x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 4 - ABOKAN GABA

  • 9001 words
  • 11905 words
  • Out of 11905 words

Category: Adventure Stories

Views 46

09 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
‘yan lokuta ta
xauki numfashin Boka Sharbanga ta tafka masa
wani nagartaccen sara a dokin wuya ta tsinke masa
kai gangar jikin ta zube a wurin kan ya faxa cikin
teku.
Ta juya ta dubi Bokanya Namsu cikin
kwantar da murya tace mata.
“Ni ce ‘yarki Sultum”.
Bokanya Namsu ta rungumeta cike da farin
ciki da jin daxi a yau burinta ya cika ‘yarta ta
zamto jaruma mai ji da jarumtaka ga tsafi daga
gada a gareta, wannan ranace da take fatan
zuwanta take xaukin zuwanta, ga shi ta ganta suka
juma a rungume da juna daga bisani suka rabu a
hankali Bokanya Namsu ta ce mata “Ya aka yi
kika san ina nan?” Sultum ta dubeta da murmushi
sannan tace mata.
“Wani madubi na tsafi na samo a hannun
wani boka da muka yi yaqi da shi a duk lokacin da
na buqaci zuwa wurin mutum ina ambatar sunan
shi sai na duba jikin madubin zanga inda yake, to
da na so dawowa gida wurinki shi ne na ambaci

sunanki sai na ganoki kuna fafatawa da boka
sharbanga shi ne na yi gaggawar tahowa gareki,
domin kawo miki xauki domin nasan halinsa
gwani ne wajen iya yaudara”
Ta gama faxa mata tana mai fitowa da
madubin ta nunawa Bokanya Namsu ta amshi
madubin tana nazarinsa lokaci xaya ta yi
murmushi “Ina fatan baki halaka Bokan da kika
amso wannan madubin ba?” Sultum ta dubi
mahaifiyarta cike da mamaki sannan ta bata amsa
da cewar “Ina mai fargabar ce miki Bokan ba zai
tava halaka ba, har sai wa’adinsa ya yi domin na
sameshi tsayayen jarumi mai jarumtaka wayeyye a
fannin sihiri na sirri ya karantu ya yi nisa a tsafi da
sanin alqaluman tsafi, ya mallaka min shi domin
ya yaba da jarumtakata”.
Bokanya Namsu ta yi ajiyar zuciya lokaci
xaya ta yi murmushi. Sultum ta dube shi cike da
mamaki ta qara cewa da ita “Ko kin san shi ne?”
Bokanya Namsu ta dubeta ta sake yin
murmushi kafin ta bata amsa da cewar “Shi ne
mahaifinki ba domin yasan ke ‘yarsa bace da ba
zai tava mallaka miki wannan madubin tsafin ba,
ya yi hakane kuma domin duk inda kike ya
kasance yana kallonki irin wannan madubin guda

uku ya haxa ya xauki biyu ya mallaka min xaya
kafin mu rabu da shi” Ta gama faxa mata hakan
tana mai xauko mata nata madubin Sultan ta saka
hannunta ta amsa ta yi nazarinsa ba shi da
bambanci da nata ta girgiza kanta.
Bokanya Namsu ta dubi wanda ya ke riqe a
hannunta a hankali tace “Ina son sanin inda bawa
Farsu yake” Tana gama rufe bakinta sai bakin
gavar tekun ta bayyana a jikin madubin sannan
hoton aljanin da ya xaukosu ya bayyana shi ma kai
tsaye ya nufi gabashin tekun da su.
Ta mayar da madubin ga ‘yarta kafin tace
mata “Mu nufi bakin gavar tekun ta hanyar
gabas”A hankali suka nufi bakin gavar wajen da
su gimbiya lusa suka nufa.
**
Nahiyar yamma maso kudu ita ce mahaxa
da ta tattara taron baqa fata wanda adadinsu ba zai
qidudugu ba, amman duk bayi ne qasar Margas ta
zamto fitattaciyar qasa da ta ke yankin. Domin ta
zama qasa da mutanen cikinta suka gwanance
wurin sana’ar kamun kifi wato ma sunta ne, sai
kuma saye da siyar da baya hakan yasa qasar ta
zamto mahaxa ta nahiyar yammaci.

Ko wacce safiya jama’ar qasar sukan fito
bakin tekun garin su yi kamun kifi amman banda
ranar juma’a da asabar wannan ranakun ba sa
zuwa kamun kifaye. Sarauniya Zultum itace ke
mulkin qasar, ta hau mulkin qasar kimanin
shekaru uku da suka gabata a lokacin shekarunta
ba su gaza sha takwas ba, a rayuwar sarauniya
Zultum babu abinda yake birgeta tamkar ganin
mutum ya nuna wata bajinta ta ban mamaki,
wannan dalilin ya saka duk shekara a qasar take
saka gasar kamun kifi duk wanda ya kama wanda
ya fi na kowa girma to za a yi masa kyauta mai
qayatarwa talakawan qasarta suna matuqar jin
daxin wannan gasar da sarauniya Zultum ta ke
sawa.
A wannan shekarar gasar ta sauya salo
domin sarauniya Zultum ta fito da kanta ita ma
zata yi kallon gasar savanin sauran lokutan baya
sai dai ta tura wakilai kuma ta yi alqawarin cewar
zata auri duk wanda ya samu nasara a gasar amma
zata faxa masa sharuxan sadakinta wanda ta
tabbatar ba qaramin namiji ne zai samu nasara a
gasar ba har ya aureta. Wannan kalamin nata ya sa
masoyanta suka dunga varkowa daga duniya
mafiya yawansu ‘ya ‘yan sarakai ne sai tsarukansu

‘ya ‘yan attajirai da talakawa domin daman
masoyanta sun daxe suna jiran su ji sharuxan
aurenta.
‘Ya ‘yan sarakuna da attajirai suka yi ta
neman sa’a a wurin bokaye da masu sihiri domin
su samu su shiga cikin tekun ba tare da wata
matsala ba kuma sa’a ta tabbata a garesu. Habaru
ya kasance saurayi matashi mai tsananin
taqadiranci da rashin jin magana a kullum sai
Habaru ya janyowa iyayenshi magana, ba a kawo
qararsa gida wajen iyayenshi a rana ba a kawo
qara sau saba’in ko ma fiye da haka domin duk
wurin da ya je sai an kawo qarashi. Baban Habaru
wani tsohon masunci ne da sana’ar sa bata
magance masa komai game da talaucin da suke
ciki.
Habaru bai wani tsaya ya mayar da hankali
ya koyi sana’ar babanshi ba ga kuma tsufa sosai ya
kama shi. A yayin da shi kuma Habaru kullum
tunaninsa ta yaya zai mallaki dukiya ta wata
hanyar, domin shi dai ya yi duba sosai ya ga cewar
a duk masu sana’ar kamun kifi bai tava ganin
wanda ya yi kuxi da sana’ar ba. A lokacin da
labarin gasar sarauniya ya zo masa sai shima ya ji
cewar ya kamata ya shiga domin ko banza idan ya

samu nasara zai samu damar auren sarauniya
shima ya shiga cikin ma su mulki, ya kasance ana
kaxa masa tambari tare da kirarin.
Sai Habaru xan tsohon masunci, talaka mai
qashin arziqi.
Wannan tunanin da ya yi shi ya ja
hankalinsa ya je ya bayar da sunansa a cikin masu
shiga gasar. A lokacin da labari da labari ya watsu
cewar Habaru ya shiga gasar auren sarauniya sai
jama’a da dama suka riqa yin addu’a Allah yasa ya
mutu a wurin gasar domin sun gaji da irin
taqadirancinsa. Mahaifin Habaru yasan babu wani
abu da xansa zai iya kuma lokaci ya qure balle ya
koya masa dabaru na kamun kifi don haka ya
kirashi domin ya yi masa nasiha. Da Habaru ya
samu mahaifinsa sai ya samu wuri ya zauna ya yi
shiru yana kallonsa mahaifinsa ya dubeshi a
hankali yace masa.
“Abubuwa biyu zan gaya maka” Ya yi
shiru yana kallonsa sannan ya ci gaba da cewar
“Na farko ka saka a ranka cewar nasara Allah shi
ne yake bayarwa ga wanda ya so” Ya kuma yin
shiru karo na biyu yana dubansa kafin ya ci gaba
da magana “Na biyu ka yi addu’a a koda yaushe
domin Allah yana taimakon bawansa” Ya sake

saurarawa kafin ya ci gaba da magana “Waxannan
abubuwan su kaxai zan gaya maka daga su babu
wani abu da zan iya yi maka sai fatan alheri xana”.
Habaru ya yi shiru yana kallon fuskar
mahaifinsa wadda ta tattare domin tsufa da ya
kamashi, wannan shi ne karo na farko da
mahaifinsa ya gaya masa wani abu da zai
amfaneshi a rayuwarsa. Domin abunda Habaru ya
xauka game da mahaifinsa a baya babu abinda zai
iya faxa masa.babu kuma wani abu da zai tsinana
masa sai talauci da ya yi masa qabe-qabe a
rayuwarsa. Habaru ya tashi a kasalance ya koma
xakinsa ya zauna ya yi shiru yana tunanin
abubuwa da dama da suka zo masa kai da kuma
waxanda suka tunkaro rayuwarshi. A zahiri yana
da masaniyar cewar ba shi da wata dabara ko
qwarewa da zata taimaki rayuwarshi har ya kai ga
samun nasara, ba shi da wata mafita kawai dai zai
jarraba sa’arsa a sana’ar da iyayensa suka gada.
Habaru ya tashi a hankali ya je ya yo
alwala ya yi sallah ya xaga hannunsa sama ya
soma roqon Allah akan ya ba shi nasara game da
gasar daya shiga.
A haka ya tafiyar da lokacinsa.

Rana ta xaga bakin teku ya cika maqil da
mutane kowa yana jiran ya ga yadda gasar zata
kasance da kuma ganin wanda zai samu nasarar
zama wanda zai auri sarauniya zultum. Duk
waxanda suka shiga cikin gasar sun gama halarta a
wurin suna juran zuwan sarauniya Zultum domin
soma gudanar da gasae duk wanda ka duba za ka
samu ya shirinsa wasu sun rataya kayan
tsatsubarsu a wuyansu wasu kuma a ciki, wasu a
baki kowa ka kalla akwai irin shirinsa..
Xan Boka Margadasy ya fi kowa qwarin
gwiwar samun nasara tana gareshi domin
mahaifinsa ya ba shi wata sanda da ya riqeta a
hannunsa wanda da zarar lokacin fitowa ya yi idan
ya fito zata rikixa ta zama qatoton kifi da babu
wanda zai kama kamarsa domin babanshi
mashahurin matsafi ne da shahararshi ta kai ko ina.
A haka lokaci ya yi sarauniya zultum ta qaraso
wurin ta samu wuri ta zauna a cikin tanti da aka
tanadar mata, daga wajen da take zaune tana
kallon duk abinda yake faruwa ‘yan takara suka
gabato gabanta suka yi gaisuwa ta girmamawa ta
dunga kallonsu xaya bayan xaya a haka suka
kammala zuwa daga nan aka bada damar shiga
cikin teku domin soma gabatar da gasa.

Makaxa da mawaqa suka soma kaxawa
masu gasar kixa suna kambama gwanayensu da
kalamai da suke qara musu qwarin gwiwa a haka
har suka qarasa zuwa ga bakin teku kowa ya gama
shirinsa sanna aka soma shiha cikin ruwa domin
fara gudanar da gasar. Habaru ya juma a tsaye a
wurin yana addu’a domin neman samun nasara a
wajen ubangiji daga nan ya yi tsalle ya faxa cikin
teku ya nutse ya yi qasan ruwan domin laluben
kifin da zai kamo. A hankali lokacin ya tafi
waxanda suka shiga cikin gasar suka soma fitowa
xan Voka margadasu ne ya fara fitowa daga cikin
tekun janye da wani murgujejejn kifi daya baiwa
kowa mamaki domin a tarihi ba a tava ganin wani
wanda ya kamo tamkarshi ba tun daga lokacin
kowa ya saduda ya yarda cewar lallai shi ne mai
nasara a gasar babu wani da zai iya kamo wanda
ya fi nashi.
Sarauniya zultum tana zaune tana kallon
duk abubuwan da suke tafiya duk wanda ya fito
sai ya fito da kifin da bai yi ko da rabin na shi ba
da zarar ya qyallara idanu ya ga sihirtaccen kifin
da xan Boka Margadasu ya fito da shi sai ya yarda
nashi domin yana da tabbacin ba zai kai labari ba.
Xan Boka ya yi ta qyalqyala musu dariyar

mugunta yana mai alfahari da yiwa kansa kirari
gami da ambaton nasaba a haka kowa ya gama
fitowa ya kasance sauran Habaru can bayan
tsawon wani lokaci sannan Habaru ya fito yana
janye da wani abu da qyar domin matuqar nauyi
da ya yi masa idanuwan kowa ya koma kanshi.
Habaru ya fito daga cikin ruwan yana janye
da wani murgujejen kifi wanda ya ninka na xan
Boka Margadasu sau biyu, domin yana ganin na
shi shima ya tsorata da ganinsa domin tunda yake
a rayuwarshi bai tava tsammanin wani xan Adam
zai iya kamo kifi kamar wannan ba. Jama’a duk
aka bar kallon sihirtaccen kifin da xan boka
Margadusu ya kamo aka koma kallon na Habaru
sarauniya Zultum da kanta ta tashi ta je ta taryo
Habaru da kanta ta yi masa jinjina bisa nasara
daya samu.
Mafarkin da Habaru ya yi ya kusa zama
gaskiya.
Washe gari Habaru ya zo fada cikin kayan
alfarma fadawa suna take masa baya, ya zube
gaban sarauniya ya yi gaisuwa ya sunkuyar da
kansa yana jiran ya ji abinda za a yanke masa a
matsayin sadakin auren sarauniya zultum bayan
wucewar wasu ‘yan lokuta sannan ta nisa gami da

faxin “A yau na tsayar da mijin aurena, sannan
kuma a yau zan yanka masa sadakin aurena ko a
yanzu ya samo ya kawo mun shi za a xaura mana
aure” Ta xan yi shiru kafin ta ci gaba da magana
cikin nutsuwa “Ka yi sani cewar a lokacin da
mahaifinmu ya haifemu mun kasance ‘yan biyu
mahaifiyarmu ta haifa. Duka mu biyun kamarmu
xata babu wani bambanci wata rana sai wani aljani
ya sace xaya daga cikinmu domin tsabar son rai
nasa wannan abun ya matuqar qonawa
mahaifinmu rai wanda sanadin wannan baqin cikin
shi ya zama ajalinsa, ita kuma mahaifiyata tun
lokacin take fama da baqin cikin abun kullum tana
cikin kuka. Saboda haka wannan ‘yar uwar tawa
nake son ka nemo mun wacce a yanzu haka tana
cikin wannan duniyar tamu wannan shi ne sadakin
aurena”
Ta xan yi shiru sannan ta qara da cewar.
“Kamarmu xaya sunanta Gimbiya Lusa”.
Habaru ya yi shiru yana jinjina lamarin a
ranshi, a rayuwarshi wannan shi ne karo na farko
da zai aikata aikin wahala ya sunkuya yace mata.
“Insha Allahu zan nemo miki ita” Fadawa
suka yi kabbara domin qarfafa masa gwiwa.

Washe gari Habaru ya gama shirinsa ya fita
mahaifinshi ya rakasa har bakin qofar gari ya
xauko wata takobi ya ba shi suka yi sallama da
juna.
**
Su gimbiya Lusa suka sauka a daidai gavar
teku suka yi shiru suna duban-duba suna tunanin
abinda ya kamata su yi, suka soma shawarwarin
hanyar da ya kamata su bi. Suna cikin shawara ne
bawa Farsy ya hango mace a kwance a gefen
gavar tekun ga alama ruwa ne ya ciyota da sauri
ya nufi wurin ya qarasa ya janyota ya fito da ita ya
dubeta a nutse ya ganta baqar fata kyakkyawa
wacce idanuwanshi ba su tava ganin mai kyawunta
ba ya zuba mata idanu yana kallonta cike da
mamakin irin kyawu da ya gani tana da shi, a haka
su Gimbiya Lusa suka qaraso suka sameshi.
Gimbiya lusa ta tsuguna a gabanta ta saka
hannunta ta danna qirjinta take ta soma aman
ruwan data sha, zuwa wani xan lokaci ta farfaxo ta
zuba musu idanu tana kallonsu har zuwa wasu
‘yan sakani kafin tace mata “Na gode da taimakon
da kika mun”.
Bawa farsu ya yi murmushi a hankali yace
mata “Ba komai dolen mu ai mu taimaki

kyakkyawa kamarki” Ya gama maganar yana mai
wasa da sarqa tsafin dake hannunsa.
Ta kalleta kafin ta sake cewa “Wannan
sarqa tana da kyau, ta matarka ce?” Ya dubeta ya
dubi sarqa ya bata amsa da cewar. “Ba ta matata
bace, ni bani da mata” Ta yi murmushi tare da
qara kashe murya tace masa.
“Na ga tana da kyau za a iya bani na ganta?”
Bawa Farsu ya kalleta ya kalli sarqa ya xanyi shiru
na wasu ‘yan sakani tamkar ba zai bata ba daga
bisani ya miqa mata ta miqa hannu zata amsa sai
Gimbiya Lusa ta yi sauri riqe hannunsa su duka
suka mayar da kallonsu gareta a hankali tace da
bawa Farsu “Kar ka yarda da ita mayaudariya ce”.
Maganar ta tsaya wa bawa faru a rai ya
juya ya kalli fuskar budurwa kyawun fuskarta ya
mamaye masa rai ya juya ya dubi Gimbiya lusa
yace mata.
“Ba mayaudariya bace sai dai kece
mayaudariya” Yana gama gaya mata ya juya ya
miqa mata sarqa a hankali yace mata “Ga ta ki
gani ki dawo mun da kayata” Tana saka hannu ta
amsa ta dubeta a tsanake sannan ta dubi bawa
farsu ta qyalqyale da dariya ya dubeta a tsorace
dariyar ta janyo hankalinsu. Suka zuba mata idanu

suna kallonsu ga mamakinsu sai suka ga ta miqe ta
yi wata girgiza take kamaninta suka sauya zuwa na
sarauniyar aljanun cikin ruwa ta xaga sarqa akan
idanunsu kafin tace musu.
“Ta tafi kuma ta dawo, don haka yanzu zan
halakar da ruhinku gaba xayanku” Tana gama
maganar bawa Farsu ya zare takobinsa da sauri ya
kai mata sara, tayi tsalle gefe xaya saran ya wuce
ta yi tsalle akan iska ta koma can gefe nesa kaxan
da su, ta dube su ta yi nuni da hannunta zuwa ga
wani wuri nan da nan wuta ta kama itatuwan da
suke dajin ta nufi wurin da suke da zumar halakar
da ruhinsu.
Sarauniyar aljanun cikin ruwa ta qyalqyale
da dariya.
Bawa farsu ya dubi sihirtaciyar wutar data
yo kansu tana cinye duk abinda ta samu, sai ya
juya ya dubi su Gimbiya Lusa yace musu.
“Duk wanda zai iya yakan iya biyoni”
Yana gama maganar ya nufi wurin da wutar take
tahowa a guje takobinsa a zare. Gimbiya Lusa ta
bishi da kallo a hankali ta juya ta dubi sadauki
Ansar tace masa.
“Wannan baqar fatar ba qaramun hatsabibi
bane, ban tava ganin mutum kamarshi a”>

Wutar ta ci gaba da nufosu da zumar
halakar da su…
Alhamdulillahi masha Allah.
Sauran labarin zai zo muku a cikin littafin
ABOKAN GABA 3


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels
End Ads