa yaje kitchen koda yakai hanun shi zai tab'a k'ofar sai komai ya tsaya tchak, ya bud'e k'ofar ya shiga babu alamu wani abu ya faru a kitchen d'in, a lokacin ne ya gane eh lale akwai abinda ke faruwa a gidan nan, yakai hanun a kashe wutar kitchen ta kashe kanta ya jante hanun ta kuna kuma m, ai ba shiri ya arta da gudu kafin ya kai kofar kitchen d'in ta rufe kanta yayi yayi taki bud'ewa, daga bayan shi yaji motsin kwano koda ya juya sai tukane da kwanoni da cup suke fad'owa suna fashewa, sai ya fara ihuuuuuuuuu a bashi agaji kamar wani karamin yaro, rufe fuska yayi yana rufewa kamai ya tsaya, ya bude idon shi, k'ofar kitchen ta bude kanta,ya fito yaji kukan mage (chat 🐈) bayan shi koda ya juya wannan matar doguwa mai riga bak'a, da gudu sai dakin barcin shi tareda k'anwar shi.

Lya sai kuka take, yace" ui shuru k'anwa ta zan kare ki babu abinda zai cutar da ke".
Bindiga ya d'auka ya haka ta yana jiran ko ta kwana.

Suna nan lab'e cikin dan lungu yana ta kalon kowane lungu na d'akin yaga ta ina abin zai b'ulo, can idon shi ya kai wani hoton mahaifin su, yaga hawaye na zuba a idon mahaifin nasu amma a cikin hoton dake bangon dakin, yace wa Lya ta diba,koda itama ta juyo taga mahaifin su na kuka harda share hawaye sannan ya d'ago masu hanu🙋🏽‍♂️ hiii sai kuma yayi dariya ya kashe ido daya😉, ai da gudu dan sun tsorata ainun har basu son zama a gidan sai suka d'unguma zasu fira amma su kayi su kayi k'ofar taki bud'ewa yasa clé amman ta kiya, can suna nan tsaye suke jin tafiya mutu na tukaro su daga cikin d'aki, duk sun firfito da idanuwa waje😳😳 suna juyowa mi zasu gani ☠️kwarangwal na mutum yana tunkaro su Lya koda taga wanan squelette sai suma tayi, shi kuma yana ta harbin ta amma a banza harbin iska ne nake har saida alburshi (cartouche) ya k'are,koda kwarangwal ta kawo daidai samman kansu, soja an saduda rufe ido yayi yana jiran abinda zai faru dashi.....
Can sai yajin ana buga k'ofar d'akin kamar za'a b'alata, David ne koda ya bud'e "mi ke damun ka ne cikin gida nan bazaku barci na huta ba?"
Soja ya bud'e baki....amman ya kasa magana.

"Bakada harshene komiye kayi magana mana"

Sai ga soja a some yabi sahun k'anwar shi......





(To na gode da adou'oinku naji sauki Alhamdulillah, mu had'u gobe insha Allah a GODIYAR SU CE🌺)






*Domin gyara ko shawara ku tintub'eni a wannan lambar+22792494512 na gode*😇😇






*PRINCESSE CE*👸🏻✍🏼
24/07/2020 à 12:53 - 👸🏻Princesse👸🏻: 😈😈😈😈😈😈😈😈😈😈




*MAK'OTAN ALJANA*





😈😈😈😈😈😈😈😈😈😈




_TSARAWA DA RUBUTAWA_
*RAHIMA FALOLA*
_PRINCESSE_





*Marubuciyar*
*SARAKUWA TA*
*GODIYAR SU CE*
_and now_
*MAK'OTAN ALJANA*






🇳🇪 *TAURARIN NIGER*🇳🇪
(Tsintsiya mad'aurin d'aya)✍🏼✍🏼



4️⃣0️⃣↪️4️⃣5️⃣



Bayan duk wannnan abubuwan da suka faru da Soja tare da k'anwar shi Lya'atou, harbin bindiga ya tada mu muka d'unguma sai k'ofar d'akin su, ni da Naïma muna tsaye kansu, soja ya fara farkawa yale tambayar "mike faruwa ne?"

Nace "kai zaka gaya mana dan a haka muka isko ka kaida Lya"

Soja ya d'aga kai "ohhh daren jiya" ya fara kale kale kamar yana neman wani abu.

Naïma tace "mi ya faru daren jiya ne?"

Nan dai mutunan ku ya fara ratatowa duk abubuwan da suka faru daren jiya, muna so muyi dariya amma ba halin yi.

Naïma tace et"abun mamaki yanzu ka yarda da abinda k'anwar kantake gayama ko?"


Soja yace "eh na yarda gaskiya, tana ina ma ban ganta ba?"


Nace mashi "kwantar da hankalin ka tana dakin kwance"

Wannan karon mu duka mun yarda akan wannan gidan akwai abinda ke faru cikin shi bale gashi bamuda nisa da cimetière (mak'abarta).

Muna cikin rautaunawa nace "yzt kamata muje muga mai gidan domin sanar da shi abinda ke faruwa kar wani abu ya faru yace ba'a sanar da shi ba, sabida tin zuwan wannan mak'ociyar bamu samu salama ba amman da can lafiya muke"


Soja yace "wace mak'ociya kennan?"


Naïma tace "kudai dan irin maganar da zaku ringa fad'i (les murs on des oreilles, dan katanku suna da kunnuwa👂🏼)"

"Badan naga mutuwa ta da idanu na a daren jiya ba wallahi bazan gazgata abinda kike fad'a ba, to mizai hana muje mu same shi domin sanar dashi" cewar soja.


Muka d'unguma zuwa d'akin David mun isko yana shirin fita wajan sana'ar tashi ta sa ido k'ofar gida, yace "Allah yasa kud'in haya ne kuka zomin dashi, kai soja daren jiya kayi Harbin katangu na yanzu kuma mi zaka harba ko ni?"


Naïma tace "a'a munzo ne mu maku magana"

"Magana akan mi kennan?"


Soja "mu Shiga daga ciki dan bai kamata muyi maganar a waje ba"


Mun shiga daga ciki d'aya bayan d'aya kowannen mu ya fad'in abinda ya faru dashi.


David "to duk naji abubuwan da kuka fad'a yanzu kuna nufin ita Fouraiha Aljana ce?"


Nace "ko alama babu wanda ya furta hakan, saidai akwai alamar tambaya a cikin tin bayan zuwan ta ba abubuwa ke faruwa kennan kawai kuma kuyi tunani da hankalin ku"


David "duk da ban tab'a samun korafi daga gareku ba shekaru un kuna zaune lafiya kuma ina sa ran ya zama k'orafi k'arshe"

Naïma tace"kuyi duba da idon basira"


David "kuje kawai zuwa dare k'arfe takwass akwai had'uwa annan gida na kuma halarta kowa ya zama wajibi dan asan abin yi"


Kowa yayi na'am da wannan maganar don shi mai ba kowa hakin shi ne indai wajen magana ne to ko fito ka kare kanka. Kowa ya watse ana jira dare yayi, (ni kuma nace da kunsan abinda ke jiran ku a daren da bakuyi zumud'in yazo ba).


Wajajen uku da rabi na marece David na k'ofar gida,aka sauke Fouraiha a mota nan ya tsayar da ita sun gaisa take tambayar shi ko lafiya, yace "idan na gaya miki to kinsan cewa ba lafiya"

"Go ka isko ni gida zuwa hud'u et sai muyi magana"

"To sai nazo"
David yana d'aya daga cikin mutanen da idan suka samu labari to sai sun kaishi dan bai iya bakin shi ba.


Hudu dadai yana k'ofar gidan Fouraiha.
"Toc toc toc...."


Shigo a bude take aka amsa mashi.
Bayan ya shigo daga can cikin kitchen ta ke ce mashi ya nemi wuri ya zauna gata nan, nan nima na k'arewa d'akin kolo daidai gwargwado tanada tsafta ga anyi décoré (décoration) d'akin duk ja ne da bakin ya bada kala sosai.

Sai gata ta fito suka k'ara gaisawa ta aje mashi tiren abun gaban shi, abinka ga tuzuru rabin da ya ci abinci irin haka har ya manta, nan kuma ta juya ta kawo mashi lemo da dai kayan tab'awa, tace nansan la da giya Bari na kawo maka tsoho yaji kaya nanfa ya et fara fitar da hakora waje, ta zuba mashi abinci shima itama ta zuba suna ci suna fira sama sama can tace "bari na kuna maka télé (telenbijin) lokacin kwalo yayi"

Can saida ya saki jiki dan har ya manta abinda ya kawo shi, sannan tace "tsoho mafanar miye zamuyi?"

"Kin tunamin dan har na manta wallahi, to wad'ancan mak'otan naki ne suke k'orafi wai ana basu tsoro ana hanasu barci tin bayan zuwan ki gidan nan ko kema ana baki tsoron ?"


"Tsoro kuma ni a'a, kamar miye kennan ?"et
Nandai ya bud'e baki ya sanarda ita ce abubuwan da muka sanar dashi.

Tace "to Kai mi kake gani yace ai matsala ce kawai k'arfe takwass a zauna a magan ce matsalar"

Sanye take cikin wata yololuwar riga, ta mik'e tace "Allah ya kaimu dare lafiya, amma nidai babu wata matsala dana ke fama da ita sai ta tsagewar gini d'aki na, ko zaka duba domin samo mai gyara?"


Ya mik'e ya bita zuwa dak'in ta ta nuna mashi yana cikin dubawa koda yake juyowa ya isko ta sitir ta tub'e, ya kasa magana, ta bashi zuwa gado, yana kiciniyar kwatar kanshi tace kaleni ya d'ago ya kaleta sai wani haske ya fito daga idon ta zuwa nashi tace ya bud'e baki ya bud'e wani maciji ya fita daga bakin ta zuwa nashi tace ya had'e, koda ya had'e sai barci, kamar wani karamin yaro..........






(To nima bari na ware kafin David ya farka muka yanda zata kaya)






*(Ina bara adou'oinku🙏🏼🤲🏻)*


_domin gyara ko shawara ku tintub'eni a wannan lambar +22792494512 na gode😇😇_









*PRINCESSE CE*👸🏻✍🏼
24/07/2020 à 12:54 - 👸🏻Princesse👸🏻: 😈😈😈😈😈😈😈😈😈😈




*MAK'OTAN ALJANA*





😈😈😈😈😈😈😈😈😈😈




_TSARAWA DA RUBUTAWA_
*RAHIMA FALOLA*
_PRINCESSE_





*Marubuciyar*
*SARAKUWA TA*
*GODIYAR SU CE*
_and now_
*MAK'OTAN ALJANA*






🇳🇪 *TAURARIN NIGER WRITER'S ASSOCIATION*🇳🇪
(Tsintsiya mad'aurin d'aya)✍🏼✍🏼



4️⃣5️⃣↪️5️⃣0️⃣





Bayan ya had'iye maciji nan ya b'ingire sai barci.
Fouraiha ta kewaye gadon da David yake kwance da wani farin abu, tayi zaune ta lankwashe k'ahuwan sannan ta zura hanun ta karkashin gadon ta fito da wani gwangwani ja ayi mashi ❌❌ a jikin gwangwani,ta fitar da wata kwalba katuwa daga ciki tare da wani litafi, ta fara karanta wani tare wanda ko ni ban gane abinda take nufi ba, can sai na hagin kurwa shi David ta fito, Fouraiha tace "zo, zo gareni ka zama nawa ni d'aya" sannan ta saka kurwar a cikin wannan kwalbar t rufe ruf ta maida komai mahalin shi sannan ta tashe da David.

"Ina nake nan?"

"Gidan mu ne, mike maka ciwo yanzu?"

"Kaina ke ciwo"

"Zai dena, sannan duk abinda nace shi zakayi babu musu"

"To masoyiya ta"

(Ikon Allah🤔😅😂🤣 🤐)


"To je la shirya ma réunion (taton mu na dare"

"To ma chérie"

Ya fito daga cikin d'akin ta tuna dazu bai gama cin abincin nan nashi ba, "to ina kuma sauran abincin nan yake?"

"Bakai babu tambaya sai abinda nace zaka yi ok?"

"To masoyiya na gane"

David ya koma kamar karamin yaron duk sai abinda tace yake yi kama rakumi da akala.(na tausaya maka David).




Bayan lokaci yayi duk mun had'u a gidan David cikin falon, "barkan ku da zuwa duk na gaisheku, mun had'u a wannan wuri ne domin magance wata 'yar matsalar da ta adabin wasu daga cikin mu, domin fida zargi a zukatan ku, kamin mukai ga farawa inason na gabatar maku da masoyiya ta, sannan daga yau itace patronne (shugaban ku yanzu ma'ana ita zata ringa kula da gidan nan).


Duk munyi murna ganin shima d'an tsoho ya samu wata.


Wa zamu gani ta fito daga cikin d'akin David wai Fouraiha!!!😳😳😳😳
Ta fito tana rangwad'a tana karkad'a kugu da wasu tsinanin kaya a jikin ta.
Kowa yayi mutuwar zaune babu mai magana.

Fouraiha tace " nasan duk kunyi mamaki da ganinan a nan to daga yau nice mai gidan nan, kuna so ko baku so kuma zan buga sandar iko na babu wanda ya isa ya ja dani, dan haka ku b'ace min da gani banason ganin ku"

Naïma tace"mi?
End Ads